Showing 75001 words to 78000 words out of 228147 words

Chapter 26 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10380

fatan Allah ya sa ba abinda yake ganni bane wato Yarima tsugune gaban UMMU zigidir baki daya jikinsa na rawa harta da hannayensa da dukan gabai nasa da irin kalaman da yake fadi yana talabota da hannayensa yana fadin"
















Barka da safiya
[31/03 Γ  21:39] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



26


"Innalilahi wa'ina ilaihi raj-une! Wacece wannan? Daga ina ta fito? Na halaka kaina na halaka yar mutane, wayo Allahna na kashe rayuwar yar mutane na kashe kaina, wayo na shiga ukuna yau na tafka kuskure mafi muni a rayuwana, wayo ni ba mazinaci bane zanen k'addarata ne, wayo matata ce ta janyo min ta hana min kanta bayan ina da ita, na shiga uku na lalace."

Hannunsa na dama ya saka ya tare hanyar da Ummulkhair ke son lekowa sakamakon kalamansa da suke daukaka girman fitowar furucinsa

Wani ihun ta saka itama hakan ya saka shi daukan NAJEEBA dauka irin na jarirai ya fito

Hannunta ya damka kafin da idannuwansa ya yiwa ZAHRA nuni da ta biyo bayansa

Gaba daya bari jikinta yake
Dukan gabanta kamar ba nata ba haka ta ringa hada hanya ita tama rasa me take ciki har suka idasa shigowa falonta ya shinfide NAJEEBA nan kasa saman cafet sanan ya yi masu nuni da su zauna

Juyawa ya yi da sauri ya koma, lokaci daya mazan dogaran sun fara farga har an fara nufi wajen sannan tuni an kaiwa sarki kabarin ana jin murya na kuka sama sama kamar ta yarima da kuma wata mace hakan ua saka shi fitowa da saurin gaske bayan ya warto sharbebiyar wukarsa ta yaki mai sunna Babarbara

Yana komawa ya saka hannunsa ya karbeta a hannunsa, kafin yake rufa mata mayafin da ya shigo da shi a wajen sirrinta

Haske ya kunna hakan ya saka Yarima saurin wartar wandonsa jikinsa na bari ya shiga kokarin sakawa

Wajen wuyanta ya shiga dora hannunsa, lokaci daya yana waigen bayan da yake sama ne suke yana hangen yanda gidan ke ta kai kawon dogarai wasu na tambayar daga inda ihun yake sai kokarin karasowa suke

Matan sarki ne suka fito a firfirgice du sunna kokarin yin inda ake fadin ihu na fitowa

Giftawarsa da dogarai majiya karfi sai kirarin yaki suke a bayansa ya saka jikin matan nasa kwasar rawa

Da sauri suka bi bayansa kowace da irin abinda take sakawa a kasan zuciyarta, fatan Gimbiya ta tarar da amarya ce ta mace!

Dakatawa ya yi duba da falon amaryarsa ne za'a shiga ya tsayar da baki daya dogaran waje daya sannan ya shige da saurin tsiya

Saurin kawar da kansa ya yi daga kansu gannin du jikinsu da shigar baci ne sannan sun zagaye yar uwarsu

Wajen da yake jin muryar yarima baban dansa ya nufa da sauri babarbararsa a hannunsa

Yana hankada kofar wajen ya shige da sauri yana tambayar abinda ke faruwa da yaren buzanci

Abubuwan da yarima ke kara maimaitawa da irin yanda SHAHEED ya gyara mata kwonciya tamkar mataciya ya saka sarki zaro idannuwansa baki daya jikinsa ya kama bari

Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Da wani irin bacin rai ya nufe shi da wukar nan yana dagawa a fili ya furta" tirr da kai FARID, gwara na kasheka da hannuna na huta

Da sauri ya yi wata irin dira ya tari gaban mai martaba kafin yake saka hannunsa ya tare wukar nan da hannu daya ya janyeta daga hannunsa ya riketa taf a hannun nasa

Ihun kukan da ta saka tana dora hannayenta duka biyu a saman kanta ne ya ankarar da fitowarta hakama mahaifiyarsa gaba daya jikinta ya dauki wani irin bari itama ta dora hannayenta saman kanta tana jin abinda ke shirin riskarta duka a zuwa bakaken halitar nan! A yau ta ga balakin da ko mutuwar ubanta bai girgiza mata kwakwaluwa irinsa ba
Tashin hankali ya risketa na mamaki kafin ta gama fahimtar wani ko baci ya ki daukanta ga wani ya sameta yau itace tsaye a gaban tarin abin kunyar nan
Sai kawai ta dafe kirjinta ta silale kasa

Muryarsa a dake ya furta" idan har magana ta daukaka ta fita tsakar gida ba abinda zan iya yi maku baki daya! Ku sanni sirrin masu mulki, da manyan malamai ya fi tarwatsa al'umah, ya fi lalata tarbiya! Ku sani idan har waje ta dauka haka ya faru da yariman garin agadez to kuwa matasan garin agadez zasu dauka su mayar da hakan abin yi! Ana iya tankwasa rigima idan bata yi yawa ba!

Yana gama fada karasawa ya yi ya sungumeta ya fito da ita

Dakin Zahrau ya nufa da ita kafin ya kuma fitowa ya sungumi NAJEEBA itama ya nufi dakin da ita sannan ya yiwa sauran alamun su biyo shi

Saman bed du ya jera su kafin ya yi tsaye ya kura masu ido
Ta ina zai fara? Me zai ce? Tabas sun shiga rudani mai girman gaske, shi kansa ji yake kamar zuciyarsa zata samu matsala a irin lamari

An dauki kamar mintunna ashirin sai ga bugawar kofar, du a zaune suke sunna ta kuka su biyun, Ummu ta dawo hayacinta aman bata iya komai waje daya kawai take kallo sai hawayen dake bin gefen kumatunta
Shi kuwa yana tsaye ya kura ma waje daya ido

Karasawa ya yi ya bude kofar

Likita ce ta shigo Sarki kuwa na tsaye daga baki baki bai shiga ba domin ya san ko a yanzu basu saka kaya ba, irin yanda yake zufa sai abin ya baka tausayi ya koma ya jingina da kofar yana kallon yanda iyalansa suka rikice

NAJEEBA dake sume ta fara baiwa taimakon gagawa
Ai kuwa ta farka a rikice tana ta waige waige, sai ta kwala ihu mai karfin gaske ta fashe da matsanancin kukan da ya saka yan uwanta suma fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya da zafin gaske sunna ririke junna

Karasowa ya yi ya saka hannunsa ya bambare hannun Zahrau daga jikin Najeeba kafin ya kuma saka hannunsa ya k'ara cicib'arta.

Bai zame ko ina da ita ba sai cikin bayi direct ya idasa wajen bath da ita.

Zaunar da ita yayi sai ihun take tana kuka kamar ranta zai fita ga gazar gazar din gashin idannuwan nan nata sai kara far suke.

Bata tsamaci jin ruwa ba sai saukarsa ta ji a kanta hakan ya saka gashin kanta gaba dayansa ya yi lingib a bayanta da wani karfi ta so zabura ta tashi sai dai ya saka hannunsa ya maida ita cikin ruwa ya zaunar da ita sannan ya riketa tam a ciki.

Tun tana gunjin kukan har ya zama ta ringa rage sautinsa tana yi sannu sannu har ya dawo na zuci ne take yi sai hucin da take furzarwa.

A hankali ta langab'e a saman damtsen hannunsa shima ruwan ya jik'a masa jalabiyar jikinsa
cikin wata shak'ak'iyar murya dake cen ciki ta furta" Ya halakamu, ya wulak'antamu, ya goga mana penti, me mukai masa? Ya ketawa yar uwata hadi."

Gani yake ta d'aukaka firgicinta, gani yake ta zurfafa firgicinta bayan ba haka ya dace ta nuna ba duba da ita din aikinta kennan, harkar maza ya zame mata abinda ta fi k'warewa a kai, akan me zata ringa irin wannan abu? Sai yake tunanin tana pretending ne, sai yake gannin kamar so take ta raina masa hankali
Jin rawaninsa na son jik'ewa ya saka ya ringa janye jikinsa a nata
Idannuwansa ya sauke a kanta da niyyar yi mata magana sai dai da kansa ya kawar da kansa da wani irin sauri yana mai rintse idannuwansa domin ruwan nan da ya jik'a mata jiki da shi baki daya ya lafe mata da rigar nan mai santsi a jikinta a yanzu ne hallitar k'irjinta ta wani irin bayanuwar da ta saka shi ji gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa.

*(mai damagaram yana ruwa, kusa da kada inji breaker🀣)*

Mik'ewa yayi da sauri ya juya ya fita a bayin.

Yana fitowa ya tarar da su sun saka suturun da suka rufe masu suturarsu, sannan sunna zazaune gefen kanta likitar kuwa ta bata maganin da zata sha dan rage rad'ad'in dake damunta na bak'on lamarin daya ziyarceta bayanshi bata samu wani mugun raunin da zai saka a kaita asibiti ko a mata d'inki ba, tana shiga ruwan zafi komai zai dawo normal sai dai abinda aka yaye din da ba za'a iya maido shi ba.

Tawul ya d'auko ya mik'awa Ummu ya nuna mata bayi hakan ya ganar da ita abinda yake nufi.

Wasu kayan ta d'aukar mata ta nufi bayin da su.

Kamata tayi ta fitar da ita daga cikin ruwan dan har lokacin tana ta zubar da hawaye wani irin ciwo take ji a zuciyarta domin a rayuwarta idan akoy abinda ke tayar mata da hankali, ya sakata a firgici to fa irin abinnan ne.

Kayan ta saka jikinta a mace suka fito tare.

K'arasawa tayi ita ma ta zauna ta d'ora kanta gefen wuyan Ummu
Muryarta a sanyaye ta ce" Ummu, kiyi magana mana, dan Allah ki ce wani abu mana."

Suma hawayen suka ringa sharewa shi kuwa yana kallonsu.

Sun d'auki kamar minti goma a haka kafin a hankali ta bud'a bakinta, hawaye ne wasu ke korar wasu cikin disashiyar muryarta ta furta" Dama me kuke jira da rayuwata? Kun manta wacece mahaifiyata? Yanzu haka idan kuka je tudun jamus layi na biyu babbar k'ofa mai ruwan blue gidanta ne, zaune take tana amsar kud'in wannan."

"Ki yi min shiru!" Ya bud'a bakinsa tun d'azun ya fad'a da wata murya ta tsawa wace ta saka du suka rintse idannuwansu suka sada kawunansu

Muryarsa ya kuma bud'awa yana cijewa yace" ku tashi baki d'ayanku mu fita!"

Da sauri Najeeba ta d'ago tana kallonsa, sai dai ba damar yin magana domin har ya juya ya fara fita.

Zahrau kam bata da katab'us, baki d'aya duniyar ce ta yi mata zafi ta rasa wani tunani zata yi da irin wannan lamari, aman tsawatarwar daya yiwa ummu ta sakata jin dama dama domin idan har haka zata ringa fad'i idan bakinta ya bud'e tana iya idasa halaka masu tunani su yi ta kuka.

Kamata suka yi ta mik'e da k'yar tana rintse idannuwanta kafin ta sauko.

Kamata suka yi a hankali tana tafiya suka fito domin basu san inda zai kaisu ba, su kuwa basu isa su k'i fitowar ba.

Irin yanda suka ga duk mutane ne a zazaune kama daga Sarkin Agadez, na damagaram, Gimbiyoyin, yarima da matarsa sai du suka ji hankalinsu ya k'ara tashi.

A hankali suka k'arasa da niyyar zaunar da ita a kasa, sarkin garin Agadez dake kallonsu ne kamar zai fashe da kuka shi kam ko rawanin babu a kansa yau an yi abinda ya cujewa buzu nad'i ya nuna masu doguwar kujerar dake ajiye."

Nufar wajen suka yi suka zaunar da ita kafin su zauna kusa da ita sosai a jikinta.

Najeeba irin kallon da take bin yarima da mahaifiyarsa da shi irin kallon nan ne wanda zaka ji kamar ka kashe mutun.

Yayi d'agowar kansa ya fi a k'irga sai zai bud'i baki sai ya kasa hakan ya saka Gimbiya saurin zamowa kasa ta had'e hannayenta tana kallonsa muryarta na rawa ta furta" dan girman Allah a rufa mana asiri, kar ku manta yarima shine mai jiran gado, sirrinsa ya fita tamkar sirrin baki d'aya gidan nan ne zai fita, Allah ya huci zuciyarka a rufawa yarima asiri a gafarta masa."

Tayi gaggawar juyar da kanta wajen SHAHEED ta d'an k'ara rarafawa hannayenta a had'e ta ci gaba da fadin" Ku rufa mana asiri, wannan sirri namu ne baki d'aya, dan girman Allah ku rufa mana asiri."

Du wani motsin kowa yana hakimce ne yana bi da kallo, bai furta ko A ba.

Kansa dake kasa ya dago, irin kukan da yake sai ya baiwa mutun tausayi.

Da sauro ya rarrafa ya nufi wajenta hakan ya sa sarki sakar masa tsawar da ta saka bai idasa idasawa har inda take ba aman ya ja daga d'an nesa.

Hannayensa ya had'e ya kara duk'awa sosai yana ta kuka kamar zai mutu yace" Dan girman Allah ki yafe min wannan lamari da na aikata maki, na rantse maki da Allah ni ba mazinaci bane
na je d'akin iyalina ne ta fito ta bar min d'akin sai na biyo bayanta a tunanina inda kike tsaye itace a tsaye domin idannuwana sun rufe, satina biyu kennan tana guje min a shinfid'ata, zaki ga na rufe maki ido da bakinki ba dan komai ba sai dan sannin tana iya k'wala min ihu ta tara min jama'a ni kuwa na yi alk'awarin a daren sai ta bani hakk'ina, ban san cewa ba da ita nake mu'amala ba sai da na kai ga shiga wajen da ba nawa ba, wallahi wallahi ni ba mazinaci bane, sannan ba mai afkawa mutane bane, na kasance ina koyi da halayen nagartatun mutane dan na kasance nagartace,
ban tab'a aikata zina ba ko a lokacin da bani da aure, dan girman Allah ki yafe min wannan b'arna da na aikatawa rayuwarki sannan na aikatawa rayuwata, ki maka ni kotu a yanke min hukunci daidai da laifina ko ki kaini kotun musulunci a yanke min hukuncin jifa domin ba zan iya rintsa ido da hak'inki irin haka a kaina ba."

Mahaifiyarsa ce ta fashe da kuka mai tsanani.

Da sauri ya juya ya k'arasa kusa da SHAHEED ya duk'a ya kama k'afafuwansa yana gunsheken kuka ya shiga fadin" Dan Allah yaya ka saka baki ta yafe min, ka saka baki ta gafarta min kar abin nan ya tab'a d'iyan d'iyana, ka ga wannan dake zaune zata iya maimaita abinda ya faru tsakanina da ita kafin ta baro d'akina, hakan yasa na biyota da sauri ban san inda ta lab'e min ba na fito da gudu ina nemanta sannan itama wando ne a jikinta da rigar baci na rufe bakinta da hanuna da idanuwanta dan kar ta min ihu ko ta fad'a min abinda zai fitar min da son zuwa gareta a raina hakan ya sa na afka mata, ba zan iya fahimtar ba da matata nake ciki ba, hankalina ya gama tafia burina na samu nutsuwa."

Gannin ya k'ura masa firgitatun idanuwan nan nasa masu matuk'ar abin tsoro ya saka shi sakinsa ya juya wajen mahaifinsa ya karasa ya kama k'afarsa.

Kafin ya fara magana ya hamb'are shi da k'afar tasa hakan yasa ya fad'i gefe aman bai gaza ba ya kuma tashi ya kara ruk'unk'ume k'afar tasa yana wani irin kuka murya a cakule ya furta"BABA."

Sarki ya saka k'afarsa yana kiciniyar kuma hamb'are shi aman ya gaza dan baki d'aya jikinsa yayi sanyi lamarin ya shige shi a lokacin da bai shiryawa hakan ba.

Muryarsa ya bud'a a birkice ya furta" Inna lillahi wa'ina ilaihi raj'une."

Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une! Sai kawai muryarsa ta shiga rawa sai kuka ya k'wace masa, hakan ya saka SHAHEED saurin rintse idanuwansa ya sadda kansa.

Muryarsa na rawa ya shiga furta" Lalle kana wasa da adininka, kana wasa da ibadunka, idan kuwa ba haka ba kaima k'addararka mai tsauri ce domin kamar yanda ka fad'a saina hukuntaka! Wani irin rayuwar aure kake da macen dake gudunka har cutuwa ta shiga tsakaninku haka mai tsanani mugun raini ya shiga tsakaninku har ya kaika ga neman afka mata da tsiya ya kasance ka fad'a kan wace ba ita ba?"

Dubansa ya kai kan matar tasa dake kukan ita ma cike da dana sani ya furta" Anyi haka? Mijinki ya zo maki kin fito da suturar da tayi kamanceceniya da ta baiwar Allahn nan? Idan waje ya ga kin nufa ina kika lab'e masa ya fito waje nemanki? Kina ganni ya aikata haka baki katse masa hanzari ba ko baki gani ba?"

Fashewa tayi da kuka tana k'ara sada kanta muryarta na rawa ta ce" Allah ya huci zuciyarka a yi mana afuwa, a gafarta mana, a ji k'anmu, tabbas hakan ya faru daidai da abinda ya fad'a, kuma a lokacin da na zo fita lab'ewa na yi dan ina jin haushinsa ya hana min wasu kud'ad'e, dan ina so yana fita na koma na d'auka domin mun jima muna gaba tsakaninmu sakamakon mahaifiyarsa ta nunan cewa kar na yarda ya yi yan mata ko ya yi tarayya da 'ya'yan turawa a waje shi kuwa yayi budurwa shine ni kuwa nake nuna masa fushina ta hanyar hana masa abinda yake buk'atar."

Sai kuma ta k'ara sadda kanta tana kukan da na sani da tarin nadama.

Kansa yake girgizawa ya ma rasa me zai ce? A hankali ya furta" Ga irinta nan, ga irinta nan, kin yiwa sarakuwarki muguwar hud'ubar ita ma kar a mata kishiya ga inda abin ya kaiki, lalle ke ba uwa ta gari bace, ke ba mata ta gari bace sannan ke ba shugaba ta gari bace, tabbas kema hukunci zai hau kanki domin ba zan iya ci gaba da zama da ke a matsayin matata ta aure ba."

Baki d'ayansu a zabure suke kallonsa sai a lokacin SHAHEED yayi gyaran murya yana kallonsa ya furta" Allah ya huci zuciyarka, Allah ya ja da zamaninka tuba muke."

Baki d'aya suka ringa maimaitawa banda su NAJEEBA.

Kansa ya k'ara sadawa ya shiga fadin" Tabbas wannan lamari idan ma da ganganci a ciki to fa zanen k'addara ce, abin ne ya zo a harhad'e, shi ga abinda ya fitar da shi daga d'akinsa ita ma ga irin lokacin da ta kai tare da yan uwanta suna shashanci maimakun su kasance a cikin bautar ubangiji!"

Sasautawa yayi ya kuma d'auka da cewa" Tir da matar dake gudun shinfid'ar mijinta, tabas kina cikin tsinuwar ubangiji sannan kina da naki kason a cikin wannan lamari."

Dubansa ya maida wajen yarima ya kausasa muryarsa ya furta" Tir da namijin da ba zai iya rige arzizimun wandonsa a lokacind a fitinarsa ke harbinsa ba!"

Sai kuma ya maida dubansa wajen Gimbiya ya sasauta muryarsa ya furta" Kaico ga uwar da zata ringa shinfid'a hanyoyin b'araka a cikin ahalinta, domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login