Showing 162001 words to 165000 words out of 228147 words

Chapter 55 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10363

yarinya ce ya saka nake kawar da kaina a kanki MARDIYA! Yaya kike son sai kin kureni wajen da zan iya hukuntaki tamkar yar da na haifa da cikina ta hanyar dane ruwan cikinta na matse bakinki na zaneki da bulala?, ki kiyayi shiga sabgata, na rantse maki zan iya matse hancinki na rufe numfashinki! MARDIYA ke yarinya ce, kuma a duniyar kishi ke yar kauye ce ki je ki zauna da mace ta koya maki kishi, ki bambance MIJI da KISHIYA , ki iya yiwa MIJI magana, ki iya tafia a gaban miji kafin ki dawo ki tantance ni din abokiyar gabarki ce ko makashinki ce!"

Abin yankan Farcen ta ajiye da karfi saman table din glass din wanda hakan ya saka wajen yin kara ta mike tsaye, sannan ta dan duka ta dafa hannayenta bibiyu saman table din tana kallonta da idannuwanta dake nuna tsantsar bacin rai ta ce" zama da tsoho ai ya kare tunda kika auri tsoho da yarintarki dan son zuciya kika zauna, shirme ai ya kare a macen dake tunanin zata ci galaba a wajen namiji bayan tana kin y'ayansa, ke kam wawuya ce tunda har kike yiwa mijinki hauka a gaban kowa, ke din sakarai ce tunda har kike tunanin ihunki zai hanna wani abun rayuwa! Mazan nan da biyayarkima yaya kika gama da su? Bale ke tsagera karamar kwari?, shin mahaifiyarki ta rasu da kika rasa magaya ne ko me?"

Baki Mardiya ta daga zata yi magana da yannayin tsoron da ya darsun mata na yannayin UMMU, sai dai kafin ta yi UMMU ta zabura ta idasa matsawa kusa da ita sosai ta ce" dis, idan bakinki ya furta min A ba cikin kalmar da zaki hada dan gaishe ni ina maki rantsuwa da wanda raina ke hannunsa sai na sauke maki hakori irin yanda zan hukunta dan cikina, domin ke din y'ar cikina ce!"

Wuki wuki ta shiga yi da idannuwanta

Ummu ta juya ta fara tafia ranta a matukar bace, sai kuma ta tsaya ta juyo ta kalli MUTALAB da MARDIYA ta dan daga muryarta ta ce" me zan yi da aurensa? Bana so, ki kwontar da hankalinki in dan wannan kike hauka!"

Wannan kalmar ita ta fi batawa Abih rai, ya muke da sauri ya taka yana biye da UMMU wace ta kara saurinta zata shige dakin su NAJEEBA ya ce" NANA nine bakya so? Nine bakya so Nana? Sai me dan bakya so na, idan baki aureni ba mutuwa zan yi yo? Aman walahi ba wanda zaki aura in dai ina raye , mu zuba ni da ke"

UMMU ta juyo ta zazaro idannuwanta ta ce" mu zuba MUTALAB, idan an zo daura aurena ka hanna! "

Tana kokarin rufe bakinta sukai ido hudu da NAJEEBA wace yar hayaniyar ta fitar da ita, irin kallon da take mata ya saka jin kafafuwanta sun yi mata nauyi,

A hankali ta furta" NAJEEBA"

NAJEEBA ta lumshe idannuwanta zafafan hawaye suka zubo a kurmin idannuwanta, itama a hankali sannan a sanyaye ta furta" *sai kin aure shi MAMA, idan kuwa ba haka ba mu zuba*"
Tana gama fada ta juya da sauri ta yi dakin kannenta da aka kora su da niyar labarta masu abinda UMMU ke yiwa Abihnsu

Wani irin farin ciki ne ya saka UMMU jin saukar hawaye mai dumi a gurbin idannuwanta,
Ba na komai bane sai na wannan kalma da take ji daga bakunnan y'ayanta goma sha shida banda dayar, a yau ta fito daga bakinta cike da rigima ta hanyar turo dan bakinta mai kyau ta ce *MAMA* ,

Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta da sauri ta bi bayansu dan a yi komai a gabanta

Murmushi Abih ya yi ya juya da sauro da takamarsa ya zo wucewa ya jiyo ihun kulan Mardiya da ta yi dakinta da gudu tana maimaita ba zata yi zaman kishi da UMMU ba ya mikawa SHAHEED da ya talabe kuncinsa yana kallon ikon Allah hannu ya ce" a tayamu da adu'a su kara rikice mata har ta aminta sai ka daura mana aurenmu"

Shi kam Shaheed sai ya samu kansa shima da yin murmushin ya mika masa hannun suka gaisa ya juya ya yi ficewarsa

Dubansa ya maida Kan AMMI dake ta kalle kalle ya sakar mata murmushi ya mike ya karasa kusa da ita

Hannunta ya dauka na dama ya manawa bayan hannun nata kiss a hankali ya ce" AMMI, i lv u"

Murmushi AMMI ta yi tana kallonsa cike da kaunarsa,
Ya ce" zan je, Ammi zan dawo idan har ban samu gamsuwa da irin hukuncin Umani ba"

Ita dai tana mai binsa da murmushin har ya tafi

Kamar yanda ya fada masu hakan ne ya kasance, a zaunen ya tarar da matansa biyu su duka sun sha kwaliyarsu sai kamshin turare dake tashi, aunna zaune a kujeru masu nesa da junna ba wada ke yiwa yar uwarta magana

Da mamakin ganninsa ba rawani, da shiga irin ta jaruman maza du suka bi shi da kallo

Sunna jira ya zauna ya hakimce su kai gaisuwa sai suka ga ya ja ya tsaya a tsakiya,
Muryarsa a dake ya ce" shin daga baya kika fasa ko menene dalili?"

Zinaria dake kallonsa gannin maganar da ita yake ta kara buda kunnayenta dan jin a kan abinda yake magana,
Sai kuma ta ga ya juya wajen NADIA itama a kausashen ya furta" Daga baya kika fasa ko tunda kika zo baki san wannan shine abu na farko a cikin layin abinda zaki yi dan samun dorewar zama da ni tare da kwonciyar hankali da nutsuwa ba? Shin baki san shine dalilin da ya saka na yi dogayen hanyoyin da zasu kai kowacenku wajen ba tare da ta fito ta bi cikin baban gida ba?"

Kara sada kanta ta yi itama cikin rudu, aman ta kasa furta komai domin a ganninta Zinaria itace baba itace ta san kan mai gidan gannin bata ce komai ba sai itama ta yi shirun ta kara sada kanta sosai

SULTAN ya ajiye wayarsa saman table a hankali ya ce" ku kiyaye"

Gannin yana niyar shigewa ciki ya saka ZINARIA kara saukowa ta rage muryarta sosai ta ce" Allah ya taimake ka, shin a kan me kake magana?"

Ja ya yi ya tsaya na dan sekwani sai kuma ya juyo ya ce" ina magana kan zuwa gaishe da MAHAIFIYATA, kowace safia kafin ku gaishe ni ku tabatar da kun fara gaisheta sannan ku biyo hanyar gaishe ni, domin kuwa albarkarta nake nema"

Yana gama fada ya yi gaba, hakan ya saka su bin bayansa da kallo

Ficewar Zinaria ya saka Nadia zabura itama tama sauri ta yi gefenta cike da tunanin bata san ana hakan ba, sai dai ta cika da tsoro, tsoron haduwa da Najeeba domin ta tabata a wajen take, tana tsoron abinda zata iya yi mata idan suka kasance a waje guda!

Zinaria kuwa bakinta ta tabe a kasan zuciyarta tana ayyana 'ai an yi walkiya na ga komai walahi, matar da ta wanke makiyiyata ta baka shine zan ci gaba da jerangen zuwa da zowa dan gaisheta? Ba zan je ba'
...................................

Wasu irin fararen jigida masu dauke da duwatsu kananu yas yas sannan sunna ta zuba kamshi ne Zahrau ta yi cinikinsu har kwaya goma sha biyu biyu gida hudu, hakan ya saka aka zuba su a cikin kwalabensu masu dauke da wani irin ruwan turaran shafawa aka mayar da su gefe bayan ta caje kudadensu masu yawan gaske

Cike da ladabi Zahrau ta ce" Balaba, dan Allah ki taimaka mana da sirrikan sabulan wanka na fatoci kala daban daban mana, kama daga fatar farar mace har zuwa bak'a, Harta da irin wanda wace ke shafe shafe ke oya anfani da shi dan samun farar fata mai kyau da santsi da tsari ba tare da ta shafa mayukan nan masu kona jiki ba?"

Hamshakiyar matar dake zaune cikin madaidaiciyar kwaliya tana zuba kamshi bakinta dauke da hakoran maka biyu sai kyalkyali suke ta dan yi murmushi ta gyara zamanta ta ce" yaya kike so na baki sorrin sana'ata Gimbiya Bilkissu bayan na san kanwarki Gimbiya Najeeba nada saloon? Idanfa ta mayar da wannan sana'arta tawa ta kare domin ina mai tabatar maki da zata kwacen kwastoma, a yanzu haka da wadinnan kawai nake kara kwatar kaina a kan shagonta"

Murmushi Zahrau ta yi ta ce" ba zata mayar da yin sabulai sana'arta ba, na maki alkawari balaraba, ina son ki bani wadinnan sirikan ne dan ina nesa, sannan ina son kanena su uku su lakance su dan yiwa kansu"

Balaba ta kara yin murmushi ta ce" idan akai haka kennan ba zasu zo na ringa hada masu ba?"

Zahrau ta yi wani murmushin ta ce" bayan a yanzu a gabanki na mayar da ke wace zata ringa hada turaran wutar fada? Kin san da mun iya hada turaran wuta irin namu tsumamun turaran wutar da kuke so ruwa a jalo aman kuma na baki wannan damar ai kin san dan mun iya hada sabulai ba zai hana mana zuwa ki hada mana ba idan hakan ta taso, juste ina son na san sirrin nan, ina matukar mamakin matan da suke anfani da sabulun wanka na ruwa da na sabulu fatarsu na daukan yannayi na kwailin dake hanna masu yin bakin nan na hannu da kuma kafafuwa, ina mamakin irin yanda fatarsu ke yin santsi da sulbi , sannan irinmu masu bak'ar fata ina matukar son sannin wai menene sirrin dake sakawa fatarmu na daukan yannayi na sheki , santsi, da wani irin ni'ima tamkar wa'inda bama shiga rana ko ba zafi a garinmu?"

Murmushi Balaba ta yi ta mike ta dauko litafi da byro ta dawo ta mika mata, a hankali ta ce" tabas zan baki sirrikana, bismillah ki rubuta daifai misali, aman kafin nan zan fada maki wani sirrin, wato *zafi*, zafin rana davan, gumi daban, Zafin rana shine abinda fata bata so, aman gumi daifai misali shine abinda fata ta fi so dan karbar gyara.....misali........



Shin kuna son sirrikan nan ne?😁🀣🀣🀣🀣, idan kuna so ku lalaba ni na yi tunani sai mu ga abinda za'a yiπŸ€£πŸ˜†πŸ˜, amanfa iya gyaran fatar zqn bayar, domin kuwa shi baban gyaran cen ai kowama ya iyaπŸ˜ŒπŸ™ˆ


Taku ce SAJIDA
[31/03 Γ  21:56] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



5 1


GUMI daidai misali na gyara fata, yana sakawa fata karin laushi, yana saka fata karbar ko wani irin gyara, ke harta da JESIKA (HQ) na bukatar jiki ya kasance da dumi dan hakan ke sakawa itama ta kasance cikin dumin
Sannan masu shafa man bleating, ba wai masu garwaye nake maki magana ba, aa, manyan masu shafa bleating wa'inda suka san darajarsa sukan shafa mai ne sai su rufa da abin rufa mai kauri , hakan har ya daina wahalar da su domin kuwa sun saba sukan yi bacinsu a haka, lale fatarsu na karbar mayukan nan fiye da wanda baya shigar

Da farko dai zan kawo maki ire iren hadin da muke yi na sabulun wanka na macen da bata Bleating da kuma wace ke son fatarta ta koma fara (a gaskiya zan fada maku gaskiya, zan kawo iya na bak'ar🀣 kar yan Allah tsine su ce na kiyawa y'ayansu shafa man bleating)
Da farko zaki samu sabulun VICTAGO ana so a same shi isashe domin kuwa shi wannan sabulun anfaninsa a jikin fata shine kashe kuraje da du wani fari fari da sauransu na fata, ko wace irin fata kuwa ki gwada zaki bani amsa, sai ki samo hade haden sabulu irin su carotte, na zumar nan, su Mon savon, su la vie belle, su savon de Marseille, su Roger Cavalaisses, idan kika hada wadinnan sabululukan sai ki sayi zuma mai kyau sosai wadataciya, ki sayi madara peak, ki sayi dankalin turawa ba da yawa ba wanda zaki dan yanyanka shi ki dake shi ko ki markada shi yanda dai zai narke, ki sayi resain shima murje shin zaki yi a ciki, ki sayi kankana wace ita kuwa zaki cinye saman sai kasan nan zaki yanyanke ki markade, idan kina son fatarki bayan bakinta ta dan kara haske kadan kina iya saka kurkum yellow ba da yawa ba, sannan ki saka dilka ita kina iya daketa sosai sai ki zuba kadan dan warin nan nata, haka kuma ki je wajen masu hada turaruka ki ce da su na hada sabulu kike so, sai ki zabi kamshin dake kwontar maki da hankali ki sayi madaidaici ki kawo ki hada a hadin sabulun ki , idan kin gama hade sabulun nan baki daya da kayan nan sai ki samu turmin karfe baba ki kara wanke shi ki kara dake hadin nan sai ki zuba a bokici ki dadane shi sosai sannan ki ringa bude shi dan ya kara hade jikinsa. Iya wannan kika rike matsayin sabulun wankanki zaki rabu da kuraje da wasu kananun matsaloli na fata in sha Allah (na Bak'ar fata kennan, sannan da farar fatar da take so fatarta ta kara laushi da santsi kennan, aman fa ba na wanda ke son na bleating bane, na bleating dinma akoyshi dan dai ina tsoron iyayen y'ayanmuπŸ˜…)

Zaki iya markada tumatir danye ki hade shi da colgate ki ringa shafawa, yana gyara fata da sakata sulbi
Ruwan Alovera yana kashe kuraje, aman kafin ki shafa ki goga a gwuiwar hannunki, idan baki ji zafi ba zaki iya shafawa fuskarki , idan kuwa da zafi kar ki shafa bai karbi fatarki ba

Dan tsagaitawa ta yi a lokacin da Zahrau ta gama rubutawa ta ce" ba dai za'a bamu na bleating din ba?"

Dan murmushi Balaraba ta yi ta ce" ku dai na san bakwa shafa man bleating, baki data gidanku bakwa wannan, bakwa sabulun bleating to me zaku yi da shi?"

Itama murmushin ta yi, ta so ta fada mata ko dan gaba, shi ai ilimi ne sani ne sannan ita du farinta ai tana anfani da sabulun na bleating shi yasa tamkar kwai kulun haka take sheki gashi dai da shekaru a kanta aman sun boye , Zahrau ta ce" to mayuka fa?"

Balaraba ta ce" kin san shi mai da kika gani daukan fata fata ne, zan iya baki wanda ba shi ke karbar fatarki ba shi yasa idan ka tashi siyan mai to ka san wani meye baya son fatarka wanda ke iya saka maka kuraje ko wata matsalar daban, kin ga ni ko ido rufe aka bani carass zan jefar da shi domin ko a miya na ci shi sai na yi kuraje, shi ya sa ko siyan mai na tashi bana siyan wanda aka hada da carass komai kyansa, aman akoy dangin su Roger cavaills, su secret de teint da dai sauransu mayuka ne masu kyau dake kama yawancin fata

Ummulkhair ta ce" abinda ke bani mamaki Balaba, yanzun an rage shafa mai dan samun hasken fata sai ki ga sabulu kawai ya wadatar ko kuwa sabulun nan na ruwa da ake hade hade ki ga baki daya jikin mutun ya dauka ba bambanci harta da kafa da take da taurin kai"

Balaba ta ce" haka ne, kin san shi mai idan ba iya shafa shi ka yi ba yana haifar da matsala ta hanyar saka maka jiki ya yi daban daban, ka samu bakin gurbin ido, bakin kunne, wanin hannunsa baya taba jin mai ko wani irin ne, duda shi mai idan kana so ya kama maka jiki zaka ringa shafa shi da dare ne idan ka gama komai ka yi wanka sai ka shafa ka bi lafiyar gado, a lokacin da ka tashi salar asuba kuma sai ka yi wanka, sannan saka tube a mai ke saka fuska ta yi bakin gurbin ido domin a lokacin da rana ta daki wajen an gama in dai ba nikaf zaka ringa anfani da shi koda yaushe ba, su sabulan ruwan da na wanka shi yasa suka fi anfani a yanzun, domin sabulun ruwan nan mu ba na yanda bama hadawa a shagon nan dan kuwa su baki daya suke kama fata basa barin wani wajen daban"

Ummukulsum ta ce" ni dai ba wannan ba, kin ga du cikinmu nice marar gashi mai tsayi da kuma kyau, sannan tafin kafata tana min wani mugun abu ta cika yin kaushi idan sanyi ya zo har tsatsagewa take, ki taimaka Aunty balarabarmu"

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsu, kafin ta ci gaba da fadin" dan gyaran gashin ki ki samo *kwai, sabulun salo, ruwan tumatur* ki hade su waje guda ki shafa a kanki, zai sa gashinki ya yi kyau da shikin, sannan ki ringa markada albasa idan har zaki jure warinta kina wanke kanki bayan ki shafata zaki dan jima da ita a kanki sai ki wanke da sabulun *salo da yodo*,
Kina iya hada man gashinki da abubuwa kamar haka *Man kwakwa, man albasa, man zaitun, Man Oil, Man kadanya, Man alayahu, wadatacen man shannu* hade su zaki yi ki ringa shafawa a kanki
Idan kuwa na mutanenmu na gida zaki iya jurewa sunna anfani ne da iya dungulen mai, wato man shannun nan mai wari danye, anai masu manyan kisto a lafta sai su kawo bakin dan kwali su nade kanπŸ˜†, akoyfa wari aman akoy result mai kyau,

Sannan *Gyaran kafar* kuwa kina iya samun Man shanu, Man kwakwa, Man ridi, Man Alayadi , zaki hade su ne waje daya da dare ki shafa koda a wajen kaushi ne ki saka leda sai ki dora safa a kai, da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi"

Wadatacen murmushi ne ya wadaci fuskar Zahrau bayan ta gama rubucewa ta ce" kwanaki kin min magana a kan na kiyaye cushe cushen magungunnan nan na zamani, harma kin ce min garin neman gira kar na rasa ido,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login