Showing 93001 words to 96000 words out of 228147 words

Chapter 32 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10423

sai dan gudun a goranta masu, ya san mutane da izgili da neman fitina, gashi Allah ya bashi y'aya mata har goma sha shida baya so sakamakon hakan su ringa samun matsalar rayuwa, ya fad'a mata ne dan ya d'auka ita d'in tunda ta kasance matarsa to fa sirrinsa ce.

Ya fad'a mata maganar nan ne dan kar ta ji a gari ta tuhume shi da b'oye mata babbar magana irin wannan, kawai daga jin labarin an d'aura auren Zahrau fitintunnu suka tashi kamar zata kama da wuta, saima da ta ji wanda ya aureta nan fa hankalinta ya k'ara tashi idanuwanta suka rufe ta ko wace hanya neman abinda zata lalata lamarin take, shine ta ringa tak'ale tak'ale ganin dai b'angaren Zahrau yarinya ce mai matuk'ar biyayya da matsanancin kamun kai, hakama mahaifiyarta sai kawai ta shiga yada masa magana cewar yanzu da sarkin ya ji ya aikata haka yaya za'a yi ya so had'a zuri'a da shi? Shine fa shima ya ce da ita "In banda abinki Mardiya ni kuwa na had'a da ke?" (Wato idan baki ya san abinda zai fad'a bai san amsar da za'a bashi ba) shine fa ta ringa fad'e fad'en maganar da idanuwansa suka rufe ya wan wanka mata mari domin fadi take" yanzu haka ba ita kad'ai bace shegiyar har sauran duba da irin yanda suke da halayya na shegu." Kamar wani wanda shege yake da halayya tasa daban, hakan ne ya saka Abih hankad'ata yana nunata da yatsa ya ce ta daina sheganta masa y'aya.

Sai aka yi rashin sa'a ta kaiwa madubi duka, dama abinda zai kaita gidan sarki take nema sai kawai ta fad'a motarsa ta nufi gidan sarkin, tun da aka fito daga sallah ta tsaya a hanyarsa dogarai na kakarewa aman sai da ta yi yanda ya gane itace kafin ta fasa kuka ta yi hanyar b'angaren Anmy.

Burinta ta fasa wannan sirrin y'ayansa su san abinda ya aikata, ta wanzar da tashin hankali tsakaninsu da mahaifinsu da su kansu.

A hankali Anmy ke girgiza kanta kafin ta ringa furta "Innalilahi wa inna ilaihi raj'une."

Da sauri ta shiga tatara k'annanun da su suna cike da tsoron ganinsu zaune gaban mai martaba dan su tsoronsa ma suke, sai Nusaiba dake ta mak'alar wuyan DAYABU tana wasa.

Anmy du ta tattara su ta tura su ciki tana jin kamar juwa zata kifata da k'asa.

Shi Kansa sarki sai ya sada kansa k'asa yana jin yanda kansa ke sarawa, ayau yana tare da b'acin ran da wannan fitinaniyar ta haddasa masa, sai ga wani gagarumin da ya tabbata Anmynsa sai ta shiga matsanancin tashin hankali, uwa uba Abih.

Abih gaba d'aya jikinsa ne ya ji ya fara masa wata mijirya kafin ya d'ora hannunsa daidai zuciyarsa ya rintse idannuwansa wasu zafafan hawaye suka shiga biyowa gefen kumatunsa.

Anmy ta sada kanta sai kawai ta fashe da kuka tana girgiza kanta tana b'oye fuskarta dan kunyar da take ji da irin maganar Mardiya.

Baki d'ayansu hankalinsu ne ya k'ara tashi, hakan ya saka du suka rasa ina zasu nufa, wajen Anmy din ko wajen Abih?

Da rarafe wa'inda suka fi kusanci da Anmy suka yi kanta suka ruk'unk'umeta, wa'inda suka fi kusanci da Abih kuwa Ummukulsum ce da Dayabu suka yi wajensa da Nusaiba suka had'e a jikinsa.

Mamakin hakan ya saka Anmy d'agowa hannunta na rawa ta kai dubanta wajen SHAHEED ta ga kansa a sade, aman ya damk'i sandar dake kusa da k'afarsa da damk'a mai tsananin da ya hadasa jijiyoyin hannun nasa k'ara yin tsaye rad'o rad'o.

A rikice take tatab'a jikinsu ta shiga fadin" baku yi mana fushi ba? Wallahi zan fad'a maku yanda aka yi, kun san k'adarar bawa bata fice shi kar ku yiwa mahaifinku da ni kaina da na taya shi b'oye sirrin nan fushi."

DAYABU dake dafe da hannun Abih wanda ya dafe daidai zuciyarsa muryarsa na rawa rawa ya ce" ABIH, kar ka kashe kanka a irin wannan lokacin da matarka take son tona asirinka dan manufarta da mu kanmu bamu sani ba,
Abih mun san da maganar nan dan girman Allah ka sassauta kar ka had'iyi zuciya domin idan ka mutu mu mukai asara ba ita ba."

UMMUKULSUM ta ririk'e hannayensa tana dannawa ta ce" Abih zafi nan ke maka? Idan yana zafi mu je asibiti, Abih wallahi wallahi bama jin kunyar ubanmu ko haushinka domin a haka muke son ka."

NAJEEBA ta k'ara rik'e Anmy tana b'oye fuskarta a jikinta tace" Anmy, meye na kukan? Kanmu aka fara ko kanmu za'a rufe?Anmy, koda mu dukanmu ne shegun shine aka ce zamu zo mu shak'e maku wuyan a kan me hakan ta faru? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Anmy ba shege bane abin gudu, d'an halal d'in aman mai halayan shege!
Anmy, ai ba daga yannayin da aka haifeka kake nuna halaya ba, halayanka na nuna wanda ya baka tarbiya."

"Anmy, kowani tsuntsu kukan gidansu yake yi! Koda dubu ya tara mu ubanmu ne, babu wata hallitar da zata zagar mana shi bamu sauke hak'oranta k'asa ba na rantse!"

Ummulkhairma kukan take tana kara share hawayen Anmy ta buda bakinta ta ce" Anmy, ku daina kukan nan haka, kin ga fa Abih sai rike daidai zuciyarsa yake

Najeeba ta saketa tayi wajen Abih ita ma ta d'ora kanta gefen k'afarsa tana jin kamar ranta ne ake wasa da shi, irin yanda iyayen nata ke zubar da hawaye sai ta ji tsoron Allah ya k'ara shigarta,
wai kunyar duniya kennan, duniyar ma yayanka, ina ga kunyar Allah? (ALLAH, ALLAH, DAN GIRMANKA DAN SOYAYARKA DA FIYAYEN HALITA ALLAH KA SHIRYE MU, KA YAFE MANA, KA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIA, KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA KIYAMA).

Anmy da Ummulkhair ma da rarafe suka k'arasa wajen Abih, Anmy ta d'ora hannunta inda hannunsa yake tana hawaye tace "Ya isa, daga yau nauyin sai ya tafi ya baka lafia, yaya sun ji, sun sani sun sani." Sai ta had'e kanta da su suma sunna ta hawaye, shi kuwa da hannunsa yake daddab'a su yana jin wani irin a cikin ransa.

SHAHEED kuwa abu d'aya ya hana shi tashi daga zaunen da yake shine shara'a, ya hau kujerar nan ne dan ya yi shara'a tsakaninsu
tana zaune ta kawo k'ara ne, du irin kukan da mahaifiyarsa ke yi tamkar ana narka dalma ne ana zuba masa a k'irjinsa.

Mardiya kuwa baki da hanci duka a bud'e suke ta yi wani fik'i fik'i tana ganin abin na neman juyewa a kanta.

Anmy dake kuka tayi saurin d'agowa, hannun Dayyabu ta damk'o sannan ta damk'o na yayanta tana hawayen nan ta ce "Insha Allahu ba zamu yi kunya ba, insha Allahu Allah zai yi ta rufa mana asiri."

A hankali ta kuma fad'in" *YAYA, DAYABU, SHIN ZAKU BAIWA MAI MARTABA AUREN Y'ATA?* *INA BARAR AUREN YARINYATA WA SARKIN DAMAGARAM, INA BARAR AUREN Y'ATA WA YARON KA*?" Ta karashe tana mai hade hannayenta da nuna Abih.

Tunda ta fara neman auren ya d'ago da rinanun idanuwansa ya tsura mata daga ita har yayan nata da kuma y'ayan nata, suma y'ayan mata biyu da suka yi saura sai ya zamana kukan nasu ya d'auke d'if sai kallonta da suke da kallo irin na son ta idasa maganarta.


Anmy ta k'ara kamo hannun Abih na dama tana mai k'ure shi da kallo, gwara a yita ta k'are, gwara ta nunawa Mardiya a lokacin da ka so wulak'anta bawa Allah kan rufa masa asiri, gwara ta fad'i muradinta idan ya so ko wace wace, idanuwanta a kansa, su kuwa idanuwansu a kanta inda zuciyoyi suka shiga bugawa tamkar zasu b'allo su fito daga k'irjin da dama a wajen.

A sanyaye tace "





_Idan kun yi comment zafafa, zaku samu zafafa🀣, wasan fa yanzu ne ya fara._







NADIA ta yi murmushi tana kallon Auntynta ta ce" a ranar da suka suka yi fada a kan abin nan sai da ta ringa maimaita kalmar nan sai sitin da uku ina irgawa

Hannun Auntyn ta riko ta ce"




Happy juma'atπŸ₯Ί

*Yan uwa ina k'ara gode muku, Allah ya bar k'auna.*
[31/03 Γ  21:42] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



31



Irin yanda NAJEEBA, da UMMULKHAIR suka dago suka tsatsare Anmy da ido tamkar zasu dauketa da idannuwansu dan yannayin girman maganarsu masha Allah
Hakan ya saka Anmy daburcewa ta juya ta kalli SHAHEED
Ganni ta yi shima ya dago kansa daga duken da yake ya kura mata duban da ya sakata jin gaban jikinta sunna kara mutuwa tsoron abinda ta yi niyar fada ya darsu a cikin zuciyarta harma ta ringa dan kokarin sakin hannun Abih

Hannunta Abih ya riko da kyau yana kallonta ya ce" ki fadi muradinki kai tsaye kan yaren nan, kin isa da ni ubansu bale su, BILKISSU ki fadi koma me kike son fada kai tsaye, idanma ba zaki fada ba ki saka rana da lokacin da kike son a daura auren da ko wa kika zaba cikinsu ina mai tanatar maki mutuwata da mutuwar wace kika zabar kawai zai hanna wannan lamari

Mardiya baki daya jikinta rawa yake hakan ya saka ta shiga kokarin matsowa

Hankalinsa ne ya kai kanta
Sai da ya dan girgiza kansa kafin ya ce" MARDIYA, ki fita mu yi maganar sirri da masu rike sirrina, domin ni a yanzu ko lokacin cin abincina da izinin Allah ba zaki kuma sani ba kar ki je waje ki saka speaker ki ringa ihun na cika ci

Irin kallon tsanar da DAYABU ke mata da kallon gargadin dake shaida mata idanfa ta yarda ta matso kisa da su sai dai wata ba ita ba ya saka tana dogon wiya jikinta na rawa ta mike ta kai dubanta wajen mai martaba
Sai dai irin yanda ta ga idannuwansa ya saka ta fice da sauri ta tsaya kofa hankalinta tashe sakamakon rashin jin da waye kuma za'a daurawa sarkinsu aure a cikin y'ayan da ta tsana?
Fatanta kar ya kasance da wace sanadiyarta ta shigo rayuwarsu
Domin kuwa ta rantse da Allah idan har aka aurawa sarki Najeeba ta tabata gaba ta ci ba baya ba dan kuwa shi kansa saurayin nata ba wani uban mai kudin bane bale mulkin da zai yarda ya kama kafar Mai martaba
Kennan ta yi a banza ko me?
Alkawarin da ta yi cewar sai dai ta ji ana yiwa wata buda sai ta tabatar da shi koda kuwa hakan zai yi sanadiyar rabuwar nata auren

Waigawa ta shiga yi dan samun mafita

Da sauri ta nufi bangaren ZINARIA domin ta san wacece a halin kishi dan irin haukan da ta zuba a auren bintu ko a gari fadi ake ita ta kasheta!, ta yi niyar zata fara fada mata maganar da sarakuwarta ke shirin aikata mata idan ya so sai ta zama makiyarsu ta gasken gaske

Anmy ta kara kallon Najeeba kafin ta kuma sada kanta, a sanyaye ta ce" yaya, ina so cikin su biyun nan da suka kawo, a hada auren SHAHEED da daya

Wata wawuyar ajiyar zuciya ce Najeeba ta saki wace ta saka Anmy sauke dubanta jiki a mace

Ajuyar zuciyar ta kuma saki tana kamo hannun Anmy, irin zata yi convincing dinta ta ce" Anmy, Alhamdulilah, dama Anmy Ummulkhair ce bata da saurayi, Anmy kin ga ni ai na maki maganar Huzaifa ga kuma likita, a cikinsu koma wa kika zabar min na yarda zan zauna da shi Anmyna

Jikin Ummulkhair har rawa yake a lokacin da ta ji abinda Najeeba ke fada
Hakan ya saka baki daya ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce" Eyah Najeeba, Eyah Najeeba, wace irin magana kike haka bayan kin san cewa kaf cikinmu na fi ku rauni? Ni a gidan sarauta? Ko sujada na kai ina fadawa Allah ya hada ni da kunu huce in sha ka domin ina matukar tsoron ringingimun yau da kulun , Najeeba ke kuwa kin sha fada ke ai su kike so ko?

Najeeba ta yi gagawar fadin" ke, ki rufa min asiri, ki rufa min asiri da wata fitinar gwara na san salar gawata ake yi, bayan wannan ni Huzaifa nake so, yanzun nan tafiar da ya yi mun tsayar da maganar zan kawo maganar gida ne fa

DAYABU dake kallon su da matsancin mamak8n shin sun manta cewar sarki na zaune ya daka masu tsawar da ta saka du suka zube jikin Anmy

Ransa bace ya ce" lale baku da kunya da kawaici
Gardama kuke a kan maganar da aka yi ko me kuke nufi da maganarku?

Ku tashi ku bacewa mutane a wajen nan, kuma magana ta riga ta yita a yanzu yanzu zamu yanke wace ta dace idan ya so in an yi auren dan Allah ta kashe kanta!

Hankalinsu du a tashe suka shiga mikewa , du sai suka shiga gware da junna tsabar rikicewar hanyar da zasu bi

Sunna shiga daki Najeeba ta karasa da sauri ta rukunkume Ummulkhair ta saki kuka tana fadin" ashe ba zaki ringa daukan girma irin na aunty zahrau ba? Ashe kin manta irin tsanar da wannan bawan Allahn ya min har zaki nuna kina jin tsoron zaman aure da shi? Ummu, a titi ya min wanka da ruwan sanyi cewar na dauki niyar yin wankan jannaba shin karuwa ce ni? Kaf cikin mu ku kun fi kowa sannin ko rigima ta kawo mu fada ya kama hararana tamkar zai kashe ni da idannuwansa da mugun kallo
Ummu, kin fi kowa sannin a duniyata ina jiran damar da zan rama irin cin wulakancin da jifana da mugayen magangannun da ya yi nake nema ko? Kafin aunty zahra ta bar gariin nan sai da ta sakani rantsuwar fita a harkar matarsa
Ummu, me na mata? Du idan mun hadu ko ta zartar da yawu ko ta kirayeni banza talaka
Ummu wace irin rayuwa kike son saka yar kanwarki a ciki bayan kin san a duniya *SULTAN SHAHEED MAKIYINA NE?*

UMMULKHAIR ta yi gagawar rufe mata baki ta kara janta ciki ta dungurar da ita saman kujera
Tana kallonta ta ce" ohk laifi na yi da na zilewa auren mutumen da ya kasance ko hauka nake idan na ji sunnansa nake wartsakewa?
Kaf cikin namu waye yake dago kansa ya yi masa duban ido cikin ido a lokacin da kowa ke rawar jiki? Kaf cikinmu waye ya daga hannu ya wankawa matarsa mari ya kwana lafia bayan nan muka ringa nafilar Allah ya sa kar a sace ki a je a datse hannayen ki?
Najeeba, a gaban Anmy kika nuna mata ke kina da wanda kike so? NAJEEBA yaya kike tunanin zan iya zaman kishi da matar da nake tsoro kamar raina? Kin taba gannin na gaishe da matarsa a tsaye ba tare da na duka ba? Ke kin taba gaisheta tun da kike?
Najeeba ni, ni Ummulkhair auren Sultan SHAHEED? na tabata maki tsoronsa zai saka nima a tardo gawata a ajiye kafinma a sadani da dakinsa
NAJEEBA a kan mema Anmy zata so hadin nan? Me ya sa zata nemi wannan abin bayan mu tsakaninmu da shi ubane sarki ne a wajenmu?
NAJEEBA waye ke bibiyar matar da yake aure? Idanfa wani ne ke kashe masa mata?

Najeeba ta ringa binta da kallo kafin ta ce" idan fa ZINARIA ce ke kashe masa mata?

Da sauri Ummukulsum dake tsaye hannayenta rungume a kirjinta ta matso ta ce" kai, ku yiwa mutane shiru kar garin haukan ku ku yi kokarin kauce hanya! Zato? Zato irin wannan?
Wai da kuke ba ni ba , ba ni ba, an fada maku shi yana da ra'ayin aurenku ne?
Banda masifa, rigima, fitina, tara samari, iya shege me muka iya ne y'ayan mutalab? Ikon Allah ne ke giftowa yana hada mu da na kirki, idan ba wannan ba ku fada min a samarin tsayuwar titin waye ba dan airs ba?


Najeeba ta ringa gyada kanta ta ce" ka ji uwarmu ta yi magana, ke Ummukulsum na rantse kika kuma ce mana yan iska sai na fafala maki mari malama a nan, kuma ba dai sarki ba ? A kai kasuwa, ko ina numfashin karshe aka daura min shi zan mike na murje ido na ce bana so!

Gaba dayansu da mamakinta suka kura mata ido, lale ta cika mutun mai karfin hali,
Yanzu itane ke fadin haka a kan sarki?
Ummulkhair ta ce" aman an fadi ba nauyi, an ji kunya
Na tabata yau Anmy ba zata iya rintsawa ba idan ta ringa tunowa kin nuna kin fi son wani dan daudu a kan yaronta!

Najeeba ta yi shiru jikinta du a mace tana kallonsu idannuwanta suka ciciko da kwallah
A sanyaye ta ce" Ummu, Huzaifan ne dan daudu? Ummu Huzaifa ba dan daudu bane na rantse
Kuma kin ga, ban taba sannin yaro zai juri iya shegena sai da na zauna na ringa masa yana taro ni
Ummu, ina son Huzaifa har raina, ya jima yana fama da ni
Meye laifin Huzaifa?, saurayi tsayaye yaro mai jinni a jika
Ummu, Huzaifa ya iya sangarta ya iya hira ya iya yi min kallo irin na mutun mai daraja
Ummu me ya sa zaki zagar min shi bayan shi zan aura nake so na zama uban y'ayana?
Ummu, kin manta irin namijin da nake so?
Huzaifa du ya hada abubuwan nan Ummu, shine tsakani da Allah dan ki tayar min da hankali zaki zage shi ki ce da shi dan daudu kuma ummu dan kawai na nuna aa ba ni ba sai ki ce na tayarwa da Anmy hankali? Ni yaya kike so na iya yin bacin ne? Ummu aunty Zahrauna kan sadaukar da farin cikinta domina
Na tabata da itane ake magana a kanta, da ba zata taba kawo sunnana kusa ba dan ta san idan na tsani abu na tsane shi, zata amsa ne koda kuwa hakan na nufin karshen numfashinta
Ummu, a hannayenku ta barni ashe ta yi aikin banza shine kuke tayar min da hankali fisabililahi?
Ta karashe wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login