Showing 207001 words to 210000 words out of 228147 words
Chapter 70 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
yau yau din nan kafin ya kai kayan UMMU a kimtsa mata su dan an gama gyara an zuba kaya an gama jera komai mai dakin kawai ta yi saura, Mardiya kuwa tana wancen gidan na Abih
__________________________
Washe gari ta tashi da rashin kuzari, haka ta yi wanka ta kimtsa kanta suka ci gaba da ayukansu da yan uwanta
Wajen karfe goma suka yi waya da Zahrau da dukan yan uwansu hakan ya sa wayar ta dauki dan lokaci kafin su katse
Garin dan wake suke gyarawa zasu jwfa dan wakensu shelar shigiwar Sultan ta karade wajen
Ai kamar ana wuwurga su suka ringa tserewa kowa na shigewa ciki, hakan ya baiwa NAKEEBA daria har ta dara abinta ta ci gaba da hada garin da kanwa da miyar kuka ko foku
A lokacin da ya shigo sai da ya gama da iyayensa sannan ya karasa wajen da yake hangenta ta dage tana kwaba garin hankali kwonce da muciya
Zama ya yi yana kallonta, a ransa fadi yake hankalinta kwonce, yanzu haka ko tinawa da ni bata yi ba, dama fama take ta dawo ta zuba sangartarta
Gaishe shi ta yi tana dubansa, a lokacin shi kuwa sai ya zame ya zauna saman ledar da suka shinfida dan kar su bata wajen
Daga UMMU har AMMI ido suka zaro daga inda suke zaune da matsanancin mamakin gannin ya zauna a nan ba kan kujera ba, ba cike da takama ba
A hankali ya ce" Na ji, ko ki kiraye ni ko? "
A ranta ta furta'ina ni ina kiranka kana tare da matar so raina ya baci ', a fili kiwa baki ta dan tabe bata ce komai ba
Zamansa ya gyara da niyar yi mata tambayar da ya zo da ita, Allah yana ganni yana matukar mamakin lamarinta, haka kuma bai taba sakawa ransa wai tambayar na iya kawo matsala ba, dan haka hankalo kwonce ya ce" BEEBAH "
Dan dakatawa ta yi da motsawar tana kallonsa, jin ya yi mata irin kiran dake kasheta dan haka ta kura masa idannuwanta masu hadasa masa kasala
Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da fadin" Me zai hanna ki baiwa kawarki abinda kike sha kike kasancewa haka? Na san mata fa bakwa rabo da dan taimakawa kanku"
Idannuwanta ta dan wara dan neman karin bayani, hakan ya sa ya dan kara matsawa kusa da ita a hankali ya ce" idan wani abu ne na sha kike sha , ki taimaka mata itama ta ringa sha, irin na saukar da ni'imar nan "
Ya salam, wani irin faduwar gaba mai hade da bacin rai ne ya ziyarceta, idannuwanta ta saka cikin nasa tana kallonsa kafin ta cire muciyar tana nuni bangarensa ranta a bace aman kuma muryarta ba sama sama ba ta ce" Ai ba sai ka min haka ba zaka nuna min ka sadu da matarka ba Shaheed, koda baka fada ba na san matar so dole ka kula ta, waima yaya kake tunanin zan saka damuwa a raina dan ka kwatanta min ka kadaice da matarka bayan kiri kiri ka nunawa duniya ji din ba kowa bace ta hanyar karbar hadin da akai maka a fili aman a zuci ka hadani da aminiyata? Sai me dan baka so na? Allahn da ya sa nima ban rasa mai sona ba, kafin kai nima ina da mai so na, kuma nima ina son abuna dan haka kana iya...............................................................................................DIF maganarta ta dauke sakamakon wani azababen marin da ya sauka a gefen kumatunta da kunnenta kadan ya yi sanadiyar dauke jinta harma ganninta ya fara nuna mata biyu biyu uku uku
Zabura AMMI ta yi tsaye ta furta" Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, SHAHEED lafia?"
Tana fada ne tana yiwowa wajen da wani irin sauri
NAJEEBA kam daga tsayen da take ta durkushe kasa saman gwuiwoyinta , dan kwalin dake kanta ya fadi, kitson da akai mata ya bayana kansa sai yar sarkar dake wuyanta mai heart ta shiga dan yawo kadan kadan a wuyan nata, still hannunta na jikin kincinta
AMMI na karasowa da sauri ta duka ta kamata tana maimaita " meye haka? Me ta yi maka daga zuwa sai mari? Me ke faruwa? Me aka yi? "
Du a rikice take fadin hakan , shi kuwa yana tsaye kikam idannuwansa sun kada sun masa wani irin ja, gaba daya jikinsa ya dauki rawa tamkar yana filin yaki, hannayensa kuwa ya jimke ya saki, nan da nan jikinsa ya yi ja irin na bacin rai, idannuwansa suka kara kadawa
Kuma dagowar da AMMI ta yi ta ga yannayinsa a haka ya saka gabanta faduwa
Da sauri ta kama NAJEEBA ta mikar da ita , bata kuma ce masa komai ba sai jan NAJEEBAR da ta yi da sauro ta turata cikin kicin ta janyo kofar ta rufe
A tsayen nan da yake idannuwansa a kansu har AMMI ta rufo ta dawo ta tsaya nesa da shi tana kallon ikon ALLAH
Sai da ta sanyaya muryarta daga inda take ta ce"
Saura 😁😁😁😁😁💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
[31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
64
A sanyaye AMMI ta ce" Haba Shaheed, kai da kanka ne yau ke marin fuskar Najeebana? Bayan ka san ko musulunci yayi hani da marin mutun? Mari fa cin fuska ne, wani irin laifi ne ta yi mai tsanani haka? "
Idannuwansa ya lumshe sakamakon zafin da yake ji a cen kasan zuciyarsa kafin a hankali ya zauna yana mai kara jimke hannun nasa
Rawaninsa ya idasa warwarewa ya yar a nan kasa sannan ya ja babar rigar da yake jin ta masa nauyi a yanzu ya sabuleta daga jikinsa
Hannun nasa na dama ya kuma kurawa ido, wani irin haushin hannun yake ji a kasan zuciyarsa
A hankali ya kara sauke ajiyar zuciya ya dago idannuwansa da sukai masa jajajir, muryarsa a sanyaye ya ce" So take sai ta kashe ni ido rufe ne? Me na yi mata da zata ringa hada ni da wani dan iska? Me ya fi ni da shi da zata ringa cewa wai tana son sa? Ammi sai kawai ta ringa ce min an mata auren dole itama ba so na take ba? Me ya yi zafi tsakani da Allah da take so sai ta kashe ni cikin ruwan sanyi? Me ya yi min saura? Ta amshe komai, ta gama amshe komai, ran nawama so take ta ga ya fita ko so take na ringa daga hannu a kanta , ko kuwa so take na je na halaka yaron mutane ne? AMMI bana iya yawan maganar nan, ashe ba zata gane yarena ba? "
AMMI ta kai dubanta wajen UMMU da ta taso ta taho, a hankali ta karasa ta zauna itama a kusa da su
Ammi ta ce" Me ka yi mata da ta fadi haka? "
UMMU ta ce" haba Bilkissu, harma tambaya zaki yi abinda aka mata? Fitsaririyar yarinyar nan shin bata san darajar girman igiyar dake kanta bane da zata ringa magana irin na jahila? Inma me ya mata ina hadin ta kwara masa ba sonsa take ba? An fada mata shi son nata yake? NAJEEBA ba sonki yake ba biyaya ya yiwa iyayensa dan an isa da shi, fitsararoyar malan! "
SHAHEED ya kalli UMMU da mamaki, ba sonta yake ba fa ta ce? Kansa ya dan girgiza ya rage muryarsa ainun ya ce" UMMU ba haka zaki ce mata ba, kin ga yanda hankalinta ya tashi da marinta da na yi fa, ni bama wannan ba daga tambayarta ne fa sai ta kama fadan nan, ko sun yi fada da wani ne ni zata tada min hankali haka kawai? "
Tausayinsa ne ya kama AMMI, kwarai yanzun bata da dar cewa yar tata ta gama yiwa yaron nata illah a zuciya, ransa a matukar bace yake, hankalinsa a tashe yake, baki daya jikinsa rawa yake aman kuma ya ji za'a fatataketa ya tare, kar a mata haka, kar a ce da ita haka
A hankali ta ce" MARIAM, wace irin tambaya ce ya yi mata ne? "
Ummu ta sada kanta, tsakaninta da Allah Allah tausayinsa take ji a kasan zuciyarta, kuma ba wai dan ita ta haifi Najeeba ba ko wani abun, sam kawai bata so ya zurfafa har Najeeba ta gane dan kuwa ta san wacece Najeeba
Kansa sade a kasa ya ce" daga tambayarta abinda take sha ta taimakawa yar uwarta dan ta gyara kanta shine ranta ya baci har take fada min wasu magangannun banza"
Su dukansu da mamaki suka kuma kallonsa, sai kuma kunya ta hanna masu hada ido da junna
A hankali AMMI ta ringa murza gaban goshinta cike da mamakinsa, dama haka ne ko likita idan abu ya shafe shi ne yakan rikice ya kasa gane gabas bare yama, kudu bare arewa, to ita yanzu mai zata ce da shi ne? Ta ina zata fara kwatanta masa lamura ne?
A hankali ta ce" SHAHEED, wannan wace irin tambaya ce zaka yiwa macen da ta san darajar kanta? Ai ko mace bata son ka zata iya jin zafin tambayar nan, kaima menene haka da girmanka? "
Kallon AMMI kawai yake cike da mamaki, to wai shi menene laifin da ya aikata haka ne?
UMMU ta ce" aa AMMI, shi din ko ba mijinta bane ai yayanta ne kuma ubanta, bai isa ya yi magana da uta ba dan rashin kunya zata mike tana nuna shi da muciya? Sa'an yinta ne? Ko mahaifinta ya isa ya nuna shi da muciya, ai daraja ce, Allah ya daraja shi dole a bashi darajarsa "
Ammi ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce" haka ne, ban ki ba domin a yanzun ko ni da wahala na yi garajen nuno shi da muciya, sai dai dan abin danki ne kina son takewa ki rufe harma ki dorawa yarinya laifi salon gobe ya kara dora hannunsa a jikinta? Idan shi Allah ya bashi darajar kasancewa sarki, ita sai Allah ya bata darajar zama matar sarki, kina so ki ce min itama mulkarta zai yi? Da kuwa na yi tir da ita harma na rantse cewar ba jinnin mutalab da Mariama bace ita! "
UMMU ta ce" AMMI, kar ki yarda ki fadi haka Najeeba ta ji, ki murje idannuwanki walahi a kan Najeeba, to ita waye da ba za'a hukuntata ba? "
AMMI ta kara sada kanta kafin ta dago ta ce" zan fadi gaskiya, iya abinda nake gannin shine gaskiya a kan zancen nan
Ku dai kunna so ku take sanni ku take gaskiya ne bayan ba'a kyauta mata ba, na yarda matar mutun kabarinsa aman an yi wasa matuka da yarinyar nan, an dora mata auren nan ta amince kuma aka hadata kishi da aminiyarta? Nadia fa ta sha kwana a dakin Najeeba, itama haka, su yi fadansu su shirya, shikenan dan ya kuntata mata a laifin da ban san ko na meye ba sai ya aikata haka, duda na san matar mutun kabarinsa, ama Najeeba ta yi kokari kuma har ga Allah ina gannin girman hakurin da ta yi dan kuwa ban zaci zata iya cire kanta ta mayar da komai ba komai ba da sauki haka , dan haka gaskiya a daina, sam bans so, idan kana haka zaka iya hadasa rigima fa tsana a tsakanin matayenka, sannan zaka rasa kwonciyar hankali a wajen du wace ta ji zafinka a zuciyarta, ina kara fada maka mace fa ba hula bace, ka daraja mace, ka kara mutunta mace ! "
Ajiyar zuciya yake sauke a karo na ba adadi, a yanzun so yake ya ganta gashi iyayen nasa sun saka shi tsakiya sun ki barinsa
Najeeba kam AMMI na kuleta sai ta samu kanta da yin shiru na dan lokaci hannunta dafe da kuncinta kafin ta silale kasa ta fashe da wani irin kuka maran sauti mai cin rai
Kanta ta dora saman gwuiwowinta, idannuwanta rintse kukanta take kashirban ta kasa baiwa kanta hakuri
A hankali cikin kukan nata take fadin" Why me?, me na rasa Shaheed da zaka ringa nuna min iyakata? Ka san cewar nima ba da gangan na shigo rayuwarka da matayenka ba, ka san cewar ko da na shigo rayuwarka ban so wata shakuwa ta shiga tsakanina da kai ba, aman shine zaka saka na ringa jin tamkar ni kadai keda kai kana wulakanta ni? Menene na nuna min ka tara da wata bayan ni? Na san dama tunda ka kula matar cushe ai wace ka aura dan soyaya sai inda tunaninka ya tsaya a kanta, na san cewar zaka kulata harma ta ji tamkar ta haukace, aman me yasa zaka nuna min hakan a bayane? ........" Wani kukan ta kuma fashewa da shi har tana girgiza kanta dake sara mata , sai wani irin yamutsawa da cikinta ke
A hankali AMMI da ta baro su da UMMU ta idasa shigowa cikin kicin din
Da sauri ta je ta kashe gaz din dake ci tukunyar ruwan ta tafasa sai bori take tana dan kukan nan dake nuna tukunya ta tafasa
Wajen Najeeba ta karaso da sauri ta duka tana kokarin dagota
Cike da tausayinta ta ce" Sorry baby am, sorry hearty am, ba zai kuma dukanki ba in sha Allahu, ba zai kuma gigin taba min fuskarki ko wani bangare na jikin ki ba"
Kanta saman hannayen Ammi, sai ta shiga tariyo marin, kwata kwata ita bama marin take tunawa ba, mari dai ba yau ta fara sha ba, duda wannan marin sai da ta ji kamar ta fara sakin fitsari sai dai wani takaici da ikon Allah zafin maganarsa ta gyashe zafin marin da ta shigo tana juwa dan jinsa
Bata yarda cewar ta zama jaka a duka ba sai yau
A hankali ta kara lafewa a jikin AMMI tana ta sauke ajiyar zuciya, me ya sa? Me ya yi zafi? Me ya sa yake son yi min haka? Marin nawama da ya yi dan ita ya yi? A kan Nadia?
Idannuwanta ta rintse tana jin dacin hakan a kasan zuciyarta, ba dai matarka ba? SHAHEED na yarda ni bani da wani power ban isa ba, kuma in sha Allah zan tatare tabarmata na daina yaudarar kaina na baiwa masu waje su shinfida, domin bani da karfin kokowa da kai, Shaheed ka gama yi min ilar da idan na tsaya jin bakaken magangannunka ina iya macewa bani da ja da zabinka, in sha Allah zan tsawatarwa du wani banzan tunanina a kanka!
Jin jikinta da zafi ya saka AMMI lalabawa ta mike da ita a jikinta
A hankali ta kama hannunta da kyau ta ce" Na jefa maki dan waken zaki ci? "
Najeeba ta yatsine fuskarta ta girgiza kanta a hankali ta ce" Na daina jin yinwar Ammi, zuciyata ke tashi"
Daidai sun zo fita daga kicin din Ammi ta dan kura mata ido tana kallonta, sai kuma ta cire dubanta tana jaye da hannunta a hankali suka ratsa suka wuce dakinta
Tun da suka fito komai ya tsaya masa, kwata kwata ya daina gane yaren UMMU da irin tataunawar da suke, a hankali yake kallonta har suka bacewa ganninsa kafin ya sauke ajiyar zuciya, Kuka? Kuka ne ta yi fa , kennan marin ya yi mata mugun zafi a jikinta da har ta yi kuka? So yake ya mike ya bi bayanta ama ya kasa wani motsin kirki bale ya iya aiwatar da hakan
Ummu ta ce" SHAHEED "
Dagowa ya yi yana kallonta ya kasa amsawa ta ci gaba da fadin" Ka gane, ba zamu iya tunkarar matarka da wata magana ta gyara ba, bama haka, a nan ba'a haka, aman kai ke aurenta, kaima cikin dabara zaka iya kwatanta mata ba kai tsaye zaka fada mata komai ba, domin idan ka fada mata kai tsaye komai na iya faruwa tana iya daykan maganar ta kaita du inda fahimtarta ta nuna mata, hakan kuwa sam bashi da dadi, sannan ko da wasa ka kiyaye fadawa wata maganar wata, mata matsala ne da mu , kamar yanda ka ga kana fama da shara'ar kishiyoyi kala daban daban wace a kowace safia kafin dare ya yi sai an sha shara'ar abokanan zama to hakan ne, wata rigimar bata taka kara ta karya ba ama take zama baba a yi ta yinta har sai Allah ya yi mata tsawa, baban abinda ke daukaka kiyayar mata idan Mijinsu na nuna bambanci, fifiko, ko ya ringa zancen daya a gaban daya haka kawai, idan kana gaban daya ba ruwanka da takalo maganar kowata mace "
Dagowa ta yi tana kallonsa, kawai waje daya ya kurawa ido, kuma cikin ikon Allah har zuwa yanzu a cikin yannayinsa barin jikin nan ne kawai ya daina aman baki daya yannayinsa ya cenza baya cikin nutsuwarsa
Ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta dauko masa ruwa masu sanyi ta mika masa
Ruwan kuwa ya kwonkwade kafin ya kuma dubanta ya ce" Umani ai ita ta ja har na mareta ko? "
Shi fa dama ba damuwa ba ya iya, idan damuwa ta shafi cikin zuciyarsa yakan rasa madafa, idan abu ya shafi AMMI yakan rikice ne, ya iya dakewa a gaban mutane ama idan ya samu wanda zai iya fayacewa damuwarsa fila fila to fa yakan manta waye shi ya kasa rikewa, bare ta tabata Najeeba ta shiga wani hali ne, ta tabata a yanzun Najeeba ta afka a ramin da bata shiryawa hakan ba, ita kanta tausaya masu take su dukansu, dan sun zurfafa tsanar junnansu ne hakan ya haifar da zazafar soyayar da suke aikatawa junna aikin fushi da fasara maganar dan uwa
AMMI ce ta karasa shigowa, rigarsa dake yashe a kasa ta dauke babar rigar sai fitar da fitinanen kanshin turarensa take , dakakiyar shadar mai tsadan gaske ta sha aikin sarakunna milk color ta ajiye gefe ta zauna ta ce" tashi ka je bangarenka SHAHEED "
Duban da