Showing 102001 words to 105000 words out of 228147 words

Chapter 35 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10415

fuska bayan ke din kadara ce da ta fi lu'u lu'u daraja?
Najeeba nan da kwana goma idan Allah ya yarda za'a zafa fatiyar daurin aurenki da mutun mafi daraja da mutunci, mai girman mulkin da Allah ya nada tun a kannanun shekaru, mai zamani mai takawa da Alfarmar Annabi, mai watsa taron yan daba mai rikita taron tsageru, Najeeba zaki kasance daya daga cikin mata masu girman daraja wa'inda idan sun zo ficewa ake sada kai ba'a hada ido da su tsabar yanda Allah ya daukaka su ya darajanta su ya fitar da tarmamuwarsu ko da rana take kyali? Najeeba zaki kasance hakima, gimbiya, wace zata zama daya daga cikin wa'inda ko sarakai na jinjina mata kasancewarta matar daya kwalin kwal din sarkin da ya kafa tarihi, Najeeba yaya zaki yarda ki je wani sakaran da ko baran gidan nan ya fi shi mukami a damagaram ya kai hannunsa jikin ki?
*NAJEEBA, ZAKI KASANCE DAYA DAGA CIKIN MATAN MAI DAMAGARAM NAN DA KWANA GOMA KACAL* kike faman saka mu a uku?

Tun daga wannan kalmar kunnayenta suka dode ta daina fahimtar abinda yake fada har sai da ya dasa aya ya ga ta kurawa bakinsa ido kamar wace ta suma a zaune

Hannunsa ya kai wajen kuncinta dan gannin yana furya sunnanta a sanyaye ta kasa amsa shi ya shiga dan taping a hankali ta ce" Najeeba kina ji na kuwa?

Sai a lokacin ta yi wani firgigita ta farka daga summan zaunen da ta yi kafin ta kurawa fuskarsa ido a karo na biyu

Wani irin hantsilowa ta yi daga saman bed din ta fadi kasa har tana take doguwar rigar dake jikinta ta kuma dagowa

Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta kafin ta takarkare ta kwala wani firgitacen ihun da ya saka Dayabu saurin kai hannayensa wajen kunnensa ya dode lokaci daya kuma yana nufarta dan rufe bakinta daga wannan ihu da ta saka daya kwal ta ja shi da wani irin jan da ake yi kamar wace ke kiran sallah...






Happy juma'at jama'atul musulmi😲
[31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



34


Hannayensa dode da kunnayensa ya diro ya karasa inda take ihun nan
Yana zuwa ya saki kunnensa ya damke bakinta da hannunsa sannan ya saka dayan hannun nasa ya riketa da kyau

Sikewa ta yi, lokaci daya numfashinta ya dauke ta tafi luuu a jikinsa

Ido ya zaro cike da tsoro da mamakin suma ta yi?
Lalle ya dauki abin da wasa ashe har ya kai cen?

Jikinsa na bari ya samu ya kaita saman gadon ya shinfideta sannan ya mike ya karasa wajen kofar dakin

A hankali ya bude hakan ya saka Anmy saurin juyowa a lokacin da Abih ya rike hannayenta yana lalabata cewar kar ta shiga ta bari har su fito

Ummu da Ummulkhair dake tsaye jikin kofar ne suka kutsa kawunansu cikin dakin hakan ya saka ya basu damar shiga sannan ya maida kofar da sauri ya datse dan ya ga Anmy ta zaburo ta nufo wajen

Dakatawa ta yi kusa da kofar hankalinta tashe ta kalli Abih, a sanyaye ta ce" me ya sa ya hana min shiga? Baka jin shirun ya yi yawa ko wani abu ne ya sameta?

Abih ya kara kamo hannunta suka koma falo suka zauna, a sanyaye ya ce" mu yi jira, idan yana irin wannan hali da kannensa nakan basu dama, idan na saki mace na dauko wata haka muke shiga da su du su rikice, shi ke rufe kofa daga shi sai su, ban san ta yanda yake lalaba su ba, in sha Allahu zai lalabata (Ya Allah, du wani yaya da ya dauki girma ya kasancewa kannensa tamkar bango, wajen da suke kai kukansu ya share masu, wajen da sun san uba ne a gare su, Allah ka dafa masa, ka masa albarka, ka kare shi, Yayana JAMILU Allah ya kara daukaka baban yaya👏👏👏)

........................................

Cike da tashin hankali Ummulkhair ta yi kanta, ita kuwa Ummukulsum ta yi bayi da gudu dan dibo ruwa

A rikice Ummulkhair ta ce" yaya, summa fa ta yi? Innalilahi wa'ina ilaihi raj'une daga fada mata ta summa yaya zamu yi da ita ta nutsu?

DAYABU ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Ummulkhair, kar ki yi kuka, kar mu saki ta ga rauni a tatare da mu idan ba haka ba na rantse zata botsare mana ne ya kasance mu dake son tirsasata ta amince da maganar nan mu zamu dawo mu goya mata bayan bata so,abinda bana fata sam, kun dai san wacece Najeeba, tana da karfi a cikin zukatanmu, rigimarta ta fi ta NUSAIBA girma dan haka na roke ku kar na ga wace ta wani zubar da hawaye

UMMUKULSUM ta share hawayenta ta shiga tofa adu'a a cikin ruwan sannan ta mika masa ta jingina da jikin gadon a sanyaye ta ce" eyah, Najeeba ta cika daukan abu da zafi, in ba wannan ba na zata zata kama ihun murna ne, meye a cikin auren Mai Damagaram? Ka ga kamar kaza yanzu ta zama daga abu ya dan daga mata hankali sai kawai ta summe

Zuwa ya yi kusa da fuskarta a hankali yana shafa mata ruwan nan

Kamar second goma yana dan shafa mata ruwan ta ja wata irin doguwar numfashi ta sauke kafin ta buda idannuwanta a tsorace

Ido hudu suka yi da yayanta, sai yayunta da du suka matso sosai kusa da ita

Da sauro ta janye hannunta daga na yayanta ta kai saman hannun Ummulkhair da take yiwa fushi aman tashin hankalin nan ya saka ta manta da wani fushi, hannunta ta damko tana kallonta ta ce" Ummu, mafarki na yi ko? Ki yiwa Allah ki samo wani faskare ko ki dauko wani birgi ki kima min na farka dan mafarkin nan sam bashi da dadi kar na mace a cikinsa

Ummulkhair ta sada idannuwanta tana jin kamar ta mayar da hannun agogo baya ta ce ita zata aure shi da wannan tashin hankalin da kanwar tasu ta shiga, shin tsoronsa ne take har yaka ko menene? Dama rashin kunyar tata a boye ne take yi ko meye?

Jiki a sanyaye ta saki hannun Ummu kafin ta kai hannayenta biyu duka saman kanta ta ce" kennan da gaske ne? Da gaske ake za'a min aure da shi? Da gaske kuke zaku yi min wannan abin? Yaushe aka fara auren dole a familly dinmu da za'a fara a kaina? Kun san ina da wanda nake so, har na gabatar da shi a gidan nan aman shine za'a min haka? Ku ce da shi bana son sa! Ku ce da shi kar ya soma halaka min rayuwa wayo Anmy, wayo Abih zaku halakani da kanku?

Da tsawa tsawa DAYABU ya ce" zaki mana shiru da fadin shirme a wajen nan Najeeba ko sai na tataka ki?

Sasauta muryarta ta yi tana kallonsa ta ce" yaya? Kai da kanka? Kai fa uba ne a wajenmu, kai din uwane a wajenmu yaya yau kaine kake son turani rami da kanka?

Idannuwansa ya lumshe yana control din emotion dinsa kafin ya bude ya ce" kin taba gannin uwa ta tura yaronta rami ne cherie (dear) ? Kin taba gannin inda uba ya kai dansa ga halaka kansa kalau? Na san kin san ba dukiya ko mulki ya saka mu yanke wannan hukuncin ba, ke kin fi kowa sannin ba wani kyale kyale na duniyarnan ne ya kaimu ga haka ba, me yasa ba zaki nutsu ki saurari kalamaina ki yi masu kyakyawar fahimta ba?

Najeeba dai kuka take har jikinta na rawa tana jan hanci ido rufe

A hankali Umulkhair ta dora hannunta gefen kafadarta ta ce" Najeeba?

Dagowa ta yi ranta a bace ta ce" ki bar kiran sunna na, kina kallo za'a min wannan abin ba zaki iya hannawa ba? Kina ganni aka ce ko ke, kin san sarai irin tsanar da ya yi min aman shine kika yi shiru aka dauke ni bayan kin san bakin cikine zai kashe ni a gidansa

A hankali take girgiza kanta tana jin tamkar zata fashe da kuka
Bakinta ta buda zata yi magana sai kawai ta kasa da sauri ta yi cikin bayin dakin ta duka tana kuka, a gaskiya bata san me ya taso mai tsananin girman da ya hadasa tsana a zuciyar Najeeba ba, ta rasa me ya sa zata yi tunanin dan ya halakata, dan an tsaneta ne, aka hadata aure da shi maimakun ta yi tunanin alkhairi
Tabas akoy wani lamari na rashin dadi da yake nuna mata ita sai ta fi ajiye hakan a matsayin dan tana yawan fitar da rashin jin maganarta a fili ne hakan ya saka yake mata irin haka
NAJEEBA a gabansa fa ta mari matarsa, NAJEEBA sau nawa zata kacame da fada a cikin gidansa ko a kofar gidansa a yi ta tashin hankali da ita bayan ta san labari zai kai masa? Idanma ya ji haushinta ai kamar ita take take dokokinsa ne mana, Allah ya taimaketa ta kasance wace Anmy ke yawan rokar Alfarmar ya kawar da kansa daga yarta? Akoy wata shara'a da ya taba zartarwa wace ta raka makociya, a wannan ranar Amintacensa ya yi mata wani duba wanda sai da hanjin cikinta suka motsa kafin ya furta" Hatara yarinya, ki saku daga mayen da ya kama ki idan ba haka ba zaki samu kanki a kabari domin kuwa ba'a hada ido da mai damagaram, ana ganni a gaban kowa ya daga masa hannu, hakan ya saka shi yin gum da bakinsa cike da gannin rashin kunyar yarinyar sannan an nuna a barta kar a hukunta ta

DAYABU ya kurawa fuskar Najeeba ido, gaba daya zufar tashin hankali da ta sakawa ranta ta jike mata fuska da abin hwaye tun daga gaban goshinta har fuskar baki daya hakan ya saka du wani gashi dake fuskar ya kwonta luf luf

Hannayenta ta hade tana kallonsa ta ce" ban san kamaninsa ba, wace kalar fuska ne da shi? Tsoho ne ko yaro ne karami? Wani irin mutun ne? Dan karami ne ko yana da girma?, yaya kai ka san bana son farin mutun, burina kulun shine na auri mutun mai lokacin kansa, wanda yake da lokacina kowani time, wanda zamu yi wasa da daria da shi, wanda zai mayar da cikin gidanmu filin nishadinmu, filin kwonciyar hankalinmu, filin samun nutsuwarmu, yaya...ta kuma fada a sanyaye ta ce" ina da burin mijina ya zamo abokin wasana, idan na yi niyar ganninsa koda a tsakiyar dare ne bani da wani shingi tsakanina da shi, babu wani abu da zai hana min ganninsa.

Yaya, ka san bana son mai mata, ina ji a cen kasan zuciyata cewar idan har na auri mai mace ba zamu zauna lafia ba domin ina da madaukakin kishi a kan abinda yake nawa
Idannuwanta ta kuma lumshewa ta kara sanyaya muryarta ta ce" ya tsane ni, ban san me na masa mai girma har haka da ya tsane ni ba, yakan min kallon da ba zai yiwa kashinsa ba, ya jefe ni da mumunar kalmar dake nuna yana zargina, shin yaya dama ana aure da zargi?

Hannayensa ya saka ya janyota jikinsa, ya kasance kanta saman kirjinsa hannunsa kuwa saman gashin kanta
Ummukulsum na rike da hannunta ta kara matsowa sosai kusa da ita suka sakata tsakiya
A sanyaye ya ce" ba kulun bawa ke tsara rayuwarsa kuma ya ganta yanda ya tsarata ba,
Shin kin san lokacin mutuwarki? Ko da za'a halice ki an maki shawara ne? A hankali yake dan shafa gashin kanta dan ya samu ta rage kukan da take yi,
Ta sasauta kukan ba dan komai ba sai dan ta ji ya furta mata cewa" NAJEEBA, dan wannan ne kike kuka? Ba zan iya gannin kanwata na kuka haka ba dan haka an fasa maki auren hadi da mutumen dake jiran hanyar halaka ki ba!

Sai kawai ta ji ya ci gaba da fadin" Njaeeba, ba kai tsaye muka tunkari abin nan ba, haba Najeeba meye a tatare da dan uwan naki wanda har kike irin wannan dan an ce za'a aura maki shi?
Najeeba shine kike hada soyayar wani dan duniyan da yake maki ta karya da girman darajar auren nan?
Ina yanzu kika gama fada min abinda shi saurayin naki ya saka ki yi, take dokarmu, ya ingizaki kika yi satar hanya kika tarda shi, sannan harma ya so ya wulakanta ki? Najeeba shin bakya mamakin irin yanda Allah ya ringa kare ki har zuwa wannan rana? Zaki butulce masa ne? Ina so ki kwontar da hankalinki kin ji an kanwana?

Ya karashe yana dan taping din bayanta

Kanta ta dago tana girgiza kanta a hankali ta ce" ka kasa ganewa yaya, ni fa ba wai butulci zan yi ko wani abin ba, ni kawai sonsa ne bana yi shi yasa na ce ba zan aure shi ba, sam bai min ba, sam bana son sa, baki daya ya saba halin irin mutumen da nake so

Hannunsa ya saka a gefen damtsenta ya riketa da kyau kafin ya ce" Najeeba Mutalab, bismillah!

Yana gama fada ya mike ya saketa ya daga muryarsa a zafafe ya ce" ke wace irin mai taurin kai ce? Ko kunya bakya ji? Yau ke zaki nuna bakya iya auren dan Anmy na cikinta? Koda yana dauke da cutar da zata iya halaka ki, koda yana dauke da cutar hauka ina ga ido rufe zaki amsa tayin aurensa balema ba daya? Ke Najeeba kin san alfarmar da Allah ya saukar a kanki kuwa? SULTAN SHAHEED kike tambayar yaro karami ne ko tsoho ne shi ya sa za'a hada aurenki da shi?

Murmushin takaici ya yi yana gyada kansa, ya ci gaba da fadin" Ke gani kike roka ya yi? Najeeba da ace kadarar da ta samu yayarki a kanki ta fada kice da du mun mace da damuwa zuwa yanzu? Gatanan gabanki zaune, tana cikin jin ciwon abinda ya sameta aman ta dane ta shanye take cudanya da kowa dan ta san Allah ya dora mata ba wani ba kuma shi zai bata mafita

Najeeba?????
Sai ya rasa me zai kara furtawa daga cikin bakinsa
A hankali ya kai zaune ya sada kansa kasa
Ya tabata wannan lamari ne kadai zai yi ta saurareshi
Kansa na kasa ya rintse idannuwansa ya yi forcing din kansa hawaye ya shiga bin kumatunsa

Dago fuskarsa ya yi da muryar kuka ya ce" na zata na isa da ke, na zata idan na haka rami na nuna maki na ce fada zaki fada ne ba tare da kin tsaya tunanin komai ba,
Sai gashi Najeeba, saboda maganar aure, maganar aurenma mai daraja kike tunanin zan cutar da ke ni DAYABU? Najeeba Anmy da Abih kike tunanin zasu cutar da ke?

Baki daya jikinta ne ya kara daukan rawa
Da sauri ta diro ta nufo shi aman sai ya mike yana mai dakatar da ita da hannunsa
Yannayinsa a hargitse ya ce" Najeeba, ba komai ki yi hakuri na yi katsalandan a rayuwarki ashe ban isa da rayuwar taki ba

Hannayenta ta kara dorawa a saman kanta ta karasa da gudu tana neman fada masa

Kuka take bilhaki tana furta" da wane kake so na ji yaya? Da wane kake so na ji? Nima kai din kaine zan fadawa tashin hankalina, walahi ina cikin tashin hankalin da ban san iyakarsa ba, yaya zuciyata zafi take , ban taba zaton haka a rayuwata ba

Idannuwansa ya lumshe jin ta fara sasauta muryarta a kan tasa
Da hannu ya yiwa Ummu nuni kan ta gyara shinfidarta

Da hanzari ta gyara wajen kwoncinta sannan Dayabu ya nufi bed din da Najeeba

A hankali ya shinfidar da ita sannan ya kamo kafafuwanta ya dora sama
Safar dake jikin kafafuwanta ya cire mata sannan ya karasa kusa da kanta a hankali yana shafa gashin kanta ya ce" *FA'INAMA AL USRI YUSRA*,
na fi so ki fadawa Allah , ki ringa fadin" ALLAH, idan alkhairi ne ka tabatar min da shi cikin kwonciyar hankali da kosashiyar lafia
Idan kuwa ba alkhairi bane, ka saka a fasa koda ana gobe daurin auren ne

Idannuwanta ta lumshe a kasan zuciyarta tana furta wani alkhairi? A ina yake? , tana jin Ummulkhair ta fito daga bayi ta ci kukanta ta koshi ta wanke fuskarta ta aro jarumta ta kara nufo wajen kanwar tata
a hankali ta kwonta gefenta ta rike hannunta na dama,

Ummukulsumma ta dawo gefenta na hagu ta hau ta kwonta itama ta rike hannunta na hagu a cikin nata
Tamkar wasu kannanun yara sai da ya masu adu'ar tsari , ya kara tsayawa a wajensu har ya ga ta daina kukan baki bude sai hawaye dake bin gefen kumatunta, sosai abin ke damunsa aman zai jure dan idan bai nuna mata ba wani abu dan tana kuka ba tabas zata rikita su
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fita ya ja kofar yana kara sauke ajiyar zuciya tare da goge hawayensa

Cikin nutsuwa ya yiwa su Anmy bayanin cewa a ci gaba da shirye shirye!

Nan take Anmy ta dauki wayarta ta koma gefe ta yi kiran mutanen da ita suke jura, mutanen da ta yiwa wannan lokacin tanadi, wa'inda zasu saka Najeeba daka har sai lokacin ya yi su fito, mutanen dake kula da gimbiyar saudiya, tun da aka fadi maganar ta kakabe dukiyarta ta shiga shirye shirye, ta dauko su ta sauke su a wani tankamemen gidan SULTAN, jiran yau suke dama su taho


Tun da suka zube kawunnansu ke kasa jikinsu ke bari basu iya dagowa ba haka kuma bakinsu bai daina furta kalmomin ban hakuri da neman afuwar saken da suka yi har ta bace masu

Amintacensa ne ke fada tamkar zai kai masu bugu tare da nuni cewar zai cenza su ya maida su filin horon dogarai domin a irin abinda suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login