Showing 135001 words to 138000 words out of 228147 words

Chapter 46 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10421

zo su tafi, daka ta shige ta yi kiransa ta kwontar da muryarta, sai da ta gama rarashinsa tamkar wani yaro da dadadan kalamai kafin ta furta masa ya bata kwana uku kawai, in sha Allah zata zo koda bata gama abinda take yi ba

Kwarai ta rike wannan abu a ranta, ta yiwa kanta tambaya....yaya aka yi yake zumudi a kan yayar tata? Gashi dai Gimbiya na nan, rabonsu da ita tun haduwar da aka yi wai tana jinyar Zinaria, sun hadu sun dinke a bangaren Zinariar ita kanta ko barorinta rabonsu da su ganta sati dayan kennan, Anmy da Ummu da su ummu da Zahraun zuwansu biyu aman Gimbiyar kadai suka gani ita din wai baci take.

*Ranar tarewarta*

Zaune suke a falo su biyar, UMMU na kitse kan Zahrau da wasu irin kannanun kitso masu bala'in kyau tana yiwa Anmy Daria
Ba dariar komai bane face irin yanda tun dazu takan dan rafka tagumi sai kuma ta cire ta kai dubanta agogo ta furta" yaya zamu yi da y'ata? Yau ranar zuwanta turaka ne, gashi har an yi magariba."

Wani irin sansanyan kamshi, mai hade da kamshin turaran wuta, da takun takalmin mai dan tsini ne ya saka su dan juyawa.

Ya Subahannalah,
NAJEEBA ce ta bayyana cikin shigar wata abaya bak'a sid'ik mai dan ado fari fari
Tsaf ta zane fuskarta da simple mak'up kafin ta gyara gashin kanta ta yane dan kwalin rigar bak'i mai shara shara.

Irin yanda rigar ta bi shap dinta abin ba'a cewa komai.

Hannunta kuwa dauke da wata jaka mai dan girma fara kal itama wace ta zuba abubuwan buk'atarta.

Wauh, Ummulkhair ta fada tana mikewa da yannayin tsokana ta ce" Najeeba, wannan kwaliyar du ta oga ce?"


Murmushi ta yi ta ajiye jakar tana rufe fuskarta da hannayenta bibiyu.

Wani farin ciki da sanyi ne ya ratsa zuciyar Anmy har ta kasa boyewa, UMMU ta dan cije lebenta na kasa tana murmushi a kasan zuciyarta kuwa mamaki ke son kasheta, ya salam, wannan yarinyar ba abinda ta bari nata ko meye? Bangaren halaya bayan ba tare suka rayu ba?

Farin cikin Anmy ya kasa boyuwa hakan ya sa ta mike da matsanancin farin ciki ta yi cikin dakinta da wayarta, dan zata yi kiran Jakadiya ne, sannan ta dauko dahuwar da UMMU suka yi da ZAHRAU wace da kanta ta shaida masa cewar yau ita zata tura masa abinci, sannan ta nemo Alkyabar da zata hau da irin shigar yarinyar nata.

Cike da Tausayi zahrau ke kallonta, bata san dalilin da ya saka UMMU ta saka maganin nan a cikin abincin da za'a kaiwa SULTAN ba, abinda ta sani shine tana da dalilin son dole dole hakan ta tabata.

Hannunta ta kamo ta janyota kusa da UMMU sosai kafin ta kaleta, muryarta ta sanyaya ta ce" yau tsal, ina so na ji kun yi magana."

Najeeba ta kaleta, aman sai ta dan cure lebunanta masu shegen kyau ta kasa cewa komai.

Ummu ta yi murmushi tana jin tamkar ta ciro zuciyarta ta buda mata ita ta nuna mata irin ilar da soyayarta ta yi mata, shin yaushe zata dubeta? Yaushe zata yafe mata? Sai kuma wani tausayinta da take ji na daren yau wanda ko wace uwa take iya kasancewa, wato cikin zulumi da tsoro da tausayin y'arta,
Ta tabata abinda ta je ta siyo ta zuba a abincin SULTAN ko dokine shi sai ya motsa shi bale mutun dan adam mai rai da lafia tabbas ba zata iya fitowa ta nuna rashin jin dadinta a abinda ya faru da y'ar tata ba, aman ta yiwa kanta alkawarin gyara auren yarinyarta ta kasa
Yanda kowata mace cikin matansa ta samu kulawarsa a lokacin da ya yi niya, to fa zai kalli Najeeba koda bai shiryawa hakan ba
Kwarai bata kulaceshi ba, aman kuma zata saka shi ya fara cire zargin dake damunsa, duda ita kanta bata da tabacin idan har zai cire zargin.

Najeeba na zaune tana kallon yan yatsun UMMU. Tsoro take ta kasa ci gaba da gaba da matar, tsoro take karfin soyayar matar ya yi rinjaye a rayuwarta bayan ta yiwa kanta alkawarin in sha Allahu itama ba zata kulata ba.

D'an d'ago dubanta ta yi sai idanuwansu suka sarke da junna
tsantsar kauna, had'i da yanayin tausasawa take hange a idannuwan matar, da sauri ta cire dubanta.

Ummu ta sauke ajiyar zuciya tana gannin an fara fitowa da kulolin gidan sarautar sababi masu mugun kyau.

Yayunta ne suka amshi kayan, Jakadiya ta rike jakarta
Ta coridor suka bi suka tafi UMMU ta lumshe idannuwanta a kasan zuciyarta tana furta" I'm sorry JANNUH."

Anmy ta zauna a hankali gefenta kafin ta kamo hannunta ta ce" MARIAM, ki kara mata lokaci kadan kin ji? Na tabata ita kanta karfin hali take, shi yasa na daina mata maganar na zuba mata ido, zata zaburo ne a lokacin da bamu yi zato ko tsamani ba.

Murmushi UMMU ta yi ta dora kanta saman cinyar Anmy, a sanyaye ta furta" da na sani, da na zauna komai wahala, da na sani da na zauna komai tashin hankali da bacin rai, Aunty Bilkiss na tafi, yanzun na dawo du irin dukiyata, mutanena, na kasa samun nutsuwar tunanina.

Cike da tausayawa Anmy ke k'ara tausarta.

Dayabu da ya sanyo kai sai ya juya dam ya koma, ba zai shigo ba a irin lokacin nan, dama yau yana da wajen zuwa budurwarsa ta dawo daga karatu zai je su ajiye magana a yita ta kare, dogon karatun nan ya ishe shi haka.

Basu jima wajenta ba suka juyo, su Ummulkhair sai santin falon suke , ita dai Zahrau ta yi gum abinda ke zuciyarta na zuciyarta.

Mikewa ta yi bayan ta cire Alkyabarta a hankali ta nufi dayan dakin da ya saka Nadia wancen lokacin
Hannunta na hagu rike da yar wayarta karama wace rabonta da dubata har ta manta

Jikin kofar ta tsaya tana k'arewa irin kofar kallo.

Bakinta ta yatsina ta saka hannunta a hankali da niyar budewa
Sai dai ta yi ta yi kofar ta ki ta bude
A fili ta furta" Munafurci!

Juyawa ta yi wajen dayar kofar ta karasa
Idannuwanta ta lumshe sakamakon jin wannan turaren du ya cika dakin harta da kofar idan ka rabo sai ka ji shi butu butu

Fasa budewar ta yi ta juyawa kofar baya tana gannin kira na shigowa wayarta

A tsanaki ta daga kiran ta yi salama

Aida ta ringa ihun murnar jin muryar uwar gidan nata a rikice ta ce" Aunty wai dan Allah da gaske yanzu Sultan SHAHEED kike aure? AUNTY wai aure kika yi da gaske? Aunty yaushe zamu zo mu ganki? Aunty shago fa?

Najeeba ta dan dafe goshinta a hankali ta ce" Aida wannan ihun fa, sannan wace kike so na amsa maki cikin tambayoyin?

Sam bata ji budewar kofar ba, sannan bata ji fitowarsa ba, domin Aida ta kasa daina ihunta sai murna take ta ce" Aunty ba zaki gane bane, mutane da yawa sunna zuwa wai a taya su murna kin yi aure, su yanzu so suke su koma yar mutunci da ke kin zama gimbiyar garinmu , wai harda matar Ambasador ta zo gyaran kai fa tace ita so take ta zama mai classs yanda mijinta zai daina fade fade, ta zama client dinmu daga yau tana so a ringa kula da ita a shago

Murmushi Najeeba ta yi a bayane, kafin a sanyaye ta furta" waye ya ce mata zan bar mata mijinta ya huta ne? Ai ba zan taba barin mata shi ya huta ba dan ba dan ita kadai aka yi shi ba

Da mamaki Aida ta ce" aman ba an ce kin yi aure ba? Kin auri Sultan? Aunty Ummulkhair ce ke fada mana da kanta fa

Najeeba ta ce" ke, tsokanarku take, ni ba wani sultan da na aura, Aida HUZAIFA ya zo kuwa?

Idannuwansa ya mayar ya rintse daga tsayen da yake, du hirarta yana ji hakama ta wace ta kirayeta domin Aida tana magana ne da karfi karfi so excited, ita kuwa Najeeba duda yanda take maganarta a hankali a sanyaye cikin voice dinta mai fita lafazi by lafazi bai hanna shi jiyo maganarta ba domin Allah ya hore masa ji

A hankali ya tako har zuwa inda take tsaye
Hannunsa ya saka a hankali ta wajen tsatsonta
Lokaci daya ya janyota baya ya kasance ta hade bayanta da jikinsa, ta yi masauki a fafadan kirjinsa ta baya

Gabanta ne ya yanke ya fadi a hankali ta kai dubanta wajen hannun
Ta yannayin girman hannun ta gane ko na waye sai kamshin turaransa da ya mata dirar sauri a hancinta

A hankali ta lumshe idannuwanta sakamakon jin sajensa a wajen dokin wuyanta hade da hancinsa yana sinsinawa

Boyayiyar ajoyar zuciya ta sauke tana hangen takunsa karara da abinda yake nufi da kusanta jikinsa da nata har haka

A hankali ta dora hannunta saman nasa ta saka dan karfinta da niyar bambare hannunsa daga tsatsontsa muryarta cen ciki ta furta " Assshhhhhhhhhhhhhhhhhhh, ka bari mana,

Maimakun ya barin sai wani irin yar yar yar da ya ringa ji baki daya jikinsa ya fara amsawa sakamakon maganar da ta tashi yi sai da ta yi yanda iskar bakinta ta sauka a gefen wuyansa , irin jan maganar da ta yi ya sakashi rintse idannuwan da bai shiryawa ba
Bai tantance ba ya ji ta kuma buda bakinta a hankali ta ce" ina da saurin kaiwa du katon da ya kai hannunsa jikina marrrrr.....i

Dan murmushi ne ya ji zuciyarsa na yi, MARI? lolz ya fada a cikin zuciyarsa

Sai da ya kara yin sama sama kadan da hannunsa kafin ya yi kasa da su duka wajen fafadan kugunta ya dora saman manyan cinyoyinta a hankali ya furta" baki san maza sunna suka tara ba?

Dan yawo kadan ya yi da kugun nata a wajen dogon wandon yadin dake jikinsa a hankali ya furta" har yanzun dai ban hadu da wace ta kai marin nan fuskana ba,..........
Dan jan iska ya yi ya saki dan murmushin gefen kuncinsa a hankali ya furta" kin zo amsar hakin ki ne?

Da sauri ta buda idannuwanta kafin ta saka hannunta ta janye nasa ta matsa gaba kadan sannan ta juyo ya kasance yanzun sunna kallon junna

Sai da ta lumshe masa idannuwanta sannan ta furta" *NI AI BANA RABA NAMIJI DA WATA*
Tana gama fada ta dauki wayarta da ta fadi ta juya da dan sauri ta koma saman kujerar nan

Kansa ya d'an jujuya yana mamakin furucinta, Bata raba Namiji da wata? Ya kai bata jin kunyar abinda take aikatawa?.

Direct wajen abincin ya nufa, saman k'aton diner irin na gidan sarauta, fari k'al da shi sai d'aukan ido yake ga kujeru na alfarma.

Zama ya yi saman kujera kafin ya bi kwanukan da kallo
Kwanukan sun bashi sha'awa tun daga yannayin kyansu da tsarinsu hakan ya saka shi sha'awar buda su.

Cikin nutsuwa ya buda kulolin, murmushi ya yi gannin irin cimar da aka kawo masa.

A dan plate ya zuba, sai dai ya zuba miyar da yawa domin shi akoyshi da son miya bare wannan miyar ta murjajiyar malofiya ta sha kayan had'i su dadawa da nama da kifi sai tashi kamshin yake ga curry ya saka shi jin sha'awar yin hani'an.

Sosai ya ci abincin nan har yana kara surb'ar miyar kafin ya mik'e ya nufi d'akinsa.

Sai da ya fara yin brosh sannan ya koma saman bed dinsa ya kwonta yana mai lumshe idanuwansa
haka zaki yi ta fama, a yanzun da na tabata kin san lamarin, sai dai ki gani ana yi da wasu!
Cije leb'ensa ya yi ya juya ya kara gyara kwonciyarsa da kyau yana jin dacin irin abinda ta fadawa wata, wato shi ga sakarai ko? Da aurensa a kanta aman ta furta wasa ne,
*Huzaifa* sunan nan yana masa yawo sosai a cikin kunnensa, yana tune da yaron, sannan ya san yaron shine wanda ke daukan mai a gidan mansa mai sunna SHAHEED SS, yana sane da manya manyan mutanen da yake kasuwanci da su domin idan ana zaman fada da yawa kan zo su kawo gaisuwa harma su kawo shawara a irin ci gaban garin Damagaram.

Kansa ya d'an jujuya ya mike zaune ya dauki laptop dinsa ya shiga aiki da ita, ba komai yake had'awa a yan kwanakin nan ba sai tarihin mutane hud'u da suke tsaye a ransa wa'inda ya saka ayar tambaya a kan lamuransu harma ya aniya saka ido a dukan motsinsu hotunansu ne, na iyalansu ne, na muhalansu, da dukan wasu dama na rayuwarsu.

Yana zaune shi daya sai ya ringa jin baki daya tsigar jikinsa na tashi.

A hankali ya ringa gyara zamansa, tun abin na haye masa kasa kasa har ya ji sosai wani lamari na gundurar zamansa harma yana neman hautsina tunaninsa.

Dawowa ya yi kan turbar da ya kasa gane abinda yake aikatawa a computer, harma ya fara hada sak'o da sak'o.


*Mai damagaram fa da magana.*
[31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



43

A hankali ya janye yan yatsunsa ya kashe computer ya rufeta

Saman kujerar ya kara gyara zamansa yana dan balancing kadan kadan yana sauraron wani irin al'amari dake ta harhada kansa a tatare da shi
Baban tambayar da yake yiwa kansa shine" *Shin zan iya shiga hakinta ta hanyar kiran wata daga cikin matana na sauke gajiyata dan kawai ina tare da kyankyamin kasancewa da ita?*

A hankali ya buda idannuwansa da suka cenza launi sunna karbar amsawar da jikinsa ke yi

Ko a wancen ranar na yi haka ne dan na san inada damar fara zama da wace na yi niya ne
A yau da yake ranarta ne, dole dole ranarta ne,

Idonsa ya rintse dan kawai ya gwada idan har zai iya jurewa?

Mintuna kamar ashirin tsakani ya gama gane cewar a yau baya jin wani yaren daniya ko jurewa idan har ba rage abinda ke mararsa ya yi ba

A hankali ya mike yana kunce arzuzumin wandonsa cike da mamakin yannayinsa

Me ke damuna haka? Ni ba wani abu na sha ba, sannan sam lamarina baya min haike irin haka

Bayi ya shiga ya sakarwa kansa ruwa , ruwa masu sanyi sosai
Sai dai maimakun ya samu lamarin ya lafa aa, sai ya kara daukan damarar ko wace wace

A hankali ya dan rabawa kansa tawul kafin ya shiga takowa sannu sannu hannunsa dauke da remote din da yake iya control sin hasken wutar dake falon baki daya

Abu daya ya fito da shi a kasan zuciyarsa, shine zai je gareta ya samu dan sauki ta hanyar romance

A hankali yake takawa inda dariarta ke dan tashi sama sama kadan a lokacin da take amsa waya,

Wa ya fada maka? Shine abinda ta fada kasa kasa, kafin ta ce" kai bana son hauka, ka ga zan tura maka komai a detail yanda zaka je ka bugo min sabuwar takardar da zan baka ka kaiwa client dina,

Amsar da ya bata ne ya sakata fadin" kai ajo bana son iskanci ka ji ko,?

Ai ba zaki daina ce min kai din ba? Ai dan kin san du wannan aikin ba wanda zai cika maki shi irina ne ya sa kike lalabani yau, yanzu Najeeba ba zaki fada min gaskiya ba cewar wai da gaske ogan oganni kika yi mana wufff da shi? Kai Najeeba akoy babar Haja na rantse da Allah, kuma shine ko ki kira mana makadin zabi ya wuni yana mana casu muna murza duwawu?
Waima fada mini wata magana Kawar, wai dan Allah da gaske Harda aminiyar nan taki da na tsana mai shegen girman kai ya hade ya yi quf da ku? To ta yaya aka yi ita dan ubanta zata ci naman da kika ci? Ko bata san wacece ke a garin Damagaram ba?

Kitttt ya ji an datse kiran da take sauraron dan daudun dake mata aiki ta hanyar raba katinanta na shagonta

Da sauri ta dan yinkura dan gannin abinda ke faruwa sai dai bai bata dama ba ya karasa gaba dayansa saman kanta lokaci daya yana mai hade bakinsa da nata

Ido ta zazaro ta yi saurin janye bakinta tana maidawa gefe da sauri ta saka hannayenta da niyar tunkude shi muryarta na rawa ta ce" *SHAHEED, SHAHEED, ME KAKE SON YI HAKA MARAR MA'ANA?*

idannuwansa ya sauke a kan lebunnanta dake ta rawa sosai tana kama sunnansa haka kai tsaye gatsai gatsai

Bai iya yi mata magana ba sai saka hannayensa da ya yi da karfin Allah ya riketa ya fincike rigar da ta saka din dama gun dazun ta wancakalar da dan kwalinta sai ya mata saura daga ita sai bra da dan gajeran wandon da ta saka irin mai dame cinyoyin nan baki sidik sabo fill gashi ya sha turaran wuta

A yau bata tsaya jiki mace ba ta bashi damar kashe mata jiki, hannayenta duka take sakata tana tare fuskarsa du inda ya yi niyar kai harshensa sai ta tare ga hayaniyar da take kan ya barta kar ya taba mata jikinta meye haka yake son yi? Meye wannan din?
Shima a yau din cike da kokowar son ya kai inda yake so yake dan kai hancinsa yana sinsinarta ko'ina
Idannuwansa lumshe a hankali ya furta" *ki nutsu, ni kaina ba zan je na rabi gonar da wani ya raba ba! Ina cikin halin son a tabani ne, idan kika min gardama zan kama hannunki da karfi na juye maki komai a cikin bakinki*

Da sauri ta kawar da fuskarta daga nufota da ya yi, muryarta na rawa sosai ta ce" *ka ga, wannan abin bana so! Ka daina, na san ba zaka ci abincin da wani ya ci ba, Shaheed wa'inda suka cin yawa ne da su dan Allah kar ka fara*

Idannuwansa ya rintse cike da jin wani daci a kasan zuciyarsa, wai shine matarsa ta sunnah ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login