Showing 222001 words to 225000 words out of 228147 words
Chapter 75 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
ido sosai a kan tarbiyarsu, mai dafawa matarsa yana bata gudunmuwa a dukan abinda ta yanke masu na zaman rayuwa, hakan ya sa su dukansu suke tafe da rayuwarsu bisa aminci, kulawa da junna, ladabi da biyaya a tsakanin junna, sannan ko yanzu idan ka yarda ka taba daya a familly dinsu to fa ka janyowa kanka rigima ne da ahalin gidan MUTALAB......sannan a yanzu fadan ya cenza salo ne maimakun daga kan DAYABU sai ya faro daga kan MUTALAB ya zarto kan NANA MARYAMA ya dire kan NAJEEB!
...........................................
Masarautar Agadez
Wahalar da suka sha ta tsayin wata biyar biyar kowace a gidansu a karkashin ikon wanda ya isa da su ta saka sukai sanyi tamkar kazar da ta sha dukan ruwan sama
Sun yi sototo da su harma suke labewa a lokacin da aka fitar da su aka gabatar da su suka dawo mutane sak kamar kowa
Sarkin garin agadez ya yi duka da kyakyawar bulala ya gindaya rantsuwar cewa ba zai iya dagawa du wani mai wulakanta dan adam dan kawai Allah ya bashi dama ba, ya kawo misalai da ayoyi ya fasarce kan ko musulunci ya hanna da irin alkawarin azabar da zata tabata a kan masu irin halayen Gimbiya da zinariya kafin ya sanar da gayar daurin auren Yarima da Gimbiya Ummukulsum rana daya da yaya Dayabu, hakan ya saka Gimbiya kara rintse idannuwanta domin kuwa wannan lamari har ya taba lafiarta dan a yanzu fama take da hawan jinni mai karfin gaske domin bata taba tunanin zata wayi gari ita Gimbiyar sarkin garin agadez a gidan horo a gidansu ba, hakan ya sa sunna komawa ta salami masu hidimarta dan idannuwanta ganni suke daria suke mata, sun gama rainata sun gama ganninta a wulakance a yanzun kam bata da wata daraja da fada a ji a masarautar Agadez
Inda Zinaria take kara daga mata hankali da koke koke da magiya da rokon a taimaka a mayar da ita dakinta ta tuba ba zata kuma ba
A yanzun masautar na tafia ne bisa mutunta bawa, daraja dan adam, bayin masarautar kansu sun samu inci daidai misali, domin ba zaka kiraye su da bayi ba sai dai mahidimta haka
kuma har salarry ne da su
GIMBIYA Zahrau kuwa na dauke da cikinta wata hudu abinta, inda Sarki ke nan nan da dan cikin nan yana mai bata kulawa ta musaman
___________________________
A yau ya yi wani irin baci ne mai cike da mafarkai wai ana miko masa jarirai
A lokacin da ya farka salar asubahi ne ya sauke dubansa a kan Nadia, baiwar Allah ta kara budewa ta zama wata irin rusheshiya, gashi yanzu bata samun wadatacen baci sai goshin asuba, a haka yake tashinta ta gabatar da ibadarta, mahaifiyarta ta nemi alfarmar ta koma gida ta haihu aman ya kasa bari
Da sauri ya kimtsa ya gabatar da sallarsa, kafin ya zauna ya shiga tashinta
Da kyar ta iya tashi ga nauyin jiki ga nauyin baci ya taimaka mata har zuwa bayin sannan ya dawo ya zauna da carbinsa a hannunsa yana ja
Wayarsa ya dauka ya shiga dubawa dan gannin sakwanin da ya samu
A yauma ya ci karro ne da message din Zinaria, bai duba ba ya goge shi ya ajiye wayar gefe
Sai da ya ga ta tayar da sallar sannan ya mike ya nufi bangaren AMMI dan du idan aka ce ba kwanakin Najeeba bane hankalinsa kacokam na kanta, yakan kwana ya a mafarkai wani mafarkin har da su gudu zai kaita asibiti
Tun da ya buda ya fara cin karro da yaran gidan, ga wani dadadan kanshin turaran wuta da ya daki hancinsa, sai shige da fice suke murna kwonce a kan fuskokinsu, hakan sai ya bashi mamaki domin su din ba masu tashin asusubar nan bane
A hankali ya idasa kutsawa ya shige falon, nan kunnayensu suka fara jiyo masa muryarta a sanyaye ta ce" AMMI, ba zan iya shan kunnu ba ni dai , kin ga kunnu na busa mutun haka kawai na zama katotuwa a ringa yi min daria?"
Ammi na daria ta ce" NAJEEBANA, ki taimaka ki sha kunnunki kin ga yaran nan da suke mutsu mutsu da baki, ina tsoron su yi tsotsau, idan kuwa babu ruwa za'a sha rigima a gidan nan"
Wata irin zabura ya yi har yana jin zai fadi a kas dan karasawa wajen da suke hayaniyar
Da sauri ya bayana a gabansu, gaba daya jikinsa ne ya dauki rawa harma ya rasa me zai furta a lokacin da ya ga NAJEEBA zaune saman katifa mai daukan mutun biyu gefenta sange ne irin na jarirai da wasu jajayen jarirai sunna kwonce lufff sai yan uwanta da suka zagayeta
Ammi ta ringa murmushi tana gannin yanda ya rikice ya kalleta , ya kalli yaren , ya kalli Ammi, ya kalli yan matan da du suka sada kawunnansu sunna gaishe shi
"Ammi yaushe yaushe? Ammi biyu ne? Ammi yaya aka yi ba'a kirani ba? Ammi wai da gaske ko daya daga cikin mafarkaina ne?" Ya ringa fadi bakinsa na rawa kamar zai fadi ya haye saman katifar
Salamr su Yaya Dayabu da Abih ne ya saka su juyawa
A lokacin shi kuwa ido rufe so yake ya shafa gefen fuskarta koma ya sumbaceta sai kusantarta yake tana dan kaucewa tana sada kanta
Yaya Dayabu kansa sai ga hawaye yana ciro yaran yana mikawa yan uwansa da mahaifinsu sun kasa furta wata kalma mai nauyi, sai cen yaya dayabu ya ce" AMMI, wai dama ba wahaka haihuwar? Ni kulun da tunani nake kwana, irin yanda Najeeba take da son jiki idan ta tashi haihuwa du sai mun fita hayacinmu, wai sai kawai yanzu na ga message"
Ammi da farin ciki ya kasa boyuwa a fuskarta tana daria ta ce" tun karfe daya take nakuda, shima ogan ai tun lokacin na gwada kiransa ama ba'a daga ba sai na masu uzuri kawai
Muna tsaye muna kulawa da ita har abin ya idasa kankama, walahi Allah ya bata mai sauki tunda an sauka lafia, ama ai haihuwa haihuwa ce DAYABU"
Yaya Dayabu ya ringa jejera mata sannu, shi kuwa Shaheed ya rike hannunta na dama yana kallonta, wani irin farin ciki, da madaukakiyar kaunarsu baki dayansu ya saka shi jin son ya rukunkumeta ya kwala ihun sunnansa ya yi ta murna
Karshe dai a wajen nan har Nadia a nan ta same su, inda ta ringa santin babis din maza baki dayansu masu girma da kyau kamar zata hadiye su haka take ji a cikin zuciyarta
Sun hade, sun cakule, harta da yaran sun saki jikinsu a gaban Sultan wanda ya kasa ya tsare yara a hannunsa haka kuma hannunta a hannunsa ya kasa saki sai faman murzawa yake a haka har aka zo maganar shayarwa nan ya kura mata ido cike da birbewa yana kallon yanda suke kiciniya ita da Ummulkhair
Kansa ya dan girgiza yana murmushi ya mike ya bar wajen dan a baiwa masu son shigowa barka danar shigowa domin an dakatar da su a waje
Saura daya kwalin kwalππ in sha Allah
[31/03 Γ 22:04] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*Na*
*SAJIDA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*68*
*ND*
*ND*
*ND*
*ND*
*ND*
*ND*
An sha Sunna lafia, sunnan da idan na tsaya zane dole ne mu shekare a wajen nan, harka ce ta manya, manyanma saraki dan haka ki hasaso yanda lamarin ya wakana hajiata, yara sun ci sunnan ABDALLAH da MUHAMMAD
Sunna yin sati biyu da kwana biyu auren yaya Dayabu ya rage saura sati uku Nadiama ta haihu, ta samu yaronta namiji fari tass shima kato da shi
Nan aka kuma yin wani zaman sunnan, inda baki daya Najeeba ta hargitsa taron ta hanyar shigar da take sakewa, gata jegon ya karbeka fatarta ta kara murjewa , sai kawai take baza abin kallo da kanshi idan ta gita, haka kuma a tsaye take kan kafafuwanta a kan al'amura
Uwa uba mawakiyar nan ce ta larabawa ta sake zuwa, wada a lokacin da kidan ya tashi SHAHEED sai da gabansa ya fadi da sauri ya bada umarni a kaiwa Najeeba karamar wayarsa dan ya san batama san inda tata wayar take ba
Murmushi kawai take zubawa a lokacin da take jin kashedinsa na kar ta kuskura kar ta yarda, kar ta yi gigin yin rawa
A hankali ta furta" Haba takawa, haba uban gudan Beebah......zan yi maka rawarka a daki ne zan juya maka har na kada maka kugu na yi maka rawar kalangu daga ni sai kai, na daina rawa ko dan su Abdallah "
Murmushi ne ya subuce masa ya ringa dan gyada kansa cike da kasaita hakan ya sa dogarai sada kawunnansu sunna miko gaisuwa da kirari dan gannin Saraki na murmushi ya tafi duniyar shauki (π)
Gimtsewa ya yi yana mai kashe kiran tare da sauke ajiyar zuciya
An watse taro lafia, bayan watse taro ne mahaifiyar Nadia ta zo har wajen Ammi ta duka ta nemi alfarmar Nadia ta je gida ta yi wanka, ba dan komai ba sai dan ita likita ce kuma Nadia ta karu sosai wajen haihuwar nan tana son kulata da kanta
Duda ba'a yin hakan, ba'a zuwa wanka a gidan sarauta, ama sai Ammi ta yi mata wannan alfarma, domin kuwa tun saran da maciji ya yi mata suka so hakan aka hanna a yanzun kam sai ta basu wannan dama domin ko ba komai iyayenta ne ai kuma suna da karamci da kawar da kai
_________________________
Shirye shirye ya kankama, Ummukulsum ta shige dakin gyara, inda Najeeba ke makalewa itama ana bata gyaran nata na musaman domin du wani abin da Ummu zata sha tare suke sha, harma ta fita mayar da hankali domin a yanzun ta fita sannin darajar abin
auren kara karasowa yake , bai fi sauran kwana biyu kadai a daura auren Yaya Dayabu da amaryarsa ba, sannan na su ummu da Yarima
A wannan rana ne su Zahrau, su Yarima ango da baban amininsa mai sunna Idriss suka yada zango a garin damagaran tare da yan rakiyarsu tun karfe goma na safe cikin jirgin air france da ya wuce dan sauka a garin Niamey
Sunna sauka hadewa suka yi da yan uwanta suka harhada abinda suka ajiye a grup din da suka yi create iya su yan matan sukai shawara dan bada gudunmuwarsu ga yayansu abin alfaharinsu
Zahrau kanta da take babarsu wace komai ya shiga hannunta sai da ta yi mamakin irin kokarin da suka yi, nan suka samu Ammi da Ummu wace itama ta zo gidan a yau domin a nan masarautar za'a gabatar da shagulgulan auren duka biyu suka zube masu tarin kudin da takardojin adu'o'in kananun da suka rubuta ciki kuwa harda takardar Najeeba inda ya rubuta kalamai kamar haka "YAYANA, INA MAKA ADU'A KA SAMO MIN BABIES MATA DA YAWA YAWA YAWA"
Du daria suka saka , a lokacin da aka yi kiransa aka gabatar masa da irin kokarin kannen nasa sai kawai ya hade su baki dayansu a jikinsa yana dan bubuga bayansu, tabas ya ji wani irin dadi mai sanyaya zuciya sannan ya kara ji a cen kasan zuciyarsa cewa ahalinsa ahalinsa ne, jinnin Mutalab ba zasu taba zubar da dan uwansu ba
A tsaye suke kan kafafuwansu kan shirye shirye
Rana na yi suka kwasa a cikin motoci tare da dogarai yan rakiya wajen motar dogaran kanta mota hudu ce suka saka su a tsakiya cikin shiga ta alkyaba a rurufe masu ko'ina suka yada zango a gidan su amaryar yaya Dayabu
Irin tarbar da suka samu sun ji dadinta sosai, iyayenta ba wasu masu arziki bane ama mutane ne masu wadatar zuci, an masu dahuwa an gyara masu waje an shinfida masu tabarmu da darduma an kawo masu sansanyan tukudi wanda ya ji damu da sansanyar solani ya sha siga da kayan kanshi ga uban cikwui din dake ciki
Ai kau suka baje tamkar ba matar sarakai bane a wajen suka sha abinsu ana wasa ana daria inda mutane ke ta son su samu damar ganninsu aman dogaran nan sun kasa sun tsare dan kuwa kiran da sultan ke yi yana karawa ya kara saka sarkin Dogarai tsayawa kikam a kofar shiga sai muzurai yake ya kasa ya tsare domin uwar dakinsu na ciki
Abinda ya kawo su suka shiga yi, wato kitso da kunshi, sun raraba aiyukan a tsakaninsu inda kanwarsu mami itama ta kware a wajen zana kunshi kamar wata aljannah haka ta ringa zane masu kafafuwa Najeeba kam ta cire alkyaba ta ajiye ta shiga yaryarawa Auntunsu kitso wace ta sake cikinsu take kara karantarsu da jin kaunarsu a cikin zuciyarta domin ita a duniya ta tabata Allah ne ya wanke ya bata wannan bayin Allah da ake tsoro a cikin gari, ita kam sam bata ga abin tsoro a tatare da su ba, abin kaunarta ne, farin cikin zuciyarta ne, mutanen rufin asirinta ne tunda suka nuna mata kauna du irin arzikinsu da sarautarsu suka rungumeta a jikinsu sai kawai take ji a kasan zuciyarta lalle adu'ar samun miji na gari da dangi masu saukin hali da ta taso tana yi tun tana yar karamarta ne Allah ya amsa mata
Ba su su bar gidan nan ba sai kusan salar isha'i, shima kira ne ya shigo wayarta tana dagawa a dake ya furta" Zaki ja abinda zaki shiga kule ke da fita sai na maki wani cikin kin haihu, kin manta jariran da kika bari a gida ne?"
Murmushi kawai ta yi tana sakawa kitson da aka kusan gama mata ribom suka mike sukai masu salama
Nan suma suka yo masu bajintarsu daidai karfinsu inda aka hado su da uban tukudin nan cike da katon kula har biyu da kayan damunsa wanda hakan ya masu dadi dan kuwa sun ji dadin gumbar nan sosai walahi
Sunna zuwa gidan ba zama ba suka yi, a nan aka gamawa Najeeba kitsontsa suka tarar UMMU ta ci karfin kitson Ummukulsum wace ake mata wasu irin kannanun kitso masu shegen kyau
Ummukulsum ta yi wani irin fresh da ita, ta kara fitowa das da ita, dama du ta fi su hasken fata sai fatar ta kara haske sosai da santsi, ko a ido ka kaleta zaka so kuma kallonta domin abar sha'awa ce, a zaunen da take daga kasa wata yar kujera ce ta tsuguni wace balarabar ta ajiye mata, ana mata kitson tana kawo turaran wuta na tsuguni lokaci zuwa lokaci tana saka mata, wannan turaran da irin gyaran kasan da akai mata 6a saka ko yar yatsarta bata gigin gwada sakawa a jikinta domin kuwa ta yi wani irin matsewa abin ba'a cewa komai
Nan Najeeba ta zauna bayan ta watsa ruwa ta shayar da yaranta, sannan ta mikawa masu kula da su ta kama kan AMMI ta shiga kitsa masu du kuwa da irin tarin gajiyar da suka shigo da ita Zahrau kuwa ta shiga kunsa mata lalle namu na hausa
Ummulkhair ce ke ta turo baki tana hararar wayarta ta dago daga saka farcen da take yiwa Ummi ta kalli Ummukulsum ta ce" AMMI kin ga ba, walahi na san ita ta ba Yarima numberna ya ba wannan mutumen da suka zo tare, ni su fita a harkata ba zan iya ba gaskiya"
Ammi ta ce" to wai meye aibunsa? Dan kawai yana nesa da gari Ummulkhair ai idan abin ki ga gidan ya kama zaki zo ki ga gidan ko? Ni walahi nutsuwar yaron ne ta birge ni, gashi kyakyawa mai ladabi da biyaya to meye aibunsa? "
Dan bakinta ta kara turowa tana jin Najeeba na gyara zamanta tana tsaga kitson kan AMMI ta ce" Ammi, balema kudi ne da shi na rantse, kin ga fa a Abujar da yake zaune a cen aka haife shi, mahaifinsa ya rasu da wuri ne ya bara masa tarin dukiyar da shi kansa bai san adadinta ba, a haka mahaifinyarsa itama ta rasu, shine ya ki kula kudin ya je karatu , a waje suka hadu da Yarima har suka kula abota ke kam an yi solofiyo "
Da mamaki Ummi ke kallon Najeeba wace itace bakuwarta, ba komai ya bata mamaki ba kuwa sai ta yanda aka yi Najeebar ta samu information a kan mutumen
UMMU ta ce" Idon naira ta ce ki amince ke meye ki amince mana?"
Ammi ta ce" kin ga dai kar ki yiwa y'ata, ai gaskiya ta fada, to tsakani da Allah meye aibu dan ka so kudi? Ke yar albarka kudi abin so ne ehe!"
Ita dai mesage ta tura masa kamar haka" Ni dai ba zan iya auren mai yaren inglish a bakinsa ba, kai da baka da RRR a harshenka, kumama ni bana son mai kyau gaskiya "
A lokacin da ya karanta sai ya saki murmushi yana kallon Yarima dake yi masa mitar shi bai ga anfanin hanna masa gannin mata da aka yi ba wai sai an daura aure bayan matarsa ce,