Showing 132001 words to 135000 words out of 228147 words

Chapter 45 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10379

yar yololuwa ta saka ta dawo da sauri tana fadin" kar ku cinye mai dadin

Murmushi ta yi ta kalli Ummu dake dan kallonta kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta kan Anmy dake nazartarta ta ce" Anmy, lafia kalau, ina so ne har Najeeba ta tare bangarenta, kin ga kin ce sai ta yo satinta sannan, kuma mun yi magana da shi ya amince

Anmy ta gyada kanta tana murmushi suka ci gaba da cin abincin

Sai cen bayan sun gama ta kalli Ummukulsum ta ce" ummu, ki yi kokarin kula yarima, ya jima a falon nan , tabas na fahimci wani abu a tatare da yaron, na kuma yarda da gaskiyarsa

Ummukulsum ta gyada kanta tana dan sadawa irin na jin kunyar nan.......

Tana gama ci sosai ta mike ta yi saman bed dinsu

Kwonciya ta yi tana warware gashin kanta

Dubanta ta maida wajen Anmy , sai da ta shagwabe fuskarta ta ce" Anmy, Saloon dina fa?

Anmy ta kaleta da sauro, ta kalli Ummu, ta kuma kalli yan uwanta

Sai da ta kikifta ido a hankali ta ce" sai bayan sati biyu zaki koma in sha Allah Najeebana, fatana ki kwontar da hankalinki Najeeba

Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta

Ummu kuwa ta mike ta kama hannun Anmy sukai waje

Tana dubanta ta ce" wani irin zata koma saloon? An taba yi daba?

Anmy ta ce" Ummu, ba zan iya hanata aikinta ba, kuma shima ba zai hannata ba walahi, sai dai wajen aikin ne aka cenza mata, ana gina mata wajen ne a nan cikin fada daga wancen hanyar fitar, sai a buda mata kofar a saka masu tsaro, mutanenta zasu iya zuwa nan su yi aikinsu su tafi, ranar da take sha'awa tana iya shiga ta zauna, ranar da bata sha'awa ta yi zamanta masu aikinta su mata,

Ummu ta ringa jin kaunar Anmy a ranta, ita kam bata da wani dan uwa ko wani makusancin da ya kai mata wannan baiwar Allah
Irin kaunar da take yiwa yaran daban ne, hakan ke saka mata gannin girmanta da kimarta a idannuwanta


Da yama kusan karfe biyar Najeeba ta yi salama kofar dakin Anmy

Anmy ta dago ta amsa mata cike da kulawa tana dubanta
Karasawa ta yi ta zauna kanta kasa a hankali ta ce" Anmy, a jiya sam bamu rintsa ba, sakamakon ciwon ciki da ya tashi Nadia, dole sai da aka nemi Sultan, hakan ya sa na nemi alfarmar a kawota bangaren Sultan dan ko menene shi din zai fi gagawar kulawa da ita

Dan numfasawa ta yi tana hankalce da yanda Anmy din ke kallonta kafin ta ce" karshe dai Anmy bamu rintsa ba har safia, nice ma na ringa dan barci hakan ya sa ya sakani zuwa na kwonta shi kuwa ya kwana yana kula da ita

Anmy ta ce" Subahannalah, yaya aka yi haka? Ko wani abu ta ci? Yaya aka yi bai fada min ba?

Najeeba ta kamo hannunta a sanyaye ta ce" ni ce nace kar a tashin min ke daga bacin gajiyar nan, ni na hanna a tada maki hankali dan na san kin gaji da yawa Anmy
Dan murza hannun take ta ci gaba da fadin" tana dan fama da irin hakan, lokaci zuwa lokaci, shine na nemi alfarmar ta yi satin nan, idan ya so sai na yi na gaba

Anmy ta kura mata ido ta ce" an fahimta ba, kina nufin ke kika sadaukarwa wata kwanakin ki a wajen mijinku?

Najeeba ta shagwabe fuskarta sosai ta yi raurau da idannuwanta ta ce" Anmy, Nadiata ce fa, kuma yayan kansa sai da ya nunan bai amince ba, ni na yi ta magiya har ya aminta da hakan , *ki yi hakuri Anmyna*

Anmy rasa abin fada ta yi, sai take gannin zancen kamar wani shiririta, wannan wani irin sake ne zata yi haka da gagawa? Amsa mata ta yi tana mai mata nuni kan ta je ta huta zata waiwayeta

Sai da ta kara godewa sannan ta mike ta nufi wajen yayunta cikin ranta kuwa ita ta san me take nufi da hakan.....

Sai da ya gama sallar isha'i tare da jama'a kafin ya nufi bangarensa

Cikin nutsuwa ya karasa yana tube kayan jikinsa kafin ya dauki wayarsa ya zauna ya danna kiran number amintacensa

*Macizan nan, shin sunna ina?*

Cike da rikicewa a muryarsa ya furta" abinda ya tayar min da hankali kennan, yanzu haka gamu tsaitsaye da baban liman muna ta nema, an neme su a wajen da aka ajiye su an rasa sama ko kasa

Ba tare da wani firgici ba, a nutse ya ce" kai da wa, da wa ke neman?

Kai tsaye ya furta" Ni da baban Liman, da Dogari mai rike alkur'ani

Kansa ya gyada a hankali kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kashe kiran kittt

Hankali tashe amintacensa ya saka suka ci gaba da nema a wajen da suka boye su, Liman ya ringa fada kamar me, dogari ta rikice sai kai kawo suke baki dayansu sun hargitsa wajen ....
...............................

*AMINTACENA, LIMAN, DOGARI, MATATA*
Ya furta a kasan makoshinsa

Har zai mikr dan dauko litafinsa wayarsa ta dauki tsuwa

Hannunsa ya mika ya dauka gannin Anmy ya daga nan take

*Me ya sa zaka yarda da shawararta bayan ka san yarinya ce SHAHEED?* sunna gaisawa abinda ta fada kennan hakan ya saka shi yin tsai yana tunanin inda kalamanta suka nufa

Iskar da ta fesar me ta ci gaba da fadin" idan har ciwom cikin ya yi wani mugun tsanani ne a kirayi likita sannan a fada mana mana mu sai mu zo mu kula da ita baku daya aman sai ka yarda da maganar Najeeba cewar ta sadaukar da satinta a wajen aminiyarta dan kawai bata da lafia kai ne kadai zaka iya kula da ita ko me?

Idannuwansa ya buda daga lumshewar da yake ya kurawa waje daya ido
Haka ta fada? Ya tambayi kansa, maganarsa da sarkin Agadez ce ta fado masa a rai inda yake fadin" da kyar in zan iya baci, ban taba sannin darajar mace mai fatar Zahrau ba sai da na hadu da zahrau, lalle zan ringa begenta na lokutan da ta dauka
Sultan, ka riki matarka, ina mai tabatar maka zaka yi bayani
Saurin korar zancen ya yi yana tunanin meye kuma na tuna zancen?

Wayar ya duba ya ga ba'a kashe ba, wato dai a kunne Anmy take kan karyar y'arta?

Murmushi ya yi a sanyaye ya furta" Allah ya huci zuciyar Anmy

Anmy ta girgiza kanta kawai tana kashe wayar ta dubi Ummu dake sauraron du abinda ya faru ta shiga yi mata bayani

To a wannan darema ya rabu da Nadia, ya rabu da n'imarta, sun raya daren duda ita din damuwarta daya ce daga ta ga alamu sai ta kama hawaye da magiya

......................................
A haka suka ringa raya darensu tare,
A daren da ya kama na biyar a garesu ya yi kokarin kunna fitila dan kallon Nadia a fili
Idannuwansa ya mayar ya lumshe da sauri sai kawai kamaninta suka fito a fatar idannuwan nasa
Tun daga kanta har kafafuwanta ne suka saka shi saurin buda idannuwan nasa daga lumshe yana kallon waje guda

A hankali ya mike tsaye ya nufi bayi cikin zuciyarsa yana dauke da adu'ar kore shetan

Baki dayama sai ya dauro alwallah ya fito daga bayin ya nufi darduma

Ya raya daren ne a nafila kafin ya nem8 wajen hutawa ya kwonta

Washe gari, ahine ranar da zasu kuma haduwa a bangarensa baki daya
Ranar ya kasamce kwana shida da farin kwanan daya a bangarensa kwana akwai kuma da daurin aurensu

Tun karfe bakwai ta shige daki da niyar kimtsawa ta cewa iyayenta tana zuwa wa'inda suka shiga hada hadar fitar da suturar da zata saka dan wannan rana.............



A ci weekend lafia
[31/03 à 21:50] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



42

Ba wata kwaliya ta yi ba, ko daya bata sakawa fuskarta wani lamari na kwaliya ba sai gashin idon da ta zauna ta dora shi das a idanuwanta kafin ta idasa gyara fuskarta ta hanyar gyara sajen gefe da gefen fuskar nata ta hade gashinta waje daya ta d'aure.

Sket da riga na shada color blue mai duhu ne suka ciro mata
Ta zo saka sket din ya shige aman zif d'in da k'yar ya janyu har Anmy na fadin ko a cenza wasu ne?

Rigar ta saka mai dogon hannu budade sosai an yiwa rigar gidan mama dan ko bra bata saka ba kafin ta d'auki dan kwali ta sasauta gashinta kasa sosai ta d'ora masa daurin Zarah buhari das das a saman kanta.

Wata yar siririyar sarka da dan kunne siraru ne aka bata ta saka kafin ta amshi alkyabar da aka miko mata ruwan pink domin zubin jikin shadarma ruwan pink din ne.

Takalma masu tsini sosai ta saka a kafarta kafin a wanketa da turare mai k'amshin gaske.

Murmushi ta yiwa Su UMMU dake biye da ita sunna hira kasa kasa , ba komai suke son sanni ba sai wai yaya kamaninsa suke?

A daidai kofar shiga ta juyo tana kallonsu ta ce" dan Allah ku tsayani mana? Kun ji An ce k'arfe takwas ake zaman , na tabata ba za'a jima ba ni na tsani ina bin hanyar nan ana wani gaisheni uwa wata shugabar kasa.

Ummulkhair ta ce" aa, ke kuwa wani irin jira tsakani da Allah? Ki rufa mana asiri kar a je a ganmu tsaye a kofar nan a zata wani abin ne."

Murmushi ta yi ta dan tura kofar mai dauke da maduban da ba"a hango na ciki aman tun tsayuwarsu su suna ganinsu daga ciki.

Sai da ta dan shige kadan kafin ta saka hannunta ta cire alkyabar nan ta jefowa Ummukulsum da ta fi kusa da ita tana daria ta juya kasa kasa ta ce" sai ku tafin ai na gani."

D'ago idanuwanta da take suka sauka a saman fuskokinsu.

Sai da gabanta ya kwonci kwonci ya fadi kafin da sauri NADIA ta sada kanta tana jin gabanta na dukan sitin sitin.

A hankali ta yi kasa kasa da dubanta kafin ta cije ta kuma dago idannuwanta tar ta sauke a cikin nasa

A hankali ta ringa takowa, kafarta sanye da takalminta bata cire , sannan idannuwanta a cikin nasa

Murmushi ne yake kokarin subuce masa sannan tar yana mai kallon idannuwan nata yana son ganin iya gudun ruwanta.

Ji take kamar za'a dauketa a nanata da kasa , ji take ta fara jin wata irin juwa mai karfin gaske sanadiyar kallon junnan da suke
Ji take idannuwansa na zama kamar wani mashi sunna son sukar nata
A hankali ta ji kwalah na taruwa a cikin idannuwan nata
A hankali ta lumshe su domin ta yarda , idannuwansa sunna dauke da wani sirri na daban sai dai gagar jikinta ba zata tsaya daga kusantarsa ba

Sai da ta kusa gareshi kafin ta cire dubanta daga wajensa ta maida wajen Nadia

Murmushi ta kakaro a hankali ta furta" *Asalamu alaikum*

Da sauri Nadia ta dago dan duban fuskarta, kuma sada kanta ta yi kasa sosai dan jin tsoronta take har ranta

Muryarta na rawa ta furta" Amen wa alaiki salam

Dubansa ya cire daga kan NAJEEBAR ya kai wajen Nadia , kwarai ya yi mamakin yanda a bayane take barin jikin tsoron kalonta, kuma kallon NAJEEBA ya zo yo a tunaninsa stil tana tsaye somin kamshin turarenta na nan, sai dai ya ga ta je wajen zama ta zauna, kafafuwanta ya bi da kallo, takalman dake jikinsu ya bi da kallo

Neman izinin shigowar da ake ne ya saka shi lumshe idannuwansa ya maida dubansa bakin hanyar

Sai da aka dauki minutes kamar biyu kafin ya yi gyaran murya.

Jakadiya ce ta bayanna a duke sosai ta furta" ALLAH ya taimake ka, ZINARIA na kwonce zazabi ke damunta, shine GIMBIYA ta umarceni na isar da sakon gaisuwa sannan na shaida cewar ba zata samu halartar taron yau ba, tana neman alfarmar a matsa shi zuwa gaba

Kansa ya maida ya jinginar jikin kujerar da yake zaune,
Idannuwansa ya lumshe a kasan zuciyarsa yana furta" Ba zata kwontar da hankalinta ba?, me ya sa ta cika daukan lamarin duniya da zafi? Shi bai ga abin tada hankali dan an maka kishiya ba, kishiyoyinma yara kanana zata wani fitini kanta, zuwansa biyu da kansa har bangarenta, sai tarota yan uwanta suke ta saka sun tare bayan du da mazajensu aman sun kasa tafia domin nunawa take kamar zata mutu,

Idannuwansa ya bude da yan yatsunsa ya salameta hakan ya sa ta yi ta godiya kafin ta tafi.

Sai da ta zauna ta ji wata irin kunya ta lulube zuciyarta hakan ya sa ta kama lebenta na kasa ta lumshe idannuwanta tana dan tsotsa

Jin shirun ya yi yawa ya saka Nadia dago dubanta

A kan Najeeba ta fara dorawa
Lale ita tana dauke da farar fata, Najeeba kuwa bakar fata aman bata taba gannin kalar fatar dake birgeta irin ta Najeeba ba, yanzun sai take gannin Fatar tata ta kara wani fasowa
Inama ace zata saurareta? Inama ace zata iya samun kwarin gwuiwar tunkararta?
A hankali ta kai dubanta wajen Sultan,
Ita kam rayuwar sarauta ta fara bata wahala ba magana, shiru d'in nan na menene? Tana kai dubanta ta ga idannuwansa kamar a lumshe suke aman kasa kasa a kan Najeeba suke, wannan kallon, wannan kallon shine kallon da Najeeba ke yawan fadi cewar yana tsareta da kallon tsana ko wani kallo ne daban? Ita sai take fasara kallon nan a matsayin irin kallon da yake mata idan yana cikin hali na zai je gareta

Kanta ta k'ara sadawa ganin daga yanda yake, idanuwan nasa a kan Najeebar ya budi bakinsa a hankali ya furta" *Zaman yau ba zai yiwu ba, sai dai zuwa lokacin da Zinaria ta samu lafia*."

Dan saurarawa ya yo kafin ya dago dubansa ya cire daga kanta ya d'ora kan Nadia , wanda hakan ya fadar mata da gaba domin tuni launin idannuwansa sun canza kala
Ya furta" *Zaku iya tafia*."

Yana kai Aya ita ta fara mikewa, a hankali kasa kasa ya kuma dora idannuwansa a kan bayanta,
Da sauri ya rintse lokaci daya kansa ya sara masa
*WHY? WHY? ZALAMARKI TA HANA MAKI HAKURIN LOKACIN DA ZAKI MORI HAKAN YA ZO GAREKI?*
Ya tsinci zuciyarsa na tambayarsa
Bai iya cire dubansa ba sai da ya ga ta amshi Alkyabar nan kafin ya cire kansa ya mika hannunsa ya rike na Nadia

Gabanta ne ya fadi, yau take kare kwana a bangarensa, aman ji take dama ya sawake mata kwanan yau
Ta kasa sabawa, kwata kwata ta kasa sabawa
Bata yi rayuwar biye biyen maza ba, tabas sun kasance masu saka kannanun kaya aman sam rayuwar bin maza ba nasu bane
Ita, bata fiya kallon BP ba, sannan ba mai karance karance bace
Kwarai lamarin nan ke bata wahala, har yau kuwa tun kallo daya da ta masa ta kasa kuma masa wani irin kallon na tsanaki
Idan ya yi tsaye a gabanta nan da nan take rikicewa, tsoronsa take ita kam kwarai da gaske

Bayan komawarsu wani zaman hiran suka bude kafin ta amsa kiran Anmy ta sakata bacin wuri wand ata yi hakan ne dan gobe itace da daukan girki

Lamo ta yi saman bed, a hankali take shafa gashin jikin matashin kan dake ajiye
Idannuwanta ta lumshe kafin ta kuma budewa ta kai dubanta saman yan yatsunta
Hawaye ne suka bi gefen idannuwanta a hankali ta furta" *Yau gani da auren farin mutun, mai sarauta, mai takama, mai jin wahalar magana, wanda ya tsane ni, mai mata biyu bayana*
Dan murmushi ta yi tana juyawa cikin bargonta a hankali ta furta" *ABIN DARIA*

A yau da safe da murna Nadia ta bar bangaren Sultan, duda a jiyan ba wani tabata ya yi ba domin haka ya kwonta sukuku da shi , kwata kwatama a zaman da ta yi a bangarensa na sati daya cif sau uku kadai ya zo mata,kwanakin da ta sha matukar wahala a wajen angon nata, domin kuwa ya kasance du idan zai kawo mata ziyara gabanta ke kwonci kwonci ya fadi ita kuwa sai ta kasa rufe bakinta ta yi ta kurma ihu tana neman agaji da neman yanda zata yi ya sauka da wuri

Sannan tabas ta yarda sarauta wani lamari ne na Allah mai girman gaske da wuyar fasara.

Komai da ido, da hannu ko da kansa yake nuni
Sai idan yana son nuna ya ji dadi yakan dan yi wani killer smile

Bayan ta koma bangarenta Aunty ta amsa kiransa
Wani dan akwati ne ya bata a hankali ya furta" Allah ya bamu zaman lafia

Da amen amen ta amsa kafin ta baro bangaren cike da farin ciki da annashuwa, tana tunanin yanda zata yi ta koma gida, itafa walahi ta ga waje

A cikin satin nan ba abinda suke tsakaninta da yan uwanta sai zama sunna debewa junna kewa
Wani irin karfin gwuiwa ta ringa ji yana kara shigarta, wani irin tabacin decision dinta na kara zama a kasan zuciyarta
Bangaren anmy bata daina tsumamata ba wanda hakan har mamaki yake bata, domin akoy lokacin da ta ce" Anmy, shi abin nan yaushe za'a daina shi?

Sai Anmy ta ce" Jannuh, ba za'a taba daina shi ba koda kuwa Allah ya albarkaceki da samun ciki, domin bashi da matsala ga lafia, sai dai ma ya kara maki lafiar, Najeeba, mace ko
me take takama da shi sai da gyara, baki ga yanda yanzu Zahra ke dauka da kanta ta kimtsa kanta ba? Ai sannin darajar abin da ta yi ne

Ita dai murmushi kawai ta yi wai ciki, ciki fa? Da wa? Ko kare mata kallo da ya yi ya shamaceta ne, macuci kawai azalumi mai fuska biyu!,

sam ta fasa gardamar amsar gyara ko shan dadadan nonon rakumin da ake mata hade hade a cikinsa,
Takan maida kai da fata ta karba a ranta kuwa fadi take, tanadin wani ne, domin yana sakina zan maka auren rashin mutunci wanda Damagaram zata girgiza

Mijin zahrau ya kasa hakuri ya shaida masu cewar zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login