Showing 192001 words to 195000 words out of 228147 words
Chapter 65 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
domib kuwa kwarai a ciki ya yi maganarsa
A hankali ya ringa dan daga idannuwansa da sukai masa nauyi ya kuma furta" *BEEBAH, KI BAR BALAKI YA YI BACI NA ROKE KI* "
Wannan karron kam ta ji, hakan ya sa ta yi turus ta tsayar da rawar tata, wajen da take kallo dai take kallo idannuwanta rintse, sai kuma nan da nan magangannun su aunty Zahrau suka shiga dawo mata sala sala, maganar aunty Zahrau da ta ce da ita" bana son iskanci Najeeba, ai so muke mu ga iya gudun ruwansa, zaki bani hadin kai na gaskata maganar da ya yi cewar baya son bak'ar fata ko zaki ci gaba da shirmen nan ne wai? "
Yawu ta hadiye da kyar kafin ta dan duka ta dauki wayar dake kidan
A hankali ta dorata saman kanta ta tataro dukan jarumtarta ta yafawa kanta
Irin wakar nan ta falguni da suke rawa da abu a kansu, sai kawai ta dan wara hannayenta ta ci gaba da rawar nan da iya kugunta ta juyi gare shi
Baki daya ya kwalalo idanniwansa yana kallon ikon Allah, a hankali ta ringa matsowa kusan shi tana mai bin wakar nan a sanyaye sannan da hannunta na dama tana mai nuna masa kan ya matso gareta tana dan tare wayar kar ta fado da kanta bata sana hannu ba hakan ya sa idannuwansa ke yawon binta du inda ta dan juya, uwa uba da gaya sai kawai ta dan juya ta kara kada mutanen da kyam sai ya bi su da kallo sannan ta juyo har ta idasa zuwa daf da shi
A hankali ta dan kara tsayinta ta yo dadage duda bata kamo tsayinsa ba sai kawai ta dora yar yatsarta tun daga saman goahinsa kamar yanda ya yi mata a jiya ta shiga yawo da ita har ta kawo wajen lebunnansa, a hankali ta zazagaya lebunnan nasa sai kawai ta saka dayan hannun ta dan kamo bayan keyarsa ta yo kasa kadan da fuskarsa
A hankali ta kusanta tata fuskar kusa da tashi, baki daya ya sakankance ya gama shiryawa harta da bakinsa ya saki tsabar masifafen mamakin dake shirin kaishi kiyama bai shirya ba sai kawai ta kawar da lebunnanta daga daf da fuskar tasa ta mana masa peck a kunci sannan ta yi wani irin zabura ta yar da wayar a nan ta shige bayi a guje wanda a lokacin da ta yi hakan bai san inda kansa yake ba ya sakankance ne jira kawai yake
Baki daya ya kara kwalalo idannuwansa, murya a shake ya bi inda ta shige da kallo
Hasbunnalahu wani'imal wakim ya fada a bayane yana dafe kirjinsa dake wani irin dokawa fat fat fat tamkar zai ballo ya fito masa
A hankali ya ja kafafuwansa da sukai masa nauyi ya karasa kusa da bayin ya dan dora kansa a jikin kofar, muryarsa cen ciki ya ce" open the door Beebah "
NAJEEBA ta dan zaro ido, sai kuma ta makale kafadunta kamar yana ganninta tama ki yin magana kwata kwata
A sanyaye ya kara furta" plz "
Bakinta ta dan tabe , sam ta ki nuna da ita a wajen
SHAHEED ya kara dora kansa sosai , muryarsa na kara bacewa sai sanyin dake neman lulube shi , hannayensa na bari kadan kadan ya dora saman abin budewar muryarsa har rawa take ya furta" kina son kashe ni ne? "
Tabatawar da ta yi ta kile kuma ta bar kys din a jiki ya sakata matsawa ta cire pant dinta ta haye masai abinta ta gyara zamanta
SHAHEED ya dora hannunsa da dan karfi ya ce" ki bude min BEEBAh, ki bude min kar ki ilatani i beg u "
Dan idannuwanta ta zaro jin muryarsa ta fara baci, ta kara gyara zama a hankali ta ce" ehem "
Irin gyaran muryar nan idan kana bayi
SHAHEED ya lumshe idannuwansa yana jin yanda kansa ke sarawa haka kuma bugun zuciyarsa na kara girmama, a sanyaye ya ce" idan har na shiga bayin nan, sai nai maki fila fila BEEBAhhhhhhh "
Bakinta ta tabe tana kara kallon wajen da ta kile ta ci gaba da neman uzurinta ah tom
Ransa a bace ya budi baki da karfi ya ce"
Oh gidan nan, jama'a wani dan abu ne ya rike ni😭😭😭😭🙄🙄🙄
[31/03 à 22:01] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
59
Ransa a bace ya budi baki da dan karfi ya ce" BEEBAHHHHHHHHHHHH "
Sai da ta dan zabura a hankali ta ce " Um? "
Shaheed ya dan sasauta muryarsa ya ce" Bude min kin ji? "
NAJEEBA ta makale kafadarta, a hankali ta ce" to ban gama ba ai "
" Me kike yi? " ya tambaya idannuwansa a lumshe
Ido ta zaro, sai kuma ta shiga guna guni Kasa kasa ta ce" kuma sai kawai na ce maka ga abinda nake yi fisabililahi SHAHEED , to wai idan na fitoma me zan maka ne da sanyin safiyar nan? "
Shiru ya yi, shiru mai dauke da ma'anoni, sannan yana sauraron irin yanda zuciyarsa ke doka masa dan wani takaici
A hankali ya juya ya shiga jan kafafuwansa yana dan dama bai shigo dakin nan ba, da da ya ji kidan nan daga kofa ya tsaya ya yi magana, aman sai kawai ya wani shigo kansa tsaye
Tabas shi din ya jima da yin aure, ya jima da sannin mace, sai dai fa wani baban lamari na rayuwarsa a kalmar mace ba wai macen da zai yi wasa da daria da fahimtar junna da komai bace, aa , shi ya sa a yanzun da wannan yar ta AMMI ta masa wannan lamari sai ya shige shi ba haufi,
Ya jima yana kai kawo a dakinsa kafin ya nufi bayi ya shiga kintsa kansa domin kuwa zai je fada ne yau su yi zama na musaman da baki daya fadawa , zaman da ya saja kowa ya amsa kira a kan lokaci idan ba haka ba komai zai iya samun wanda bai amsa kiran ba daga hukuncin cikin fada
Sosai ya sha shirinsa ya bayana dawisunsa sai baza kamshi yake abinsa duda dan haushin yar gidan AMMI da ta rikita masa lisafi da sasafen nan, lebensa na kasa ya cije yana kallon kofar a ransa ya ayana 'zaki yi bayani ne' ya yi kwafa ya ci gaba da tafiarsa hankali kwonce ya fice
Najeeba kam sai da ta tabatar sahu ya dauke sannan ta sauka ta yi wankanta tsaf tsaf abinta
Akwatinta ta buda ta ringa dubawa da kyar ta samu atampa sket da riga, du sai aka zuba mata wasu manyan kaya shada, lesh, da alkyaba, sai kayan baci, da kyar ta iya ciro atampa
Wajen turaren nan ta koma har washe baki take ta dildila abinta a jikinta sannan ta saka riga da sket dinta suka zauna dasss a jikinta
Zuwa yanzun tafiarta ta daidaita sannan ta samu nishadin safiar nan abin ba'a cewa komai hakan ya sa ta kashe daurin zarah buhari mai hade da ture ka ga tsiya sannan ta zauna da wayar ta danna kira
ZAHRAU kamar jira take, cikin kamilaliyar muryarta da a yanzu ita take magana da ita wa kowa ba sai iya mijinta ba ta amsa salamar NAJEEBA
NAJEEBA ta ringa mata daria tana fadin "Aunty ba salama, hala wai ko kayanki baki dauka ba? "
Zahrau ta yi dariar itama dan a yanda take shakiyancin sai da ta sakata dariar dole, ZAHRAU ta ce" ke ina Ummu suke ? "
Najeeba ta ce" yanzu zan tarda su mu yita ta kare, rabonsu da ni tun da na farka na ganni a dakin SHAHEED, shine basu leko ni ba, ba waya har yanzu, irin sun manta da ni din nan ko sun goge ni a layin kanwarsu ko? "
ZAHRAU ta ce" NAJEEBA yaya Sultan din ne kike kama sunnansa kai tsaye haka? Idan ya ji ki zaki yabawa aya zakinta "
Najeeba ta yi yar daria , aman bata sanar mata sirrin abinda ta gama masa yanzu ba, sai dai kawai ta ce" Ba abinda zai min domin ni a Shaheed na san shi, ya buga kwalo da ni, ya ci namana , ya kwacen ice cream dina, dan haka sunnansa SHAHEED "
Murmushi ZAHRAU ta yi itama, a hankali ta ce" Ke yarima fa yana aeroport, kuma su UMMU basu sani ba, hasalima ko mahaifiyarsa bata sani ba, mahaifinsa dai ya sani sai kuma ni, jiya har kusan karfe goma ya nemi izinin son ganninsa, to yana bangarena shine ya same mu a nan ya duka har kasa ya kara neman gafara sannan ya nuna ya gaji, ya kasa iya hakuri , shifa ba abinda ya zuba a jikinta da za'a ce sai an ga idan bata da komai na wata uku, shi a bashi matarsa , yana son ya kara neman yafiyarta gashi ga ita, tabas tana amsa sakonsa ba laifi yanzun aman shi ba haka yake so ba, magana sak yake so su ringa yi ta fahimta, shi kam a bashi damar zuwa zance , Walahi Najeeba baki ji yanda kunya ta titsiyeni ba, aman mahaifinsa sai ya ringa sakin murmushi harda su gyara zama ya wani ce" ka je abinka, ka lalabata Allah ya sanya alkhairi " , maganar da nake maki dai yanzun yana aeroport shi ke jiran jirgin da zai yi damagaran da shi, yau babuma jirgi fa aman na sojawa zai bi tsabar ya saka rigima a ransa "
Murmushi NAJEEBA ke saki tana dan dage girarta, ta ce " muna jiransa, yanzu kuwa zan je na same su , baki san wani abu ba, ashe amintace maci amana ne ?"
Ai kuwa Najeeba ta kora mata labarin yanda aka yi, wanda hakan ya matukar girgiza Zahrau, ta yi mamaki sosai, sannan ta masu fatan shiriya, ta jinjina karfin sarautar garin damagaran da rashin tsoron SHAHEED da ya iya yanke hukunci a kan yar sarki, jikar sarki kai tsaye haka, ta ji tausayin NADIA matuka, harma ta baiwa kanwarta shawarar dan Allah kar ta yi fada da Nadia
NAJEEBA ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba har suka kashe
Sai bayan sun kashe ta yi shiru tana nanata sunnan Nadia a saman lebenta
Bakinta ta dan tabe ta mike ta dauki hijab ta saka ta kashe komai ta nufi bangaren AMMI hankali kwonce ko kari bata tsaya dubawa ba da ake ajiyewa karfe takwas
Ai kau tana zuwa ta tarar da su yau a saman cafet suke sunna cin abinci hankali kwonce
Gaishe da iyayen ta yi cike da kulawa suka amsata, ta cire hijab din ta yi wuli da shi saman kujera ta zauna hankali kwonce sannan ta zuba abinci a plate ta kai dubanta wajen yayunta ta ce " An gaishe ku "
Daria suka saka kasa kasa jin irin gaisuwar nan ta bosawa wai An gaishe ku
Sai dai basu gama dariar ba, da murya na yi mata rawa ta ce" iiina kwana NAJEEBA "
Da mamaki Najeeba ta kaleta, kaikaikai Nadia ce ke gaisheta? Me hakan ke nufi? Sai dai bata nuna wani abu ba saima kallonta da ta kara yi
Murmushi ta sakar mata ta ce" tsakaninki da Allah kunyar su ce ta sa kika gaida ni ko kin haukace? In ba iskanci ba Nadia yau kuma ni zaki gaida? Tunda Allah ya halice mu baki taba gaida ni ba, kin ga bana son iskanci ni walahi "
Murmushin ne itama ya kubce mata, harda sauke ajiyar zuciya ta samu kanta da kai lomar abincinta wanda tun dazu ta kasa ci hankali kwonce sai jujuyawa take
NAJEEBA ta ce" yaya kafarki? "
Nadia ta amsata har wata kwallar farin ciki na son zubo mata ta yi gagawar kokarin mayar da ita gannin hararar da ta wanka mata wace ta tabata ta kwalar ce
Kamar daga sama UMMU dake murmushin farin ciki ta ji NAJEEBA ta ce" wai lafia yau Mama ta yi wannan kwaliyar harda saka jan baki ko ni daya na fahimta? "
Ummu ta zaro ido ta ce" NAJEEBA ina ruwanki? "
Ai kau Ummulkhair da yake itama yar rigimar ce sai ta shiga kilkila daria ta ce" ke yau ne fa, ai na fada maki kin ga shadar da Abih ya saka yau tun karfe shida ya zo gidan nan"
Najeeba ta zaro ido, UMMU ta rankwashi kan Ummulkhair ita kuwa ta rike kan tana kwalkwal da ido, yan uwan kuwa sunna ta kilkila daria
AMMI ta ce" wato yau ku duka kun takan dokar cin abinci ko? Najeeba zaki min shiru a wajen nan har cikinki ya koshi kafin ki min surutu"
Shirun sukai aman Najeeba sai sauri take ta gama
Tana gamawar ta dauke plate din ta kai shi kicin ta wanke ta ajiye ta fito
Tun kafin ta zauna ta shiga ratabo abubuwan da ta zo da su, maganar zuwan Yarima, fadan a kan me basu lekata ba, tambayar yanzun wace makaranta yar uwarsu take domin ta tafi school, ta idasa da fadin ya dace su kira makadin da zai masu casun auren soyaya
Yanzun kam AMMI din ce da kanta ta kilkile da daria ta dauki dan filow din kujera ta jefawa Najeeba ta ce " ja'ira "
Ummu kam wata irin kunya take ji, wace da safen murje idannuwanta ta yi tasss ta fito abinta aman yanzu NAJEEBA du ta sakata jin wata irin kunyarsu walahi
....................FADA................
An gurfanar da sarkin Bulala dake rusar kuka tamkar ransa zai fita yana magiya da fadin shi bai taba yarda da maganar kisa ba
Sabon sarkin dogarai ne ya doke bakinsa cikin wata irin razananiyar murya da tsoratarwa ya ce" tuf, rufe mana baki maciji! Yi mana shiru mai fuska biyu, da na halak baya cin duduniyar uban gidansa koda kuwa za'a karsa idan bai bada hadin kai ba, tunda har ka rike shi ka kasa fada mar Sarkin Damagaran ai mai sauraronka ne, na so ace a nan za'a bara min kai da ka bambance horo shashanci "
Kara hade hannayensa yake yana rusar kuka da magiya,
Shaheed ya dago idannuwansa daga yannayin zamansa na saraki ya sauke dubansa a kansa, irin yanda suke nema masa aduwa da sauransu , suke fatan Allah ya huci zuciyarsa du gasu a zube a gabansa sai ya dan juya kai cike da haiba ya ce" Na yafe maka "
Baki daya mamaki ya saka su dagowa, bai kasa da gwuiwa ba wajen furta" ku daina hantararsa, ku daina wulakanta shi, ku bar shi da halinsa "
Da sauri sarkin Dogarai da yake wani irin jibgegen katon da ya ninka amintace a kirar da kamar mazan da dakiyar ya kai gwuiwarsa kasa ya hade hannayensa , cikin wata zaburariyar muryarsa ya shiga" Adali ne, dan halal ne, shi daya ne tak irinsa babu, Gafara dai malan dan malan jikan malan, gafara dai mai gida mai dawa, mun yarda cewar a saman hanya ka kwana, mun ruguje mai sauko min mangari mai harara, takawarka lafiya bijimi uban gaya, ya karba ya gode, Allah ke kare gabanka da bayanka, sannu sannu sarkin sarakuna, mai dogarai a baba dogarai ya gaishe ka ubana "
Da kansa yake amsawa har aka kama sarkin bulala aka fitar da shi daga fadar
Zama aka kara yi , zaman da aka gabatar da nasiha mai ratsa zuciya, aka gabatar da sharuda masu girgiza munafuki, aka tashi a kan magana daya cewar du wanda ya taka doka zata taka shi!
Daga nan masalaci aka shige dan gabatar da sallah, bayan an gama ne aka mayar da auren NANA MARYAMA UMMU, DA ABIH WATO ELHAJ MUTALAB gaban dubin jama'a ciki harda yayan Mardiya da bai san da zancen ba, suka hadu kuwa suka ringa taya shi murna domin sam hakoransa sun kasa rufuwa murmushi yake abinsa hankali kwonce
A lokacin da SARKI ya mike sunna dan takawa da kimah, dogarai na tafe da lema baba wasu da bulalai gaba da baya sunna tafe a hankali, haka kuma masu kira na yi Liman ya ce" ALLAH ya taimake ka, sai nake gannin kamar bai dace a saki sarkin bulala na da haka a cikin gari ba, idanfa ya kara aiwatar da wani cutar ta hanyar hada baki da wani a cutar da kai? "
Sai da SHAHEED ya kara taku kamar biyar sannan ya dan ja ya tsaya,
Hannunsa mai dauke da zobunnan azurfa biyu na dama ya mika ya kama hannun Liman cikin rawaninsa, a sanyaye ya ce" ALLAHN da ya fargar da ni kan wannan yinkurin cutar da ni din da suke, shi zai kuma kare ni Liman, na tabata ba abinda ke samun bawa face wanda Allah ya hukunto masa, ban raina mutun ba, na san ba abinda mutun ba zai iya shukawa ba, sai dai kuma na yarda cewar akoy wanda ya halici mutun, shi yasa nake kai masa kukana kan ya hanna, ya kare, ya kuma kiyaye jinnin ALIYU "
Murmushi ya yi yana gyada kai, ba shi ya juya ba hat sai da suka karaso kusa da bangaren Ammi sai shi ya ja ya juya, aman kuma a lokacin Yarima ya iso, hakama da manyan mutanen da suke tafe dan su shigo su yiwa AMMI ALLAH sanya albarka
Kasancewar shine a gaba sauran na take masa baya , sai da ya fara saka kansa
Sai dai maimakun ya bada hanya jama'a su samu shiga sai ya juyo ya yi tsaye a kan kofar ya kasance mutanen suma du suka tsaitsaya sunna kallon sa
Sarkin dogarai ne ya karaso ya duka sosai ya shiga tambayar ko da abinda ya manta ne a je a dauko? Sai dai bai ce uffan ba, hasalima lebensa na kasa a dan dantse yake ya yi shiru bai bada amsa ba
Gannin haka ya saka sarkin digarai mikewa ya shiga salamar mutane, yana mai fadin sako zai ishe GIMBIYA