Showing 15001 words to 18000 words out of 228147 words
Chapter 6 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
sauran likitocin da kuma masu tsaron kofar urgence din alkhairi wanda suka ji dadi sosai harma suka shiga bayanin ko shi waye cewar yan uwan sarki ne fa, kowa kuma ya san waye sarkin wanda idan ka samu kadaicewa da shi ka warke da izinin Allah
Sunna zuwa gida tun a hanya ya yi waya cewar a kawo masu Burger adadin da ya san zasu koshi kafin ya karasa shiga da motar
Talabeta ya yi a jikinsa har suka karasa shiga cikin falonsu sai kara kwontawa take tana raki tana rigima shi kuwa sai sannu yake mata tamkar ya fashe da kuka
Sunna shiga hankalin yan uwanta dake zaune ga abinci da yawa sun kasa ci sakamakon jin shiru yayunsu uku basu dawo ba wato DAYABU, NAJEEBA, DA ZAHRAU
Gannin Najeeba langwabe tana kara sakin kukan tabara ya saka su tashi a firgice sunna rige rigen karasowa wajensu
Hankalinsu tashe suke tambayar me ya sameta, ahin ko accident ta yi? Ita kuwa sai kara lafewa take a saman kujera baba ta ki amsawa
Abincin da aka kawo ya kalla
Bakinsa ya tabe ya tambayi ummu kamar haka" ke ummu wa ya kawo abincin nan?
Sai da ta tabe bakinta itama ta ce" mai gidan ce ta kawo
Bai ce komai ba sai zama da ya yi ya shiga balo maganin Najeeba ya amshi ruwan da Bilkissu ta dauko ya bale ya mika mata
Fuskarta ta yiwa takwaf takwaf hakan ya saka shi fadin" Najee, kin ga ki amshi magannin nan walahi idan kuwa ba haka ba zan dura maki shi katuwar banza kina yin amai kuma zan kara maki wani
Rauda ta ce" ya wai me ya sameta ne? Ko ciwon cikin ne? Na ga kuma ai ba karshen wata bane
Yayansu ya ce" a wajen basket aka daketa ta summa
Ido du suka zaro kafin karaminsu mai shekara bakwai ya bushe da daria ya ce" yaya an rama min dungure min kan da ta yi a school
Hararansa ta yi ta ce" NAJEEB zan wanka maka mari
Da tausayi kulsumu ta zauna gefenta tana dafa gefen wuyanta ta ce" wani dan iskan ne ya dakar min ke bayan ba'a dukan min kanwata
Langwabewa ta yi a jikinta ta saki shashekar kuka ta ce" bako ne, kuma walahi na daku baki ji yanda har yanzu nake juwa ba, ya kashe min kwayayen haihuwa
Khairy ta kai hannunta ta buge mata baki ta ce" shegiyar banza mai mugun fata, idan ya kashe maki kwayayen haihuwa ni ba sai na rike mar makogwaro ba?
Yayansu da ya shigo da manyan ledojin burger ya ajiye inda yaran suka fara tsale, sufa a dasha dan du idan manyan sukai fushi haka ake koda yaushe zasu ringa cin dadi ne, duda na gidansuma mai dadin ne aman kun san irin gashin nan na waje mai tonka akoy motsa kunne (aminiya kawar arziki maman jaririna ga kaza🤣🤣🤣)
Dubansa ya kai wajen magannin gannin bata sha ba ya saka shi yin wajen da sauri da niyar dauka ya dura matan
Sai dai bai kai ga karasawa ba Zahrau ta shigo da gudu tana kuka sama sama tamkar ranta zai fita
NAJEEBA dake langwabewa tana kamar ba zata iya tafia ba tana raki ita ta fara zabura ta yi wajenta hankali tashe
Baki daya suka zagayeta sunna tambayarta meye ita da, wa ya mutu, me aka yi take kuka?
Cikin wani irin kuka tamkar zata sike ta budi bakinta ta ce" *wai wai wai an fasa aurena*
Ta karsashe tana mai kife kanta a kirjin NAJEEBAR da ta fara karasowa sannan ta fi kusanci da ita a durkuahen da take
Shin kuna so? Idan kuna so ina comment ne mai nunan kuna bi? Free ne mutanena ku zagine mu je tare 😄😄😄😄😄
[31/03 à 21:34] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
7
A hankali NAJEEBA ke shafa lallausan gashin yayar nata da dan kwalinta ya fadi sakamakon kukan da take shekawa
Du a firgice suke, aman sun rasa wace irin tambaya zasu yi mata
Hannunsa ya saka ya janyeta daga jikin NAJEEBA ya jata saman kujera ya zaunar da ita sannan ya shiga sintiri
Baki dayansu suka koma suka zazauna
Yar budurwar cikinsu mai shekaru goma sha biyu ta ce" shikenan yanzu anko din shada da lesh da komai din da akai mana an fasa auren?
Hararanta Bilkissu ta yi hakan ya sa ta yi shiru ta rafka tagumi cike da zulumin an fasa aure shikenan ba zasu yi sabga a gidansu ba
Hannayensa da yake hadewa yana kara budewa ya kuma hadewa ya ce" wani irin ya fasa aurenki? Wani abu kikai masa?
Tana kukan dai ta ce" aa, dazu ne da ya zo yake tambayana wai me ya kaimu gidan sarki ne? Sai nace masa ziyara
Shine ya ce min" Zahrau karya kike, ashe abinda momy ke fada min gaskiya ne? Ku dangin jaraba ne baku da aiki sai masifa da fada? A gaskiya zahrau ba zan iya auren macen da ta kai karar ubanta aka bashi laya ba, kuma a gaban mutane kanwarki ta mari matar ubanku maimakun ku horata sai kuka tare mata fada, to gaskiya wace kika shakar nan aminiyar momy ce kud da kud, da ita aka kawo kayanki ita ta je tana kuka ta zayanewa momy komai ashe ku dai dangin jaraba ne?
Ummulkhair ta zabura ta mike ta rike kugunta ta ce" mu ne dangin jarabar?
DAYABU ya harareta hakan ya sa ta koma ta zauna tana gunguni
ZAHRAU cikin sanyinta ta ce" nima nace da shi ya yi hakuri, abinda ya kai mu gidan sarki sirrin cikin gidanmu ne, kuma fadan nan da aka yi suna da yawa fa suka rufawa NAJEEBA ita kadai, ta yaya yake so na kyale ina kallo a dakar min kanwata?
Shine shine.....sai ta fashe da kuka tana kara dora kanta a kirjin NAJEEBA wace du ta manta ciwonta jikinta sai rawa yake dan walahi a duniya sun rayu da rayuwar jin ciwon dan uwansu a cikin jinnin jikinsu
Ana fadin maganar dan ubanci a duniya, su basu san da wannan kalmar ba
Sunna fada tsakaninsu fa, aman idan kana son ka ga hadin kai da tsantsar soyaya wani abu ya samu dayansu
DAYABU da hankalinsa ya kara kololuwar tashi ya ce" shi ne me?
Dagowa ta yi tana kallonsa ta ce" shine ya kara kiranmu da jarababu harma yake ikirarin ko Abanna zai bashi hakuri ba zai hakura ya iya zabawa y'ayansa uwa irina ba dan sam ban samu tarbiya ba bare na tarbiyantar da yaransa
Nima raina ya baci shi ne shi ne.....
Kara tsareta ya yi da ido ya ce" shine me ZAHRA?
Ta sada kanta kasa ta ce" shine nima nace masa mu ai du da sauki, shi da yake shege wanda uwarsa ta haifa ba aure bayansama ta haifi uku kannensa baki daya su ba'a zage su ba sai mune zai saka gaba yana ta zagi
Idannuwansa baki daya ya rurubo lokaci daya ya tafa hannayensa ya ce" MAHAMADU rasululahi salalahu alaihi wa salam
Da wani karfi karfi UMMULKHAIR ta ce" kin min daidai, ai walahi da kika kai karshe baki fada min ke kuwa me kika ce masa a kan irin zaginmu da ya saka ki a gaba yana yi ba da sai na dauke ki da mari walahi, dama sam bai min ba mutun ne sai shegen taurin hannu idan zai maki kyauta sai kaf danginsa sun sani
Namijin dake buga gem kuma yana kallonsu a wayar yayansu wato Najeeb ya ce" lalala, ba yaya ya hana karami yace zai daki baba ba?
Yayansu kam dake salalami dubanta ya yi ransa bace ya ce" sau nawa zan maku magana kan koda ranku ya baci ku ringa tauna magana kafin ku fadeta? Yaya zaki masa gori Zahra dan ya zage ki? Ke baki da bakin rama zagin da ya maki koma wani kala ne aman banda irin wannan gori? Shin shi ya saka mahaifiyarsa haihuwarsa haka ko me? Ko ke kina tunanin an maki albishiri din zaki gama da duniya lafiya ba tare da wata jarabawar da zaki ringa jin kunyar kanki ta same ki ba? Ina gannin kece mai hankalin cikinsu aman sai ki bani mamaki har haka? Na tabata da Najeeba ce da ake gannin ta fi ku rashin hakuri ba zata yi haka ba sai dai ta cire masa bakinsa dan gobe kar ya kuma
Sanyi ya yi gannin du sun zuba masa ido shi kuwa yana fada sama sama
Yatsarsa ya dago ya shiga nuna su daya bayan daya ya ce" ku yi kokarin gannin kun rufe naku sirrin,
Ku sanni, bana so, bana son ku kasance masu izgili da kuma son daga fitina a duniya
Domin kunada baban tabo
Kuna tare da baban tabon da mai tabon kansa bai san na san yanada tabon ba
Bana son abinda zai taba min nasabarku
Bana son a fara da haka a kanku cewa ana fasa aurenku
Bana so abin ya yi nisa
Wata iska mai zafi ya furzar yana kallonta ya ce " to in ba rashin hankali irin na dan fari a wajen uwa ba me ya kaiki buda baki ki yi wannan shirmen?
Ita dai kukanta ne ya tsaya a lokacin da yake bayannin suma sunnada sirri, tabo! Wannan kalmar sau uku kennan tana jinta daga bakinsa idan ta tsare shi sai ya nuna sam shi ba wani abu yake nufi ba yana nufin dai ita mace ce ya dace ta kasance mai taka tsantsan
Baki Najeeba ta tabe tana hade mata gashinta
Ta riga ta shaka, ta shaka iya wuya hakan ya sa ta kasa kida tofa ufan ne sai irin yanda take ayanna yanda zata yi da shi
Ummukulsum ta ja tsaki ta ce" shine kike kuka? Kike kuka dan namiji yace ya fasa aurenki? Da me kuke jira ku a duniyarmu? Koda mun yi auren za'a sako mu ba tare da an waiwayemu ba, idan mun fito da ciki za'a irga mana ranakun haihuwarmu muna haihuwa za'a dauke dan a kaishi nesa da mu
Me kuke jira? Me kuke tunani a rayuwarmu? Yanda ya yiwa y'ayan wasu, yanda ya ringa wulakanta y'ayan mutane yana saki a kan dalilinsa na son zuciya dole sai muma an ringa sako mu ana laya masa zawarawa,
Dole sai mun cika masa gidan nan mun tsufa tare mun mutu tare......
Wani gigitacen marin da ya sauka a kan fuskarta wanda ya tsorata yan uwanta ya saka su zabura sunna kallon wanda ya yi marin a firgice ya sakata dantse harshenta har jinni ya fito na walaha
Kafin su yi wani abu ya warci igiyar cajin dake ajiye ya shiga laftar du wanda hannunsa ya kai...kun san balarabe idan ya tashi dukan yaro yakan yi masa duka kamar zai kashe shi
Mahaifinsu baya duka a banza, aman du randa hannunsa ya daga sai ya daka
Da wani irin tsinanen gudu DAYABU ya warci kananun biyu ya fada dakin NAJEEBA wace ta rigayi kowa guduwa
Yana shigowa suka dantse kofar wanda hakan ya saka uban nasu dukan kofar ransa bace yana jijigawa
Ransa a matukar bace ya ce" bude min, marar kunyar banza marar kunyar wofi, bude min ki fada min maganar banza a gabana
Ummu ni ne zaki yiwa fatan na maku aure a sako ku? Kennan ni jarabawar sake saken mata ba zata iya samuna ba ko? Zahrau shine kika zagar masa uwa kika ce masa shege?
DAYABU shine ka saka su gaba sunna munanan kalamai a kaina ba zaka tataka su ba?
Khairy shine kina ji ta zagar maki uba baki mareta ba?
Najeeba me ya hada ki fada da dan gidan docter Basheer?
Hannunsa ya saka ya kara dukan kofar NAJEEBA wace ita ta fi kusa da shi kafin ya zame ya zauna a jikin kofar yana sauke ajiyar zuciya
Dawowarsa kennan ya tarar da wanda ke neman auren Zahra da mahaifiyarsa da kawayanta biyu a kofa sunna jiransa mai gadi ya hanna su shigowa sai kunfar baki suke wai sai ta fada masu a inda ta ga ta yi shegu
Dama tun a hanya inda ya tsaya siyan fruits ya tsinci maganar fadan NAJEEBA harma ta summa
Daga cen ya nufi asibiti aka shaida masa yayanta ya daukota an sake su
Shine ya shigi ya tarar da Ummu na fadin irin wadinnan magangannun wai koda sun yi aure za'a sako su ne da ciki ko daga sun haihu a sake su
Idannuwansa ya lumshe ya yi shiru yana tunanin rayuwa
A jiya ya so kwarai ya saki Mardiya, sai dai gannin yanzu y'ayan nasa kansu sun fara fada masa magana a kan auri sakinsa ya saka shi kyaleta domin ba'a taba masa y'aya a wanye lafia
Idannuwansa ya kuma lumshewa yana tunanin inda zai bi ya yiwa tufkar hanci, ya zama wajibi ya katse hanzarinta, ya zama wajibi ya yiwa tufkar nan hanci idan kuwa ba haka ba lale watarana y'ayan nasa zasu yi abinda zasu zubar da hawayen jinni, zasu ja sirrin da yake binnewa ya fito fili
Zasu saka baki daya su tatara su bar kasar a lokacin da suka zama abin kyamata sannan abin gori a cikin kasar nan
A hankali ya ce" ku fito
Du sun ji shi, aman ba wanda ya yi yinkurin fitowa
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa ya ce" ku fito, ba zan daki kowa ba
Zahrau ta fashe da kuka ta ce" ABIH, dan Allah ka yi hakuri
Muryarsa ya dan daga ya ce" magana nake so mu yi ku fito na fada maku ba zan daki kowa ba
Shiru suka kuma yi, wanda hakan ya saka shi sada kansa yana jin zuciyarsa ba dadi
Sam baya jin dadi a kasan zuciyarsa
Karar bude kofar da yake jingine ya saka shi sauri dagowa harma ya mike tsaye ya juyo yana son gannin wanda ya iya fitowa
A hankali ta fito tana matsowa kusa da shi hankalinta a kan fuskarsa
Shima idannuwansa ya sauke a nata fuskar
Lokaci daya ya ji wata kauna irin ta da da uba na mamaye zuciyarsa
A hankali ta daga kanta tana kallon fuskar nasa, idannuwanta da ta gama sannin sunna da effet a kan mahaifin nata koda ya tashi duka sunna saka shi dakawata
ta kara masu girma sosai sannan ta yi masu kwal kwal
Nan da nan kwallah ta cika su, bakinta take son budawa aman ta kasa
A hankali ta shiga kokarin riko hannayensa muryarta na rawa tana son fitar da lafazi ta kasa, sannan hannayen nasama ta kasa rikowa dan sai take gannin sun mata nisa sosai
Idannuwansa ya rintse sakamakon jin wani irin tausayinta ya gama halaka bacin ran nasa
Tsantsar kaunar y'ayansa yana matukar yin tasiri a rayuwarsa
Ko dan sun kasance mata da yawa wa'inda ya dauki son duniya ya dora masu?
A hankali ya kama habarta ya dan dago yana kallon kwayar idannuwanta
Muryarsa ya sanyaya ya ce" kuka zaki yi?
Jin ya sauko hawayenta suka samu damar zubowa tana kallonsa sai a lokacin kuma bakinta ya bude cikin sanyin murya sosai ta ce" kar ka dake mu Abih, ka ga an summar da ni bayan bani da laifi, ka ga ya zazageta dan kawai an fada masa abubuwa
Abih ina zamu shiga mu ji sanyi ne?
Da sauri ya kama hannayenta ya karasa kusan dakinta sosai
Muryarsa ya dan daga ya ce" ku zo gare ni, ku zo kun ji?
Jin irin yanda muryarsa ta sanyaya ya saka du suke budewa sunna fitowa
Du kusa da shi sosai suka zo suka zazauna wasun su har sunna dora hannunsu saman jikinsa
Murmushi ya yi yana kallon ZAHRA ya ce" Zahra, daga yau kar ki kuma zagin mutun da nasabarsa, ko dukiya, koma menene kin ji?
Na gwamace ace da ni gaki cen kun daku da mutun na je na raba da ki yi irin wannan abin, kin san me ya sa?
Kanta ta girgiza tana kallonsa, hakama sauran
Hannayenta ya riko ya ce" abinda ya sa shi mutun ba'a gama halitarsa, baya fasa gannin jarabawar rayuwa har sai ranar da aka saka shi cikin kabarinsa
Eh lale yin fari ne kadara, na biyu ganganci na uku kuwa da gangan
Aman koda y'aya goma ta haifa na hane ki yi mata gorin hakan domin ko ke kin tsufa zaki bar baya kin ji?
Kanta ta ringa gyadawa
Ya maida dubansa wajen Ummu ya yi murmushi ya ce" haba Umana, idan inada mumunan hali ai bana tunanin zaki kulaceni haka, na fi tunanin zaki min adu'a sannan ki yi fatan kar Allah ya jarabeni da ku, wato ya dora hakan a kanku dan na rantse maki ban san wani hali zan shiga ba, ki ringa kyakyawan fata kin ji?
Kanta ta ringa gyadawa itama tana share hawayen fuskarta
Hannun NAJJEBA dake cikin nasa ya kara rikewa yana kallonta, murmushi ya yi ya ce" ni ko dai kece jinnin abuna ba ni ba? Yaya aka yi da wahala safia ta yi dare ya yi baki yi fada ba? Allah ya shirye ki
Kanta ta kifa saman cinyarsa
Ya kai dubansa wajen DAYABU dake tsaye da NAJEEB a hannunsa wanda ya ki yarda ya sauka daga hannun nasa tun da ya tsorata kar aban nasu ya dake shi
Murmushi ya masa mai tsayawa a rai kafin yana kallonsa ya ce" wa ya ce maku baku da wajen da zaku je ku ji sanyi?
Kunada wajen da zaku je ku ji sanyi sosaima
Ina raye, a doron kasa ai zan kasance maku katifar da zaku zo ku kwonta
Tunda shi ya fasa aurenta, dama yana neman hanyar silibe mata ne, da izinin Allah, Allah zai fitar maki da miji na gari
Murmushi DAYABU ya yi gannin du sun dodora kansu jikin Aban nasu
Dan haka ya karasa da najeeb a hannunsa ya ringa dauko ledojin dake dauke da burger din yana kawowa yana ajiyewa
Nan fa suka baje abincin, inda mahaifinsu ya fita ya je ya dauko yar karamar wace ta kai shekara uku a haife wajen uwarta ya dawo da ita bangaren y'ayan nasa inda uwar ta ringa cika tana