Showing 36001 words to 39000 words out of 228147 words

Chapter 13 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10411

rawa rawa

A hankali ta juya ta koma falonsa ta zauna hankalinta tashe tana jiran fitowarsa ta ga idan zai amsa gaisuwarta?...................

Kansa kawai ya dan girgiza ya maida ya ci gaba da jan carbinsa

A ranar NAJEEBA bata fita saloon ba, sai washe gari wajen karfe goma

Ta gama shiryawa cikin tsararan shirinta
A yau riga da sket ta saka na atampa
Bata daura dan kwalin atampar ba sai wani dan kwali ja irin takalmin kafarta da jakarta ta dan yafa a gefen kafadarta

Hannunta dauke da agogo dan siriri yatsotsunta kuwa basu da zobe ko daya

Kanshin turare take bazawa mai dadin gaske ga turaran wuta da ta turarawa kanta sosai take baza dadadan kamshi

Ta zo tsakiyar gidansu ta hadu da yar kanwarta wace ita daya ce ta rage a gidan sauran du sun tafi makaranta masu aiki sun tafi aiki, itama dan karama ce

Murmushi ta saki ta karasa wajen yarinyar ta duka ta dagota tanai mata wasa

Yarinyar kuwa sai daria take tana dora kanta saman kirjin Najeebar

Najeeba ta duba kitson kanta ta ce" heyi an mata kitson nan ya tsufa mu je saloon a tsefe shi a sake sabo

Daga nesa da su kadan ta ji muryar matar babansu na fadin" kar ki daukan min y'ata ta saka ta ringa ramewa dan datin dake jin ki! Ajiye min yarinyata malama

Dagowa ta yi tana kallonta
Ta ga tana fadi ne tana nufota wato zata zo ta amshe yar

Mikewa ta yi da sauri ta sungume yarinyar ta karasa wajen motarta wace ta sha wanki dan da sasafe dan saurayin mai gadin ya amshi kys dinta ya wanke mata ita tas domin Najeeba nada kyauta sosai hakan ya sa kowanensu ke son kyautata mata koda bata nema ba

Cikin motar gidan gaba ta saka yarinyar ta rufe ta koma ta zauna itama ta rufe motar

Sai da ta danne horn sannan ta tayar ta yi baya baya da matsiyacin gudu wanda take hango matar baban nasu na ihun ta bata y'arta aman ta tabe baki ta fita a gidan da baya baya

Gashin kanta ta take birki ta nade shi dan ya fara damunta sakinsan da ta yi sannan ta dauki hanyarta tana tukin tana yiwa yarinyar wasa

Cikin nutsuwa ta karasa kofar shagonta

Sai dai irin motocin da ta gani ya sakata dan yin tsam tana bin su da kallo

Tas ta gane motar dake gaba ba motar kowa bane face ta matar Ambasador domin motar tare ya siya masu ita tata ta siyar dan su yaya ba zasu barta hawa motar kato haka kawai ba

Dama sun taba message da junna inda take mata kashedin bin mijinta har tana kiranta cewa" an koro su daga kasarsu sun zo sun samu arziki sunna bibiyar mazan mutane, abin ai gado ne ga kanwar ubanta ta amshe sarki kiri kiri , ga mamanta ta tafi yawon neman kudi ko karuwanci ba!

Hannayenta ta hade ta dan murza su, ta dauko turaranta ta kara fesawa ta kara gyara girarta sannan ta dauko kanwarta tana kara yi mata wasa ta fito daga motar aman bata dauko jakarta ba dan kayan hannunta sun mata yawa


........cikin nutsuwa take takawa har ta karasa kofar shagon.................

Hannunta ta saka ta kwonkwasa dan a bude mata tana kara kallon kofar shagon ta ga tsaftarsa ta yi mata sosai


Sai da ta yi murmushin dama ke nake jira ta kalli kawayenta ta nuna masu da bakinta sannan ta mike bugudum bugudum bugudum ta karaso wajen kofar ta dora hannunta ta............
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



14



Bude matan da aka yi ya sakata saka kafarta da bismillah ta shiga shagon

Sai dai bata kai ga idasa shiga ba ta ji wata murya sama sama ana tafa hannu aka ce" oyah, gata fa ta shigo, karuwar yar dake zuwa nan ta amshe kudadenku kuma ta raba ku da mazajenku

Da sauri ta dube ta
Duba irin na tsanaki nan ta tabatarwa kanta cewa wannan itane matar Ambasador din

Ko karya na yi maki? Idan karya na yi maki ai sai ki musa ko kunya bakya ji yarinya karama da ke kin mayar da kanki karuwa kina bibiyar mazajenmu

Yarinyar dake hannunta ta kara rikewa dan kar ta fadi tana kallon matar

Zata iya rantsewa idan auren kauye ne matar nan tana iya nakudota ta haifota ba tare da an talafa mata ba
Gata ta wani zama wata kantamemiyar mace ba wani waje dake rabe ko'ina a hade yake
Gaske, shi ya sa mijinta ke haukacewa ko wani dan karamin tabara nata

Fuskarta ta dan yatsine ta juya a hankali ta nufi ciki

Mayafinta ta warto tana fadin" ke dan ubanki ki tsaya min a nan dan ko uban wa nake magana da shi bai isa shigewa ba sai na gama! Zuwa na yi ki fada min karuwancin naki a kan mijina zai tsaya ne ko me?

Da sauri Najeeba ta karasa saka kanwarta ciki ta zaunar da ita ta mika mata wayarta wace bata da wani code ta fito tana janyo kofar cikin

Mai aikinta babar ce ke ta raraba ido hannayenta saman kanta , fadi take" Hajia dama abinda ya kawo ki kennan? Ki yiwa girman Allah ki yi tafiarki kar ki rikita mana wajen aikinmu dan mu aiki muka fito

Wata bagwariya da ake dinkawa atash kuwa ta yi saurin fadin" jesus, wannan yalinya da gaske ne?

NAJEEBA ta dubeta, ta kuma kallon mutanen cikin shagon

Kafadunta ta daga ta karasa da karfi ta warce mayafinta dake hannun matar ta ce" eh haka ne, ni karuwarsa ne, nice nan mai haukata maki miji ya je gida yana ihun kiran sunnan NAJEEBA NAJEEBA NAJEEBA a tare da ke!


Dan ubanki karya kike, ke nan har mace ce? Ina wajen da zai rike har ya haukata shi? Ta fada a zabure

Najeeba ta yi far da idannuwanta ta ce" meye kuwa ba zai rike ya kasa zaburar da shi ba tunda har yake iya banbance sama da kasa, teba da mazaunai? Ke ko jiya a wajena ya raba dare mijinki!

Tabas a jiyan kuwa ya raba daren domin shi dama mutun ne mai yawan yawace yawace ga cika dare a waje, ga uwa uba a jiyan ya nemi Najeebar kamar me dan ya jima wajen shagonta bai sameta

Najeeba ta dora da fadin" kin ga kuwa idan har baka iya kiwo ba, baka iya daure akuyarka ba dole ta fita waje ta ci! Hakan na nufin ba'a karuwa daya shima mijin naki namijin karuwi ne

Abin da ake busar da gashi na kusa da ita ta kinkima wanda ke jikin abin jonawa a jone ta shanmaci NAJEEBA ta tafka mata shi daga gefenta wanda hakan ya sakata yin tangal tangal ta je ta daki garun dake kusa da ita

Ta saurin balaki ta sabule takalman kafarta ta rike guda a hannunta da yake mai dan tsini ne kadan

Da gudu ta karasa ta shigi matarnan da wani irin masifa tana doka mata du inda hannunta ya kai

Kawayenta da suka rakota basu shiga fadan ba sai rabawa da suke, wanda hakan ya fi yiwa Najeeba ciwo gannin mace kusan hudu ta ririketa

Su dukansu kallonsu take , sai a lokacin ta gama fahimtar tare suke mace kusan shida dan hudun sun riketa sunna bata hakuri biyun kuwa sun rike Hajiar sunna tausarta sunna fadin ya isa hakannan ta bari haka

NAJEEBA ta ringa kokowar kwacewa aman du sun saka mundula mundulan hannayensu sun ririketa hakan ya sakata sakin wani irin kukan takaici
A rayuwarta ta tsani tana fada a riketa, ta fi so a barta idan akai mata jina jina zara rabu dan kanta, ta fi so a barta ta ji jiki ko wanda suke yi ya ji jiki da haka raini zai rabu tsakaninsu

Tana ihun kukan take fadin" ku sake ni! Ku sake ni! Idan baku sake ni ba na rantse da wanda raina yake hannunsa kuma kun jazawa kanku fitinar da ba zaku iya dauka ba
Dan walahil azim ko mazajenku kushewa ne a tsufa, ko a masalaci suke kwana tsabar musulunci ya ratsa su, ko mata maza ne sai na birkita lisafinsu, sai na rikita maku gidajen aurenku, sai na fitine ku ba dare ba rana! Walahi sai na koyawa mazajenku cika dare, sai n koya masu bibiyar mata! Sai Na gwada maku bariki iyawa ce!

Dayarsu ta saketa da sauri cike da tsoron kalamanta
Wada ke kusanta ta ce" ke ki riketa mata idan muka saketa zata koma wajen hajia ne kin ga fa ta fasa mata goshinta sai jinni yake

Kanta ta girgiza da sauri ta ce" to ku saketa hakanan mana zaku kama riketa mu tafi, kunna fa jin abinda take fada kuma ni na san wacece ita dan haka ba ruwana

Wa'inda ke tare da hajiar ma sun tsorata da hakan, dan haka suka ringa turata waje sunna fadin kawai ta kai kara gidan sarki a mata tsakani da ita da mijinta kar ta rabata da mijinta haka kawai da y'ayansu

Da wannan shawarar suka samu suka tura hajiar waje

Sai da ta fita sauran suka saketa

Da wani irin masifa ta ringa wawurarsu tana jufansu hakan ya sa du suka fice a guje

Dukewa ta yi wajen tana kukan takaicin bata yiwa hajiar yanda ta so yi mata ba,

Da gudu yarinyarta ta duka tana fadin" aunty, dan Allah ki yi hakuri, walahi talahi ban san abinda ya kawosu wajen nan kennan ba, ki yafe mini ki daina kukan nan

Dago dubanta ta yi tana kallonta

Idannuwanta ta lumshe wasu hawayen suka zubo a hankali ta ce" kin ga wadincen? Baki dayansu sai na saka su a uku! Yanda suka tozartani bayan bani da laifi ko? Sai na tozartasu daidai da laifinsu!

Mikewa ta yi tana goge fuskarta da tissu tana gannin yanda ake ta bata hakuri

Murmushi ta yi tana kallon mutanen dake zazaune ana ta masu aiki aman an dakata sanadiyar fadan ta ce" saloon dina a bude yake daga safe har zuwa dare
Zakunna zuwa nan ne muna amshe kudadenku muna gyara maku abinda ya dace mu gyara! Inaga kun san cewa mace sai da gyara ko?

Ta kara lumshe idannuwanta ta ce" irin haka ke kara min gwuiwar fitowa daga gidanmu
Idan bana samun masu jirana dan su fada min cewa lale ni din wata kwaro ce mai bada wuta a duniya da ba inda zan je sai na boye a daka

Murmushi ta yi tana kara fadin" tawa sallon daukakar kennan kwacewa du wace ta yiwa mijinta rikon sakainar kashi da wace bata tashi tsakiyar dare tana adu'ar Allah kar ya hada mijinta d aalshe money idan dai ba matar aurensa bace

Wata yar daria ta yi tana dage gira ta furta" du Alhajin da ya saki bakin aljihu zan kwasa ne!


Ihu ihu saloon din ya kwasa ita kuwa ta juya ta shige ciki ranta du a bace tana jin haushin irin yanda bata wanwanke fuskar banzar matar nan ba

Zama ta yi kusa da kanwarta ta janyota ta shiga tsefe mata kanta da dabara dan kar yarinyar ta yi kuka, tana tsefe mata tana mata cakulkuli nan ta samu ta ji sanyi a ranta sakamakon wasan da ta ringa yi da kanwarta

Aiyukansu suka ci gaba da yi, duda a darare suke aman sun san da zata yi fushi da su nan take zata yi shi ne
Itama cikin nutsuwa ta gama gyara kan kanwarta ta yarfa mata kannanun kitso ta saka mata tsakiya sukai kyau sosai a kanta ta shinfideta sannan ta saka a kawo mata abinci

Kanta ta fita suka wanke mata tas ta shiga wajen busar da gashi
Bayan ta gama ta zauna babar yarinyarta ta shiga yi mata wani irin kitso manya manya kwara hudu kawai, wanda ake yinsa kamar zane ya tafi baki daya baya
Da yawan lokuta an fi yinsa da atash, Kasancewar tana da gashi sosai sai ake mata da gashinta hakan ya saka kitson ya yi tsayi ya yi tudu sannan ya yi wani irin kyau mai tsarin gaske tamkar ka kwace ka dora saman kanka

Tana gama yi mata ta je ta zauna ta shiga gyara kwontacen gashin dake gaban goshinta tana nanade shi tana gyara shi da gel, a haka har gefe da gefen fuskarta ta gyara shi sosai
Gashin ido ta fitar da wani sabon kala wanda ya fi zama natural, ga tsadar gaske da yake da shi

Zama ta yi cikin nutsuwa ta saka abinta tana kallon yanda yake a idannuwanta

Wata budurwa mai ji da kanta ce ke kallonta tun dazun, ita kanta ta lura da kallon sai ta share dan ba magana ta mata ba gashi kana ganninta zaka gane irin yan matan nan ne masu jiji da kansun nan

Sai da ta gama ta dauki jan baki a cikin kayan mak up din ta shafa kalar lebenta ta juyo

Wauh budurwar ta fada a lokacin da bata shirya ba tana kallon Najeeba
Murmushi ta sakar mata ta mike ta mika mata hannu

Itama hannun ta bata suka gaisa kafin ta dan sakar mata murmushi

Budurwar ta ce" kina da kyau sosai, na yaba

Wani dan murmushin NAJEEBA ta yi mata tana kallon kafarta
Irin sarkar da ta gani da kuma zobe a yatsarta ya shaida mata ko wacece ita
Dan rabata ta yi kusa da kunnenta kasa kasa ta ce" sorry, na haramta bin mata

Budurwar kadai ta ji sai ita da ta fada , tana fada ta shige ciki ta daura alwallah ta gabatar da salar la'asar sannan ta ci gaba da zama da carbinta irin na hannun nan tana dan dannawa a hankali a hankali

Sai da dare ya yi ta dauki kanwarta, ta gama hada kan kudaden da aka samu a ranar ta hada da takardar gidan wuta da ruwa da aka kawo masu ta salami sauran baki daya sannan ta rufe ta yi adu'o'i ta totofa sannan ta tayar da motarta ta nufi gida

A kofar dakin mamanta ta sauketa tana mata byby, yarinyar ta ringa nokewa ba zata je ba dan ba karamin dadi ta ci a wajen Najeebar ba ga wasan da suka yi ta yi na goyo a dakin ga ta bata wayarta ta yi ta dannawa

Daukan yarinyar ta yi ta nufi bamgarensu da ita dan sam ta ki ta shiga wajen mamanta

Sunna shiga ta yi turus sakamakon gannin yayunta du sunna tsaitsaye da alama ita akae jira

Yayanta ne da fada fada ya ce" daga gidan ubanwa kike Najeeba?

Da mamaki take kallonsa ta ce" yaya, daga saloon nake mana ina zan je ni kuwa yau?

Ummulkhair ta ja tsaki ta ce" a saloon din naki ne kuka yi fada yau? Gashi har an kai kararki gidan sarki ga samaci an kawo wai ke kam me ke yawo a cikin kwakwaluwarki na masifa ne? Me ya hada ki fada da matar ambasador?

Gaban goshinta ta dafe a lokacin da Bilkissu ke fadin" aunty, me yasa kika tafi da Nusaiba kin ga mamanta ta yi ta zage zage da fada tana fadin zaki lalata mata yarinya har a gaban abih

NAJEEBA ta ringa gyada kanta a hankali ta ce" inaga sai na sha magannin baki yaya, ka ji fa kowa ni na masa laifi yau harda kai? Yaya to ka san me ta min ne?

Koma me ta maki sai ki duba yannayin da Anmy ke ciki, gashi shara'ar karfe hudu za'ai maku da wahala ace sarki baya nan! So kike a kara zuwa a fada mata cewa gaki cen yauma wata ta kawo kararki? Ke bakya tsoron kur'anin da ake saka maki ya lalata ki ne? Ina dalili wai ke kamar yar agunla?

Bani y'ata! Bani y'ata
Kuma daga yau kar ki kuma daukan min y'ata ja fada maki, haka kawai kin fi karfin uban da ya haife ki ki koyawa y'ata irin fitintinun ki?
Tana fada tana warce Nusaiba dake hannun Najeeba

Najeeba ta sakar mata yar, tana kallonta

Zahrau ta ce" subahannalah, ke kuwa meye hadinki da shiga tsakaninmu da yar uwarmu? Kin taba gannin mun sakota a cikin matsalarmu da ke? Dan Allah ki daina zagar mana yar uwarmu, yau koda Najeeba yanda kike fadi ne ai bai dace ki ringa zaginta haka ba
Kema fa macen kika haifa, kuma kema mace ce, bale kanwata ba yar iska bace walahi, ki fita a harkar shiga tsakaninmu da Nusaiba, Najeeba ba zata taba cutar da Nusaiba ba, na san ko baki daya mun mutu koda dako ne Najeeba zata yi ta rike kanwarta dan Allah ki shafa mana lafia hakannan mana kema?

Sai da ta harareta sama da kasa ta yi daria irin ta wulakancin nan ta ce" wai kililin kasau macijin kumba
Wace ake kawo sadakinta ana fardewa ne zata nemi ta bani shawara? Munanan halayanki sun hana maki samun mijin aure kina wani kumbiya kumbiya ke ga ta kirkinsu ko? To bari ki ji, a tafin hannuna kuke baki dayanku kuma ma rantse maku baku isa ku raba ni da gidan nan ba
Ko a irin yanda na fi sauran iyayenku jimawa da mutumen nan kun san ya mace a so na
Matar ubanku nake dan haka dole a kira ni mama

Ummukulsum ta budi baki zata yi magana da sauri Dayabu ya dubeta duba irin na ido cikin ido

Muryarsa har rawa take ya ce" Mardiya me yasa kike mana haka ne? Yaya kike tunanin cin riba idan har kika shiga tsakaninmu da yar uwarmu? Kin tabata zaki kai girmanta zaki iya tarota zaki iya rayuwa da ita ke daya kin iya mata?

Tana zaro idannuwanta irin masifa na cinta ta ce" eh, ba abinda ya shafeku da y'ata ba domin baki dayanku kun kasance jinnin masifa karku koyawa y'ata

Daria ya yi yana girgiza kai ya ce" haka ne, aman masifar inaga itama jinnin nata ne idan kika yi la'akari da ubanmu ne daya baki daya
MARDIYA, ba dai NUSAIBA ba? Nusaiba dai ce ko? Ki rubuta ki ajiye daga yau daga kaina har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login