Showing 27001 words to 30000 words out of 228147 words

Chapter 10 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10400

aka saba?
Bayan su ke hukunta wanda ya aikata lalata?
Tabas a yau sai ya kamata turmi da tabarya da kansa ta yanda zai yi mata hukunci baki daya garinsa ya sani dan akan baiwa gawa kashi ne dan mai rai ya ji tsoro
Ya san bai isa ya hukuntasu ba tare da huja ba
Zai nuna mata yaro yaro ne, zai bi ta da kansa idan ta kama! Zai yi mata kamun da ba zata musa ba, zai yi mata bulalar nan a tsakiyar gari sannan shi kuwa katon banzan zai haka rami a cikin gari a jefe shi! Baya son zina! Baya son mazinaci

A hankali ya fara jin tashin zuciya yana jin wani masifafen haushinta

Tir da ke! Ke kuwa bayan rashin jin magana sai kika auri aikin da zai rarake ki ya tsufantar da ke a wulakance ya hada ki da cuta ko ya hada ki da tabo? Mace da zata ji, da ta kilace kanta a dakinta komai muninsa dan samun sakamako mai kyau zuwa gaba

Dubansa ya kai kan Ummulkhair

Da hannunsa ya yafitota

Tun da ta ga haka a hankali ta tako ta dan tsaya dan nesa da shi kanta a kasa

Wayoyin saura ya hada ya mika mata yana mai nuna mata ta koma

Da murnar samun wayoyinsu ta juya ta koma kusa da yan uwanta, Najeeba fa nan da nan tsayuwar ta isheta, tun da ta ga wayarta a hannun Ummulkhair sai kafafuwanta suka fara yi mata kaikayi harma ta ringa jin kamar wace take jin fitsari

Ta gaji da tsayuwar iskancin nan da irin duban da su Zagra ke aikawa junnansu da mai martaba da kuma irin kausasashen kallon da mai garinsu ke aika mata na kiyaya wanda ya kara fitar mata da tsayuwar kallon kallon a rai ya sakata a hanakali ta ringa dan matsowa kusa da Ummulkhair

Raf ta kai hannunta saman nata ta damki mai wayoyin wanda tsaf a kan idannuwansa harma ya yi murmushin samun nasara domin dama burinsa ta karbi wayar dan ya aiwatar da aikinsa a yau ba sai gobe ba!







..............more comment aminan arzikiπŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“









[31/03 Γ  21:37] Sadjida: πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»πŸ§•πŸ»


*Na*


*SAJIDA*


πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



11


Sakar mata wayoyin ta yi baki daya ita kuwa ta koma wajenta tana mai ci gaba da tsayuwa irin na yan uwanta

Sai da suka kuma yin magana wace iya su ke jin abinda suke fada tsakaninsu sirikan kafin SHAHEED ya kai dubansa wajen su ZAHRAU
Muryarsa kasa kasan nan ya buda bakinsa a hankali ya ce" ku koma ciki, sarki na godiya

Kamar jira take a salamesu, ita ta fara daga kafarta tama manta da sai sun risina sun kara godiya ta yi gaba a hankali ta shige ciki

Suma bayanta suka biyo sai dogarin dake tafe da wata katuwar ambulope dauke da sako dan nesa da su

A nan tsakiyar gidan suka tsaya NAJEEBA na ta dadana wayarta tana duba sakwonnin da ta bari, irin kirate kirayen da ta samu wa'inda du ba'a daga ba aman an daga na yau na yanzu

Sai tarin messages din da suka cika wajen ajiyar message suma sun cicika wajen wanda ta ringa bi da gagawa tana karantawa

Tsaf ta ga na yanzu an bude shi, kuma ta ga sakonsa

Zahrau ne ta ce" mu je mana meye wai kuka tsaya a nan bayan kun ga da mutun a bayanmu?

NAJEEBA ta waiwaya ta ga Dogarin nan ne

Karasawa ta yi wajensa shi kuwa ya sada kansa yana gaisheta

Murmushi ta yi ta ce" baba dan Allah daga kanka, ku kam bakwa gajiya da wannan gaishe gaishen? Kawo sakon ka koma abinka ka ji?

Da mamaki ya dago yana dubanta jin ta kireshi da baba
Tabas shi din datijo ne, aman kasancewarsa a karkashin gidan sarakan bai taba ji ab kireshi da sunna baba ba
Ko baki akayi in dai sun samu shiga ciki shikenan suma sun samu hanyar wulakanta mutane a bayan idannuwan manyan
Sam sarkin bashi da hayaniya baya anfani da sarautarsa dan wulakanta mutane, aman na kasa da shi sunna anfani da damar nan

Kwarai ya ji mamakin gannin kanwarsa ce, aman ta kiraye shi da baba
Sai ya ji darajar yarinyar ta shiga idannuwansa nan take harma ya sakar mata murmushi yana kokarin risinawa dan godewa

Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" ba dai zaku daina dukawar ba baba sai an jima

Gaba ta yi ta karasa kusa da yan uwanta

Tafia suka shiga yi suka nufi bangaren Anmy

Hat sauran sun samu shiga ta tsaya
Hannun Ummulkhair ta kamo ta saka mata sakon a hankali ta ce" eyah auntyna zan je na dawo wollah bako gareni

Ummulkhair ta yi murmushi jin yanzu kuma ta zama aunty bayan dazu ta gama cewa zata wanka mata mari,
Itama a hankalin ta ce" aman ai kin san ba'a zance a gidannan ko?


Najeeba ta ce" ai nima ba a gidan zan yi zancen ba

Kanta ta gyada har zata juya ta damko hannunta

Tana juyowa ta sanyaya muryarta ta ce" kar ki manta abinda Ya ke fada mana, mutuncinmu darajarmu kin ji?

NAJEEBA ta yi murmushi ta shafi gefen fuskarta sannan ta juya tana kalle kalle kamar munafuka ta kama hanyar fita

Ta jina tana leke har sai da sahun mutane ya fara daukewa sannan ta samu dam dam ta bi ta daya daga cikin kananun kofofin gidan ta fice da sauri

Tana fita ta cire alkyabar nan ta haska da hasken karamar wayarta ta samu waje ta ajiyeta sannan ta gyara lulubin lafayarta ta shiga takawa a hankali tana tafia

Idannuwanta take tafe tana lumshewa dan jin wata sansanyar iska na busawa ta ko'ina

Irin yanda wajen gidan yake da fadi da shukoki abin gwannin sha'awa, nan ne ake gudun dawakai

Tun da ta tunkaro babar kofar fita gabanta ya fara dari dari ta fara tunanin yanda za'a yi su barta ta fita

Wasu irin dafka dafkan mutane ne tsaitsaye a kofar fuskarsu harhada kamar basu san yaren fara.a ko sakin fuska ba

Me zan ce masu dan su barni fita? Ta tambayi kanta tana mai dan ja ta tsaya tana hangensu

Idannuwanta ta kuma lumshewa gannin bafa dare ya cika sosai ba ita kuwa niyarta ta je har saloon dan ko kiransu batai ba ta ga shin idan bata nan zasu iya kulawa da wajen yanda ya dace?

Rufar jikinta ta kara gyarawa kafin ta hade ranta

Tana zuwa ta ratsa tsakanin na faro, ta ratsa na biyu, ta zo na uku ne wata gabjejiyar murya ta dakatar da ita ta hanyar tambayar inda zata je a irin wannan lokacin?

Sai da ta juyo ta kalli mutumen, sarai ta san ya santa ya kuma ganeta dan haka ta masa karyar ba yar cikin gidan bane bama bai taso ba
Dubansa ta yi da kyau ta ce" sako zan karbo wajen Abih da suka fita dan rakiyar sarki

Sannin cewa sarki ya tafi kuma ta tabata mahaifinta na cikin yan rakiya ta samu wannan amsar duda tana da shakun idan har zai yarda

Ga mamakinta sai ya saki abin karewar ya bata damar fita kennan
Hakan ya sakata dan kure shi da ido tana mamaki, sai dai gannin ya hade rai shima yama daina kallon nata ya sakata daga kafadunta har tana ayanna lale gidannan sun fara sasauta tsaro

Shi kuwa tana fita ya juya ya danna kira ya shaidawa mai bayar da tsaron fada cewa eh ta fita

A hankali take takawa tana gannin yanda garin ke walwali idan dare ya yi

Manyan fitilun bakin hanya masu bada jan haske sun gama ko'ina sun haske garin

Motoci da mashin da keke da masu tafiar kafa kowa na kai kawonsa tamkar ba dare ba
Shagunna du a bubude
Shagunnan atampopi ne, na dogayen rigunna ne, na jakunkunna ne abin dai ba'a cewa komai garin nada yannayi mai dadi da tsaro koda dare ya yi

Bata da fito da ko sisi ba, dan haka ta yi niyar takawa a kafarta duda wajen sa dan nisa ta tabata ba zata rasa mai rage mata hanya ba

Wayarta kuwa ta kunna ba zata kiraye shi ba sai ya kuma kira idan yana nan sai ta fada masa inda take idan kuwa baya nan ya yiwa kansa

Har ta gifta tankamemen shagon da ake siyar da kayan kwaliya da su atash da turaruka na yan gayu masu jiji da kansu ta dawo

Da wayo ta ringa hangen ciki
Gannin yau Elhajin ne da kansa ba yaron nasa ba ya sakata hawa yar matatakalar kofar shagon ta tura baban madubin kofar dake kofa ta shiga

Irin sanyi da kamshin yannayin shagon ne ya buso mata baki daya jikinta hakan ya sa ta lumshe idannuwanta sannan ta kuma budewa tana kallon shagon

Bata yiwa kowa magana ba kamar yanda kowa ke sha'anin gabansa yana siye siyensa

A hankali ta ringa bin wajajen tana dudubawa

Abin turawa ta dauka ta shiga bi waje waje tana zabar manyan hodoji da su turaruka masu kyan gaske da tsada tana sakawa

Sai da ta ga an rarage mutanen cikin shagon sosai sannan ta nufo wajen Elhajin tana tura keken daukan kayan

Tana zuwa ta sakar masa murmushi cikin sansanyar muryar nan tata ta ce" barka da warhaka Elhaj

Elhaji dake zaune da katon tumbinsa a gaba shima ya sakar mata murmushin yana fadin" barka dai yar budurwa sannunki da zuwa

Bata amsa ba sai dauka da ta shiga yi da daidaya tana dora masa a saman table din bayan ba nan ake kaiwa ba akoy masu amsa su irga komai su fada maka nawa ne ka biya a zuba maka a leda a raka ka har wajen abin hawanka

Daya daga cikin yaran ne ya taso da sauri yana fadin" Hajia ba nan ake kai kayan ba cen ake kaiwa

Da sauri ta ce" eyah, ban sani ba ai

Hannayensa ya saka zai kwashe kayan sai ya ji muryar Elhajin na fadin" aa kai bubakar barsu a nan nima ai ba wani abu nake ba zan irga mata

Bari yaron ya yo ya koma suka ci gaba da kulawa da mutannen

Sai da ta gama ajiye masa komai sannan ta dan taka karfen jikin kujerar dake gaban table din ta hau tana lumshe idannuwanta

Ajiyar zuciya ta sauke tana yarfe hannunta ta saci kallon Elhaj ta ga ita yake kallo dan haka ta dube shi ta dan yatsina fuskarta ta rage muryarta sosai a hankali ta ce" na gaji sosai

Kamar wani wawa ko yaro karami haka Elhaji ya saki daria yana fadin" sannu hajia ai da kin sakani dauko maki da kainama sai na yi aikin gashi kin sha wahala bayan kin fi karfin shan wahala

Murmushi ta yi tana kara sauke ajiyar zuciya

Muryarsa ya dan daga ya ce" kai dahiru dauko faro maza

Da sauri saurayin da aka kira da Dahiru ya juya ya dauko ruwan faro ya ajiye har biyu a gabanta

Kayan Elhajin ya shiga warewa yana sakawa cikin manyan ledojin kampanin yana yi yana kallon Najeeba wace ta kawar da dubanta tana danna wayarta

Kiran gangan ta kara a kunnayenta ta shagwabe fuskarta sosai ta turo dan lebenta na kasa sannan ta lumshe shanyayun idannuwanta ce" yaya

Irin yanda ta fadi yayan dole ko ke mace ki kaleta harma da sakin baki, domin jan yayan da ta yi sannan ta idasa da wani dan gurnanin kukan shagwaba

Yan kafafuwanta dake jikin table din ta shiga dan bubugawa ta ce" yaya ina kampanin fa, har na zo na zabi abubuwan da nake so ka yi ka zo ka kawo kudin mana......

Ta kasan ido ta saci kallon elhajin, irin yanda yake sakin murmushi baki daya hakoransa a waje hakan ya baiwa kumatunsa damar kara girma, micik micik din idannuwansa suka kara dan shigewa sai dai kamshi kam yana ta fitar da kamshin miski kansa kuwa sanye da huka


Hular dake kansa ya kara turowa gaba yana kallon shagwababiyar yarinyar
Tashin hankali ya furt a kasan zuciyarsa
Yo wannan na sameta nima na koma danye sharaf, dan na tabata idan muka fara wasan yar tserenmu a cikin falo ta dora tabara tana bubuga kafa ta ce sai na goyata

Murmushi ya kara saki ya shiga zube mata kayan a cikin ledar

Gannin haka ya sakata dan zaro ido ta kara fadin" aman yaya kace na fito sai mu hadu kuma kace yanzu an kirayeka wajen aiki? Shikenan ba komai

Yi ta yi kamar ta kashe kiran ta dubi Elhajin

Hannayenta masu tsararun yatsotsi ta hade, bakinta ta kara zumburowa ta kyabe fuskarta ta ce" ka yi hakuri Elhaji ka ji? Ka ga dama a kafa na fito motana ta samu matsala na yi tunanin mu hadu da yayana ya maida ni gida idan ya biya kudin kayayakin nan , sai dai kash ka ji wai an kirayeshi aikin gagawa ka san likita bashi da lokacin kansama

Dan Allah ka yi hakuri Elhaj na bata maka lokaci da tsarin kayan nan

Har yana inda inda ya ce" aa aa, idan yayanmu bai siya ba ni kuwa aikin me nake? Idanma da karin wasu a kawo su nan Hajia ai ke din baba ce

Kikifta idannuwanta ta yi ta ce" ban fahimta ba Elhaj

Wayarsa ya dora saman table din yana dubanta yana murmushi ya ce" ki dora min numberki nake nufo yan mata sannan ki bar maganar wai kudin kaya bayan shagonku kika shigo

Murmushi ta yi a kasan zuciyarta tana ayanna zaka fada ne

Sai kuma ta dan zaro ido tana girgiza kai ta ce" aa aa, ka rufa min asiri idan na je da kayan nan na ce wa ya bani? Yayanmu baya bari bayan nan yaya daga shigowa dan fita da kaya haka? Aa ba zan iya amsar kayan nan ba gaskiya Elhaj

Kamar da wasa sai ga Elhaj na lalabar Najeeba cewa ta amshi kayan nan ba wani yawa kuma ai ita mace ce tana iya adana kayanta a dakinta

Da kyar ta yarda aman tana ta dafe gaban goshi irin ya takurata amsar nan

Cike da kulawa ya kara turo mata wayarsa ya ce" wanenen yayan nan namu mai sa'a a duniya da ya zama yayan wannan kyakyawar shagwababiyar budurwar?

Wayar tasa ta kala kirar samsung ce babar gaske sannan sabuwa ce dal sai walwalin sabunta take aman bata dauka ba ta lumshe idannuwanta tana masa murmushi ta ce" sunnansa Ibrahim Adam , likita ne a baban asibiti na kashi

Kansa ya ringa gyadawa cike da murnar jin hakan, nan take ya kuma tambayarta mahaifinmu fa?

Dubansa ta yi duba irin ja wai Allah? Ta tabata wannan mutumen ya girmi Abih, aman da yake irin abihn ne gashi sai kira yake mahaifinsu sannan Yaya DAYABU yayansu ko me? Oh duniya yanzu du wace ta dan yi masa shagwaba kennan sai ya fada ya karba da gudu gudu shi kuwa?

Sauka ta yi daga saman kujerar tana ganni yaronsa na jidar kayan yana fitarwa sannan tana gani ya saka kudi a leda guda irin kar ta gannin nan ta ki amsa

Byron dake ajiye ta dauka ta duka ta rubuta masa number kanninta Najeeb ta ajiye masa tana murmushi ta ce" na gode Elhaj

Shima murmushin ya yi da sauri ya saka takardar a aljihunsa har ya fara tunanin sauka da wuri yau dan ya je gida ya loda number ya yi kiranta
Gasgi bata fada masa sunnan mahaifinta ba, aman ba komai koma yar gidan waye zai sani kuma shi ba da wasa ya zo ba da girmansa ba zai tsaya bin layi da kannanun yara ba dan ya san wannan samarin na zamani sunna yiwa wannan yar cakwai din layi

Tana fitowa ta harhada kayan ta tsayar da dan adaidaita

Yaron ne ya ce" an ce a kaiki fa

Ta juya ta kalli wanda zai kaitan

Kanta ta girgiza masa kawai ta shiga adaidaita sahun nan

Direct sunnan shagonta ta fada masa sannan ta shiga lalubawa ta zaro kudin nan

Murmushi ya saki tana gannin masu aku biyu wato jaka ashirin cif sababi

Kanta ta gyada tana ayanna" yanzu haka baya fitar da zakah!


Dan sahu na ajiyeta ta bashi kudin nan , nan ya shiga neman cenji dan haka ta amsa ta shige ciki ta saka a kawo masa

Saloon din a cike take , sai aiki ake kuma a tsaftace take dan haka ta ji dadin hakan sosai

Kayan aikin ta bude ta shiga lolodawa abinta wajen kayan siyarwarta, a hankali ta furta" halal na ci

Zuwa ta yi ta zauna lokacin kuma karfe tara ta yi kuma a lokacin kiran ambasador ya shigo wayarta

Bata daga a kira na fari ba sai a na biyu

Zuwa lokacin ta amshi takardar tana duba wa'inda ke son kwaliya

Byro ta amsa ta shiga dangwala ok a kan wa'inda zata iya yiwa a cikin satin nan sannan tana dora lokaci

Sauraronsa take yana ta surutun dan me take bashi wahala ne

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" ka san dai na yi missing dinka a lot ko?

Shima ajiyar zuciyar ya sauke yana jinta

Ta ce" ina saloon ka zo na ganka ka ji?

Tana gama fada ta kashe kiran ta kara fefesa turare ta kara duban kanta a madubi sannan ta ci gaba da kimtsa abinda ba lalene su kimtsa shi yanda take so ba

Bai dauki wani lokaci ba sai gashi ya tsaya a kofar shagon

Mikewa ta yi ta fita

Bude motar ta yi ta shiga, sai dai tana shiga wata ta fito tana kallon numbobin bayan motar
Kanta ta gyada ta koma da sauri ta dauki wayarta tana neman number kawarta

Da gagawa ta ce" kin kade kawata, kin kade, kin san da ambasador ne ya fita daga shagon NAJEE?

Kawar nata ce ta zabura daga zaunen da take tana ciye ciyen naman da aka gasa mata rusheshiyar mata da ita bata da aiki sai ciye ciye, itane matar ambasador kuma uwar y'ayansa uku ta ce" wace najee din? Saloo?

Amsa ta bata cewa" kwarai yanda na gansu haka Allah datar da ni gannin annabi kiri kiri

Ji ta yi zuciyarta ta shiga bugawa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login