Showing 105001 words to 108000 words out of 228147 words
Chapter 36 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
nuna ba za'a iya bugun kirji da su ba a filin daga ba!
Sai da ya kara lashe lebensa na kasa da yake jin a yau ya cika bushe masa kafin ya buda bakinsa a hankali ya ce" a ina kuka hadu da ita? Tana cikin wani yannayi? A ina ta cenza suturar da ta fita da ita?
Baban ne ya kara sada kansa ya nemi afuwa sosai kafin ya kora bayanin abinda suka sanni da inda suka ganta da kukan da take
Komawa ya yi ya jinginar da bayansa jikin kujerar da yake zaune ya mayar da idannuwansa ya lumshe
Da yan yatsunsa ya yi masu nuni cewar su tafi
Da sauri suka kara dukawa kamar zasu kwonta sunna ta neman afuwa kafin su fito daga falon
Kara zubewa Amintace ya yi kansa kasa ya shiga neman afuwar Sultan , domin du horon dogarai na gidan nan a hannunsa yake haka kuma idan suka aikata laifi yana da baban kaso a ciki
Idannuwansa da suka kara yi masa nauyi ya buda da kyar yana kallonsa
Sai da ya furzar da huci mai zafi kafin ya ce" daga yau, bata da wani mai tsaronta sai kai, du inda zata saka kafarta ka saka, du abinda zata ci ka fara tabawa, du wanda zai mu'amalanceta ka hana
Da mamaki kansa a kasa yake amsawa, ya cika da matsanancin mamakin jin cewar shi, shine zai tsare wannan yarinyar? shi rantsatsen mai baiwa Sarki tsaro ne, ko Gimbiya bai taba baiwa tsaro ba baban yaronsa ke bata tsaro aman yau shine aka wakilta da maganar baiwa wannan yarinyar tsaro?
Kara tasowa ya yi daga jikin kujerar yana kara dunkule hannunsa ya kara kakausa muryarsa ya ce" *hukunci zai hau wuyanka ne daga bakin lokacin da ta zile maka ka nemeta ka rasa, shu'uma ce, zata iya shiga duban mutane ka lalubeta ka rasa, hakan zai wanzar da tashin hankali a rayuwarka!*
Yana gama fada ya mike tsaye ya shiga takawa shi kuwa amintacensa kansa a sade a kasa yana fadin" Allah ya huci zuciyar mai damagaram, Allah ya huci zuciyar zaki, namu sarkin sarakaine na gida da dawa, Allah ya kara maka lafia da nisan kwana
Dakatawa ya yi, bai juyo ba daga inda yake ya furta" ka saka a binciki wacece *NADIA MOCTAR a UNIVERSITY*
Daga haka ya shige ciki yana jin wani irin al'amari mai girman gaske dake damunsa
Ta ina zai bi ya horata?
Ya je ya zubar da kansa ya shiga jikinta dan ya samu kusancin da zai kamata tsamo tsamo da laifin da take aikatawa sai gashi a lokacin da ta aminta ta bashi numberta harma suka fara sakarwa junna fuska ta hanyar yin yar doguwar hira da junna shine za'a katse? Shi ne zai auri yarinyar nan, nan da kwana goma?
Kansa ya daga ya kai wajen agogo,
Idannuwansa ya lumshe a lokacin da ya ga har karfe goma sha biyu ta gifta a ransa ya furta *aa ba kwana goma bane, kwana tara ne*
Lebensa ya kara cijewa na kasa yana mai ajiye rawaninsa
Hannunsa mai cike da yannayin karfi ya daga yana yamutsa summar kansa da ta taru wace yake so ya shiga ya aske kayansa da kansa
Idannuwansa ya kuma budewa a kasan zuciyarsa yake furta" da ace kin kilace kanki, da ke din babar harka ce da ba dai yaro ba sai dai baban yaro
Sai gashi kin banzatar da kanki,
Idannuwansa da suka dauki kalar ja dan bacin rai ya kara budawa yana furta"
Zaki zama matana ne, sai dai rayuwarki zata zama cikin kunci
Abinda kika saba da shi, kina ji kina ganni zai gagare ki, sai ya zame maki fiye da zinari domin zaki nema ruwa a jalo ki rasa shi, zan saka maki matakan tsaron da ko dan jaririn namiji ba zaki gani ba bale ki hadiyi yawunki a kansa
Zan kasance maki fitinar da baki taba tunanin zata shigo ratuwarki ba! (Ma ji ma gani)
Sai da ya shige sannan ya dago kansa
Ransa bace ya mike ya fita daga falon yana cike da matsanancin bacin rai
Du darajarsa? Du girmansa za'ace yanzu an nada shi kula da yarinya karama irin wannan?
To wai, meye girman darajarta da za'a nada shi, shi ya bata kula?
Meye tsakaninta da shi?
Sai kuma maganar Nadia Moctar, ta ina zai fara bincikenta? Nadiar nawa ce a cikin University?
Dole zai dauki wayarsa ya yi aikin, tunani yake me hadinsa da wata Nadia?
Wani murmushi ya yi yana girgiza kansa, wani auren zaka sake? Halitarka ba ta mace daya bace,
Kansa ya girgiza yana kara wani murmushin a kasan zuciyarsa ya furta
*Ga fili, ga mai doki*
Idannuwanta bude suke har goshin asuba
Ta kasa yarda cewa itane haka ke shirin faruwa da ita
Ta kasa tsayar da takamaimai abinda zata yi da rayuwarta
elle n'arrive pas a y croire (ta kasa yarda), cewar ita Najeeba, itane haka ke shirin faruwa da ita
Lokaci daya ta ringa da ta sannin rayuwa
Ashe du irin tara samarin nata zata kare a auren dole ne bata sani ba?
Sai kuma ta ji zuciyarta ta raunata, a hankali zuciyarta ta ringa kara rufeta da fada kamar haka" dole Allah ya kama ki Najeeba, ke ce zalinci wancen, yiwa wannan karya, cin kudin wancen, mazan da kika saka hawaye yawa ne da su ashe ke banza bami san cewa haka zaki kare ba? Ta tabata idan har ya yarda ya amshi aurenta ba dan wani bane sai kawai dan ya idasa nufinsa na son kasheta
Wani irin shakarsa take ji a kasan zuciyarta, zata iya rantsewa rabonta da ta shiga harkar matarsa ko shi din kansa tun da ta ganni ido da ido yana rike wuyan maciji harma ya saka yar yatsarsa a wajen bakinsa ya ringa fitar da wani ruwa mai duhun gaske
Tana kallonsa yana kallonta ya yi mata wanka da ruwa masu sanyin gaske bayan ya san tana fama da cutar athsma
A haka, bata yi masa komai ba ina da ta yi masan?
Sai goshin asuba barci mai wani irin nauyi ya kwasheta wanda sam bashi da dadi sai mafarkai mararsa dadi sosai a cikinsa
Da duhu duhu mata shida suka shigo har dakin da yan matan Anmy suke, wa'inda suke saman salaya sun gama sallah aman sun raba adu'a sunna yi dan Allah ya tankwasa yar uwarsu
Saman bed din Anmy ta kai dubanta bayan ta amsa gaisuwarsu
A hankali ta furta" bata yi baci ba jiya?
Ummulkhair ta gyada kanta kafin ta sada kanta
Matan nan fararen larabawa ne, kusan su duka farare ne tas tas sai wani irin shu'umin kamshi suke ga fatarsu kamar ka kali kanka a ciki
Anmy ta kai dubanta kansu a sanyaye ta ce" ban san ta inda zamu fara ba, bana iya yi mata tsawa ko na rufeta da fada, abinda na sani idan ta farka ta ganni zata so tayar da rigima, gashi dole a yau za'a sakata dakin dumin cen da gyara ku kanku ba zaku kuma fitowa ba bale ita sai ana gobe daurin auren, ban san ta yaya zata amince da abubuwan nan ba, ga wajen aikinta, ga ..................
Hannunta da datijuwar ciki ta rike ya saka Anmy sauke numfashi a maganarta tana ta lumshe idannuwanta domin sam bata so ta ga Najeebar a cikin wani yannayi na rashin jin dadi
Cikin harshen larabci ta ce" kin san cewar wannan ranar mun ci alwashinta, muna jiranta ko? Kin fi kowa sannin mun shiryawa wannan ranar ko? Kukanta, ko ihunta, ko summarta ba zai hanna mu wanketa ciki da bai ba, domin kuwa shinfidar da zata taka mai daraja ce! Dole zata koyi rayuwa da yanda zata tafiar da sarkin mu! Mace na iya shanye wuyar nakuda, hawayen da zata zubar sune samun sasauci a zuciyarta! Maganar so kuwa
Murmushi ta yi ta kai dubanta wajen Najeeba dake kwonce ta rungume fillow a jikinta gashinta ya warwatsu ko'ina, rigar aida ce a jikinta har yanzu sai shaf din pant da kafafuwanta masu tsananin hasken tafin kafa da wani shap a jikinsu ta maido dubanta kan Anmy ta kara sakin murmushi a hankali ta ce" lokaci zai nuna mana idan har ta isa ta kaucewa zuciyar *GURNANIN ZAKI*
..................salam alll........
[31/03 à 21:42] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
35
Ajiyar zuciya Anmy ta kuma saukewa ta koma gefe tana kallon su
Karasawa babar cikinsu ta yi ta saka hannunta a hankali ta yi bismillah
Sauran du dukar da kawunnansu suka yi har sai da ta saka hannayen nata cike da kula ta talabo Najeeba
Idannuwanta ta buda a hankali kafin ta ware su da sauri tana kallon matar
A dan zabure ta so mikewa tana fitar da idannuwanta waje sannan muryarta da ta disashe dan kukan da ta sha ta ce" lafia? Menene? Wacece ke?
Bata daina kokarin tayar da ita zaune ba kafin ta mika hannunta a miko mata alkyaba wata iri ta veloor kalar baki sidik
Tana daga zaunen sai zaro ido take matar nan ta rufa mata shi a jikinta ta dora mata shi a saman kanta
A hankali cike da nutsuwa cikin harshen larabci ta ce" a kowani hali shugaba ta farka daga baci ta kiyayi saurin buda bakinta ta yi magana ba tare da ta shiga bayi ha ta wanke bakinta, domin baban abinda zata aikata na bada hanyar da Uban gidanta zai ji zuciyarsa ta hautsine da tashin zuciya shine ya ji warin bakinta, shi kuwa baci idan aka tashi daga shi koda na minti talatin ne baki kan daukan wari marar dadi, irin warin nan na saka ciki ya rikice ko mutun ya yi gagawar kawar da kansa daga wajenka
NAJEEBA ta kara zaro idannuwanta tana gannin wasu biyu sun zo sun hadu sun mikar da ita tsaye, cikin nutsuwa wace du ta fi su yarinta ta matso, sannan kana ganninta ka ga kakarfar mace
Hannun Najeeba ta damka ta kamata ta cicibata suka kama suka dorata a bayanta
Baki hangame Najeeba ke binsu da kallo ta ga an goyeta a baya luf ta aniya neman dirowa da ihu ihu ta ce" Anmy, Anmy meye wannan? Su waye wannan?
Anmy ta matso da sauri tana son kamo hannunta tana fadin" Najeeba, ba wani abu bane zamu koma wancen bangaren ne kin ji? Ki nutsu kar su nutsar da ke
Wannan kalma ta kar su nutsar da ita ya sakata yin wani irin sakalau tana bin kowa da kallo du a firgice
Kara rufa wani zani mai kamshin gaske suka yi a saman kanta hakan ya saka ta daina gannin komai sai tafiar da ake yi da ita
Kwata kwata aka fita daga bangaren Anmy aka yi bangaren da aka tanada domin gyrare gyaren
Dakuna hudu ne a wajen, baban dakin nan suka shige da ita
Mafarin barowar Najeeba daga cikin yan uwanta, mafarin shigarta sabuwar rayuwa mai cike da abubuwan ban mamaki,
A wannan ranar tana ji tana ganni sai da aka tubeta zindir kafin a saka mata wata yar yololuwar riga baka kirin wace aka fara yi mata darzar fatar jikinta da ita
Dakin wani irin dumi ne yake dauke da shi wanda da farko ta ringa zufa sosai sai daga baya zufar ta shanye a jikinta a lokacin da suka yi mata wata irin darzar da ta kusan fitar da ita daga hayacinta
Sosai suka bi lungu lungu na jikinta suka darji fatar Najeeba da wasu irin abubuwa dake dame masu fitar da kanshi abin nan basu barshi iya fatar jikinta ba har fatar kanta sai da suka darza
Da ruwa mai dumin gaske mai hade da ruwan turaren nan mai mugun tsada wato sandal FLEUR aka darwaye jikinta tas
Sabon broch da maclean aka bata ta wanke bakinta sai kakare kirjinta take da kuma kasanta tana biye da su da wani kallon mamaki irin yanda du yanda take neman botsarewa sai su tarota idan ta so nuna karfi sai a barta da wannan matashiyar ta maida ita zaune
Alwallah ta dauro suka fito
Rigar sallar da aka ware aka miko mata ta kabarta sallah cikin nutsuwa ta gabatar
Ta jima kanta a kasa tana hawaye, tama rasa me zata ce? Ta ina zata fara, abinda ta fi fada shine Allah kar ka bari su min auren nan dan kasheni zai yi
Tana dagowa ta yi tahiya kanta sade ta ja carbinta ta gama
Sai da ta gama sannan aka mikar da ita
Rigar tata suka kama mata ta cire hakan ya saka ta tsare su da kallo ranta a yannayin bace ta ce" wai zir zan yi ta zama ne ko me?
Datijuwar nan ce ta girgiza kanta tana kallonta cikin ido ta ce" idan mace zata yi magana, ya kasance ta ragewa idannuwanta tsauri da yawa, irin ta sada su kadan ita bata rufe su ba ita bata bude su sosai ba
Idan maganar fada ce zata yi ya kasance ta sada idannuwan sosai idan ta faro a sanyaye sai ta bude su baki dayansu, bafa daga murya zata yi ba, aa, idannuwan nata ne zasu nuna yannayin da take son isar da sakonta
Hannunta ta saka ta ja Najeeba ta zaunar da ita bakin bed mai dauke da zani mai duhu
Wasu oil ne dake hannunta ta raba zamanta ta shiga tsaga gashin kanta a hankali tana dan shashafa mata shi ta ce" idan kuwa zata yi tambaya ne, ya kasance da kwayar idannuwanta zata dasa question mark din, wato ta yi yawo da su ta dasa su ta hanyar kai kwayar idannuwan nata kasa
Manyan kitso ne ta fara yi mata irin da ake kira zane kwaya hudu ne ta yi niyar yi mata dan haka ta ringa yin kitson a hankali tana lalumata tana tufke har karshen gashinta
A sanyaye ta ce" bale ke din daga yanzu kin zama uwar talakawa, nauyi mai girma ne ya hau kanki wanda yake a wuyan mijinki, zai kasance ke ce mai tarbarsa a du halin da ya shigo maki
Shugaba kan daukan abubuwa, yana shanye duka a waje, yana shanye du wani tashin hankalin talakawansa,
Daga bakin da ya shigo wajenki, sai ki ga ya gaza, a gabanki ne zai iya fitar da bacin ran da ya shaka, a gabanki ne zai iya fitar da tarin yannayi na tausayi, tsoro, ko firgicin da yake hange a tatare da talakawansa wanda hakan zai taba shi sosai, harma ya nuna maki hakin da zuciyarsa take ciki
Ke kuwa *Kece mai shanye damuwarsa*, zaki mayar da shi a gabanki tamkar yaron dake da kiwya kike son ke kuwa sai ya saba da ke, hakan kuwa zai faro daga yannayin idannuwanki
Zaki kasance idannuwanki dauke da haske da kwali, zaki kasance mai sada dubanki a gaban kowa bale a gabansa, zaki kasance mai lumshe idannuwanki a gabansa
Dan saurarawa ta yi tana tsaga na karshe ta ce" sai movement din hannayenki da jikin ki baki daya
Zaki kiyaye irin motsinki a gabansa, ba daga ya nuna maki bacin rai ba zaki tarbi magana da" wa ya isa? Aka yi haka? Ina ba'a isa ba?
Ta hanyar maganarki zaki daukaka muryarki har ki ji maganarki ta girmi tasa,
Daga bakin lokacin da muryarki ta girmi tasa zaki ga ya yi lakwas yana jin zuciyarsa na kara ruruwa yana son kara daukan abin da zafi
Ke din nan, ke ya dace ki sanyaya muryarki ki sada kanki da dubanki
Muryarki ta kara sanyi, ki nuna kin fi shi shiga damuwar da ya shigo maki da ita, a hankali ki nuna masa kowani tsanani yana tare da sauki kafin ki nuna masa cewar idan har yana fadarki, farin ciki mai dorewa shine abinda zai wanzu a tatare da shi
Dago kanta ta yi ta kalli matar, sosai take jin abubuwan da take fada tana kuma anfani da su, idan ta nuna a wanda zata aikatawa ne sai ta yi murmushi karara ta dan girgiza kanta
Za dai ta anfanarwa HUZAIFA, domin ta tabata Allah zai amshi adu'o'inta
Kanta ta mayar ta sada matar ta karasa kitse mata gashin kanta tas sannan ta bi shi da wani man mai dadin kamshi
Mikar da ita ta yi da rigar nan ta jikinta sannan ta kwontar da ita saman bed din
Ji take gajiya sosai na damunta sakamakon irin darzar da aka mata, abu da rashin sabo
Wani hadi ne ta nufota da shi wato APKI da MAN KADANYA cakude da wasu graine kannanu maroon
Hannayenta ta kama ta tayar da ita zaune
Cikin nutsuwa ta ce" cire rigar
Ido Najeeba ta kura mata da mamaki, bata yi magana ba aman yannayinta ya nuna kwari ba zata iya kallo ana ci gaba da wani yi mata zirr ba
Zama matar ta yi da abin a hannunta ta ce" kin san shekarana nawa? Shekarana sitin da biyar a duniya
Da mamaki Najeeba ta zaro ido tana kallonta, sam bata yi kama da wace take da wadinnan shekarun ba
Matar ta ce" wannan din, shine aikina, sannan ban taba yiwa koda yar sarki bane sai matar sarki, matar sarkin ma, sai wace Allah ya yi,
Dan sasautawa ta yi ta ce" SUNNA NA PRINCESSS FADIMATU MUHAMAD, nice yar farko a wajen sarki MUHAMMAD,
Na yi awani a jirgi dan zuwa nan dan mutuncin Mahaifiyarki da kanwar Abihnki
Bani da jiyar juyawa sai na gama abinda ya kawo ni
Kuma lumshe idannuwanta ta yi kafin ta dan buda idannuwanta da yannayin gargadi wanda sam a muryarta babu aman idannuwanta sun nuna ta ce" zaki cire rigar ko na cire maki?
Hannayenta ta saka tana jan rigar cike da mamaki, a hankali ta bada hankalinta kan macen ta ringa gannin yanda take du wani motsinta,
Wannan hadin ta kawo wajen mamanta ta shafa mata a yan mamanta da basu da girma sosai ya kasance ta shafa masu sosai sannan aka kawo wata bra wace ana iya rageta ko a karata aka daure mata su dam
Sakata ta yi ta yi ruf da ciki sannan ta ringa shafa mata shi a wajen duwawunta masu fadi da girma, duda haka ta kara