Showing 213001 words to 216000 words out of 228147 words

Chapter 72 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt

13 May 2025

10417

hagu ya fara takawa tana masa nauyi ama a haka ya ringa janta har ya karasa wajen AMMI dake kuka ido rufe tana maimaita innalilahi wa'ina ilaihi raj'une

A hankali ya dora hannunsa wajen jinnin yana kallon yanda idannuwan yarinyar suke kakafe sannan jikinta ya dauki wani irin sanyi harta da fatar jikinta ta yi fayau

Da sauri ya saka dayan hannun nasa yana gurgusa gashin kanta , muryarsa hade da wani ihu ihun kuka yake fadin" UMMU, wayo mun shiga uku, Ummu ku tare jinninta kar ta mutu, Ummu wayo ta kashe mana kanwarmu, ku kama mana kar jinninta ya kare, wayo Nusaibata, ku tare jinnin nan ya bar zuba kar ya kare AMMI, wayo Abih, Wayo Ummulkhair, NAJEEBA, wayo Bilkissu, wayo Najeeb zo ku tare jinnin kanwarmu na zuba daga kanta"

UMMU dake kuka ta saka hannayenta tana janye nasa, muryarta a ciki dan tsabar kukan da take ta furta" innalilahi wa'ina ilaihi raj'une, Allah ka yi mana maganin masifar da ta fi karfinmu, Allah ka jikan yarinyar nan, ka sa ta huta, DAYABU ka bar dannawa Nusaiba ta rasu fa baka gani ne? "

Qi kamar wada ta kara rikita dakin, gaba daya wa'inda ke jijiga wa'inda suka summanma sai suka kara rikicewa, Najeeb kam ya rukunkume mahaifinsa ya cusa kansa cikin kirjinsa yana kuka dan shi tsorata ne ya yi da gannin jinnin dake fita daga kan kanwarsa wace shekara daya ce tak tsakaninsu yanzu haka da kokowa suka rabu ta fara rigimar da ta zame mata jiki kwana biyun nan, domin haka kawai zata kama kuka tana dora kanta a jikin du wanda ke kusa da ita, kuma jikinta lafia kalau ba rashin lafia ba ba komai ba, hakan ya sa Ummulkhair ta goyata suka fito falo shi kuwa ya kwonta ya shiga baci

Wani irin ihu DAYABU ya yi, a lokacin da NAJEEBA ta fashe da wani irin kuka hannayenta duka biyu saman kanta tana nuna Mardiya da ta yi wani irin wuri quri hannayenta duka biyu a saman kanta tana maganar da ba'a jin me take fada, ama da alama ta zauce ne dan kuwa magangannu ne take ta saki tana kuma kallon du wani mahalukin dake wajen

Kukan kuran da Dayabu ya yi ya damki wuyan Mardiya ya kaita kas hannayensa bibiyu a rike da wuyanta ne ya saka Abih zabura da wani irin gudu yana kokarin bambare Najeeb daga jikinsa

Ummu da gudu itama ta yi kansa tana furta" Mun shiga uku ku kawo mana talafi, Dayabu saketa, saketa kar ka dora laifukanta a kanka "

Shi kuwa ido rufe haka yake furza yawun bacin rai yana fadin" kema sai kin bita, zan kashe ki da hannayena kowama ya huta da jarabarki, sai na halaka ki "

Ido ABIH ya zaro gannin Najeeba hannunta wuka ne ta warto daga kicin da gudun balaki, sai ya rasa inda zai nufa
Da sauri AMMI ta juya ta ajiye Nusaiba kusa da Ummulkhair da ta summe tun da aka furta Nusaiba ta rasu ga jinni na fita a hannunta itama da gudu ta yi niyar tare Najeeba

Basu ga shigowarsa ba, sai hannun Najeeba mai rike da wukar nan da ya tare

Rike hannun ya yi da dan karfi hakan ya sa ta saki wukar

Wukar ya mikawa sarkin dogarai dake tsaye jikinsa na tsuma kafin da wani irin sauri ya zagaya wajen da tuni Mardiya ta summe dan azaba ya kama hannayen Dayabu ya shiga kwalkwata da wani irin karfin da ya saka DAYABU dago da dubansa yana kuka kashirban yana kallon mai bambare shin

Irin yanda zuciyarsa ke bugawa har ana ganni ta makogwaronsa ya ringa girgizawa SULTAN SHAHEED kai, bakinsa ya buda yana cracking ya ringa fusgar magana ya ce" Ta, ta kashe min kanwata, ka barni na kasheta........dama so take du ta hahahahalaka mu, shikennan nima sai a kash...................n" kasa karasawa ya yi, jikinsa ya ringa saki a hankali ya lumshe idannuwansa ya taho zai fada mata

Tare shi SHAHEED ya yi hakan ya sa Sarkin dogarai da gudu ya karaso ya kama shi ya yi saman babar kujera da shi

Sai da ya bi falon da kallo, daya bayan daya kafin a sanyaye ya furta" Ammi ku shirya ta , Allah ya sa mutuwa hutu ce a gareta"

Ya maida dubansa wajen ABIH dake tsaye kansa sade kasa, a hankali ya karasa ya dora hannunsa na dama gefen kafadar Abij ya ce" ABIH "

ABIH ya dago da kyar yana kallonsa, a hankali ya ce" ABIH ka yi hawaye, ka zubar da hawaye ko zaka ji sanyi a cikin zuciyarka, sannan ka yi hakuro, ka yi hakuri, ka yi hakuri ABIH, taka kadarar rayuwar kennan, ka salaceta ka sakata a makwoncinta da hannayenka sannan ka yafe mata, yarinya ce duda haka kowa ya yafe mata, muma namu lokacin muke jira, ba wanda ya san musababin abinda zai kaishi kiyama sai Allah, dukan mai rai kuma mamaci ne Abih "

ABIH ya kuma busar da hucin dake cikin zuciyarsa

Zuwan likitoci ne ya saka SHAHEED ya gyara tsayuwarsa ya shiga yi masu nuni da su duba mutanen dake zube a summe, duda irin yanda suke ta kallonsa da son gaskata wai da gaske kamanin wanda suke ganni a gabansu ne SULTAN SHAHEED?

Najeeba dake tsugune kanta a jikin hannun Ummukulsum ce ta dago a hankali ta mike tsaye da niyar barin wajen, sai dai wani irin luuuuu da ta yi zata zube ne ya saka shi daga kafarsa da sauri ya karasa ya tare ta, lokaci daya kuwa Sarkin dogarai ya shiga buga tsawar kowa ya sada kansa

Da kirjinsa ya hadeta, a hankali ya karasa saman kujerar dake da girma ya zaunar da ita
Kafafuwanta ya rage tsayinsa ya dauke a hankali ya dora saman kujerar , kafin ya gyara mata kwonciyarta yana gyara mata kitson kanta
A hankali ya mika hannunsa ya dauki hijab din da ya tabata na Ammi ne ya luluba mata
Hannunta ya rike na dama, a hankali yana shafa gaban goshinta , muryarsa a sanyaye ya furta" Kar ki daga min hankali, ki karfafa min gwuiwa ta hanyar zama jarumata, ki yi mata adu'a idan ba so kike du mu kwonta ba BEEBAH "

NAJEEBA t lumshe idannuwanta, hawayen da suka bushe ne ta ji sunna harhada kawunansu, a hankali suka bale mata ta kai dubanta kan fuskarsa ta ce" Shikenan ta kashe min kanwata? Nusaiba ta rasu? "

Hannunta ya kara jimkewa ya furta" ki yi ta hailala BEEBAH "

Idannuwanta ta mayar ta lumshe

Sakin hannun nata ya yi ya mike yana kallonsu

Sai da ya kara kausasa muryarsa ya ce" du wanda ya farka ya dawo kusa da kujerar nan ya zauna, bana son na ji ihun kuka ko magangannun da basu da tsari, soyaya kuke yiwa yar kanwarku? Ku rakata da adu'a, ita ta bara mana duniyar, da ta tafi bata yi gagawa ba, mu dake raye bamu yi jinkiri ba, du zata dauke mu ne koda kuwa bama so!"

Dubansa ya maida wajen sarkin dogarai cike da juriya dan kar yan uwansa su ga gazawarsa abin ya lalace ya ce" ka bada sanarwar jana'izar NUSAIBA"

Wannan mutuwa ta Nusaiba ta girgiza al'umar damagaram, daga bakin lokacin da aka gama zana'izarta aka dora zaman makoki gidan ya ringa dinkewa da al'umah na nesa da na kusa, mutuwar kankannuwar yarinya ta samu halartuwar jama'a tamkar zasu fasa gidan sarautar

Dangin MARDIYA daga bakin lokacin da suka ji takamaiman abinda ya faru sai kunya ta hade su, mahaifiyarta ta yi kuka, ta yi kuka, ta sanarwa Allah, sun hadu su dukansu sun kai gaisuwa sun kuma nemi afuwa cike da jin kunya kafin mahaifiyarta ta kara yiwa Abih gaisuwa, ta nemi afuwarsa sannan ta dora da fadin" Tabas du wanda ya ce a duniya son ransa zai bi karshensa nadama, yau gashi Mardiya taurin kanta, da jajircewarta dan gannin wani ya halaka ta halaka kanta da kanta, a yau Marfiya ta tashi a banza babu gidan mijin babu yar da zata iya tunata ta yi mata adu'a, kaya, nima tawa kadarar harda haihuwar MARDIYA, ta tsananta kishi, abin ya dawo bakin ciki, ta zamanto bata san alkhairi ba, ta so duniya, duniya ta bata sakamako, tsakanina da ahalin Mutalab sai kyakyawar adu'a, har gobe ni din mai bin ku da kyakyawar adu'a ce" ta karashe tana mai fashewa da kuka, Abih da har yanzu bai samu kukan ba kansa kawai ya ringa dan girgizawa, sai dogarai ke bada amsa a haka suka bar gidan suka koma gidansu dan ba abinda zasu ci da Mardiya, hukunci ya hau kanta, hakan zai zamo ishara ga du wata mai taurin hali irin nata!

Sai da suka dauki sati biyu sunna zaman makokin NUSAIBA kafin kafa ta dauke

A wannan ranar ce Sultan ya bada umarnin UMMU ta fito ta je gidanta

Basu musa ba, ama y'ayan nata yan matan ne kawai suka zauna domin baki daya sauran bin bayanta suka yi suka cika motar DAYABU ya tuka su har sabon gidan

Sunna zuwa DAYABU ya shiga nununa masu kowa wajen da yake nasa, nan ya kara zubar da hawaye a lokacin d aya kawo kan gadon Nusaiba, sai da ya yi mai isarsa sannan ya share hawayensa ya yi mata adu'a


.............morning....................
[31/03 à 22:04] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻


*Na*


*SAJIDA*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_



66



A hankali UMMU ta idasa bakin bed din da Abih ke kwonce, royal bed ne rantsatse wanda ya amsa sunnansa, idannuwansa a rufe suke tamkar mai baci, sai dai ba baci yake yi ba,

Cikin nutsuwa ta saka hannunta ta janyo farar takardar dake ciki

Warwareta ta yi ta karanta,
Fuskarta dauke da yannayi na rashin jin dadi ta ajiye nan gefe domin igiya dayar da ta yi saura tsakaninsa da Mardiya ne ya tsinke

Sannu sannu ta haura saman gadon
Hannunsa daya dake kusa da idannuwansa ta kamo cikin nata, a hankali ta furta" Gani na zo Aban Dayabu, ka buda idannuwanka , ka fada min dukan abubuwan da suka faru da kai tsayin shekarun nan, ka fada min wanda ya bata maka ni kuwa zan je mu gwada karfi da shi komai girman tsayinsa da karfinsa"

A hankali ya ringa sauke ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta ya dora gefen fuskarsa yana mai kurawa fuskarta ido, sannan yana mai jin sanyi na ratsa dukan zuciyarta da tunaninsa, muryarsa a shake ya ce" Ki dawama da ni har karshen numfashina NANA, ki zame mana uwa baki daya Nana, walahi na ga rayuwa, ba zan sake fade fade ba Nana "

Idannuwanta ta lumshe a hankali ta kara matsawa kusa da shi kafin ta shige jikinsa ta lumshe idannuwanta bata ce da shi komai ba

Shima idannuwan nasa ya lumshe dan ya amsar kennan, wato ta aminta, kuma ta dawo gare shin kennan, baci ya shiga nema domin rabonsa da bacin har ya manta sai barawon dake fuzgarsa ya dan taba ya farka tsabar damuwa

A washe gari aka tafi da MARDIYA, domin koda kuwa labarin mutuwar ya nuna ba da gangan ta kashe y'arta ba hukuma ta ki aminta da haka, sun tafi da ita sai yanda hali ya yi (Ku mu saba da dane zuciyoyinmu, ku mu ringa yiwa kawunnanmu adu'a kan Allah ya sa mu fi karfin zukatanmu)

A hankali abubuwa suka fara komawa gurbinsu, du mutane suka kama gabansu ciki harda Zahrau da yarima da dayar kishiyarta

Sosai yayan Ammi suka yi sanyi da rayuwa, barema Ummulkhair, ta jima tana nisa cewar a bayanta Nusaiba ta rasu, sai Najeeba da take dan fama da zazabin dare da kewar kanwarta

Nadia a wajen take wuni sai dare take tafia bangarenta
Sultan kam ido ya kawo ya zubawa ikon Allahn Najeeba, rabonsa da wani kusanci tsakaninsa da ita tun shinfidetan da ya yi a kan babar kujera
Ya rasa ina take shiga da idannuwansa suke gaza ganninta, kwata kwata ta yiwa ganninsa tsada, yakan sauke ajiyar zuciya ya dan girgiza kansa kawai, domin yana yiwa al'amuranta uzuri, lalle tana da tata hujar

Ita kanta Nadiar lokaci ya barta har ta kara warwarewa, iyayenta sun zo sosai haka kanwar mamanta na nan har zuwa lokacin

A hankali komai ya dawo normal, ya rage samun mutane a kai a kai na gaisuwa
Ya zamanta ya koma rayuwa yanda yake yi, a hankali komai ya ringa daidaituwa har du wani tunani nasa ya dawo jikinsa
Sannu sannu rashinta a kusa da shi ya fara tasiri
Sati uku kennan da rasuwar Nusaiba abin ya gama kama jinni da jikinsa
Bilhaki a yanzun kewarta yake, idan ya tuna magangannunsu da ita kuwa irin furucinta yakan ji tamkar an dake shi da karfe mai karfi a dukan gabobin jikinsa, da ace zata kasance mai yi masa uzuri da ta gane ta taka matsayin da ba wace ta taba takawa a duniya, da ace zata iya ganewa da ta ture du wani abin sun zauna, bai je mata da wata magana ba sai dan ya yaba, bai je mata da rokon ta gyara kawarta kuma yar uwarta ba sai dan ya jita daban, ba cin fuska bane, yabo ne

Yakan girgiza kansa, a hankali ya furta" Ban yi haka da sanina ba BEEBAH "

Sai ya shafa gemun dake habarsa a hankali ya ce" da ace zaki yarda, da na furta maki irin ilar da kika gama yiwa rayuwata Beebah, kin kai wajen da nakan ji a kasan zuciyata cewar ba zan iya babu ke ba"

Wayarsa ya dauko a karo na bakwai kennan da zai tura mata mesage ba amsa, shi kansa tun abin na bashi mamaki har ya dawo ya daina bashi mamaki irin yanda yake da naci a kan lamarinta, shine zaune da aikin yiwa mace message, shi da ko aurenki zai yi mai zuwa ya masa zancen daban shi kawai sai an kawo ki zaku hade, dan murmushi ya yi

A hankali ya dora dogayen yatsutsansa ya shiga taping din message kamar haka" Kin manta da bawan Allah ne? Ki bani amsa alfarmar rasululah S.A.W "

Sai da ta amsa da sallalahu alaihi wa salam, kafin ta tura masa da salama

Ajiyar zuciya ya yi yana kallon salamar kamar wani dogon message mai dadi kafin ya dora da fadin" Ina muradin gannin matata, ko zan samu wannan alfarmar? "

Bata maida masa da amsa ba sai kurawa Nadia ido da ta yi wace ke ta ciye ciye abinta, sam yanzun ta sake da mutanen gidan tana cudanya da su tamkar yan uwanta na jinni, sannan ko tsakaninta da Najeebar sukan taba hira, maganar sirri ce ta kau, basa wani sirrin junna irin na da

Mikewa ta yi ta shige ciki
Katon hijab ta sanyo hade da nikaf ta fito

Wajen Ammi ta je ta dan duka ta yi mata magana sannan ta mike ta yi gaba

Saloon dinta ta nufa
Tana shiga ta je ta zauna su Aida suka saki aikin da suke yi suka bita dakin da ta shige
Umarnin su gama ta basu sannan ta fara tsife kitson kanta da ya tsufa
Sai bayan sun gama ne suka rufu a kanta, wasu na tsifar kan, wasu na wanke mata kafa da akaifu, daya na gyara mata akaifun hannu , mai kunshi na hada kunshin da zata yi mata dan kadan ba mai yawa ba iya hannayenta

Ba ita ta bar saloon din nan ba sai da yama sosai kafin ta koma bangaren AMMI

A cenma wanka ta shige cikin nutsuwa ta gama kimtsa jikinta cikin lalausan lesh ja mai adon baki a jikinsa kafin ta fito hannunta rike da dan mayafi ruwan baki sidik mai shara shara
Ido kawai AMMI ta zuba mata, kalar fatar jikinta wani sheki take kara yi tamkar ta rihana, a yanzun sai ta kara budewa ko dan abinda suke zargin tana dauke da shi ne?
Kiraye kirayen salar isha ya sakata daukan hijab din AMMI ta gabatar da sallar sannan ta zauna nan sunna dan taba hira

Sai da karfe tara ta yi ne Ammi ta kuma kallonta a karro na ba adadi , muryarta sanyaye ta ce" NAJEEBA, tashi ki tafi mana "

NAJEEBA ta dan yi murmushin, ita kanta ta kusan minti ashirin tana saka ta tashin to sai ta kasa tashin, dan haka ta mike
Har ta fara tafia AMMI ta ce" Kar ki manta, k8 fada masa gobe in sha Allah zaki koma bangarenki kin ji? "

Ita dai ta amsa ne kawai ama ba wai dan tana tunanin zata iya zaman wani bangarenta ba, ita kam me zata je yi cen ita daya kwal? Duda ta san tana kaura yan uwanta zasu bita ne aman ta fi son wajen da take jin shige da ficen jama'a, tana jin sasaucin abubuwa da dama idan tana jin motsin mutun a kusa da ita

A hankali ta tura kofar glass din dake sadaka da falonsa
Sansanyan kanshin turaran wuta hadi da kanshin turaransa da sanyin AC ne suka daki hancinta

Dan lumshe idannuwanta ta yi tana jin zuciyarsa na yin sanyi
A hankali ta fara bin fallon da kallo sai kuma ta ringa hasaso irin zaman da suka yi da mai falon

Jikinta a mace ta idasa shiga, sai a lokacin ta ganshi zaune , ya kura mata ido yana kallonta bayansa jingine da kujerar falon wa'inda aka cenza su aka zuba farare tas tas, hannunsa daya a daudai kahon zuciyarsa, dayan kuwa ajiye saman kujerar, kansa sumar kan ta fito sosai ta yabanya

Ajiyar zuciya ta sauke, gayen nan mai kyau ne......ta furta a kasan zuciyarta, sannan mai aji ne......ta kara baiwa kanta amsa

Hannunsa dake ajiye ya dago a hankali yana miko mata

Sai da ta bi hannun da kallo sai ta dauke kanta
A hankali take karasawa inda yake zaunen, ama ba da niyar kama hannunsa ba
Tana zuwa ta nemi waje ta zauna tana kallonsa

Ido ya zuba mata yana jin yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login