Showing 33001 words to 36000 words out of 228147 words
Chapter 12 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
suka gama kimtsawa suka hadu a saman tafkeken table din wajen du suka zazauna
Cike da farin ciki ta shiga zuzuba masu abinci da kanta tana yi tana dubansu
Inama ace su dawama da ita haka? Gashi yau har zasu koma gidajensu inama ace mahaifinsu ya iya bata koda matan ne ya rike mazan?
Abincinsu suka ci cikin nutsuwa kafin ta dauko ambulope din nan ta budeta
Abubuwan ciki ta zubo wanda hakan ya saka su baki daya zazaro idannuwansu ciki kuwa harda GIMBIYA
Da sauro ta dauki farar takardar dake ajiye ta buda, a fili ta karanta" *ina rokon alfarmar daga yanzu du wata dawainiyar gimbiyata ta dawo hannuna, idan nace kowace ina nufin kowace ciki kuwa harda kudin kari da kati.....fatan zaki rike wannan catin na banki sannan ki faranta min ta hanyar anfani da shi a kowani lokaci daga ni mai ke in sha Allah*
Wani ihu ihu yan matan suka kwasa sunna dariya, NAJEEBA dake firfito ido ta daga hannayenta duka biyu tana sarawa ZAHRAU ta ce" *AN BASHI DAMA, AN YARDA*
Zahrau kam kanta ta sada da mamakin kalaman ciki, dama zai iya neman wata dama a wajenta maimakun ya bata umarni?
Ashe sarakai na neman dama maimakun su bada umarni ko dai shine mai saukin kai?
Irin kallon da ya ringa yi mata jiya ta tuna hakan ya sakata saurin kara sada kanta tana murmushi kafin ta sauke dubanta saman makudan kudadan da suka zubo wai na karinta ne da kuma katin da yar agogon azurfa kamar dai soyayar yara masu ji da kansu
Kanennta ta bi da kallo tana gannin yanda suke shoki
Sannan ta sauke dubanta saman Anmy
Ganni ta yi Anmy harda su tagumi tana kallon NAJEEBA wace ke murmushi tana kada kai tana hangota ta zama aunty
Anmy ta dubi kananun ta ce" ku tashi ku je falo
Bayan sun bar wajen Anmy ta dubeta cikin nutsuwa ta ce" bana so ki amince masa dan dukiya daughter
Na fi so ki ji kin amince masa duda kin ga ba yaro karami bane da zai zauna yana soyaya irin naku na yara, sannan ba zaman jiranki zai yi ba duba da irin darajarsa
Aman ko da wasa ba zan yi maki auren dole ba kin ji?
Kanta ta ringa gyadawa a hankali sannan anmy ta dubi su NAJEEBA
Murmushi ta yi masu ta ce" kar ku manta, ku ringa kiyaye darajarku ku rike mutuncinku kun ji?
Su duka suka amsa mata da nutsuwa kafin du su tashi su tafi bayan sun gama yin salama da ita
.............................................
Kansa a sade yake gaban mahaifiyarsa
Kunyarta ne ya ji ta lulube masa zuciya sai wani irin takaicin zinaria da haushinta da mamakin ashe har yanzu bata da hankali? Yarinta ce ko raini ne ya shiga tsakaninsa da ita?
Cikin tausasawa Anmy ta kara tambayarsa kamar haka" *SHAHEED, SHIN ZAKA IYA FADA MIN KAMSHIN TURARAN WA MATARKA TA JI A JIKINKA KAFIN ZARGI YA SHIGA TSAKANINKA DA ITA DA NI KAINA MAHAIFIYARKA KO BA ZAKA IYA BANI AMSA BA?*
Me zai ce mata? Ce mata zai yi ga mai turaran ta tambaye shi me ya kai turaranta jikinsa? Ko fada mata zai yi ga abinda ya kawo turaran nata jikinsa ta titsiye shi kan a kan me?
Aman yana tunanin ya yi girman da zai iya tara mata hudu shine zinaria ta masa gangancin kawo irin maganar nan kunnen mahaifiyarsa? Ta kuwa san irin yanda yake kiyaye lamarin mamansa shine ita zata masa wannan shirmen?
Anmy ta shiga girgiza kanta a hankali sannan ta ce"
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
13
Kansa ya kara sadawa sosai kafin a hankali ya ce" Allah ya huci zuciyar Anmy
Zamanta ta maida ta gyara tana mai girgiza kanta, kennan ta tabata wata yake ganni har kamshin turaranta ya zauna a jikinsa?
Cikin nutsuwa ta ce" kar ka manta kai ne mai hukunta laifin da ya kai hukunci, shin aikata abin hukuntawa ka yi?
Sai da ya kuma lumshe idannuwansa ya bude a hankali ya girgiza kansa
Ajiyar zuciya ta sauke jin aa, dan haka cikin nutsuwa ta ce" bana gane gabanka bare batanka SHAHEED, bana fahimtar me kake boyewa a cikin zuciyarka
Maganarka ta kasance kadan
Wata ajiyar zuciyar ta sauke sannan ta ce" koda kai sarki ne, ni mahaifiyarka ce
Ka yi kokarin yin shawara da ni idan bata girmi kwakwaluwana na mace ba ka ji?
Kansa ya ringa gyadawa a hankali sannan ya dan dago ya dubi fuskarta
Muryarsa dai cikin nutsuwa ya ce" ALLAH ya huci zuciyar mahaifiyata
Murmushi ta yi tana lumshe idannuwanta ta ce" idanma wacece ka aureta
Wannan karon da idannuwansa ya bata amsa yana kara sada kansa a gabanta
Murmushi ta yi ta furta" Allah ya yi maka albarka
A hankali ya amsa da amen
Bai tashi daga gabanta ba sai da ya cike lokacin da yake dauka a gabanta sannan ya mike ya yi mata salama ya koma bangarensa dan yau ba zai fita fada ba su waziri na cem sunna gabatar da shara'ar garinsa mai mutane masu rigima da saurin kawo kara
Kamar wace ta jima bata zo dakin nata ba irin ta shekaran nan
Da murna da komai ta shiga tana ta kara kallon dakin
Jingina ta yi da jikin garun dakin nata, kai a duniya fa tana ji da dakin nan nata domin rabin tanadinta a cikinsa ya kare
Bata tunanin ko dakin wata mai kudin mai auren zai nuna mata wani abu shi yasa take gannin idan ta tashi aure za'a kwashe komai a kai mata gidan mijinta ne
Kalmar miji ta sakata buda idannuwanta
*Mijina* ta furta a hankali
Ina ka buya? Ina kake ? Yaushe zaka zo?
Ko a ina kake na san baka da aure,
Idanma kana biya yan mata kana da budurwa ka yi gagawar salamarta
Zama ta yi saman kujerar dakin nata wace take da yannayin takalmi mai tsini ta dan talafe kuncinta
A hankali ta ce" bana so ka zama farin mutun, dan rike NAJEEBA sai tsayayen namiji Farin mutun kuwa ya cika son jiki da sanyi sanyi
Murmushi ta kuma saki ta dora kafa daya kan daya ta daga kanta kadan tana dan wasa da habarta ta ce" sannan ina so ka kasance mai lebe pink iya na kasan na saman ya zama baki....bai dameni ba idan an ce dan shaye shaye mai baki ja aman fa bana so ka zama dan shaye shaye ka ji?
Hannunta ta dora wajen kirjinta tana kara dora kafa daya kan daya ta ce" kirji fafada, askin yan tasha........murya irin ta zaki, damtse mai taurin gaske
Idannuwanta ta rufe da hannayenta irin ta ji kunyar nan ta ce" fafadan kirjin da zan iya kwonci na yi isashen baci da juyi
Wani murmushi ta saki tana fadin" na san sai ka so mata, ....na san sai an so ramawa a so min kai abinda na fi sani shine ba zan yarda a karya min kara a ido ba!
Ke NAJEEBA!
Muryar zahrau ta sakata zabura tana kallonta , a rikice ta ce" meye?
Zahrau ta ce" kin haukace ne kina zaune kina magana kasa kasa kina ta murmushi kina wani irin abu a saman kujera lafiarki kalau kuwa? Yanzu da nace kowace maza ta gyara dakinta ke ko kakaba baki fara ba bale shara bale guga kina zaune kina uban meye?
Da sauri ta mike tana hararan Zahraun ta shiga yaye zannin saman gadonta ta ce" yaya ake so mutun ya yi kiba idan akoy irinku a waje? Shikenan ba zan zauna na hasaso yanda nake son gannin mafarkina ba sai an samu mai dirowa ciki ya katse ta hanyar sako nasa maganar?
Yaya ake so mutun ya iya labewa ya samu lokacin kansa idan ba wada bashi da kys din dakin wani?
Ni gaskiya ana takura min
Zahrau ta tabe baki ta ajiye wayarta ta shiga tayata gyaran dakin tana fadin" yaya ake so a yiwa gandamemiyar budurwa aure a kaita dakin miji ta aikata abin kirki idan gyaran dakinta kawai na daukan mata awa biyu?
A yi mata a ga ikon Allah, aunty ta yayama zan ringa aiki a cikin gidan ni daya bayan na gama tsara zan rayu da mijina tamkar abokan junna? Zamu raba aiyukanmu ne, mu rufe dakinmu mu saka kida muna yi muna casu abinmu, aunty ba zan iya auren namijin da bai iya rawa ba, ba zan iya auren namijin da bai iya sakani daria koda bana so ba, ba zan iya auren namiji mai tsare gida ba....Najeeba ta fada tana cilowa auntyn nata babyn nunus na zaki
Cafewa ta yi utama ta jefa mata tana daria ta ce" gidan aure zaku gina ko gidan shedanu? Mace ai ita zata yi aikace aikacen gida , ta tsaftace ko'ina ta kimtsa ko'ina
Bayan kin san da Abih ya fada da ihu ya fada a nasiha cewar ba zai taba bari a daukar mana yan aiki ba har sai mun tara y'aya? Ban san nufinsa a kan hakan ba ni sam
Najeeba ta ce" ban ga aibu ba dan mun gyara datin da muka bata tare da kai! Maza da suka amsa sunnayensu na maza
Mazan da suka rayu da adini a jikinsu, sukan taya matayensu aikace aikacen cikin gida
Bana gannin walwala da sabo a wajen namijin da zai gimshe min fuska shi ga mai gida ni ina dauke cen goge cen gyara cen wanke cen shi ko gani baya yi bale ya yaba
Aunty ni zan koya masa sannin zafina, ya kama min mu taru mu rufawa junna asiri
Kina son sannin dalilin Abanki na hanawa a kawo maki yan aiki? Ba komai bane face shi burinsa ki gina gidanki, ki shaku da mijinki, ki san kanki ki san wa kike aure kafin a kawo maku masu sangartar da ku ta hanyar kuna zaune kafa mike ku ringa saka su dauko maku ruwa, kawar da plat din abincinku
Zahrau ta zauna bayan ta jefa mata tsintsiya ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" nima na so haka a tare da ni sosai
NAJEEBA ta duka ta shiga share dakin tana dukawa har kasan bed dinta kasancewar kasansa a bude yake tana sharowa sosai ta dago tana dubanta
Murya a sanyaye ta ce" bai zama lale ki amincewa rayuwar gidan sarauta ba! Bai zama lale ki auri mutumen nan ba
Farin cikin ki na gaba da komai
Idan har zuciyarki ta ki amince maki da hakan ba dole bane!
Dan murmushi ta yi tana share dan karamin cafet din wajen ta dan dago ta ce" sannan kina iya mayar da lokacinku naku wanda zaki saka sarkin Agadez shara a daka, a lokacin da ba masu yi maku hidima, babu idannuwan bafadanku
Ta karashe tana kashe mata ido da yannayi na shakiyanci
Daria ta yi tana girgiza kanta , NAJEEBA ta ce" namiji, ya kasance namiji a gaban wasu bakin fuska, aman amini a cikin gidansa
Zahrau ta karkato sosai tana dubanta ta ce" ta yaya? Ta yaya kike tunanin zan iya aiwatar da wani abin da zai zo masa sabo a rayuwarsa?
Ke kin sha gannin vidion gimbiyarsa inda take takun kasaita, wuyanta hannayenta kafarta dauke da zinari
Kin ga irin yanda take zuba kudi
Ke kin ga kalar fatarta kin kuma ga kalar kyawunta
Bayanta akoy wata guda dake taka rawarta itama
Wacece ni da zan iya jerawa da su? Kin ga kalar fatana bak'a ce,
Bani da wani kyan da zan iya dukan kirjina na jera da matan nan
Jikina ke mutuwa NAJEEBA
NAJEEBA ta yi sakalau tana kallonta
A hankali ta ce" da ba dan ke yayata bace, da sai nace ki tashi ki fitar min a dakina domin a duniyata bana son macen dake raina kanta ko wacece!
Muryarta ta dan daga tana kallonta da tsintsiya a hannunta ta ce" shine me dan kina bak'ar mace? Ita bak'a ba zata je gidan sarauta ba kennan sai fara? Kin manta halayan mace ke siyan mata mutunci idan mutuncin ne , soyaya idan soyayar ne?
Meye aibunki a jikinki meye baki da shi?
Meye laifinki a fuskarki me ya gaza na mace?
Kina nufin fatar naki ce ta fara baki haushi a yanzu kuma bayan mun kasance masu takama da kalar fatarmu?
Bakinta ta turo ta ce" kudi kuwa, kudi aunty, kina tunanin sunna da wata matatsa ne ta fi aljihunsa?
Zaki amshi kudin mijinki da dabara ki kashe da hikima ba tare da shi kansa ya gundura da tunanin kina da kashe kudi ba
Wani gwauron numfashi ta sauke tana kallon NAJEEBA , idan Najeeba na fadi sai take jin abin ba wahaka, sai ta shiga aunawa sai ta fara tunanin anya kuwa? Anya hakan zai zo da sauki kamar yanda kanwar nata ke fada?
Wayarta dake saman bed din NAJEEBA NE TA FARA KUKA
duban wayar suka yi a tare
NAJEEBA ta dauko tana kallon number
Zahrau ta ce" waye?
NAJEEBA ta daga kafadunta ta ce" nima ban sani ba ba sunna ai
ZAHRAU ta juyar da kanta ta ce" tun da safe ake kirana da number ko ba mai 00 karshe ba?
NAJEEBA ta gyada kanta tana kara kallon number
A hankali ta ce" aman number nan batai kama da irin number yan cenken numbobi ja
Tana fada ne tana dagawa ta kara a kunnenta
Dan shirun da akai yi ne ya saka Najeeba kuma kallon number ta ga ba'a kashe ba
A handsfree ta saka ta ajiye sannan ta yi mata nuni da su yi shiru
Sharar da take ta ci gaba da yi tana gyarawa da kyau
Sai da ta gama sharar ta kwashe ta zubar ta dawo ta shiga ciciro kayanta tana gyara masu ninkinsu tana mayarwa a muhalinsu
Wata kamilaliyar murya ce ta yi magana kamar haka" Asalamu alaiki gimbiyana
Dan shiru ya yi kafin ya dora da fadin" ki ja ajinki da kyau sarauniya ....aman yaya aka yi baki nemi number mijinki kin ji inda jirgi ya wurga maki shi ba?
A tare suka zazaro ido a lokacin da suka fahimci mai sanyaya maganar nan ba kowa bane face sarki
Wata wuntsilowa Zahrau ta yi tana kara firfitar da idannuwanta
Da gudu NAJEEBA ta warto byro da takarda ta janyo wayar tsakiyarsu
Da wani irin sauri ta yi rubutu sannan ta nuna mata
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta sanyayar da muryarta sosai da sosai kafin ta ce" amincin Allah ya tabata a gareka
Murmushin manyan mutane ya yi jin da kyar dai ya samu jin muryarta a karo na hudu tun bayan nemawa Zinaria afua, da godiyar da suka yi masa
Ya tabata yarinyar ba sai an bata lesson din jan aji kafin magana ba, da alama saraurar a jinninta take ba sai an koya mata wani abin ba
Shima shirun ya yi mata, domin shi dai ai sarki ne abin nan a jinninsa yake ba wai hawa ya yi daga sama ba
Wani rubutun ne ta nuna mata dan haka a hankali ta yi dan murmushi ta ce" yaya hanya? Ya gajiya?
Shima murmushi ya yi kafin ya bata amsar cewa" gajiya ba zata kau ba sai na kilace ZAHRA
ZAHRAU ta kuma zaro ido hakama NAJEEBA
Da gangan Najeeba ta rubuta " to wai shekarunka nawa?
Ta nunawa Zahrau
Allah ya taimaketa sai ta karanta take maimaitawa dan haka bakinta ta cije tana wurgawa Najeebar fillow
Lokaci daya ta ce" NAJEEBA bakya jin magana walahi
Murmushi ya yi jin kamar kokowa suke, shima ya maimaita sunnan Najeeba
Zai iya cenko ko wacece Najeebar nan, yana ga itane wace suka fiya dunguri a boye idan sunna tsaye tare da yan uwansu
Tana mintsinnin Najeeba tanai mata cakulkuli ne tana fadin" baki da kunya Najee mijin nawa zan yiwa wannan tambayar?
Sai kuma ta yi dif ta yi saurin kallon wayar
Da wani irin sauri ta sauka tana fadin" na shiga uku, da sauri ta warci wayar ta kashe tana zaro ido
Shi kadai ya ringa daria a bayane na kuruciyar yaran,
Da yake ya shigo hutun yama ne sai kawai ya rubuta mata message ya tura sannan ya ci gaba da abubuwan da yake
Da mamaki ta ringa bin message din da kallo, hakan da suka yi bai bata masa rai ba, saima magana irin ta tsokana
Dama saraki na da raha haka? Ta kuma tambayar kanta
Da baya baya ta fada saman bed din tana daria, a hankali ta ji dan tsoho na raf da zuciyarta..............
.............................................
Sannin cewa a gobe zai yi zaman fada ya saka shi gama komai nasa da wuri sannan ya kwonta saman bed dinsa ya shiga jan carbi
Ta shiryawa yauma, ta gama sabawa da irin jarabarsa hakan ya sa a yanzu idan bata ji shi a tare da ita ba take jin sam ba dadi
Tana wani irin kishinsa wanda ya zarce misali bale a matsayinsa na sarkin garin ta tabata ko tana so ko bata so wata rana sai wata ta so shiga rayuwarsu
Abinda ba zata iya aminta da shi ba kennan
Irin yanda ko mahaifiyarsa take jimawa bata ga kalar fuskarsa ba bale wata cen yar banza ta gane mata sirrin dake haukata zuciyarta a kansa?
Tana godewa Allah da yake rufe fuskarsa wanda mutane da yawa sai dai su shaida hotonsa aman basu taba ganninsa a fili ba
Wannan na kara daukaka darajarta ko a cikin gidan sarautar cewa itane macen dake gannin fuskarsa a duk lokacin da hakan ya raya mata
Salama ta ringa yi, a hankali ya amsa mata ya maida kansa ya ajiye
A hankali ta ringa takawa dan karasawa wajen da yake sai dai bata kai ga idasawa ba ya dago ya sauke idannuwansa a saman fuskarta wanda hakan ya saka ta ja da sauri ta tsaya tana jin gabanta na faduwa
Me ya bata masa rai? Irin kallon iyakantarta da shi kennan
Gabanta ne ya yi wata irin yankewa ya fadi, tsoro ta ji kan kar dai a je mahaifiyarsa ta fada masa cewa ita ta fada mata ta ji kamshin turaren da ba nasa ba a jikin rigarsa?
Gannin ya koma ya kara kwontawa ya saka jin kafafuwanta sun fara yi mata