Showing 39001 words to 42000 words out of 228147 words
Chapter 14 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
zuwa wannan yar karamar dake kusana
Yana nuna yar kanwarsu wace bata fi shekara shida ba
Ya daki kirjinsa ya ce" Ni DAYABU MUTALAB idan har na isa da kannena daga bakin zahra har zuwa ummi na kankare mana wannan yarinyar daga cikinmu, yarki ko? Ki rubuta ki ajiye bamu isa mu tatse jinninta daga jikinmu ba aman mun isa mu kankareta daga cikinmu! Ko a titi, ko a cikin gida ba mu ba ita!
Gaba daya yaren mutuwar tsaye suka yi sunna kallon irin yanda ran yayansu ya gama baci,
Yana gama fada ya juya ya yi ciki ransa a matukar bace ya je ya gyara shinfidar kananu du ya kora su daki
Manyan kansu silalewa kowace ta yi, zuciyarta da mugun rauni, me ya sa ta yi wannan aika aikar ne? Me ya sa sai da ta kai mutun mai hakuri da kare yan uwansa bango har ya aiwata haka yau? Ya fi su saukin hali da kawar da kai ko dan ya kasance mamiji? Aman a yau ta kaishi bango har haka ta faru
Sun yi baci hankalinsu ba a kwonce ba
Da sasafe ta rigayi kowa barin gidan ta zarce saloon
Yau da kanta ta ringa yin aikace aikacen ta jirga zaman kujerun ta kakabe atach din dake tare ta wanwanke abubuwan wanke kafa ne, ta goge du wajen da ya yi dati
Sai da ta yi aiki jina sannan ta zauna tana maida numfashi
Da wuri wuri aka ringa cika wajen
Nan ta shiga aikinta tana yi tana duba time
Ba abinda ta ci sai da karfe uku ta yi ta bara masu ta shiga ciki
Wanka ta yi mai tsari ta gyara jikinta tsaf ta fito sanye da wata abaya mai ruwan ja mai duhu da bakin hannu
Dan kwalin abayar ta rataya a wuyanta ta fita ta shiga motarta
Bata zame ko'ina ba sai fada
Tana tsayawa ta saka gilas dinta fari dan siriri ta fito a motar
Cirko cirko ta gansu su biyar a tsaye
Ido ta zaro ta karasa wajensu a hankali ta ce" me ya kawo ku nan ku kuwa?
Yaya DAYABU ya harareta ya ce" baki da kowa ne da zamu barki ki zo ke daya?
Fuskarta ta sanyaya ta ce" eyah, na ga du na bata maku rai ne
Zahrau ta kamo hannunta ta ce" mu je lokaci ya yi Najeeba, komai bata mana da zaki yi ba zamu barki ke daya gaban mutane dubu ba
Wani sanyi da kaunarsu ce ta ji a ranta, nan suka rankaya da su ummu suka shiga bayan sun cicire takalmansu
Tun da suka zauna yake yi mata mayatacen kallo
Matarsa ta shiga bayanin a yi mata tsakani da mijinta ba ita ba shi
Da sauri ya ce" aa, Allah ya taimaki waziri ni kam ba da yawuna ba, yarinyar nan ni na je na ce ina son ta, idanma laifin ne ni na yi mata dan haka bana cikin maganar a rabani da ita dan aurenta nake son yi!
Gaba daya wajen ya yi tsit, sai Najeeba da ta kara sada kanta dan kunyar da take ji na irin kallonta du da ake
Daga inda yake tsaye ta wajen tagar dakinsa yake hango komai
Irin yanda ya fahimta yauma itace aka kawo kara
Juyawa ya yi ya karasa wajen wayarsa karama ya danna kira, idan yana son jin abinda ake fada yake hakan sai a ajiye yana jin komai
Zama ya yi ya yi zamansa na sarki ya bude litafi a hannunsa na hadisi yana dubawa still yana sauraron abinda ake fada
Kansa kawai yake girgizawa a lokacin da ya ji ambasador na neman yin sakiyar da ba ruwa ta hanyar sakin matarsa har yana daga muryarsa cewa idan har ta yarda aka sakawa Najeeba wannan layar to ta tabata a bakin aurenta
Karshe dai sai itane ta dawo bayar da hakuri cewa a bari kar a saka
Abinda ya fi bashi takaici da haushi shine yarinyar ko A bata furta ba mutanen wajen ne ke ta hayaniyarsu tun dazu, ita ga isashiya
Karshe dai kashewa ya yi a lokacin da ya ji shara'ar ta koma neman sasanci tsakanin matar ambasador da kuma Najeeba, inda aka shiga sasanta su da gindaya masu sharudan kar wace ta kuma tarban wata da neman fada, shi kuwa aka yi masa kwakwaran kashedin ya zama namiji ya tsawatarwa iyalinsa sannan idan auren Najeeba zai yi ya maida hankali ya aureta ba ya ringa neman fitina da girmansa ba
Sai kusan magariba aka sake su
Ranta kwata kwata a bace yake a yau din nan dan haka ta zarce wajen da ake siyar da shawarma
Siya ta yi isashiya sannan ta karasa wajen hutun da takan je lokuta da dama
Wajen bai cika mutane ba, idan ka ga mutane a wajen tabata irin manyan yan gayun nan ne
Salaya ta shinfida ta gabatar da sallarta a wajen da hijab dinta dake cikin mota
Haka ta yi ta isha ta shafa fatiya
Mikewa ta yi ta adana komai ta dauko shawarmar ta zauna saman daya daga cikin kujerun wajen a lokacin duhu ya shigo sosai ta shiga harba yan kafafuwanta tana bude takardar shawarmar
A hankali ta rike a hannunta tana fadin" Aikin banza! Aikin banza aikin wofi! Shirme shirme shirme kawai! Ta karashe tana murguda bakinta
A hankali ya furta" ke da wa?
Da sauri ta dago dubanta, sai dai bata idasa dagowa sosai ba gabanta ya fadi haka kawai ba tare da ta san dalili ba
Wannan mutumen ne na ranar, wanda ya taimaketa ya fitar da ita
Yauma wani irin turarensa ne ya fara yi mata salama kafin ta sauke dubanta saman jajayen lebunansa
Irin yanda tsarin haliyar jikinsa take kuwa shi ya fi komai bata tsoro
Haka kawai ta ji jikinta na yi mata wani yam yam yam dan irin yanda take gannin idannuwansa da girma ga kwali sai ta ji tsoron kar dai aje aljani ne?
Bata idasa tunanin da take ba ya karasa saman kujerar dake daf da tata ya zauna yana jan dan karamin tsaki a cikin zuciyarsa yana mai dannar kansa cewa ka yi hakuri, ta hanyar nan ne kawai zaka iya cinma burinka! Ka yi hakuri.
a fili kuwa sai ya furta" kema an kona maki zuciyar ne? Ya Allah ban san menya sa mata suke haka ba!
Gaba daya sai ta ji kanta a takure, abincine fa zata ci ya wani sakota gaba, to wai wayema shi? Ina ruwansa da ita ne? Ita dake boyon cin abinci idan ba da yan uwanta bane sai anmy sai abih
Haka kawai wani garjehen kato ya wani shiga yi mata bayanin da bata tambayeshi ba? Yanzu haka da budurwarsa ya yi fada, shirme! Shirme! Aikin banza kawai!
Da yannayin tsiwa ta dube shi ta ce"....
......
Commetn comment na sis
Ina jin dadin comment dinku, karo min zai karan karfin gwuiwa hajiyoyinaππ
[31/03 Γ 21:37] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*Na*
*SAJIDA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
15
Da yannayin tsiwar nan ta ce" ka sanni ne?
Kwarai hakan ya bashi mamaki, ya matukar bashi mamaki, shi? Shine yau mace macenma wace ya fi rainawa take furta masa magana haka kai tsaye?
Saurin kawar da hakan ya yi yana kirmiro murmushin da bai yi ba baki daya wunin yau ya miko mata hannu irin su gaisa din nan yana fadin" je suis desoler ( i'm sorry), ban gabatar maki da kaina ba, FARID ELHAJ BASHIR by name, ni dan Abuja ne ina shigowa garin nan ne dan kawowa yayana ziyara Elhaj Muctar Garba mai gold, ni matukin jirgi ne sannan dan kasuwa ne
Du wannan jawaban da ya yi Najeeba ta yi sakalau da abincinta a hannunta tana kallonsa
Tambayar da take yiwa kanta shine, to ita ina ruwanta ko tambayarsa ta yi ne?
A hankali ta bi hannun nasa da ya miko mata yana nufin su gaisa ko me?
Wani sakaran murmushi ta dan sakar masa ta maida hankalinta kan ledarta ta dan duka ta dauke sannan ta mike tsam ta koma kujerar dake nesa da shi ta barshi nan sakaye da hannu baki da hanci bude cike da mamakinta
Wai bata ganninsa sa kyau ne?
Duba da irin shigar da ya yi tau ya yi shiga ne irin ta yaran atajiran nan, ya saka riga da wando na wani mahaukacin yadi wanda koda baka san yadi ba idan ka gansa a idannuwanka zaka gane ba fa na wasan yara bane
Ya dora yar hula a kansa wace ta kara kashe kyansa ta fitar da dogon hancinsa zuwar sannan ta kara masa kima
Rigar ba wata mai budadan hannu bace, dinkin ya kama hannayensa sosai har kana iya gane hannayen nan nasa bafa na wasa bane
Sai ya ringa dan kara kallon kansa a kaikaice kafin ya yi gagawar karyata abinda yake tunani ta hanyar fadawa kansa kalamai kamar haka" ranta ne a bace, shi yasa ta ki baka hannu, idan ba wannan ba yarinyar dake jira a tayata ta karba a guje?
Tuna hakan da ya yi ya saka shi kara baiwa kansa hakuri ya mike cimak ya koma kusa da ita, wannan karon face dinta ya zauna yana dubanta ya ce" i'm sorry plz
Na bata maki rai ne? Nima ina cikin damuwa ne shi yasa kika ga ina yi maki magana haka sannan kamar na taba ganninki
Sai kuma ya dan zaro ido ya ce" oh yes, ke ce, ranar nan na fitar daga stade kun je ke da saurayinki nah?
Tsatsareshi ta yi da ido ga abincinta ta cira ta fara taunawa hakan ya saka ta kasa ci gaba da taunawa sai kawai take kallonsa
Ko maye ne? Abinda ta tambayi kanta
Idan ba raini ba shi a nan bai gane ni ba sai yanzu?
Ta kuma tambayar kanta
Sai da ta juyar da kanta ta labe fuskarta ta karasa taune abin bakinta sannan ta juyo tana dubansa ta ce" aman bawan Allah fisabililahi me na yi maka ne? Ka dai san tunda na baro gidanmu na zo nan kadaicewa nake da bukata kuma shikenan sai ka shiga zayano mon magangannun da ya shafeka? To waima an rubuta a goshina cewa ga NAJEEBA maganin damuwarka ne? Plz ka girma ka je ka iya da matsalar budurwarka haka kawai ka wani matsa min , to ni ba ni ka ganni a inda kake tunanin ka ganni ba
Tana gama fada ta mike ta bara masa ledar a nan ta yi gaba da sauri ta karasa wajen motarta tana jan tsaki ta fada ta rufe ta tayar ta warceta da gudu gudu ra bar wajen
Zuwa wannan lokacin har sai da ya talabi habarsa dan mamaki
Wato ita bata tsoro ga tashen iskanci ko? Bata tsoron ko shi wani mugu ne ya fafalawa fuskar nan tata mari ta zo ta saka abin idannuwan nan dake mayar da ita tamkar wata aljannah ta tata masa rashin mutunci ta tafi
Kansa ya girgiza ya kai dubansa wajen ledar
Dauka ya yi ya buda ya ciro abinda ke ciki
Jujuya abin ya ringa yi kafin a fili ya furta" da na halal din ko da na haram din aka siye ku?
Mayarwa ya yi ya ajiye a nan ya mike yana tafe kamar mai jin tsoron taka kasar ya bi ta cikin duhun da ya ratso ya shigo wajen yana mai ayanna" sanu sanu dai bata hanna zuwa, zaki yi bayanni ne daga bakin lokacin da na kama ki da laifinki, na rantse maki sai na fitar da ke waje zan hukunta ki a wajen da ba wada zan iya kallo na daga maki kafa marar mutunci kawai!
.......................................
Hotunnan y'an matan da aka turo masa ne yake bi ta compte professional dinsa
A gajiye yake tilis, ga kallon hotunnan da yake yana son a yau a yau din nan sai ya fitar da yarinyar da za'a kawo masa a matsayin mace ta biyu gidansa
Yana son kara auren nan ba yau ba sai gashi da banzarsa ta buda masa hanyar yi
Ya yi hayaniya mai yawan gaske hakan ya hadasa masa da gajiya mai yawa sai kawai ya dawo juyawa a saman bed din yana sauke ajiyar zuciya
Shi kam a kan hitunnan wasu yan mata uku ya tsaya
Ba dan komai sai dan irin shigarsu ta kamala sannan iyayensu mutanen kirki ne
Biyu y'ayan hausawa ne sak, dayan ce bafilatana
Turawa wanda ya turo masa ya yi, kafin ya mayar da kansa har ya turo masa da message kamar haka" *Su duka ukun uban gidana?*
Tambayar ya kurawa ido, su duka ukun? Sai ya ji wani abu na ce masa me zai hana ka dauke su su ukun? Idan ka yi hakan ka gama cikewa sai ka koma gefe ka karbi salon kowace
Bai bashi amsa da gagawa ba, shi kuwa ya yi ta jiran amsar karshe shima ya bar wayar a kunne ya kasa kashewa dan gudun ya sauka a je ya turo amsar
bayan ya gama salar asubah ya dawo bangarensa ya kwonta yana duba agogon dakinsa ya lumshe idannuwansa
Irin yanda zinariya ke ta tsatsareshi da ido aman ta kasa tambayarsa abinda ta masa ke bashi mamaki
Me ke damun kwakwaluwar yarinyar?
Shin sarautar ce ko sakarci ne?
Yakan cika da mamakin wasu abubuwan nata
Tabas shi mutun ne mai son sauki a rayuwarsa bai san dalilin da ya saka mutane da yawa ke tunanin ya cika son zafi ciki kuwa harda abokiyar rayuwarsa wace ya dace ta fi kowa sanninsa da fadin halayansa
Yana so ace matarsa ta san cewa shi mutun ne mai son shakuwa da mace
Yana son ya gabatar da rayuwar aure irin yanda ma'aiki ya koyar
Yana so koda bai cika komai daidai hakan ba ya kwatanta
Ya so ace shi din mutun ne marar nauyi a kansa, da ya rantse abinda zai hana shi zuwa ga matarsa lalle baba abu ne
Sun yi auren biyaya ga iyayensu da zinariya, ya sameta a matsayin cikakiyar budurwa, sai dai a kulun abinda yake nema ido rufe ya rasa shine kasancewarta irin matar da yake so
Yana so idan ya fita ya bayar da umarni idan yana daka a umarceshi cikin kissar da shi kansa ba zai gane umartarsa aka yi ba
Yana so tsakaninsa da matarsa idan da ido ta yi bayani ya fasara abinda take nufi koda a cikin duban mutane ne
Yana so tsakaninsa da matarsa ace idan akoy wani abu mai sunna kirari to fa ta yi shi ne a lokacin da idan ta yi shi zai kara kaimin faranta mata ya farantawa kansa ya lula da su a cikin duniya mai dadin gaske
Sai kawai aka samu matsala tasa matar takan kwashi kirari ne kamar wata jakadiyarsa a duk lokacin da suka hadu
Shin sai ya koya mata ne ko sai ya karo auren ta ga yanda wata zata wakanar sannan itama ta dauki hannu?
Murmushi ya yi yana adu'a dan samun hutu, ya gaji walahi yawan maganar nan ta jiya ba karamin gajiyar da shi ta yi ba hakan ya sa ya takaita maganarsa daga jiyan zuwa yau a wajen gaishe da mahaifiyarsa ta hanyar sirrinsa ne kawai ya budi baki ya yi wata maganar
Bai waiwayi wayarsa ba sai da garin Allah ya waye sosai har kusan karfe goma sha biyu
Yana gama daura agogonsa ya janyo wayar nasa
Direct cikin message dinsu ya shiga ya rubuta" halayanta su zamo nata ne ita daya, ta kasance mai halayan dawissu
Ina son wace ta san kanta
Ina son wace ta rufe kanta
A yanzu ka ware daya a cikinsu ka tabatar komai ya gama a yau dan ina so nan da kwana hudu a gama komai ba zan ja ba, ba zan yi wani gangami ba dan ba aurena ne na fari ba!
Yana gama turawa ya zauna bakin bed dinsa yana jin wani haushi haushi
Ya tabata bai isa ba, komai yanda zai kiyaye tara mutane sai sun taru an masa yawan magana da tsarewa
Shi kuwa alkawari ya yiwa kansa sati ya baiwa kansa sai ya ajiye wata macen a saman bed dinsa wace zai raya sunnar ma'aiki da ita,
Wace zata cike zargin zinariya, ta faranta ran Anmynsa ta hanyar bin umarninta,
Ajiyar zuciya ya sauke duba da bata lokacinsa ne yake sannan ya mike ya koma dakin da yake hangen abubuwan dake wakana a masarautar
Kansa kan daukan caji fiye da tunanin mai karatu
Matsalolin cikin gidan marauta a gaban idannuwansa suke, da yawa sun fi karfin titsiye su tashi daya dole ta sannu yake binsu ya ruguje su, da yawa rainin hankali ne yakan yi kamar bai ji ba bai gani ba
Shi dai a matsayinsa na sarki mafi yaro a wannan karni yana iya yinsa dan gannin yana kare wasu abubuwan
Shi mutun ne mai son motsa jikinsa kamar me, motsa jiki a wajen da ba wanda zai zo kallonsa ko ya san shi waye hakan ya saka yake fita da mutun kwaya daya tak su je wani tafkeken filin LAKD ya bale a guje ya yi ta gudu son ransa
Idan ya yi ya gama ya yi pompe mai yawan gaske sannan su je wajen da yake shan dadar iskar garin ya zauna ya saje da kowa ya sha iska ba tare da ya yi aboki ko budurwa ba
Ya saba fitarsa ba yau ba, idan bai yi fitar sirrin nan ba tabata wani abu mai karfi ne ya hanna masa yin hakan......
Wannan kennan
............................................
Kallon sarkokin Abih yake daya bayan daya wa'inda Dayabu ya saka aka yi masa tun daga kansa har zuwa kannensa
Irgawa ya yi ya kuma irgawa ya kalli DAYABUn, to ko ya manta su goma sha takwas ne?
Sai abin ya so bashi dariya da ya ambaci hakan a zuciyarsa
Me zai hanna shi mantawa kai kuwa? Ya kuma tambayar kansa
Abih ya kuma daya sarkar ya kalle shi ya ce" to kaima sakawar zaka yi?
Murmushi ya yiwa abih ya ce" hum Abih rigimar y'arka ce wai yo sai na saka mana kamar wani dan daudu ko wani dan duniya
Daria Abihn nasa ya yo yana bin yan siraran sarkokin zinarin da kallo
Tabas yana