Showing 114001 words to 117000 words out of 228147 words
Chapter 39 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
ta juyi fuskarsa ta ce" hei dan uwa, me ka ce?
Hannunta ya janye daga fuskarsa cike da jin haushi ya ce" tambayata kike abinda nace? Nace kin ji kunya son kudin naki ya rasa wa zaki cuta sai ni jinnin ki?
Da sauri ta ce " bla bla bla, ba shi din nake son ji ba, auren Najeeba da sultan? Waye sultan kuma?
Lalle kin iyabiskanci Nadia, ya fada
Mamarta ce ta ce" kai Huzaifa wai meye haka? Me kake fada haka?
Huzaifa ya juya wajenta ya ce" mama, ni Nadia zata boyewa Najeeba kawarta ce kishiyarta da za'a daura aure da Sarki yau? Yanzu ina zaune aka daura auren Najeeba da sarki kafin na baro wajen
Nadia ta zazaro ido kafin ta dora hannayenta saman kanta, a rikice ta kara yiwowa kusa da shi ta dafa shi da hannunta da ya kwashi rawa ta ce" yanzu domin Allah me na maka zaka zo min da zancen dake iya halaka ni Huzaifa? NAJEEBA fa tana gida kwonce bata da lafia inji aida da ta zo ta min kwaliya, kai kuwa sai kace wai Najeeba Najeeba Najeeba ce aka daura aurenta da Sarki?
Daria ya fara yana kallonta hade da hawayen dake zuba a idannuwansa
Nunata ya ringa yi da yatsarsa ya ce" wawuya, meye ya tayar maki da hankali? Kema kin san zaki ci kakanki ne? Kema kin rikice ina ni? Kin min bakin ciki yarinya kuma sai Allah ya saka min!
Wani irin ta kurma hannayenta saman kanta ta zube ta shiga burgima fadi take" mama bilahilazi ku yi kiran baba na fasa, walahi na fasa auren mijin Najeeba, dama Najeeba ce dayar? Mama kin kuwa san Najeeba? Mama Najeeba fa kawata wace muke zuwa nan wani sa'in wace kike cewar yarinyar nan tana birge ki dan bata shafe shafen nan na yan matan zamani gata saliha mai kyan hali
Mama na rantse maki da Allah Najeeba kililin kasau ce, kanta a kasan nan take harbi irin na bakin maciji ko harbawa ba'a yi ake macewa
Mama Najeeba ce fa? Walahi halaka ni zata yi, idan wani bai kashe ni ita zata kashe ni dan na tabata sai ta ci uwani da na auran mata miji! To wai me hadinta da shi bayan a duniya ko maganarsa bata so ina mata, irin idan zance ya kawo zance sam bata so a kawo maganar sarautar garin nan bale sunnansa ? Mama ni ke zaune da Najeeba tun safe har dare a saloon dinta, ni ganau ce ba jiyau ba mama da ubwan waye bata dakuwa idan ka kawo mata simple raini bare ni da zan auri mijinta? Mama ki rufa min asiri tun ina numfashi ki hanna abin nan
Da mamaki mamanta ke binta da kallo hakama auntynta ke tareta tana fadin" ke meye wannan, rage muryarki kar ki sa a fara taruwa mana, ki bari mana
Mamanta ta ce" ke yanzu ai abin murna ne ace Najeebar nan dai da na sani ce kishiyar taki, yarinyar da bata taba gaisheni a tsaye ba sai ta duka, yarinyar da in tsintsiya na dauka zata amshe ta share wajen da nake son kimtsaya? Yarinyar da nan in ta zo sai ta baiwa kannenki abin dadi ni kuwa du da ina aiki sai ta min kyautar kudi masu yawa? Yarinyar abin mangari wace nake fadin da Ibrahim dina ya girma sai na aura masa ita domin a duniya tarbiyarta na birge ni shine ke marar kirki zaki ringa fadin kalamai irin haka munana a kanta? Haba Nadia , Haba Nadia nan abanku baya so kina kawaye aman yarinyar nan da kansa ya furta eh lale wannan tana da tarbiya ya yarda ki yi kawance da ita aman shine Nadia zaki fadi haka a kan yar mutane? Ni walahi sai yanzu hankalina ya kwonta zan fita na ci gaba da bikina cikin farin ciki
Nadia ta zabura ta mike tana neman wayarta a haukace ta ce" ina, ina ba zaki gane ba mama, ba zaki gane ba, a daki kike mama, mama baki fita kin san me duniya take ciki ba, mama a zamaninku babu kililin kasau, kai ko akoy ta yanzu nata salon daban ne, mama ki manta wata maganar cewa wai zan je na shinfida sarauta ko na je na yi tinkaho ko na je na kwace miji a hannun zinariya, walahi walahi sai na zama uwa akuya a gaban Najeeba
Kai ina, a watse, walahi a watse an fasa auren nan
Kokarin fita take dan watsar da taron mamanta da kanwar mamanta suka rikota suka yi ciki da ita sunna fadin Huzaifa ya kama masu
Bakinsa ya tabe yana jan hanci ya kama hanyar fita, komawa zai yi wajen auren dan mahaifinsa na cen, zai je na fada masa ashe matar nan da ya fara kekyarawa palas itace aka yi masa wuf da ita
Dannata suka yi ciki suka rufe kafin auntynta ta zaunar da ita tana kallonta ta ce" ke dallah banza zaki mana shiru ko sai na ci ubanki a wajen nan? Dan ubanki kishiyar ce kike yiwa haukan nan? Ke ba mace bace ko ba abinda take da shi kike da a jikinki ba? Dan hauka ko wacece ita zaki nuna ne har ki ringa fadin wai a fasa aure? An ce mana an kashe matarsa kin ce kin ji kin ganima bale wai zama da kishiya? Kishiyarma mamanki na fadin tana da halaya shine zaki zo kina mana hauka a nan? Idan gabdancin ne ke ba zaki iya kwatar kanki a gabanta ba? To Nadia ko a dadaure sai na kaiki gidan nan yau, dan walahi sai an dama da mu, me aka fi mu? Yarinya ke da zaki amshi girma kan girma? Tun da abin nan ya samu nake takawa ina daga kai da bakin gilas a garin damagaram, kin san da rububin kawance ake da ni dan yar yayata zata auri sarki? Zan ci uwaki idan kika raba ni da farin cikin nan walahi! Idonki idonta zaki mata murmushi ki ce da ita" hello yar uwa ki bata hannu ku gaisa!
Sai me? Ke ko yar uwarki ce idan halal ne ku jera an fada maki zamu tsaya ne? Yarinya ko ni uwarki yace yana so idan halal ne bara ki ji zan zo mu jera ne bale wata kawa
Dallah warware mana maza shiga wanka mu fita mu yi jiran dan sahun dan na ga take taken ki yar iska ce ke kina iya saka min hawan jinni!
Mahaifiyarta kam mace ce mai sanyin gaske, kuma ita bata ga wani abin tashin hankali a nan ba, wai Nadia bata ji tsoron an ce ana iya kasheta ba sai tsoron dan za'a mata kishiya kawarta mai mutunci? Du irin yanda suka ringa fadawa mutane auren nan? Ita kanta sanadiyar auren nan yau mai gidansu baki daya ya zo daurin aure tun da safe da shi aka rankaya gidan sarki har ce mata ya yi ta sama masa number sarkin shine wai Nadia zata yi mata haka?
Karshe dai tun a lokacin auntynta ta gama shiryata ta fita ta samu hanya ta ce ta fita gatanan
Ta san sarai wacece auntynta, tabas kamar yanda ta ce ta kiyayeta zata ci kaza kazancinta zata aika dan haka da nikaf din tamkar munafuka ta fice a gidan ba tare da an farga cewar amarya har ta fita ba
Sai da ta bushi kasa ta ce zata je ta karbo dinki da dabara ta fice a gidan banda yayarta ba wanda ya san nufinsu sai mahaifin Nadiar wanda shima sarkin ne da kansa ya masa bayani bayan an gama daurin aure
Bakin titi suka samu suka zauna, Nadia kam wani irin murdawa cikinta ke yi, ita fa kallonsu kawai take, ba zasu taba fahimtar abinda take nufi ba, baki daya wani zumudinta, wani farin cikinta, wata takamar da ta dauko ta yi mata sanyi, abu daya take furtawa auntynta shine" aunty, ni na zauna da Najeeba, Najeeba uwata ce a iya bariki, ki barta kawai inda kika ganta dan na tabata kema zaki so ta idan kika hadu da ita bare mai Martaba, ita fa ba wai bakin hali ne da ita ba, aa, abinda zata aikatawa du wace ta kalar mata sahibi ne mai yawa, takan ce na tsani kishiya, ba zan auri mai mace ba, idan kuwa mijina ya kali wata sai na mata *salatu* irin na maza
Daria auntyn nata ta yi tana gannin yanda ta rikice, lale zata tsaya har a sada Nadia da dakinta domin a irin yanda du irin firiritar Nadia ta haukace din nan daga jin maganar daurin auren nan ina da an kaita gata gata?
Kallonta ta yi ta ce" kin ga, zuwa an jima zamu cika fadar nan kwonmu da kwarkwatarmu, du abinta zata ganki zagaye da dangi dan haka ke da ita sai dai kallo, idan ta zo da mutunci a yi, idan kuwa ta zo da rashin mutunci a yi
Nadia ta dago kanta tana gannin wani adaidaita sahu da bashi da number a jikinsa, sannan sabo ne dal ua tsaya a kusa da su bai masu magana ba aman su yake jira ta ce" baki san su waye MUTALAB FAMILLY BA? ai inda zamu je din gidansu muka je, zamu tardata tatare da iyayenta da yan uwanta danginta, aunty idan ta kama a zane mu za'a zane mana jiki ne tasss walahi
Itama zuea lokacin jikinta ya yi sanyi, sai dai bata nuna ba, ta jara karfafa mata gwuiwa ta ce" Nadia, ai yanzu ba ke ba, ko ni zane ni sai ruwan sama walahi domin na zama uwar matar Mai Damagaram, tashi mu je, mijinki na kare lafiarki kina hauka, na tabata sonki yake a yanda ya damu kar a kashe ki
Haka suka tafi cikin dan sahun nan su duka da nikaf
Abinda aka bincika kawai shine idan basa dauke da wani mugun abun kafin su shige ciki
Sunna shiga kuwa Jakadiya da Anmy ta turo tarbarsu, ita kanta bata san ko su waye ba ta ja su bangaren Amaryar sarkin ta buda masu sannan ta yi baya
A nan suka zauna sunna karewa tanfatsetsen falon kallo cike da wani yannayi
Kai da ace hankalinta a kwonce da idan ta fara daukan hoton wajen nan? Yau itane zaune a cikin gidan sarki, a cikin daki, malakinta, a matar sarki? *Akoy shagali*
A lokacin da karfe hudu ta yi na yama, a lokacin Anmy ta bada umarnin a kai ZINARIA, da NADIA dakin gyaran amaren da tuni aka shige ciki da Najeeba aka shiga gyarenta ,
dan kimtsa su domin baki dayansu za'a fitar da su ne babar runfar da a nan za'a hadu da MAI MARTABA bayan salar isha'i dan a gabatar da junnansu a babar runfar wace ake cen ana ta kara kawatata domin ba kowa zai kasance a wajen ba sai shakikan amaren da kuma su Anmy din da shi kansa sarkin
Shirin ba na wasa bane, dakunnan duka aka shige da amaren da kuma Zinariya ya kasance kowace da wada ke tsaye kanta
Sai da kyar aka samu Zinariya ta yarda da shirin nan, shima sai da Anmy ta yi hakuri ta kara tura masu jakadiyar sarki kafin mamanta ta yarda a fita da ita a je wajen shirin amaren
Shiri ake masu mai tsafta, shiri mai class, shiri mai daukan hankali
Mai mak'up ce ta fara zane masu fuskokinsu da royal mak'up mai shegen kyau da tsari lafin masu gyaran kai su shiga kiciniyar yi masu abinda suka zaba a yiwa gashinsu duda Nadia bata da gashi sosai aman a haka akaiwa kanta wani irin coiffure ba tare da an saka atach ba ya yi kyan gaske harma ta ringa ayana dama gashinta na kwaliya?
NAJEEBA kam kallon mutane take, masu gyaranta a yau sunna yi ne sunna rarashinta, wani girma ta dauka a yau wanda suke girmamata da shi, ko magana zasu yi mata da wani yannayi na daban mai matukar girmamawa suke yi mata shi
A daidai wannan lokacin ta fi daukan shiru a kan ta ringa zubar da hawaye
A jiya zatonta ba zata waye ba, irin yanda jikinta ya tsananta zafi, a tunaninta za'a fasa, sai dai tana ji tana gani aka ci gaba da dura mata abubuwan dake kara saka mata kasala , tana ganni Abihnta ya ringa murnar gannin yanda fatarta ta dawo da irin yanda ake kula da ita, tana gannin yanda yayunta ke wani irin farin ciki harta da Nusaiba an yanyara mata kitso kannanu an shiryata cikin yar rigarta ta barbi mai kyau
Tana kallon yanda yayanta ke amsa waya hakoransa waje yana ta fara'a yana shaida yana gaiyatar daurin aure gobe a fada zai aurar da kanwarsa
Daga nan ta kara sarewa lamarin sai kawai ta aro shiru ta yafawa kanta, tsakaninta da kowa ido ne bata cewa um bare um....um
Irin yanda take fitar da kamshi ko fitsari ta yi baki daya kamshin turaran ke fita a jikinta, irin yanda suka mayar da fatarta ita kanta takan ji a yanzu take mace mai classs
Irin lesson din da suke bata kamar da wasa ya zama attitude dinta, domin a yanzu a cikin idannuwanta zaka fahimci halin da zuciyarta ke ciki
Suturunsu duka masu ruwan sararin samaniya ne, sai alkyabobi farare kar masu dauke da duwatsu da wasu irin kwaliya
Zinaria, har zuwa wannan lokacin bata san wa aka aurawa mijinta ta biyun ba, domin yayarta da ta fita neman rahoto tsaf ta ji ko wacece aman tsoron ta kai labarin nan da bakinta ya sakata nuna kai ita bata fahimci ko wacece ba
Abinda ya sa kuwa shine, ba yau ba Najeeba ta zama makiyiyar zinaria da mahaifiyarsu , idan har suka ji wannan bayani ta tabata ba za'a yi da kyau ba abin zai shafi har ita
Yannayin zinaria har yanzu a bayane ranta a bace yake fiye da tunanin mai tunani
Sai dai ta fasa ihun kukan domin ta wuni yi a jikin mahaifiyarta, sannan itin alkawarurukan da mamanta ta mata cewar ta zuba ido ta gani ba wata shegiya da zata yi kishi da ita ya sakata yin shiru tana sauraron ana mata kwaliya ana shiryata
Sallah kawai ke tashin su, har zuwa lokacin da aka gama shirya su
A lokacin da Anmy ta ringa bin dakunnan su ita da Ummu sun ga kwaliya
Sosai Zinaria ta fito a hajia matar sarki hakorin makarta ko yaya ta juya ta dan daga bakinta yana walwali
A haka suka ajiye sarkar da suka shigo da ita dan a saka mata sannan suka nuna cewa ita za'a fara rakawa dan ta tarbi kannenta
Ita dai kallonsu kawai take har suka fita kafin ta ja wani uban tsaki har mahaifiyarta ta yi gagawar banka mata wani kallon da ya sakata sada kanta domin masu kwaliyar ba tafia suka yi, su kansu da mamaki suke kallonta haka kawai sai suka ji girmanta ya zube a idannuwansu domin mahaifiyar mijinta ne ta yima haka, yo kishi hauka ne? Bale gidan sarauta ai ta san da za'a mata kishiya!
Dakin Nadia suka shiga
Irin yanda ta sada kanta abin ya basu sha'awa, gaishe su ta yi kanta a sade sosai
Ummu ce ke kallonta, kwarai ta so shaida ta sai dai sam sai ta ki yarda ko wacece, a haka itama suka ajiye tanfatsetsiyar sarkarta suka fadi cewa nan da minti ashirin za'a shigo a tafi da ita
Daga nan sai suka yi wajen Najeeba
A lokacin da suka shiga, ZAHRA ce tsaye tana ta yi mata vidio tare da wani sauti mai sanyi da ratsa zuciya su duka tana daukansu vidion ne har ita da yaya Dayabu wanda shima ya shigo a karo na uku a yau yana hankalce da kin maganar Najeeba sai dai ya yi murmushi kawai ya kyaleta, gwara ta yi shirun da ta ringa ihun kuka haka kawai kan abinda ba za'a fasa ba
Tun da Anmy ta shigo sai ta ji idannuwanta sun cika da kwallah
Ta kasa yarda cewa Najeebanta ce zaune a wajen nan, saman wata kujera mai alfarma an rufa mata alkyabarta a saman daurin dan kwalin da ta sha mai tsari da kyan fasali
Karasawa suka yi su dukansu sunna kallonta
Anmy ta fi kusanci da ita inda yan matan du suka kara rukunkume Ummu, hakama yaran da ta yi yan kwanakin nan sun matukar sabawa da ita kamar wata mamansu
Anmy ta kamo habarta kadan ta dago dubanta
Sunna hada ido Najeeba ta yi raurau da idannuwanta
Kai Anmy ta ringa girgiza mata a hankali ta ce" kar ki bari su zubo su bata kwaliyar nan an matana, kin ga yanda kika yi kyau? Kar ki bari wannan rana ki yi hawaye
Najeeba kin san farin cikin da nake ciki kuwa?
Da kin san yanda nake jin nutsuwa da auren nan da sai kin fi kowa murnarsa
Kuma juyota ta yi sosai tana amsar sarkar da Dayabu ya bude ya ciro ta zinari ce su dukansu iri daya
A hankali ta shiga daura mata kafin ta ce" abinda muna tare, ina nan fa, ina tare da ke fa
Najeeba ta ringa sauke ajiyar zuciya
Mahaifiyarta ce ta matso kusa da ita
Itama idon ta kura mata, wai ita ta haifi santaleliyar yar nan? Lalle Allah ya mata kyauta ta saka kafa ta shure ta tafiarta?
Murmushi ta yiwa Najeebar dake kallon fuskarta, mamanta sam bata tsufa , bata da kaurin jiki hakan ya sa bata wani zaune ba, sannan cikinta bashi da yannayin wace ta haihu dan mace ce mai matukar kula da kanta
A hankali ta dan lumshe mata ido bata cire dubanta da karfin nan ba hakan ya saka Ummu sakin ajiyar zuciya a boye tare da saka ran watarana zata dubeta
Nan suka lalace sunna ta daukan hotunna da vidio,
Ba wanda ya dauki maganar nasiha, Anmy ce ta katse hakan cewar su bar mata y'a zata yi mata a nitse, to nasihar wacece ba'a mata ba, har mai wa'azi aka kirawo ta mata sosai sai dai abinda ba za'a rasa ba
Sai da aka dauki kusan minti arba'in sannan su Anmy suka fara tafia
A lokacin da suka nufi runfar aka shaida masu Sarki ya hana zama a nan ya umarci a je falonsa na kurya mai dauke da su camera da sauransu
Nan suka nufa cike da ayar tambaya, sunna cike da mamaki
Kasancewar tuni yana cen ciki ya saka Anmy na samun waje suka hakimce ita da Ummu tana hangen su Gimbiya kusa da zinaria da wata yayarta,