Showing 42001 words to 45000 words out of 228147 words
Chapter 15 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
godewa Allah da samun baban d'a mai hankali da nutsuwa wanda yake iya yinsa dan gannin yana gyara irin barnar da shi ke aikatawa
Koma meye dalilinsa na sakin mata bashi da kyau domin saki Allah ya halata shi aman shi kansa baya son sa
Shin y'ayansa sunna jin haushinsa ko? Irin yanda yake korara matansa haka kawai
Akoya matarsa da ya saka wace zai iya rantsewa bai kamata da laifin komai ba, ya saketa ne dan ya wayi gari da maganar cewa a kan me ita zai barta bayan ya rabu da iyayen sauran? Sai mahaifiyar NAJEEBA wace ta maka shi a kotu sai ya saketa
Murmushi ya kuma yi yana kallonsa ya ce" yayansu ka manta ku goma sha takwas ne y'ayana na cikina?
DAYABU ya dago ya kurawa fuskar Abih ido, a hankali ya ce" aa mu goma sha tara ne Abih
Gabanta Abih ne ya yi wata irin yankewa ya fadi wanda hakan ya saka shi saurin zabura yana kallonsa
Su goma sha tara ne?
Ku goma sha tara ne? Ya maimaita masa da sauri ya dora da fadin" a ina ka samo ta cikon sha taran?
Fuskarsa dai ya kuma kurewa da ido yanai masa kallon nan da ake fadin kai ka san na san da hakan
Sai ya yi gagawar basarwa yana murmushi ya ce" Abih, na manta ne, wani sa'in fa garin magana har cewa na yi mu goma sha uku ne sai da zahrau ta yi ta min daria
Wata biyayiyar ajiyar zuciiya uban ya sauke sai dai sak ya kasa sakin jikinsa su ci gaba da hirar kamar yanda suke a dazu
Sarkokin ya kuma rikewa yana fadin" ina ta NUSAIBA?
duban mahaifinsa ya yi ido cikin ido a karo na biyu ya buda bakinsa ya ce" ban yi da ita ba
Uban ya tsare shi shima da ido, kamar yaya bai yi da ita ba? Amsar ba wata a boye take ba a bayanne take cewar bai yi da ita ba
A kan me bai yi da itan ba? Mantawa ya yi ko yi ne bai yi da ita ba? Aa ai ba cewa ya yi ya manta ba, cewa ya yi sak bai yi da ita ba
Sai ya ji wani shaku da tsoron son jin abinda ya saka yaron nasa na farko a rayuwa yin wani abin kyautatawa wa kannensa banda daya a ciki
Hakan ya saka shi fadin" gaba kuke da mahaifiyarta har yanzu wanda ya shafeta ko wani abu mahaifiyarta ta yi maka ne?
DAYABU ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi ya ce" Abih, ka san bamu taba zuwa muka kawo maka karar matarka ba
Da yawa wasu matan ka sake su ne dan kawai idannuwanka sun kama wani abinda bai dace ba a kanmu
Ban san girman laifukansu ya dame nata ya shanye ne? Ban san ita din lale gaskiyarta ne itace rayuwarka ba? Abinda na sani shine na gaji da sakin mata da kake, kuma bana so ka kuma sakin mace dan a yanzu na lura lalefa kanena sun taso har sun fara gabatar da mazajen aure wanda nake fatan idan sun shiga sai dai a fitar da gawarsu fita na har abada
Abih abin zai yi matukar wahala sai dai ikon Allah kawai zai kubutar da su
Shine nake so ka yi kokari ka yi zamanka da matarka , in sha Allah idan dai mune damuwar ba zamu kuma zama damuwa ba aman fa Abih muma a kiyaye namu rayuwar dan kai ka san cewa ba zan iya lamuncewa mutun shiga hakin yaran da nake yiwa kallon marayu
Basu rayu da baban jigo na rayuwa ba wato uwa
Hakan ya saka nake yi masu uzuri a rayuwar yau da kulun, hakan ya sa nake kara jin tausayinsu
Abih kam ba amsarsa ya samu ba, sai dai gannin yaron nasa ya daure shi da jijiyoyin jikinsa sai kawai ya yi masa shiru bai kuma tofa komai ba aman ya kuduri niyar tambayar ita natar tasa dan ya tabata bafa zasu fada masa komai ba tunda har yayansu ya hana............................
Sarkokin ya mike da su ya nufi cikin dakansa
DAYABU na zaune yana kallon ikon Allah, Abihnsa zai fito ya bashi sarkokin ko ba zai fito ba? Har ya kusan cin rabin awa karshe ya mike yana murmushi ya girgiza kai ya yi gaba dama ya yi hakan ne dan ya isar da sakon cewa ya cire y'arsa a cikinsu!
Ihu ta saka bayan ta kashe kiran da suka gama da Anmy
Da wata irin daria ta ce" jama'ar gidanku wannan karron ina gayya, ina gayya ne da kaina kuma sai na buga wasa a kofar gidan sarki
Ummulkhair ta dago daga yankan akaifunta tana yiwa kanwar nata kallon anya Najeeba baki haukace ba kuwa?
Najeeba ta ce" ke ke aunty, wallahi du jarabar da za'a yi sai na kirawo ANNABO MAWAKI ya kada min waka da orchestre na shiga na cashe domin kuwa *DUNKUM* zai kara aure inji Anky, kuma auren nan da kwana biyu ne taxe maza maza mu je wajen mai dinki ta tura sakwanninmu mu zabi kalar da muke so
Zahrau ta fito da waya tana daria itama ta ce" haka fa sannan Anmynki ta ce kar ki yarda ki dauki dinkin da bai mata ba dan ba sakashi zaki yi ba!
NAJEEBA ta waiwaya tana kallonta ta ce" wai kin san aurensa mai yake nufi? Hehehe, yana nufin za'a kawo wata yar rainin hankalin ta biyu wace zata ci min uwar wace ta raina halitar Allahn ta farko ta dane min kan banza ta daki bakin mai bakin shegun nan, zamu ga karyar zagi da takama za'a yiwa zinariya kishiya da gold🤣🤣🤣🤣
Hum a dai a slow najee
[31/03 à 21:37] Sadjida: 🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻🧕🏻
*Na*
*SAJIDA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
16
Hakan ne ta kasance abu na manya nan da nan abubuwa suka kankama cikin dan kankannin lokaci a wajen mutanen da suka iya aiki da lokacinsu
Nan da nan mutanen da anmy ta ringa fadawa suka fara halara cikin masarauta
Su Najeebama sun tare a gidan ne tun ana gobe daurin aure hakan ya sa gidan ya ringa yiwa Anmy dadi ga uwa uba irin yanda Najeebar ke ta yi masu kitso da kunshi cikin nutsuwa a daka
Idonsa cikin nata ya ce" in sha Allah gobe za'a dauran aure ZINARIA
Irin yanda maganar ta daketa ta sakata baki daya yin luuuuu zata kifa hakan ya saka shi yin taku biyu ya damki damtsen hannunta ya tareta a jikinsa ya yiwa bayanta mazauni a kirjinsa
A hankali ya kuma fadin" ki daina yi min garage da yaron cikin nan, dan shine abinda zaki yi mafi ganganci a rayuwarki wato barar min da shi da gangan
Tabas ta gama yarda cewa kwananta ne ya kare a wannan rana a irin wannan lokaci a tare da sarkinta
Kukan da take rikewa ne ya samu damar kufce mata da karfin gaske har tana cicije lebunnanta
Me ya sa? Me na yi? Me na gaza? Kyauna ya rage ne ko hasken fatana da ya saka aka min lakabi da zinaria ya disashe ne ya mai garina? Ta fada tana rike hannayensa baki daya ta kuma fadin" kar ka yi auren nan, idan ka yi na koma baya, idan ka yi ko a cikin kawayena na daina tinkahon kaf cikinmu nice bani da kishiya, idan ka yi min haka ko a masarautar AZ za'a kafa tarihin lamarin domin mahaifiyata ta jima kafin a yi mata kishiya kuma daga ota ta rantse ba kari! Kar ka min haka dan kishiya mafisa ce, balaki ce,
Shin y'ar gidan wani sarki zaka aura? Wani sarki ne ya baka y'a? Wata gimbiya ce ta yi gigin hada aurenka da y'arta bayan ta san wada ke cikin gidanka?
Ikon Allah shine abinda ya tsaya ganni a tare da Zinariya
A yau sai yake gannin ta fi sako reputation dinta a kan gaba fiye da ainahin kishinsa da ya dace ace ta furta kalaman tana son sa tana kiahinsa tana kishin hada shinfida da shi
Da karfi ya juyota sunna facinha din junna inda ta sada kanta kasa jikinta na bari tana mai ci gaba da kukan nan
Ya so kwarai da gaske ya rarasheta koda kuwa itane silar karin auren nasa a yanzu
Aman irin kalamanta sai suka nuna masa ita tana tunanin wani abu na ta isa ya jinkirta masa karin aure? Ashe har takamar mahaifiyarta kennan cewa wancenma da ta shigo da kyar ne kuma daga ita ba kari?
Murmushi ya sakar mata daga cikin rawaninsa wanda rabonta da gannin fuskarsa kiri kiri tun randa ta shigo ya yi mata gargadi da idannuwansa
A hankali ya furta" sai ki ce da du wanda ya yi maki tambayar yanda aka yi aka maki kishiya cewa *komai ai mai shudewa ne, ko ya bace bat ko a cenje shi*
Yana gama fada ya juya yana tafe cike da kasaitarsa da mulki ya shige cen ciki domin dama a falonsa baba ne suka yi maganar
Wani ihun kukan ta saki tana ta rike kanta mai sanye da hular alkyaba
Da sauri ta juya dan komawa bangarenta, ya zama wajibi ta yi kiran mahaifiyarta ta sama mata mafita
Baban abin takaicin auren gobe? Me ta masa? Shine abinda ta fi maimaitawa hankalinta ba a kwonce ba
Ashe shine dalilin tarewar wadincen yan iskan yan uwan nasa a bangaren uwarsa ko? Shine dalilin zuwan mutane a yau din nan sosai gidan ko?
Har ta fita tana takama ta bi ta gabansu ashe su daria suke mata sunna kallonta ne kawai???????
?..................
Tana zuwa ta samu ta yi kiran mahaifiyarta tana kuka ta fada mata labarin da ya zama mumuna a wajensu
Ranta bace ta daki gefen bed dinta ta ce" ke, ki nutsu, ki saki ranki a yi komai da ke
Aman yanda na hakura mijina ya rabi wata y'ayana na haramta masu
*ZINARIYA na rantse maki ba dai shi ya rabi wata ba in dai ina raye!*
Da wadinnan kalaman ta samu jin dan sanyi a ranta sai dai cikin bacinta ta ringa jin mararta na kulewa, tana farkawa ta ganta cikin jinni, wanda dama an daure mahaifar ne dan kar ya zube tunda Aliyu ya rasu ta ringa dan zubar da jinnin nan
Washe gari
Abin da akai a kuraran lokaci sannan mai auren ya nuna ba zai yi taro ba aman bai hana cikar fada ba
Sosai ake shagulgula an yanke sa dankara dankara wasu an shiga gashinsu wasu an yi madafa wajen masu aikin abinci aun dora su sai yi suke
Masu busa na yi kamar ba da bakinsu suke busar ba, hakama masu doka gangar kidan barebari da makadan larabawa
Kidan barebarin ya kasance kidan gado ne na mafi uawancin mutanen dake cikin garin damagaram *DAMAGRAM*
Ko sunnan Damagram ya samo asali ne daga yaren bare bari wato barbarci hakama zinder dake nufin zindir
Wajen ya dauke su, dangin mahaifinsa sun halarta du mata ne sai baza kamshin turaren wuta suke da takama da mulki...dama an san babarbare da dan karen isa koda kuwa ba jinnin sarauta bane
Fararen barebari ne da suka samun farin a wajen mahaifiyarsu Allah ya jikan rai, mahaifinsu kuwa tsabar baki har wani shuni shuni yake
Maakadan bare barin na yi ne da busa inda manyan mata masu ji da kansu ke dan takawa kadan su yiwa jinnnin sarautar kara
Bangaren Anmy kuwa itama daga waje ne masu harkar larabawan ke yi wata mata ce ke wakar da makadanta sunna karkada wani abu yana yin cas cas cas
Tun dazu a nan Najeeba ta fi auki, idan ta mike dan ta amsa kira ne da sauri ta dawo tana kallon dukan yanda suke yi
Sai da ta gama fahimtar takun rawar nasu da irin yanda suke juya kugunsu da wani karfe a kugun nasu mai dauke da yan kannanun karafuna farare tass sunna kara yas yas yas ta mike ta zagaya wajen daya daga cikin marayan
Da murna ta cire abin ta daura mata saman watsetsiyar shadarta da akaiwa wani irin zubi tun daga sama har kasa
Na kafar ta amsa shima ta daura da kanta sannan ta kunce irin daurin dan kwalin da ta nada ta samu ta dora shi sama kadan ta dan soke shi ya bada kalar ture ka ga tsiya
Ana gama dayar wakar aka saka wata,
A hankali ta shiga karasowa wajen rawar tana kada iya kugunta banda saman jikinta tana dan juyi a hankali a hankali sannan na kafar natama tana kadashi da dabara hannanenta su duka biyu tana wasa da su ta hanyar juya su tamkar na macijiya tana wasa da su sak irin rawar kwararun larabawan nan
Gaba daya wajen ya hautsine da buda da daria ,
Ido Zahrau ta zaro cike da mamaki tana kallonta, Bilkissu kuwa ta shige da gudu itama tama biye da yayarta sunna yi tare abin dai ba'a cewa komai
Da sauri Anmy ta mike da alkyabar jikinta ta shiga takowa cikin nutsuwarta ta fito dan gannin da gaske ne abinda abinda Rukayya ta fada cewar ai ga Najeeba ta shige filin rawar
Ai kuwa itama sai da ta zaro ido dan rawar da take din bata san a ina yar ta koya ba, uwa uba ita din kanwar sarki ce, gashi sarkin yana cikin gidan yana falonsa , falon da yana iya hangen du abinda yake wakana ta nan ta droon din dake yawo yana daukan dukan rahoton wajen ko ta windows dinsa wanda tana fitowa droon din kuwa na daidai ita
Ajiyar zuciya ta sauke gannin gaba daya mawakiyar ta nufota tana ta kodata da larabci hakan ya saka har wani yam yam take ji
Abin fa ya karkato da hankula dan harta kannen mahaifinsa sun maido hankalinsu, wasu daria suke sunna tafi wasu kuwa cike sa takama sula cire kai sunna dan tabe baki irin abin ya basu haushin nan
Yarinyar baiwar dake bin Anmy da jakarta ne ta bi bayanta a lokacin da ta nufi wajen kidan
Ido ya kura a hankali daga kwoncen da yake yana biye da droon din daidai anmynsa dan shi har ga Allah baima ga abinda ke faruwa ba ya dai ga fitowarta ne
Gannin tana nufar wajen kidan nan ya dan lumshe idannuwansa a ransa ya furta" anmy, me zaki je yi wajen nan ne?
Bai karasa tunaninsa ba idannuwansa suka sauka a kanta
Irin yanda take kada kugunta tana yiwa anmy murmushi gefenta kanwarta ce itama tana kokarin yin irin na yayar wato mai sunnan gimbiya
Aubahannalah
Shine abinda ya furta a fili a hankali
Fuskarsa ne ya shiga hadewa yana mai bin abin da wani kakausan kallo kamar a gabansa take
Tunaninsa Anmy zata janyota ne ta fitar da ita, sai ya ga ta yi mata magana a kunnenta kafin ta kalli yarinyar dake rike da jakarta
Buda jakar yarinyar ta yi ta duka sosai gaban Anmy
Anmy ta saka hannunta ta dibo wani irin damin kudi dami har hudu masu aku ta dora saman kan NAJEEBA mai dauke da dan kwalin nan
Bata gama hautsina wajen ba sai da ta ciro sarkar zinari ta dora sama
Ai kuwa mawakiyar nan me zata yi banda kara kwarin muryarta da rangada guda sannan suka duka Najeeba ta sauke masu karinsu
Hannunta Anmy ta riko suka fice a hankali suka fita baki daya
Sunna fita ya kuma binsu da droon din
Anmy ta juyo ta kalli abin
Yar karamar yatsarta ta nuna ta ce" kin kyauta Najeeba, kin san sarai yayanku ya tsani rawa ko? Shine yau kika cashe a gabansa domin wannan abin da kike ganni yana nufin a hannunsa abin sarafashi yake
Wani mukut ta yi da yawun bakinta ta matsa kusa da Anmy ta rage muryarta ta ce" Anmy ai kina nan ba zaki bari a min komai ba, kuma anmy alkawari ne na yi idan zai kara aure sai na yi rawa ni so na yi fa na kirawo Annabo
Gaba daya ya zaro ido domin baki daya wani motsi da magana idan kana son ji zaka iya dannawa ka ji hakan ya saka shi dannawar dan jin da me zara kare kanta sai ya ji ashe ita so ta yi ta dauko makadin nan dake kade kade a cikin garin ta kawo shi wannan gida na alfarma ya kada mata me?
Sai kawai ya ji yana sakin wani kakausan murmushi yana girgiza kansa
Shi kadai ya san da abinda zai yi masu daga ita har makadan sai kamaninsu sun sauya
Anmy ta ringa gyada kanta tana kallon yar tata
A hankali ta ce" Najeeba, maza zo cenza kayan nan ku je tare da yan uwanki ku yiwa amaryar kwaliya domin daga an shiga salar magariba za'a shigo da ita ta baya
Kanta ta gyada ta yi gaba abinta
Sai da sukai salar la'asar suka fito su hudu reras cikin wani irin danyen lesh kowace da kalar da ta dauki fatarta
Wasu tsadadun alkyaba ne suka dora sama wanda dole ka kale su ka kuma kallo sannan ka yaba koda baka shirya hakan ba
Bayan wata dankareriyar mota fara kar suka shiga su dukansu
Direba ne gaba da wani bajimin dogari zaune fuskar nan tasa uwa an zagi mamansa sam ba fara'a
Da wani irin gudu yake ratsa manyan titunnan garin fit fit fit
Kasancewar motar da number gidan sarki ne ya saka sojojin dake hanya da polisai sam basa gigin tsayar da ita duda ba sarkin ne a ciki ba
A hankali NAJEEBA ta ce" *kudi* masu gidan rana kuna gannin mutannen mu da su sai kallo basa tsayar da motar dan tambayar takarda
Ummulkhair ta yi murmushi ta ce" aa Najeeba, sarauta dai
Kudi ai kowama yana iya yinsa
Sarauta kuwa gado ce
Ko baran gidan sarki wani ne a cikin garin sarki bale ka shiga wannan mota? Inaga ko kwaya ka dauko zaka samu hanyar shiga da