Showing 87001 words to 90000 words out of 228147 words
Chapter 30 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
kanshi uwa uba saukin kansa ya saka eh lale zata iya zumunci da shi
Kwarai ta ji dadin da ba soyaya ya nuna mata zai yi da ita ba, domin kuwa a tsarin rayuwarta farin mutun baya cikin tsarin namijin da zata iya soyaya da shi ko na second daya
Kuma kai dubanta ta yi kansa, mutumen na tare da wani irin kwarjini, girmansa ya bata mamaki irin yanda farinsa kuwa yake har ya zarce matan nan masu karin mai a kan nasu
Wayar ta amsa ta saka numberta wace idan an kirayeta ana samunta ko wani irin time kafin ta mika masa ta juya tana daga masa hannu
Daga inda yake tsaye ya bita da kallo inda dogarin ya koma da gudu ya bude mata wajen zama ta shiga ta zauna
Wani uban tsaki ya ja yana yin kwafa ya koma ya zauna da wayar a hannunsa wada ta saka numberta
Ni SHAHEED ni ne yaro? Sam halitata ce bata yi mata ba? Wani murmushi ya saki yana dan kara cije leben nasa na kasa cike da takaicin abinda ta fada
Haka kawai ya ji yana jin haushin kalamanta
Kansa ya dan kara girgizawa yana mikewa dan karasawa ya huta a ransa kuwa fadi yake" sannu sannu bata hanna zuwa yarinya, abinda na yi niya a kanki sai na cinma burina marar kunya!
Sun hade a falo sun yi hira kamar yanda suka saba, Anmy na tare da su tana jara hankalcewa da yannayinsu baki daya, sai Ummu da ta wuni da ita tana ta kokarin gannin ta fitarwa da yarinyar abin daga ranta , ba laifi ta dan kara sakuwa kan yawan shiru da kukan da ta dauka na kwana biyu
Da sasafe wajen karfe tara, Najeeba ce tsugune kusa da kafar Anmy bayan sun kara gaisawa cikin kara sada kanta ta ce" Anmy, dama saman maganar tsayar da mutumen da aka ce din nan ne, akoy mutane biyu da muke tare nake son a rokar min alfarmar su fara zuwa a cikinsu sai a ware guda in sha Allahu
Da sauri ta dubeta, da wani yannayi mai cike da rashin jin dadi, saurayi? Zance? Kennan tana da wanda take so ko me?
A hankali ta ce" Najeeba, kina da wanda kike so ne a cikinsu?
Najeeba ta kara sada kanta irin kana jin kunyar nan ba zaka iya yin magana ba, hakan ya kara sanyaya gwuiwowin Anmy
Muryarta kasa kasa ta ce" ki basu dama
Kara sada kanta ta yi ta yi godiya kafin ta mike daga ita sai rigar bacin dake jikinta wace ta kafe a jikinta , rigar bata da shara shara sai dai kasancewar ta velour sai ta lafe a jikinta ta yi mata dass ta fitar da tsarin halitarta
Da kallo Anmy ta bita har ta shige dakinsu dan zuwa ta shirya ta fita wajen aikinta kafin take sauke wata nanauyar ajiyar zuciya
Shin da wa zata iya yin irin maganar nan wanda zai bata kyakyawar shawarar da mutane ba zasu ga ta yi son rai ba? Da wa zata zanta wanda zai dubi lamarin da duba irin na fahimta ba zai bi bayan dayan biyu ba ya bata shawarar da ta dace?
Tabas ba zata iya tauye yarinyar kai tsaye haka ba,
Waye wanda zai bata hanyar da zata bi cikin ruwan sanyi ta samu cikar burinta? (ya mama ta ce ku shige daka tana da kyakyawar shawara Anmyπ)
A yau da ta tashi sai ta yi shiga cikin wando na jins irin wanda ke dame kafar nan daga cen kasa sannan ta saka riga ruwan pink color mai dogon hannu da botira daga gaba
Da ta zo bala botiran sai ta bar daya bata bale su dukansu ba sannan ta caje gashinta da kyau ta daure shi a tsakiyar kanta
Turare ta bulbulawa jikinta kafin ta dauko wata abaya baka sidik wace sam bata da siri domin tamkar sange haka take ita dai an sakata ne dan kar a ce ba'a saka abin rufa ba ta dora abinta ta dora abin kan saman tarin gashinta mai tsayi da baki
Kusa da Ummu ta je ta rage tsayinta ta mana mata kiss a kumatunta sannan ta buda Jakarta ta ciro kudi kimanin jaka hamsin ta mika mata tana kallonta ta ce" kin rage fara'a yayar Najeeba, hakan kuma na saka ni aiki da rashin kuzari
Da murna da kuma mamakin yau ta bata kudi daga tambayarta ta dauki kudin tana kallonta ta yi yar dariya ta ce" yau nice yayar taki? Kin yarda kennan?
Najeeba ta yi daria har fararan hakoranta suka bayana ta ce" idan har zaki saki ranki, idan har zaki daina tunani kina dorawa kanki abubuwa zan yi ta kiranki aunty na rantse
Murmushi Ummukulsum ta yi tana saka kudin cikin jakarta ta mike itama ta dauko hijab dinta dogo ta saka ta ce" mu je, nima yau zan yi aikin
Ai kuwa da murna Najeeba ta kama hannunta suka fito,
Takalmi ta saka mai ruwan pink sai jakarta itama yar karama pink mai kyan gaske suka jero
Salama sukaiwa Anmy dake zaune tana neman wayar maman Najeeba ta kasa samu suka fito
A yau masu tsaron sun kasance har mutun hudu hakan ya baiwa Najeeba daria ainun
Mota biyu suka fita da ita dole, motar Najeeba da motar Ummukulsum har zuwa shago
Ta yiwa mutane kwaliya sosai, ummu na tayata hakan ya saka ta saki ranta har tana ta murmushi inda kira ya wuni shigowa a wayarta aman ta ki dauka domin Najeeba ta tare ta hanna ta ce" tabas ba zai samu lamarin da sauki ba!
Sai bayan magariba suka zauna inda suka samu indomi da kwai da kif8n gwangwani suka gwongwaje
Mikewa najeeba ta yi ta dauko masu wata gora ta dauki kofi ta cikawa ummu ta miko mata
Ummu ta amsa ta kafa kai ta shanye tass kafin ta yi yar gyatsa
Najeebama ta cika ta kwankwada sosai ta rufe ta mayar frij
Ummu ta ce" Najeeba da me da me kika hada wannan kuma ke dai akoy fitinaniya
Najeeba ta yi murmushi ta ce" baki ga hadin da maman Zahrau ta kawo mata ba? Shine na saka ta tambayeta me da meye a ciki
Ai sabuwar tatsa ce ta rakuma sabon haihuwa na hada mata karanfani mai yawa da kuma zuma sabuwar saka ke ni idan na sha dadi nake ji a zuciyata
Ummukulsum ta ce" walahi kuwa, nima ai wani sanyi na ringa ji a zuciyata sannan abin kamar yana ratsa gaban jikina
Sai da dare ya yi suka fito suka kama hanyar gida yau ba inda zata je domin sun cika dare a saloon din
Tun daga bakin kofa suka ga wani lamari, yau su da kansu sai da suka fito aka duba motarsu kafin su samu shiga ciki
Sunna shiga suka samu Anmy su take jira, sai da ta ga shigowarsu sannan hankalinta ya kwonta
Cike da kulawa take basu amsar tambayarsu kamar haka" wasu manyan barayi ne aka kawo dan a yi masu nasiha, shine baban cikinsu ya fitar da layar zanarsa ya so ya bace a gaban mai martaba
Hakan da ya yi ya saka Shaheed gane abinda yake nufi tun kafin ya saka layar bakinsa ya zabura ya damki hannunsa ya kaishi kasa sannan ya take hannun nasa ya saka masa layar a bakinsa ya kuma rike masa numfashi har ya hadiyeta sai dai abin mamaki bai bace din ba
Hakan ya saka Shaheed yin fada mai tsauri a fada domin baki dayansu sai da ya saka suka fitar da asirinsu ya take kafin ya shiga fadin" ashe idan har karyar asirinku zata ci a gabana ni ba jinnin marigayi bane!
Ya daki kirjinsa ya furta" na rantse da wanda raina ke hannunsa daga yau kuna ji kuna ganni sata zata gagareku domin kun hadu da faduwar gaba kennan in dai zaku ayanna sata a ranku!
Sai kuma ya kai dubansa wajen amintacensa ya umarci a je da su gidan horo sannan an bazu neman sauran da suka aikata satar gidan Elhaj Hamza domin sai da suka yiwa y'ayansa biyu fyade sannan suka kwashe komai na matarsa ita kuwa suka sumar da ita
Najeeba ta zauna dabar kusa da Anmy ta ce" Anmy, aman shima mai martabar yana da asiri ne?
Ummulkhair ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Najeeba, daga nan muka yi kallon abinda ke faruwa, Najeeba kin ga irin yanda ya murde jikeken katon nan kuwa? Dogarai suka zaburo da polisan dake tsaitsaye aman da hannunsa daya ya dakatar da su ya kuma murde masa hannun sai da ya hadiye layar da balaki wanda layar ana sakata a baki ake bacewa sai gashi dar a tsaye ba inda suka bace , Najeeba wai kin ga wani irin abu da ya ringa bin jikina na tsoro wani yam yam yam, ni walahi baki daya sai na ga kamar ba uaya shaheed da muke gani a nan dakin Anmy ba, kike maganar asiri, ai da uban asiri yake takama shine ayar Allah
Anmy ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" na san shi da zafin zuciya, aman ban san cewa yana da karfi irin wanda idannuwana suka gani a yau ba, baki daya dogaransa sai suka bude filin kirari maganar da nake maki da kyar yan jarida suka watse suka barshi ya shige ciki dan yin sallaj, tun dazu ina son shiga na kasa
Najeeba ta yi wani malalacin murmushi, a kasan ranta kuwa fadi take, oh yanzu haka wani sarkaci ne ya samu marar karfi, in ba haka ba mutumen dake cikin malunmalunma bashi da wani girma sai tsayi me zai iya yiwa gagarumin barawo?
.............................................
A yau kam cike da wani irin takama ta sadar da kanta da dakinsa, baki daya yau tun da abin nan ya faru aka zagayeta ake mata wani irin kirarin da ya sakata jin du duniya kai babu matar sarkin da ta kaita isa da takama, mijinta jarumi ne a kowani fani, irin yanda ya nan da nan labarin yanda ya yiwa wannan barawo da ya gagari gida da waje, barawon dake tsinkawa manyan alhazawa mari idan ya yi niya, ko kuwa sai ya yi kiranka ya shaida maka rana da lokacin da zai maka sata yana takama da layar zanarsa zai shiga kuma ya dauka ya kuma tafi ba yanda zaka yi da shi, shine yau ya shiga hannun SHAHEED wanda ya jima yana jiran irin ranar da zai kasance gashi gashi su gwada ga da ga su ga wanda zai ci
Wannan lamari ya saka gidanjen TV da radio suka dauka, nan da nan labarai ya shiga gama garin sai murna ake ana shewa ana fadin" wane yaro wane uwar yaro! Wane dan karamin tsagera da tarban babansa, Gurnanin zaki mai ban tsoro yake, shine sarkin sarakuna, tabas a shekarunsa ya kasance yaro ne a kan karagar mulki wanda a lokacin hawansa da yawa sun shiga zulumin yarintarsa zai hau karagar mulki? Da yawa sun shiga tsoro da firgicin lamarin , sannu a hankali suka dawo suke dukan kirji su fadi cewa" su yan kasar damagaran ne, sarkinsu na nan ya kwana lafia, kuma du wanda ya taka su zai taka shi!
Har yanzu bata yi waya da mahaifiyarya ba, hasalima wayar ta kashe ta fi so ta je gata gata su yi wace zasu yi
Cikinta ya fice, tun a jiya kuma jinnin da ta dan zubar ya tsaya duda ba samun karfin jikinta ta yi sosai ba aman ta yi niya zata je ta mika gaisuwarta
Ta san bata isa ba, bata isa ta kawo masa wargin a kan me ya daurawa mahaifinta aure ba, aman ta rantse sai ya yi dana sannin auren da ya daura daga shi har du wani wanda yake tare da shi! Amarya kuwa ko? Zata dawo gidansu da kafarta ko a kawota......
Tun da ta shigo tana binsa da kallo bayan ta zube ta gama yi masa kirari da gaishe shi
Agogon da ya ciro yake dubawa ya dan dakatar yana kallonta
Har ta dan fada, ya san barin da ta yi ne ya hadasa haka ko?
Da kansa ya ringa takowa har inda take
Hannunsa ya saka ya mikar da ita tsaye
Cikin nutsuwa ya janyota jikinsa ya bata kyakyawar rungumar da ta sakata jinta a cikin nutsuwa nan da nan
A hankali ya ringa dan kawo hancinsa jikinta har wajen kunnanta na dama
Muryarsa ciki ciki ya furta" shin jinnin nan ya barki ko yana nan?
Sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta so girgiza kanta dan irin yanda take da sarau din haduwarsu a bed abinda ya saka kennan har a yi a gama take a takure da kasa sakin jikinta sai dai jin da ta yi da gwuiwarsa ya gane bata saka abinda zai tare mata daudar ba ya saka shi tun daga tsayen ya shiga haukatata ta hanyar yin anfani da sajen fuskarsa da dan gemunsa yana giga mata shi a wuyanta
Alkyabarta ya sabule ya yar nan kafin ya saka hannayensa duka biyu ya dauketa cimak ya yi saman bed din da ita
Shinfideta ya yi kafin ya bi bayanta ya shiga cire mata tufafin jikinta, yana yi yana kara kallon yannayinta idannuwanta a rintse suke sannan ta yi aikin da ta saba ta kwonce masa luf ya kasance ko cire tufafinsa ba zata taya shi ba dan ta kara saka masa abin a ransa
Haka ya dane ya shiga dan kokarin gannin ya samu nutsuwar dake matukar damunsa
Ba wani wasa mai armashi, domin du inda ya kai hannunsa ya taba maimakun ta bashi dama sosai ko ta nuna masa tana jin dadi duda ta fi son romance fiye da komai aman ba hali ta sandame idannuwanta rufe
Bai yi kasa da gwuiwa ba ya ringa damkarta yana son ya ringa jujuyata ya samu stl kala daban daban ko zai samu ya samu nutsuwa da wuri, aman abin ya ci tura dan kwonciya daya tak take iya hakuri itama ba wai a daneta da kyau a raraketa ba aa sama sama
Shi da kansa sai da ya wahala bale ita da take wani irin shashekar da ya skaka shi jin abin du ya tsaya masa a rai
Da kyar ya iya kawowa ya sauka a kanta dama ko rigarsa bai cire ba iya abinda ya san zai anfanar mata ya fitar domin ko ya cire din aikin banza ne ba shafa masa jiki zata yi ba bale ya ji dan dadin da yake hasashen ana iya ji idan an yi hakan
Bayi ya nufa yana jin wani iri a cikin zuciyarsa, shin ko zai samu wata malamar dake wayar da kai a irin wannan fannin ya kirawota ta shiga ta wayewa Zinaria kai ne? Ko zai samo irin shawarwarin hakan na wa'azuzuka na waya ya zaunar da ita ya kunna mata ne?
Irin yanda idan yana neman agajin ya samu nutsuwa yake nuna mata cewar ta rike shi, ta shafa masa jikinsa ta taya shi, aman sai ta ringa rintse ido kamar wace ke shan wahalar kasancewa da shi? Shin ya fi karfinta ne take boyewa suke zaune da cutarwa haka ko ita a rayuwarta bata dauki sex da mahinmanci ba? Ko bata da lafia ne?
Ruwa ya kunna ya shiga wanke najasar dake tare da shi da niyar ya yi ya fito ya sameta ya zaunar da ita
Yau kam zai yi mata tambayoyin da yake son idan har ta bashi amsoshinsu ta nan zai fahimci abinda ke damunta, in sha Allahu zai zauna ya yi doguwar magana da ita ya nuna mata shi fa yana son macen da zata zama yar bariki a cikin dakinsa
Idan yau zata daka cinyarsa da kafarta dan ta haukata shi zai bude mata ya yi mata rashe rashe ta taka
Idan yau zata haukata shi da salonta da ya rantse ya gama samun nutsuwa
Abubuwan sun masa yawa
Rigimar cikin gidansu, rigimar waje, ga kuma rigimar cikin jikinsa!
Zai so ya samu nutsuwar jikin nasa dan ya san idan har fa baya tare da nutsuwar nan yana yawan dauke wuta
Da tawul daure a kugunsa ya fito ya kai dubansa saman bed din
Sai dai wayam ba ita ba alamunta
Wani irin takaici ya saka shi bin kofar falonsa da kallo
Ya tabata ta tafi!
Haushin hakan ya saka shi daukarwa kansa niyar koda ta zo da bukata ba zai kulata ba! Yama gama yankewa kansa hukunci a yau aure zai daura a kwanannan, dama abinda ya saka shi dan jinkirtawa rasuwar Bintu
......................................
Bayan kwana
Biyu
Ya kasance yau laraba ce, ranar da yake zuwa fada tun karfe uku dan a cen yake gabatar da salar isha'i, sai dai yana zaune a falonsa na ciki carbinsa karami a hannunsa yana ja hankalinsa kwonce yaka dauke da abin droon dinsa mai hasko masa komai dake wakana a cikin gidan dama dakunan
Tun sunna daka ran fitowarsa har karfe biyar na yama ta yi, su dai basu motsa daga wajen da suke tsaitsaye dan jiran fitowarsa ba
Tunda yaron ya zo ya ga zuwansa kusan minti talatin yana zaune a wajen da aka sauke shi an kayata masa zaman nasa da komai na bukatar bako aman wace ya zo din dominta bata fito ba
Wayarsa dake haskawa kadan kadan ua kai dubansa,
Dauka ya yo ya shiga amsa kiran domin mai martaba ne da kansa
Cike da mutunta junna suke gaisawa kafin ya gabatar da bukatarsa na son a kara baiwa Ummukulsum hakuri ta daga wayar yarima domin har zuwa yau bata daga wayarsa ba
Yana shirin bashi amsa ya kai dubansa kan abinda ke nuna masa abubuwan dake wakana a cikin gidan
Bai san lokacin da ya zaro idannuwansa yana kallon ikon Allahn dake haskowa a alon tablette din
Sosai ta gurfana da juss din dake cikin kofin glass tana murmushi ta kai daidai bakin saurayin nata dake ta sheka daria yana wani irin lamari kamar zai rungumota jikinsa
Irin suturar da ta saka a jikinta kuwa sket ne da rigarsa sun mata wani irin cifcif daidai da halitarta abayar da ta dora a sama tana shiga ta cire ta yar saman kujera mai cin mutun daya sannan cike da son rigima ta tunkare shi ta tsiyaya jus a cikin kofin da gangan ta kai bakinsa dan gannin abinda zai faru hakan kuwa ya yi daidai da dawowar idannuwan SHAHEED WAJEN...
*Alhamdulillah*
[31/03 Γ 21:41] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»