Showing 198001 words to 201000 words out of 228147 words
Chapter 67 - MAGE (Mai kwanciyar Daukar Rai) Book Complete Na Sajida complet.txt
ba? Zamu yi, zan fadawa Ammina a sako min aboki haka kawai? Malan walahi ni bana son tashin hankali, bana son fada da maza haba, ni kaucewa mutun nake aman ana bi na, garinka a dake yake a tankade daga kai har Nadiar , hasalima ba zan iya zama da mijin kawata ba! "
Murmushi yake ta dokawa a kasan zuciyarsa, a hankali ya dan muzguta dan yana son cire babar rigar nan ya samu damar kallon drama girl din nan tasa hankali kwonce, sai dai hakan ya tsoratar da Najeeba a tunaninta mikewa ne zai yi a kanya sai kawai ta juya ta fala da gudun balaki ta shige dakinsa tana kokarin danno kofa
Yar daria ce ta subuce masa ya raba bayanta da kallo har ta shige tana son rufewar, kansa ya ci gaba da dan jujuyawa a hankali a kasan zuciyarsa kuwa fadi yake 'yarinyar ba dai kujera ba, ka ga sun hanna mata gudu yanda ya dace sai kwana take abinta yar rigimamiyar'
Yana kokarin tashi ne wayarsa ta kuma daukan tsuwa
Sai da ya cire rigar ya ajiye ya koma ya gyara zamansa a hankali ya ce" NAJEEBA, ki fito ki ciyar da ni na shigo da yinwa "
Bakinta ta turo daga wajen da take, tana ta ayanna yanzu tsakani da Allah magana ne ya mata a hankalin nan kamar zata ciro daga bakinsa? To ita ta yayama yake so ta fito ta bashi wani abinci bayan yanzu ta gama zanenta hankali kwonce? Sai kawai ta yi mukus tana sauraron irin yanda ya amsa salama cikin nutsuwa kafin ya dan saurara
Cen ya mike tsaye domin baya so ko da wasa su ji wani damuwa tsakanin junnansu, dan kawai yana gudun lamari na kishin mata ne
A hankali ya ce" Allah ya ja da kwana, haka ne, kwarai laifin Zinaria ya kai wajen da ta ja har na bata saki "
Ajiyar zuciya da wani huci mai dan zafi na takaicin gurbataciyar tarbiyar da y'ayan nasa mata suka samu daga wajen mahaifiyarsu,
Muryarsa a dake ya ce" Gimbiya ki daina min ihu a kaina, idan ba haka ba zan dauki mumunan mataki a kan ki! "
Shiru SHAHEED ya yi, domin ya fahimci muryar kukan da magana sama sama da yake ji na mahaifiyar Zinaria ne
Sarkin Agadez ya ce" Alhamdulilah, Allah ya sa hakan ya zame mata izna da ita da dukan wani mai halayanta ko wanda halayenta ke baiwa sha'awa,
Dan saurarawa ya yo kafin ya dan kara karya muryarsa ya ce" ina rokom Alfarmar a sasauta fushin, idan har da hali ta koma dakinta koda nan da shekaru ne "
Sai da SHAHEED ya dan saki dan murmushi a hankali ya ce" in sha Allah, burina ta gane rayuwa, ta gane abubuwa kamar haka : Dan adam ba abin wulakantawa bane komai rashin arzikinsa ko mumunan kamaninsa, ina so ta bambance mahinmancin zaman aure da zama domin ta birge kawayenta, ina so ta koyi sannin cewa mulki ko sarauta kafin ta hau dubanta sula hau, kuma suka sauka suka bari, a yanzu a matsayinta na yar sarki matar sarki tana iya amsa kiran mai duka, za'a kaita ne daga ita sai farin likafani sai hali sai sallah, ta gane ita ba kowa bace ko a wajen Allah daga bakin sa'in da ta dage kai da fata ita ba zata bi dokokin Allah ba, ina so ZINARIA TA SAN RAYUWA : , ya dan nisa ya dora da fadin " hakan ne ya saka ni mikata ga gidan horo na ahalin cikin gida "
Murmushi ya saki mai sanyi , kafin ya furta" Dama na san kai din adali ne, mai nazari ne, mai sowa dan uwansa abinda yake soea kansa, tabas na yi imani da cewa da ba dan ta samu gurbataciyar tarbiya ba da ta jima da fahimtar cewa adali, zababe, managarci ne Allah ya wanke ya bata, da ta jima da fahimta ta karba harma ta koyar da wata waye mijin da take aure, sai dai kash, sannan a gaskiya ka yi hakuri SULTAN SHAHEED, gidan horon Damagaran yar karamar aljannar duniyar mabukaci ne, ba zata taba shan wahala ba domin kuwa abubuwan da ta rasa kadan ne a ciki, zata dan hakura ne har a fitar da ita ta ci gaba da daukan banzayen hudubobi, ama idan har ta samu kyakyawan horo, zata je ta hada labari ne harma ta kwabi bakin du wani mai sakata aikata mugun abin, dan haka daga bakin lokacin da za'a samu sakamakon bincike cewar ba hannunta a rasuwar marigayiya da kuma kokarin son kashe yar uwarta za'a miko mana ita ne sai mu bata horon da ya dace ga marar kunya! "
Wani murmushin SHAHEED ya yi, kafin ya shiga mika godiyarsa cikin jin kunyar sakar masa y'a da ya yi aman kuma shine har ya fahimce shi haka
SARKI na ajiye kan wayarsa ya maida dubansa wajen mahaifiyar Zinaria dake ta rufe bakinta dan kar ta saki kuka tun karfinta domin kuwa bata so ko da wasa kishiyoyinta su yi gaba da ita
Kai ya girgiza a kausashe ya ce" wato bawa ba zai taba yin asara irin ta yayi asarar uwar y'ayansa managarciya, tabas asarar kudi ko wata kadara ba zata taba kamo asarar rasa mata ta gari ba "
Kansa ya dan girgiza a hankali ya warware nadin dake kansa sai da ya sauke ya ajiye ya ci gaba da fadin" meye wannan nadin? Me ke tatare da shi bayan tarin hatsari da tarin tashin hankali?, a wannan nadi bawa na iya haduwa da halakarsa, a wannan nadi kana iya kwonciya cikin fushin ubangiji, a wannan hadin zaka iya rasa lafiyarka, nutsuwarka, wadatacen lokacin kanka kai idan ka yi wasa harta sa ibadar ba zaka tsayar ba.....tabas nima wannan nadi ya min ilah, daga bakin lokacin da ya dauki girman kai, neman fitina, izgili, hayewa a kan matata da y'ayana mata, haka kuma ya hanna min wadatacen lokacin da zan ringa hankalta da irin abinda ke wakana da ahalina ta hanyar fahimtar yaya mu'amalarsu take da talakawana, da jama'ar garina koda kuwa sunna boyewa a cikin gida, a tunanina matar kirki nake aure da ita harma na kasa tunanin cewa tarbiya fa ba iya mace kawai ake sakarwa ba, dole ka kama a matsayinka na namiji, dole ka rintsa tsawatar da abubuwa da dama ciki kuwa harda iyalan naka....."
Shiru ya yi ya sada kansa, cen ya dago yana bin su da kallo ya ce" sai gashi nima na baiwa mulki madaukakin darajar da iya shi kawai yake da lokacina, shi kuwa sai ya samu wannan damar ya yi min ilar da ya lalata min tarbiyar y'aya, ya kara baiwa matata kofar lalata tata tarbiyar ita kanta "
Sai da ya share zufar dake keto masa sannan ya kausasa muryarsa ya tsatsare su da duban da du suka kara shiga hankulansu ya ci gaba da fadin"" Sai dai ba zan kuma sakacin nan ba, ina mai tabatar maku zan yiwa mulki rashin kunya ta hanyar kiyaye masa na yi masa jan ido na nuna masa mahinmancin iyalaina, da ni kaina, yarinyata mace ta aikata laifin da ya fitar da ita daga gidan miji, sanadiyar hakan zan kaita dakin horo na cikin masarauta cen cikin bangaren bayi! "
Gaba dayansu abin ya dake su, ciki kuwa harda Zahrau da ta san da maganar rigimar aman bata san saki ba da kuma decision din mijin nasu
Ai kam a yanzu sai Gimbiya ta kasa rike kukanta, a bayane ta fashe da wani irin kuka ta budi bakinta ta ce" me na yi da tsanani haka?, me ya sa komai ke son juye min kuma ake gannin laifina? Haba adalina, haba uban gidana me yasa a yanzu kake yanke hukunci mai tsanani a kaina? Haba aban yarimana, me ya sa kake son ido rufe sai ka wulakanta ni a gaban makiyana?, ka duba ka ga matar yarima yanzun ta sameni da kukan wai ya tafi Damagaram, shi SHAHEED din maimakun ya fara kiranka ya maka bayanin laifin da ta yi sai takardar saki ya turo maka maimakun kaima ka sakar masa kanwarsa sai ka bige da wani rarashinsa?, shin meye laifina ko na y'ayana dan mun ki kishiya?, kishi haram ne? "
"Ki min shiru ko na sabauta maki halitarki na saba kamaninki na gigita kwakwaluwar ki a wajen nan ke Baratu!" Muryar Sarkin Agadez ta karade wajen ransa a bace ya dora da fadin" tir da matar dake takama a kan kowa, BARATU ni ne sarkin ama ko ni da kin samu da kin mulke ni, kar ki yi tunanin a zaunen da muke ban san komai a kanki da kan irin rayuwar da y'ayanki ke cakulawa a gidajen aurensu ba, idan baki manta ba a zaman da kuka yi a dakin Zinariya nazajen y'ayanki sun masu magana cewa idan suka kai gobe su kam kar su dawo masu gida, baki yi tunanin maganar mai tsauri bace? Ni na tura masu da sakon hakan aman sai kika kasa ganewa domin ke din banzar uwa ce!, kin kai ni wajen da zan dauki mataki a wajenki BARATU! Tabas ba zan zuba ki a cikin dakin horon bayi bisa hujata na kin yi sake da tarbiyar y'ayana ba, ama zan tura ki gida ki nuna masu halayanki, ki gwada masu wacece ke, su ga irin wulakanta sun da kike yi, na tabata mai martaba sai ya mayar da ke baiwa kaskantaciyar baiwar da bata da wata daraja domin kuwa sam baki da halayan y'ayan sarauta!"
Yana gama fada a kausashe ya mike ya bar komai a nan ya nufi cikin uwar dakansa
Gimbiya, wato BARATU ta rasa wani tunanin zata yi a zaunen da take, tabdijan, za'a turata gida? Da tsufanta gode gode da ita? Zuwa gidanma a matsayin a saka ido a halayanta? Ita kam ita ce zata he gidansu a haka? Lalle da ta gane bata da wayo domib kuwa yayanta dake kan sarauta sai ya nuna mata bata da wayo, mahaifiyarta kuwa dama mace ce da sam basa shiri tun bata kawo yanzu ha domin kuwa tun da ran mahaifinta take alwashi a kan halayanta, a yanzu haka sai su yi kwana uku basu gaisa ba, ba dan komai sai dan tana kiranta zara kama yi mata fada a kan rayuwa
Tana nan wajen zaune har su Zahrau suka mimike suka bar wajen, domin su dai koda sun so rarashinta su nuna mata hanya ita din ba mai sauraronsu bace, idanma bata ce sun mata magani da mijinta ana son rabasu ba ai da kyau, hukunci sarki kuwa ya aiwatar da shi daidai yanda ransa ke so, dan kuwa kwarai hakan ne giyar sarauta ta dauki zuciyar Gimbiya da wasu daga cikin y'ayanta ta hura su ta yanda sun samu wani irin hauhawa da tunanin kaf duniya babu wanda zai iya kamo su ciki kuwa harta da mazajen aurensu dan haka sai suka yi gum suka kara gaba...... wuta ai ruwa ke kasheta!
..........................................
Su UMMU basu dauki wani lokaci mai tsayi a wajen yarima ba, hasalima sun kasance masa wasu irin ababe masu daraja da wuyar gani, ya zamanta muryar Ummukulsum yake mararin ta buda baki ta yi ta masa bayanai masu dadin sauraro, sai dai bayan gaisuwar da ta shiga tsakaninsu sai kawai ta yi shiru abinta tana sauraron yanda suke gaisawa da Ummulkhair,
Sai dai tarbiyar yan matan ta matukar tsaya masa a rai, jan ajinsu ya saka masa jin nutsuwa a zuciyarsa, uwa uba kunyarsu ta saka masa jin tausayin wace wannan lamari ya ritsa da su, sosai ya kara yarda cewa idan Allah ya taimake shi ya sameta a matsayin mata lalle ya samu nagartaciyar mace, zata tarbiyantar da y'ayansa, zata ja ragamar gidansa da kunya da kyakyawar mu'amala, shi dake dan sarkin sai yar bak'ar kanwar matar mahaifinsa ta zame masa itane sarauniyar, domin kuwa sai ya ringa dan takalo maganar da zata yi, har dai ya hakura suka rabu cike da begen son kara ganninta, aman ya shaida mata ba zai bar garin ba sai da amincewarta , wato ta bashi damar gabatar da magabatansa
A daidai nan ne ta dan dago dubanta, ta kuma kallon zankadedwn yaron kafin ta sada kanta da sauro domin ya yi mata wani tsatsarewa da ido ne, a sanyaye ta ce" ai ba'a yi wata ukun ba "
Dan murmushi ya yi ya bata amsa kamar haka" na san da ba sai an yi wata ukun ba, kema kuma kin sani "
Hakan da ya fada ne ya sakata da sauro ta daga kafarta ta bi bayan yar uwarta har kamar ta ci tuntube, shi kuwa banda murmushi ba abinda yake harda sauke ajiyar zuciya
Sunna karasawa kofar baban falo ne suka samu sakon su dakata Mai martaba na zaune da iyalansa, su kansu na kofar basu san cewa ya shige tuni da yar bak'arsa ba.
.........................................
Mahaifiyar Mardiya dake zaune a saman tabarmarta a waje sansaya tana kallon yayansu Mardiya da ya kawo mata maganar daura auren MUTALAB ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta wajen da Mardiya ta mike tsaye lokaci daya,
Sai da ta kara sauke ajiyar zuciyar takaicin halayan yarinyar tata ta ce" Masha Allah, Allah ya basu zaman lafia, Allah ya bata ikon kula da y'ayanta bisa amana, ai ka gani hakurinsa ya masa magani, domin kuwa a labarin da na ji a kan ita matar nan tasa sun yi zaman amana, halin rayuwa ne da kuruci ya raba su, kadara dai ta Allah, tunda yanzun ta dawo gare shi Allah ya basu zaman lafia "
Cike da datako ta karashe maganar, danta na murmushi ya ce" bakima sani ba ina, sai kin ganshi, kina gannin yannayin yalwataciyar fara'ar kan fuskarsa zaki gane yana cikin farin ciki, tabas mace ta gari ita ce sila ta zaman lafia "
Su kam hira suke, basu san irin kokowar da Mardiya ke yi da numfashinta ba, basu san ta mike ba, basu ma san ta dan matso kusa da su ba, sai Karan ihunta da zubewarta kasa ne ya ankarar da su halin da take ciki
Da gaske ta summa, summa ta yi, bata numfashi,
Hankali tashe mahaifiyarta ta ce"
Alhamdulilah ala kuli halinπ
[31/03 Γ 22:03] Sadjida: π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*MAGE*
_(Mai kwanciyar d'aukar rai)_
π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»π§π»
*Na*
*SAJIDA*
π«β¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*π
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_π€
β *[ T.M.N.A]* β πποΈ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
6 1
Cike da tashin hankali mahaifiyar Mardiya ke kallon yaronta ta ce" Summa fa ta yi da gaske, ka dauko mota wannan yaron mu kaita asibiti "
Kansa ya girgiza ba alamun tashin hankali ko wani abin a tatare da shi ya ce" ina, idan har muka ci gaba da nuna mata ita din wata aba ce mai darajar da ta fi ta kowa to tabas ci gaba rashin mutuncinta zai yi maimakun ya tsaya, ki duba ki ga yanda rayuwarmu ta samu cenji sanadiyar aurenta da wannan bawan Allahn, mutumen nan bashi da bakin ciki, bashi da rowa, bashi da wariwa tsakaninmu, duba ki ga ya bani gida ga mota sannan ya nunan hanyar nema, a gaskiya idan har Mardiya zata ci gaba da haka da kaina zan nemi da ya salameta, domin kuwa darajarsa ta kai wajen da zan iya ture Mardiya na rungume shi, dan kuwa a duniya da mai mutunci nake iya zama, Mardiya kuwa idan tana so ta yi summa bakwai! "
Baki bude ta raka shi da kallo, sai yayarta ce ta kama mata ita suka kaita daki suka samo ruwa suka shiga shafa mata
Tana farkawa a firgice ta farka, bata tsaya adu'a ko wani matacen jiki ba sai wata ashar da ta luluka tana fadin" walahi basu isa ba, basu isa ba, daga ita har shi din basu isa ba, shine ba neman shawarana ba komai sai dai na ji a gari ya auri tsohuwar matar da ta je saudiya yawon kilakinta ta dawo, matar da tana magana idannuwa na mata rawa? Dama na san abinda ya kawota gidan nan walah8 dan ta asirce min miji ne, aman bata isa ba sai ya saketa shi dinma bai isa ba !"
Mahaifiyarta ta girgiza kai ta ce" kaya, kaya, Allah wadaran naka ya lalace, to ki bi a sanny Mardiya kar ki manta igiya daya keal ta rage tsakaninki da shi, sannan da kike maganar bai isa ba ke a wa? Da acema matar mutunci ce ke sai a tausaya maki a kama maki harma ya ji tausayinki da nauyin fada maki zai kara aure, aman ai du mace mai irin halayanki sakamakonta kennan! Kuma da kike cewa ta je kilaki kar ki manta zato fa zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne, koda yake na kula ke din aikin zunubin ba yau ba kika bashi gaba ba baya ba, Allah ya shirye ki "
Yayarta ta yatsina baki tana kallon yanda take cenza kaya bama sauraron maganar mahaifiyar tasu take ba har ta gama ta dauki yar jakarta ta fice bata tsaya jin komai ba
Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta ce" inaga ban zame mata ishara ba, sai ta je ta kaso auren ta dawo mu layu idan wannan innuwar ta shige mu tarbi wata, kin ga ina bara na dauki yan cenjin nan na fara saro mana dan abubuwan batarwa dan kuwa na ga alamun yarki bata da hankali gwara mu fara nema kar abubuwa su cakude mana muna zaune yaya kuwa ga iyali sai hamdallah "
Ita dai mahaifiyarta abin duniya ya isheta hanyar da Mardiya ta bi ta fice kawai ta kurawa ido
To a wannan ranar du inda Mardiya ta san zata samu ABIH ta je harta da wajen abokannansa inda yake zama aman bata ganshi ba, karshe dai sai ta mayar da kanta dakinta ta tare tare da kudirin