Showing 279001 words to 281103 words out of 281103 words
Chapter 94 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
biye haka suka shiga shopping ɗin. Yana riƙe da Sultan har ta siye abunda duk zata siya aka zo gurin biyan kuɗi ya bada atm ɗinsa aka cire adaɗin kuɗin da ta kashe, sannan suka koma cikin motar ya ɗauki hanyar gidansu Hajiya Umaima, wato Ƙanwar Mai Martaba wacce take nan Abuja.
Ta tarbesu da far'ah daman ta jima tana masa magana akan ya kawo mata Namra. Hannu ta kai ta karɓi Sultan da ke hannun Abdool tana faɗin
“Ai har na yi fushi na ce ba zan sake maka magana ba”
“Ko yanzu ai nice na matsa”
“No.wonder ni nasan sai ƴata”
“Haba Hajiya taya zaki biyeta ni nace ta shirya mu zo fa”
Hajiya Umaimai tayi dariya.
“Duk abunda zaka faɗa ba zan yarda ba. Mardiya kawo lemu kamin abinci ya ƙarasa”
Ta ƙarasa tana ƙwalawa mai aikinta kira, ba a ɗauki tsawon lokaci ba sai ga Mardiya ta fito daga kitchen ɗauke da drinks da cups. Gabanta ya faɗi lokacin da tayi arba da Namra, ita kanta Namra tayi mamakin ganinta sai dai daga ita ha4 Mardiyar babu wanda ya iya yima wani magana, har sai da ta wuce sannan Namra ta kalli Hajiya Umaima ta ce
“Hajiya ina kika san Mardiya?”
“Wallahi daga Katsina aka kawo ta, na ce a nemo min wace zata riƙa taya ni aiki ne sai aka kawo min ita, kin santa ne?”
“Eh a Katsina take shiyasa na yi mamaki ganinta nan”
“Aiki ta zo yau satinta biyu ma”
“Allah sarki”
Umaima ta miƙawa Namra Sultan.
“Bari na duba abincin nan, kar na shiga muku da yaro Kitchen”
Abdool yayi dariya
“Wai ina su Jamila ne?”
“Wlh duk sunje biki kasan halin ƙanen naka sai a hankali idan kunnensu ya ji biki, ba manyan ba ba yara ba”
Hajiya Umaima na shiga Kitchen sai Namra ta miƙe tsaye ta miƙawa Abdool Sultan ta nufi ɗakin da ta hango Mardiya ta shiga. Da sallama ta shiga, amman Mardiya bata iya amsa mata ba saboda bata son ta gano kuka, gyaran ɗakin ta tarar tana yi. Har Namra ta juya zata fita sai Mardiya ta juyo ta ce.
“Namra Asim ya mutu, Asim ya koma ga Ubangijinsa”
Namra ta juyo tana zaro ido.
“Yaushe? Miya same shi?”
“Rashin lafiyar da ta kama shi a faɗar Sarkin Katsina bata barsa ba sai da ta tafi da ransa”
“Innalillahi wa'inna ilaihi”
Ta faɗa tana dafe kanta hawaye na zubar mata. Mardiya ta risina ƙasa tana kuka.
“Namra ki taimaki Asim ki taimake ni ki yafe mana, amanarki da na ci ta hanani sukuni, duk wanɗanda na yi ma zalumcin na nemi yafiyarsu ke kaɗai kika rage min, na tsorata da irin mutuwar da Asim yayi, bana son na yi irin mutuwarsa”
Namra ta duƙo dai-dai Mardiya tana dafata.
“Miya samu Asim?”
Babu abunda ta ɓoye mata daga rayuwar Asim daga rashin lafiyarsa da kuma mutuwarsa zuwa irin rayuwar luwaɗin da tasan yana yi, ga kuma saduwar da yake yi da ita ta baya.
“Bayan mun gama wanka aka raba mana gadon kuɗin da ya bari na gida da filayen da ya siyar, a take nawa kuɗin suka ƙare gidan da na siya kuma ya ƙone, ga rashin lafiyar da take jikina saboda saduwar da yake yi da Ni ta baya, a duk lokacin da wannan ƙaiƙayin ya taso min sai na ji kamar zan mutu, na kasa daina mafarkin wuta Namra, ada ina tunanin ko wutar da na kunna miki ce gidanki ya ƙone, amman sai nake ganin kamar har da wutar lahira ce take jirana, ki taimake ni ki yafe min Namra, na ci amanarki, na han'ince ki, na cutarda ke”
Wani kuka take marar murya saboda bata son Hajiya Umaima ta ji.
“Na yafe miki Mardiya shi ma Asim na yafe masa, Allah ya masa rahama”
Ta miƙe tsaye tana hawaye.
“Ki rufa min asiri karki faɗawa kowa sirrin, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa na bar Katsina na dawo nan ga aiki saboda na canjawa kai na rayuwa, kuma na rufawa kai na asiri da abunda zan ci, na taimaki uwata da ƙannena”
“Babu wanda zai ji, na miki alƙawari ba zan taɓa faɗawa kowa ba”
Sai da ta share hawayen sannan ta fice. Sai dai hakan be hana Abdool gane ta yi kuka ba. Tana zaunawa kusa da shi ya kalleta ya ce
“Kin yi kuka saboda kinji Asim ya rasu ko?”
Da sauri ta kalleshi.
“Ka sani kenan?”
“Abnam har gobe kina son Asim”
“No ba haka ba ne, kawai ina tausayinsa ne”
“Tausayi ne silar so”
“Ba irin wacan tausayin ba”
Ya miƙe tsaye tare da ɗansa, ya ɗauki car keys ɗinsa ya fice. Tana zaune a gurin ta ji tashin motarsa. Lumshe ido ta yi ta buɗe sannan ta ɗago tana amsa maganar da Hajiya Umaima ke mata.
“Lafiya Babangida ya tafi?”
“Wai zai ga wani abokinsa ne, yace idan an ɗan jima kisa direba ya kai ni”
“Okay toh taso muje ɗaki ga abincin nan Mardiya zata kawo yau mun ranar girki”
“Wallahi Hajiya na ci abinci”
“Ai nasan kin ci abincin, karki so ma min musu ba tarbiya ba ce”
Da murmushi Namra ta tashi ta bita suka shiga ɗaki. Kamin ta gama cin abinci ayi sallah la'asar har ta tsawwala saboda tunanin Abdool yana can gida cikin ɓacin rai. Tana gama sallah la'asar ta yi ma Hajiya Umaima magana tasa ka direba ya kai ta gida. Bata same shi a falo ba, hakan tasa ta nufi ɗakinsa, kwance ta hango shi saman gado, Sultan na saman ƙirjinsa idonsa a lumshe kamar mai bachi.
Tasan ba bachi yake ba, domin be saba bachin yamma ba, sai dai wannan baya rasa nasaba da ɓacin ran da take tunanin ya sawa kansa akan abunda har ga Allah ba haka yake ba. Be buɗe ido ba har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna saman gado.
“Ya Omri...”
“Abnam please, bana son na fara ganin laifinki, bana son zuciyata na ƙonuwa akan ki ina gudun na fara ganin baƙinki, dan Allah ki fita sai zuwa anjima”
Ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Kwantawa tayi a gurin, sai ya buɗe ido ya kwantar da Sultan gefensa na dama ya juya mata baya. Hakan ya bata damar matseshi sosai ta kurɗo hannunta ta ƙasan haɓarsa ta ɗora shi dai-dai zuciyarsa.
“Namra tana nan Ya Omri kuma tana nan a bayan ka, tun bayan abunda Asim yayi min sai na daina ganin maza a mutane ina musu kallon wani abu daban, amman daga lokacin da na ganka sai na ganka a mutun cikakkensa, kai ne mutumen da ya tsayar da zubar hawaye a lokacin da nake tunanin hawaye ba zasu taɓa tsayawa ba, kai nw ka dawo min da farinciki na da kuma na iyayena, Wallahi na rantse maka da Allah babu son kowa a zuciyata sai kai, ka shiga ka mamaye ko ina na zuciyata, ban taɓa mafarkin samu miji irinka ba, saboda ina tunanin kamar ba ayi ni dan jindaɗin rayuwar aure ba. Sai dai bana ganin laifin zuciyar mai Imani idan har taji tausayin rai da zata koma ga Allah yana kirawa kansa hallaka, irin wannan tausayin na ke ma Asim ba irin wancan wanda kai kake tunani ba”
A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannunsa ya shafa hannunta da ke ƙirjinsa.
“Kinji bugun zuciyata...! Duk ranar da kika so wani ba ni ba mutuwa zan yi Abnam don't ever try it”
“Ina son ka mijina, ina son ka sosai”
Juyowa yayi ya rumgumeta yana sumbartar goshinta, lafewa tayi a ƙirjinsa, hannunta yana gurin kunnenta tana wasa da shi, ɗayan kuma yana cikin yatsunsa.
Basu tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah magariba, shi ya fara tashi yayi alwala sannan ya dawo gurin gadon ya sumbance ta ya sumbaci Sultan.
“Tashi ki yi sallah magariba ta yi”
Sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki. Be dawo gidan ba sai da aka yi sallah isha'i, ko da ya shigo ita ta gama nata sallah ta shirya cikin wani shegen riga da ɗan guntun wando, ta kama kalabar kanta ta yi masa tukkuwa wato tayi parking ɗinsa guri ɗaya. Ko da ya shigo tana tsaye gurin dinning tana haɗa ma Sultan madara.
“Wow”
Ya faɗa sannan ya ƙarasa kusa da ita ya zagaye kwankwansonta da hannayensa yasa halshensa yana wasa da kunenta.
“Ba zaki daina bawa yaron nan madara ba ko?”
“Ya cika ci da yawa idan ba a bashi madara ba zai riƙa tsutse ni ne”
Ya juyo ta ita ya ɗagata ya ɗora saman dinning ɗin.
“Ke baki cin abinci ko?”
Ta matso da fuskarta har hancinta na gugar nasa.
“Ni abincin mutane nake ci”
Ɗayan hannunsa tasa ya ɗauke ta cak ya nufi ɗaki da ita.
“Shi kuma yaro na abincin aljanu yake ci?”
Tasa masa dariya hannayenta lanƙame da wuyansa. Ko da wasa Namra bata yarda ta tayarda firar Asim a gaban Abdallah ko da kuwa muagunarwar da yayi mata ne zata faɗa gudun kar ya ce ta tuna da su, yadda yake nuna mata kishi akan Asim baya nuna mata haka akan Lamido, wata ƙila saboda Abbah ya rigaya haɗa auren Lamido da Aisha ne, ko kuma dan yana ganin shi Asim ya taɓa aurenta ne.
Tayi zaton idan zata je bikin auren Aisha sai ya saka mata dokoki kamar yadda yake mata a duk lokacin da yasan zata je bikin da zata haɗu da wasu mazan ko da kuwa ƴan uwanta ne ko nashi, ko mata ne wani lokacin ya kan cilasta mata rufe jikinta wai hakan ne mutuncinsa da na gidansu da kuma nata, sai ya ɗora mata da cewar baya son tana sakin jikinta ko da kuwa cikin mata ne ƴan uwanta domin a yanzu akwai ɓata gari, wanɗanda siffarki kawai zasu gani sheidan ya ƙawata musu sha'awarki.
Ciki farinciki da annashuwa aka yi bikin Aisha da Lamido, ranar Assabar aka ɗaura aurenta kuma ranar aka kai amarya, a unguwar sama road dake cikin sokoto, a lokacin Sultan na da shekara ɗaya da wata takwas, Namra kuma na ɗauke da wani cikin duk da bata haye Sultan ba saboda Abdool ya hana wai zai cutu.
Duk wanda ya ga Sultan baya buƙatar tambayar ɗan waye ne, domin kamaninsa ɗaya da Abdool kai baka ce ma Namra uwarsa ba ce kasancewarta black beauty Sultan kuma fari tas kamar ɗan larabawa.
Family Lamido da kuma na Namra yanzu an koma kamar ƴan'uwa, tun da har auratayya ya shiga ciki, sai dai duk da haka Abdool be taba barin Namra taje Kaduna da sunan gaishe da Neine ba, wai ai zata iya haɗuwa da Lamido tun da yana yawan zuwa akai akai. sai Neine da Uwani sun je Abuja lokacin da ta haifi ƴarta ta biyu wato Fatima, daman suna son zuwa yi mata godiya, ta jidaɗin ziyarar haka ta haɗa musu goma ta arziki lokacin da zasu tafi, har tana waƙen sai ta zo Kaduna idan tayi arba'in duk da tasan Abdool ba zai barta ba.
Wasa-wasa Namra ta zama uwar mata domin bayan ta haifi Fatima sai ta ƙara haifo Juwuriyya da Mai sunan Ummi wato Zuwaira, wacce ake kira da Nasrin, sai kuma mai sunan Anty Amarya da ake kira da Iman, sai a haihuwarta ta shida ta haifi Muhammad Kabir. Ko da wasa ta dake su Abdallah rufe ta yake da faɗa wai bata san zafin haihuwa ba tana cin amanar ƴaƴansa, duk wani horo da zata musu sai idan baya cikin gidan, domin ji yake yi da abunsa wai ita zata iya gudunsa amman ƴaransa ba zasu guje shi ba, ita kanta yana nuna mata kulawa yadda yake treating ɗinta ba zaka ɗauka ita ce ta zuba masa waɗannan yaran ba, sai idan ka gansu. Babu ruwansa da ta haifi yara da yawa kullum kamar amarya take a gunsa, ita kuma tana kula da jikinta sosai da duk wani abu da tasan mijinta na so.
ALHAMDULILLAH.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya bani ikon fara rubuta littafin nan, kuma na kammala. Ina roƙon Allah ya yafe min kuraranda na yi akan ganganci ko rashin sani.
Zan yi amfanin da wannan damar na roƙi yafiyar duk wanda na ɓatawa a cikin rashin sani ko da gangan, mai rai ajizine, masu cewa littafin nan yayi tsawo dole zai zo a haka kasancewar labarin ya kasu gida uku ne, kuma dukan abunda yayi farko zai yi ƙarshe.
Ku yi haƙuri da yadda labarin ya zo muku, fatana dai a ɗauki darasin da ke a ciki, kuma a guji mugun hali ko ɗabi'ar da ba ta ƙwarai ba. Allah ka ɗora mu a dai-dai ka bamu ikon bin gaskiya da tsareta, ka tsaremu daga mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani...
SON SO FISABILILLAHI, godiya ta musamman ga Zagon Ƙasa paid group 1 and 2, da male abroadcast. Sai mun hadu a littafina na gaba *HAFSATU MANGA* _Yarinyar ƙauye_ I LOVE YOU ALL ♥️🌹😍😘❤💜🌷✨
Zan yi missing ɗin ku 😭😭😭