Showing 255001 words to 258000 words out of 281103 words

Chapter 86 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61229

yi nata walimar idan an kawo Amarya, saboda wasu haka suke sai idan an kai amarya sannan suke nasu walimar...








KALSOOM POV.




FIVE YEARS LATER...


“Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday dear Izzah Happy birthday to you”


Tana yanka birthday Cake ɗin suka saka ihu.


“EyyyyyPpppppppp”


Sai kawai tasa dariya ta yanki wani abu daga cake ɗin ta sakawa Kalsoom a baki, Kalsoom ma ta yanka ta saka mata a baki, sannan ta bi sauran mutanen da suke gurin tana feeding the ɗinsu suma suna bata, bayan an yi musu hotuna Kalsoom ta basu guri ita da ƙawayenta su cashe...


Kalsoom ta shigo falo ɗauke da ƴarta Amatullah da ke ta kuccekuccen a barta can ta yi wasa.


“Ba zan barki can ba Amatullah su ture min ke na koma zaune”


Faɗuwa ta yi ƙasa ta fara shureshure da ƙafafunta tana kiran sunan Ezzah.


“Ijca ijca....”


“Easy girl, Ijca yau bata da time ɗin ki casu suke”


Haka ta cigaba da kuka, Kalsoom ta share ta a gurin, ta hau whatsapp tana saka hotonsu a status. Sai ga Rafiq ya shigo da gudu ya shiga kitchen ya ɗauko plate ya fito.


“Kai Plate ɗin nan na Dadyn ku ne, karka fasa min kaya”


“Cake za a sa mana ni da Amatullah”


“Kai mata wayo ka cinye ko..?”


Yasa dariya har da ƙyalƙyatawa, ya saba duk abunda za a saka masa sai yace shi da Amatullah za a saka musu saboda ya cinye ya barta. Sai ga Ezzah ta shigo idonta tab da hawaye kamar ta fasa kuka.


“Anty kin ga Husna wai sai an bata wannan cake ɗin ɗayan, gaba daya, kuma bamu gama hotuna ba”


Kalsoom ta aje wayar hannunta ta riƙe baki.


“Yanzu Husna ce zata riƙa saki kuka gaban abokanki? Ke baki jin kunya su ga idonki ya cika da hawaye? Shekara goma sha hudu ace ƴar shekara uku tana saki ƙwalla gaban friends ɗin ki? Wallahi Izza ki rage wannan shagwaɓar”


Ta turo baki tana matsar ƙwalla.


“Je ki kirata ki ce tazo ga wayata ta yi game”


Ta amsa da to ta fice ita da Rafiq. Tana fita Ulfah ta shigo.


“Anty Momie ta kira?”


“Eh tace ba zata samu damar zuwa ba, yanzu suka taso daga Abuja”


“To Anty ki ce Ezzah ta ba mu cake ɗin mu ai Dady yace saboda mu yasa aka yi cake da yawa”


“Ku ara mata ta yi hoto, ku bari a gama nama, ai ba gudu zai yi ya barku ba”


Ta buga ƙafa tana son kuka.


“A'a ni dai ta bamu abun mu, ko na kira Dady na faɗa masa”


“Duk kika faɗa masa sai na ɓata miki miyasa baki da nasiha ne ke? Kullum ke ce cikin rashin jituwa da ƴar'uwarki haba Ulfah”


“Ai itama bata raga min”


“To bari na ga kin ɓata mata party wallahi na ɓata miki rai”


Ta faɗa saman jikin Kalsoom tana kukan shagwaɓa.


“Yi ta kuka yarinya ki ɓata kwaliyarki”


Sai kawai ta zabura ta kaɓe rigarta ta koma gurin party. Amatullahi ta miƙe da saurinta ta bisu tana tafiyarta ta ta-ta-ta...
[7/27, 9:54 PM] Khadeeja Candy♥: *90*


On Sunday Amarya da muƙarrabanta suka kama hanyar Katsina, ta rigasu isa saboda ta jirgi suka je ita da Maryam da ƴan'uwan Anty Amarya su biyu.


A wani gidan Abdool da ke can bypass suka sauka daman tun kamin su zo Ummi ta yi masa wannna shawarar na su sauka a gidan saboda su samu damar sakewa su huta.


Tun lokacin da Abbah da Anty Amarya da Hajiya Barau suka saka ta gaba suna mata nasiha kan aure, ta fara kuka, sai duk ta ji wani yanayi na daban, kamar lokacin da za ayi aurenta na farin, banbanci wannan ba irin wacan auren ba ne.


Yasa an kawo musu komai daga hotel kama daga abinci har abun sha. Misalin ƙarfe uku Yarima ya kira wata ƙanwar Abbah wacce gwaggo ce gurin Namra ya faɗa mata zai aiko da motocin da zasu shiga ita da Namra da wasu mutun uku aje faɗar Mai Martaba.

Namra na zaune a ɗayan bedroom ɗin tare da Maryam da wasu Cousins ɗinta da Aysha da suka zo tare, gwaggo Ramatu ta shigo tana faɗin.


“Ki shirya angon zai aiko da mota a ɗauke mu muje faɗar mai martaba”


Maryam ta daka tsalle.


“Yeeee kaga daɗin abun malam, mu shiga cikin masarauta muna tinƙaho kowa yayi mana iskanci musa a tsire shi a gari”


Sai duk suka sa dariya, har Namra dake leƙa duniyar gizo. Gwaggo Ramatu ta juya ta fice tana jinjina kai.
Maryam ta nufi babban akwatin Namra da aka zo da shi ta buɗe tana duba irin tufafin da Namra zata saka. Wani tsadadden lace ta ɗauko red color da mayafi ta aje saman gado.


“Raihanatu duba min wannan lace ɗin yayi”


Wacce aka kira da Raihanatu ta miƙe tsaye tana duba lace ɗin.


“Kai wannan ai sai ace matar president ce gaba ɗaya”


“Gaskiya kam wannan lace ɗin yayi kyau sosai”


A gajiye Namra ta miƙe ta shiga wanka ta shirya cikin lace ɗin sai suka gyara mata fuskarta, ana cikin ɗara mata ɗankwali wayar Namra ta yi ringing.
Tana ganin Number Abdool ta yi dariya.


“Ango ango”


“Maryam ya gajiyar biki? Ina Amaryata? Na kira wayarta ta ƙi ta ɗaga ki ce ina gaidata kuma ki ɗaukar min pictures ɗinta”


“An gama ranka ya daɗe”


Ya sauke wayar tana dariya tare da amsa sallamar Gwaggo Ramatu.


“Ku fito ga motoci can an zo da su, Maryam ke kaɗai kin isa ni da Talatu zamu je sai a samu wasu cikin ƙannen Anty Amarya su biyu kuma suje tun da ance mutum biyar sun isa”


Raihanatu ta mike tsaye tana kare ɗankwali.


“Haba Baba Ramatu wane irin Maryam kuma ita da take da aure, ai ƙara dai ki ce ni ko zan samu ɗan saurayi da zai ɗauke cikin ƙannen Yarima”


Sai duk suka bushe da dariya Gwaggo Ramatu ta ce


“To shirya har ke aje da ke”


Motocin dake waje guda biyu sun kusan awa ɗaya sannan Namra ta fito tare da Gwaggo Ramatu da su Maryam da Raihanatu suka shiga motocin.
A tunaninsu za a wace ne gidan sarkin kai tsaye sai suka ga ya kai su gidan Ummi. Kunya sosai Namra ta samu kanta da ji lokacin da motar ta faka a bakin ƙofar shiga falon Ummi. Meesha da Fauza suka fito da wayoyinsu a hannu suka ɗaukarta video, Amal kuma ta zo da gudu ta rumgume ta.
Sam Amal bata gane wace Namra ba, sai dai ita Namra ta gane ta tun a wayar Abdool da take kallon hotunan family ɗin ƴan gidansu. Cike suka tarar da gidan da mutane tana saka ƙafarta cikin falon aka ɗauki guɗa. Ɗakin Ummi aka wuce da ita yayinda su Maryam da Gwaggo suka tsaya a waje a falo suna gaisawa da jama'ah dan basa iya tantance Ummi balle ma bata falon. Namra na shiga Ummi ta shigo sai ta yi saurin yin ƙasa tana gaishe da Ummi. Domin sarai ta san ita mahaifiyar Abdool ga kamanin Abdool nan xube a fuskarta kuma tana ganin ƴadda yake koɗa mahaifiyar ta shi a instagram. Da Murmushi Ummi ta zauna saman gado tana dafa Namra.


“Tashi Tashi Ƴata Allah yayi miki albarka”


Sai Namra ta ɗago sai dai bata yarda ta koma saman gadon ba sai ta zauna ƙasa fuskarka rufe da mayafinta.
Amal ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo cike da zumuɗin ita ƙanwar ango.


“Ummi kin ga fuskarta? Mu bata buɗe mana ba”


“Ai zata buɗe muku har sai kun gaji da ganinta”


“Ni dai ba zan iya haƙuri ba”


Ta faɗa a shagwaɓe. Ummi ta miƙe.tsaye tana gyaɗa kai ta nufi wata dorowa ta buɗe ta ɗauko wasu robobi guda huɗu ta dawo ta zauna.


“Ungo wannan shanye duka”


Hannu biyu Namra tasa ta karɓa ta kafa kai ta shanye abunda yake ciki tas sannan ta sake amsar na biyu ta shanye a na ukun ma shanyewa ta yi sai a huɗu ne Ummi tace karta shanye ta raga. A nan Amal ta samu damar ganin fuskarta har ta yi mata hoto da wayar Ummi.


Bayan Namra ta gama sha Ummi tasa Amal ta ɗauke robobin ta fitar, sai mai Makeup ta shigo da kit ɗinta ta yi zaman dishin a gaban Ummi tana miƙa mata gaisuwa.
Meesha ce ta shigo ɗakin ɗauke da wani koren lace ta aje saman gado.


“Ummi ga shi”


Ummi ta kalli Namra tana nuna mata wani ƙaramin ɗaki dake gefen bathroom ta ce


“Ƴata shiga can ki shirya da wannan kayan”


Meesha ce ta riƙa ta sai suka nufi gurin tare Amal na gaba tana cigaba da leƙen fuskarta.


“Ummi hancinta dogo ne.. Kuma tana da manyan ido.. Fuskarta ma mai D ce”


Ummi ta riƙe baki tana kallon ikon Allah, gulmar mutun a gaban idonshi, wannan ƙulalaici ma Amal har ina!


Bayan ta saka lace ɗin ta fito sai duka suka fita suka barta da mai makeup ɗin, ta zauna saman kujera Mai Makeup ta fara mata fentin fuska amman mai ma'ana, bayan ta gama ta ɗaura mata ɗankwali. Ita kanta wacce ta yi mata kwaliyar sai da ta ɗauke ta a hoto saboda kyau da tayi. Three later Ummi da Fauza da Meesha da Amal suka dawo ɗakin


“Wowwwwwwwwwww”


Shine abunda duk suka faɗa ban da Ummi da ke murmushi. Ɗaukarta suka shiga yi hoto suna selfie. Farar Alkyaba Ummi ta ɗauko miƙawa mai Makeup ɗin ta saka mata. Sannan ta ɗauko fararen takalmi ta aje mata, sannan ta ɗauko akwatin turarenta ta buɗe sisters ɗin Abdool suka shiga fesa mata. Ummi da kanta ta kamo hannunta ta saka mata awarwaro, a ɗayan hannun kuma ta saka mata agogo.
Sannan ta miƙe tsaye, yayinda Namra take ƙasa risine ta saka mata sarka, sai ta miƙawa mai makeup ɗin ta manna mata ƴan kunne.


“To ku fita ku bamu guri”


Kamar umarni suke jira duk suka fita daga ɗakin aka bar Ummi daga ita sai Namra. Ummi ta kama hannayen Namra biyu ta riƙe.


“Ƴata ke tauraruwace, yanzu kin shigo cikin wani sabon shafi, ki haƙuri da duk abunda zaki ji, ba kowa ne zai faɗa miki magana ki mayar masa ba wanna ba tarbiya ba, ki zama mai riƙe sirrin mijinki da iyalansa, idan yayi miki ba dai-dai ba ki fara kawo ƙararsa a guna kamin ki kai ko ina.


Sannan yanzu zaku je gidan Mai Martaba ne wato mahaifin Abdallah, zaki gaishe da shi da iyalinsa, idan kin shiga a tsakiyar falon zaki zauna, karki raɓi kujera, idan kuma kika fito Amal zata ɗauki takalmin ta juyo miki da su ki saka, karki yarda idonki ya haɗu da na matan mai martaba balle ma mai martaba da kansa, karki yarda ki ci abunda za a baki za a miki kallon rashin kunya ko marar tarbiya.


Da misalin ƙarfe tara zaku fita gurin walimar cin abinci da Mai martaba ya shirya muku, Sai dai kamin kuje gurin walimar uwargidan Mai Martaba nasan zata nemi canja miki tufafi, zata aiko barorinta su canja miki kaya, karki yarda su canja miki komai, zan bawa Meesha da Fauza kayan da zaki canja anjima kuma kai makeup zata iso ƙarfe bakwai ta gyara miki fuska. Sai dai karki yarda lokacin Sallah yayi baki yi ba, Allah ya miki albarka”


“Na gode Mama na gode”


Ummi taɓshafa kanta tana murmushi sai ta miƙe tsaye ta fita. Bayan few minutes gwaggo da Maryam suka shigo suka riƙa Namra suka fita tare.


Mashallah shine abunda duk wanda ya kalli fuskar Namra da tufafinta yake faɗa.
Motar da Namra ta shiga daban ita kaɗai ake driving su kuma suka shiga wasu motocin.




Suna isa Faɗar Mai Martaba, aka ɗauki busa ana zuba musu kirari, sai barori suka sheƙo da gudu suna guda aka shimfiɗawa Namra carpet mai sunan Masarautar, sai wani ƙaton mutum cikin kayan dogarai yazo ya buɗewa Namra mota.


Hasbunallahu Namra ta karanta a zuciyarta sannan ta saka ƙafarta ta sauko daga cikin motar. Sai barorin suka rufa mata baya, wasu kuma suka wuce gurin tawagar da suka zo tare da Namra aka musu iso zuwa cikin gida.


Cike da hankali da natsuwa Namra take takawa barori suna take mata baya har suka isa gaban wata ƙatuwar ƙofa. Bakin ƙofar barorin suka tsaya sai Dogarai suka wangale mata ƙofar suka bakin ƙofar suna zuba mata kirari.


“shiga da ƙafar dama yar gidan girma, ƴar da tafi ko wace mace sa'ah a duniya, an gaishe ki gimbiya matar yarima, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana”


Kunna kai ta yi cikin faɗar, tana wuce carpet na farko ta cire takalminta saboda ta ga jerin takalmi a gurin. Wani irin maryaba da girma ta ji ya kamata musamman ta ta risina gaban mai martaba tana gaishe shi.


“Sarki ya amsa kuma ya gaishe ki”


Shine abunda mafadawan suke faɗi, sannan mai martaba yayi musu hannu suka tashi suka bar shi da Namra. Nasiha sosai yayi mata akan rayuwa da kuma zaman aure sai kuma kan haƙuri da iya kula da mutane.
Sai da Mai Martaba ya tabbatar Nasihar ta shiga jikinta sannan ya sallame dan ta shiga cikin gida ta gaishe da matansa.






ASIM POV.


Tun bayan da ya saka ƙarin aure a gabansa be waiwayi kowa ba, duk da da irin kuka da magiyar da Mardiya ta riƙa masa akan karka ya ƙara auren. Sai dai be ji ba sai da ya auro ƴar manyan mutane wato Balkisu.
An kashe dukiya sosai gurin auren daga duka ɓangarorin guda biyu, domin ko gidan da ya sakata mai tsada ne sosai.
Gida ne mai part biyu a ɗayan part ɗin ya saka Mardiya ta ƴar tabarmarta ta shinfiɗa saboda bata katifa kuma malamin da suka je gurinsa ya faɗa musu karta yarda ta saka katifa ko gado a gidan, abun shinfiɗa kawai zata je da shi sai kayan abinci.


Haka ta riƙa zama har tsawon wata tara duk wanda ya leƙa part ɗinta sai ya sha mamakin ganin babu komai a ciki, part ɗin Balkisu kam Aljannar duniya. Wannan matsalar ta damu Mardiya sosai har ta kai bata da wani sukuni a rayuwarta, ga mafarkin wutar da take bata daina ba, sau da dama zata zauna ta yi da kuka, wani lokaci kuma ko da tana cikin mutane zaka ganta ta koma wata iri kamar wacce aka ɗauki tunanin duniya aka ɗora mata. Ita da tayi aure dan jindaɗi abu ya zame mata ɗan zane, ta san matsalar daga gareta ne saboda yawan mafarkin wutar da take kuma gashi ita Balkisu wutar ba kama ta ko da sau ɗaya.


Ba ko wace ranar girkinta ba ne Asim yake kwana part ɗinta saboda bata da katifa balle kuma gado, sai a lokacin da yaji yana buƙatarta. Yau ma part ɗin Balkisu ya kwana, bayan yayi wanka ya shirya ya leƙo part ɗinta suka gaisa, duk ta yi wani zurun-zurun gwanin tausayi kamar marar lafiya, bayan sun gaisa ya dawo part ɗin Balkisu da yi mata sallama, sai ya samu tana tsaye jikin ƙofa tana jiranshi.


“Sai ina?”


Ta faɗa ta wani langaɓar da wuya tana kaɗa jiki, kamar wata tsohuwar karuwa.


“Gari zan shiga, amman zan dawo ajima saboda zamu je wani biki da za'ayi a faɗar Mai Martaba, kuma an gayyace mu kinsa ɗansa abokina ne”


Ya faɗa irin yana alfahari ɗin nan.


“Okay to a dawo lafiya, kar dai aje ayi gane-gane”


“Ni wa zan gani, ga ni da ke cikin gida”


Matsowa ta yi ta masa kiss, sannan ya juya ya tafi tana ɗaga masa hannu.






WHAT DO YOU EXPECT NEXT...?






[7/28, 10:15 PM] Khadeeja Candy♥: *91*


Kamar yadda Ummi tace mata a duk ɗakin da ta shiga ta kan zauna a tsakiyar ne har ta gama gaisuwar ta tashi, bata yarda ta haɗa ido da matan mai martaba. Sai dai a yadda take tararda ko wanne falo tana auna yawan family da mai martaba yake da su a gidan, wata ƙila kuma saboda tana amarya ne suke zuwa ganinta.
Bayan ta gaishesu aka kaita ɗakin Hajiya Shafa, sai aka kawo musu abinci da drinks. Bata ci komai ba duk kuwa da irin matsa mata da suka riƙa yi. Ana yin sallah magariba duk suka shiga shiryawa, wasu motocin Abdool ya aiko aka ɗauki su Maryam aka mayarda masaukinsu domin suma su shirya. Bayan sun wuce wata cikin ƴaƴan Hajiya Shafa ta shigo tana faɗin.


“Hajiya tace Mai Makeup zata zo ta gyara miki fuskarki, kuma za a kawo miki kaya ki canja”


Namra ta amsa da to. Har Amal ta buɗe baki ta gatsawa yarinyar magana sai Meesha ta riga ta.


“Ai ko har Ummi ta yi magana da mai Makeup zata zo yanzu ta mata”


“Auoak”


Yarinyar ta faɗa sai ta juya tana tafiya cike da isa ta fice. Amal taja tsaki tana binta da harara.


“Wai yarinyar nan tun ɗazu nake ganin tana ta wani shauƙi”


Meesha ta zaro ido.


“Ina ruwanki? Amal me yake cikin kan ki?”


“Aljanuna akai na”


“Ƴar gadon baƙar magana duk abunda kika yi sai na faɗawa Ummi”


Ta tsuƙe baki ta juyarda fuska. Around eight o'clock mai Makeup ɗin ta iso. Namra bata yarda an mata makeup ɗin ba sai da ta yi sallah isha'i.


Ƙarfe tara dai-dai Abdool ya aika aka kwaso ƴan'uwan Namra aka kaisu tsohuwar faɗar Mai Martaba inda aka shirya taron.


Sai tara da kwata Amarya ta iso barori na take mata baya, farin lace ne mai shegen kyau da farar Alkyaba, fararen takalmi da farar sarƙa, mai video na biye da iya ita yana ɗauka har aka ta kai zamanin da aka tanadar mata dan ta zauna. Bayan kamar minti biyar da zamanta Abdool ya shigo shi da abokaninshi, farar shadda ce jikinshi da fararen takalma sai farin rawani da farar alkyaɓa, kallonsa take kamar yadda kowa yake kallonsa, ita kanta ta san ta yi sa'ar miji, yadda yayi mata kwarjini da haiba ga fuskarsa sai annuri take, ɗaya bayan ɗaya yake tafiya ana masa kirari ana koɗashi. A kujerar da Namra take zaune ya zauna sai masu busar suka koma gefe suka cigaba da busar. Ko ina ka duba masu kaki kake gani sun cika gurin wato gayyar Abdool ne kawai sai kuma na ƴan'uwansa. Saboda Mai Martaba be gayyaci kowa ba walima ce da ya shirya a cikin gidanshi domin addu'ah kawai da kuma son tara family ɗinsa guri ɗaya, wannan walimar ta al'ada ce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login