Showing 27001 words to 30000 words out of 281103 words
Chapter 10 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
tana kishin ki”
“Amira bata da wannan Maryam baki fahimce bana”
“Bata da wannan, take kishin ki? Yai Amira tana baƙinciki ta ga kin ɗinka sabon kaya ita ata ɗinka ba, Amira tana baƙincikin ace kin fita zarra a jarabawa, Amira bata ƙaunar a tare ki a hanya ita ba'a tare ta ba, in yau kika saye sabon takalmi sai Amira ta siye, idan aBun farin ciki ya same ki a take Amira take canja fuska, idan wani abu kika samu sai tasan yadda ta shiga ta fita kika hallakarda da shi sannan hankalinta ya kwanta, ke duk baki lura da hakan ba?
Anty Namra ƙarshen duniya muke fa, kuma Annabi da kansa ya faɗa a cikin alamomin ƙarshen duniya akwai rashin amana da cin amana da rashin yarda, Wallahi kiyi hankalin da mutane.
In ma wani sirrin ki ne karki ƙara faɗawa Amira, dan daga lokacin da ke da kanki kika kasa ɓoye sirrinki a cikin cikinki, har kika faɗawa Amira Wallahi kamar kin faɗawa duniya ne”
Namra tayi shiru tana kallon yadda Maryam take tsire baki tana faɗin maganganun, zuciyarta na nazarin kalamanta. Ita kanta a yanzu tana zargin Amira tun daga abunda ya faru da ita, sai dai yadda Amira take nuna mata akwai Aminci a tsakanin su ya kan rikita zarginta.
“Forget about Amira, yanzu dai Abbah yace ki kawo Asim ze aura miki shi how do you feel?”
“I don't know, amman ina jin kamar ban kyautawa Abbah ba, kuma ba zai fahimce ni ba, idan kuma na kawo wani wanda ba Asim na aura Asim zai cigaba da kallo a matsayin mayaudariya, ban san yadda zan yi ba”
“Yanzu dai Uzair ya fasa auren ki, dan haka duk wanda zaki aura babu ruwan Abbah ba kuma ze karɓi wani excuse daga gare ki ba, kinga ƙara ma ki auri Asim ɗin, in yaso sai kiji da Abbah”
“Maryam ban san inda Asim yake ba, Mahaifiyarsa ma tace min bata san inda yake ba, saboda ni ya bar garin nan”
“Ƙarya take tace bata san inda yake ba, shi Asim ɗin yaro ne da zai gudu be faɗawa mahaifiyarsa ba? Baya gari ya akayi Amira ta ganshi?”
“Nima ban sani ba, tace min kiranta yayi a waya”
“Kin gani ko? Wannan Amirar munafukace. Ni zan taya ki nemansa, har gurin uwarsa zanje idan kuma tayi min maganar banza na ci mata mutunci”
“A'a ni dai dan Allah karki mata rashin mutunci, ki bita da lalama”
“Ke fa Anty Namra kina da matsala, mutanen duniya in ka sake sai su ci maka tuwo a ka, kawai idan mutum ya maka zuma sai ka masa wuta, idan kuma ya maka yayyafi sai ka masa ruwa”
“Nidai na ji amman ban da rashin mutunci kinji?”
Ta tsire baki gefe.
“Naji tashi mu shiga ciki, ni yunwa ma nake ji ganin Amirar yasa na shigo nan”
Miƙewar da Namra zatayi sai taji abu ya gangaro mata a ƙafa, tana ɗaga zagen taga jini. Lumshe ido tayi ta buɗe ta kalli Maryam dake kallonta sannan ta riƙa hannunta suka shiga ciki.
Suna shiga Maryam ta nufi kitchen, Namra kuma ta nufi ɗakinta, ta cire kayan jikinta ta gyara jikinta ta saka pad sannan ta saka wasu tufafin.
UZAIR POV.
Sai safa da marwa yake, hankalinsa ya kasa kwanciya, tun lokacin da Amira ta masa text ɗin shirmen data aikata. What if aikin ya dawo gareshi? Tun da malamin yace indai akayi aikin dole ne ya ci.
Najeeb ya dafa shi
“Uzair ka kwantar da hankalin ka mana”
“Haba Najeeb wane irin kwantar da hankali kamar baka san yadda abun nan yake ba, kuma kana ganin taje ta aika mana shirme, ban san abunda yake damun ƴar iskar yarinyar nan ba”
“Ka natsu mana sai mu kira malamin mu faɗa masa abunda yake faruwa”
Sai a lokacin ya zauna, tashin hankali ƙarara a fuskarsa. Kira biyu Malamin ya ɗauka, sai Najeeb yayi masa bayanin komai. Malamin ya daɗe yana jimamin abun sai tambayar yadda akayi suka yi wannan kwaɓar yake.
“Yanzu dai mu saurara nan da kwana biyu mu gani”
“Yanzu Malam babu wani abu da za'a iya yi, babu wata mafita?”
“Mafita ɗaya ce, a nemo kurciyar nan acire layar da aka laƙa mata, kasan kuma mun riga mun saki kurciyar kamunta yanzu ba abu ne mai yiyu ba, sai dai kasan ai da sunan ita yarinyar mukayi dan haka ku ɗan dakata tukuna mai yiyuwa ya iya kamata”
“Ko asa ta cire rigar?”
“A'a duk ta cire rigar ba tare da aikin ya shiga jikinta ba, zai iya dawowa, kasan lamarin iska”
“Okay toh mun gode”
Najeeb na kashe wayar Uzair ya miƙe tsaye yana faɗin
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ka cece ni Allah”
Jafar ya aje wayar hannunsa ya kalli Uzair yace
“Haba be a Man mana, ai ko aiki zai dawo ba akanka zai koma ba akan Amirar zai koma”
Uzair ya kalleshi
“Amman ai ba ita tayi aikin ba”
“Easy Man ai ita tayi kuskuren, kirata muji yadda tayi wannan banzan shirmen”
Jafar na gama maganar, Uzair ya ciro wayarsa ya danna mata kira.
AMIRA POV.
Kuka take sosai, tun da ta baro gidan su Namra take kuka har ta iso gida. Bata bari Ammy taga shigowarta ba, sai kawai ta shige ɗakinta ta hau kuka baji ba gani. Ita kanta idan za'a tambayeta bata san dalilin kukan ba, ita dai tana jin kuka yana zo mata kawai.
Ganin Number Uzair ce yasa ta ɗauka ta kara a kunne.
“Amira taya kika yi wannan shirmen? Ban faɗa miki ba a son a samu matsala ba?”
“Ai tasa rigar”
“Toh Uban wa yace ki bari tasa ba tare da haila yazo mata ba? Wace irin mahaukaciya ce ke?”
“Yanzu idan ba a yi dai-dai ba me zai faru?”
“Ban sani ba”
Sai ya kashe wayar. A take zuciyarta ta soma raya mata Namra haukacewa zatayi. Kuma ita za a zarga tun da anga shigarta gidan gashi Maryam ta haɗu da ita, hakan yasa ta fashe da kuka zuciyarta na raya mata lallai asirinta na daf da tonuwa.
Haka ta wuni ta kwana da tunanin abunda ze samu Namra, gashi kukan yaƙi ya tsaya mata, ta takure kanta a ɗaki, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin inda zata samawa kanta mafita, dan ji take kamar wani zai faru da Namra, tun da batayi dai-dai ba, kuma ba makawa ita za a zarga. Ji take duk ta tsani kanta, zuciyarta na raya mata ta gudu kawai kamin asirinta ya tonu.
MARYAM POV.
Daga Makaranta ta wuce gidan iyayen Asim. Cikin ladabi tayi sallama ta shiga. Sai Mahaifiyarsa ta amsa mata dan ita kaɗaice yau a gidan. Har ƙasa Maryam ta risina ta gaishe ta. Ta ta ɗan kawarda fuskarta dan ta gane ƙanwar Namra ce tun da sun taɓa zuwa tare da ita.
“Lafiya ƙalau”
“Dan Allah ko Asim na nan?”
“Baya nan yayarki ta zo nan na faɗa mata baya nan, ni ma ban san inda yake ba”
Daga nan sai Maryam ta canja salo.
“Kin san inda yake kam, dan babu yadda za'ayi ace uwa kamar ki bata san inda ɗanta yake ba, shi Asim ɗin yaro ne da zai bar gida yaje nesa ba tare daya faɗa miki ba”
“Au toh ko ƙarya zan miki, macuta maciya amana, bayan kun gama cin moriyar ɗana sannan zaku watsa masa ƙasa a ido, yanzu dan munafurci ne za ku wani zo nemansa kamar ya ci bashin ku?”
“Bashin mu yaci mana, yaje ya ɗaukewa ƴar'uwata hankali ta haukace tace shi take so, yace ta kawo shi a aura mata, shine kuma dan rainin hankali zaki ce baki san inda yake ba, Wallahi sai kin nemo shi duk inda yake ko kuma naje na faɗawa Abbah yasa a kulle ku dake da danginki har sai Asim ɗin ya dawo, dan ba zaku sa muna ƴar'uwa a matsala ba”
“Eh ai zamu iya, tun da ku ƴan siyasa ne ku keda gwannati, amman bari kiji na faɗa miki ni ɗana ba zai aure ƴar marasa mutucin ba”
Maryam ta matso kusa da ita tana zare ido.
“Ooo.... Uwata ce marar mutunci ko?”
“Ni ban ce ba, salon kije ki ƙulla min ƙullaliya, Toh ta Allah ba taki ba”
“Ni dai na faɗa Wallahi ko ki nemo inda ɗanki yake ko kuma duk abunda ya faru dake ke kika ja”
Mahaifiyar Asim ta nuna Maryam da yatsa.
“Ke wannan da ganin ki ba zaki gama lafiya ba”
Maryam ta tuma ta dire.
“Ƙwarai ba zan gama lafiya saboda da kika hallice ni ai baki yi dan na gama lafiya ba, ta yadda idan an je lahira zaki jidaɗin ƙoneni a wuta ko? Ai ke cw ba zaki gama lafiya ba tsohuwa dake kina ƙarya baki san inda ɗan ki yake ba ko kunya baki ji ba”
Ta daki ƙirji.
“Ke ni kike faɗawa wannan maganar?”
“An faɗa ɗin, biri ai a hannun malami ya kan yi guɗa, a hannun bamaguje sai kuka, kuma Wallahi ko ki nemo ɗanƙi ko ki shiga a matsala”
A nan Maryam ta tofar mata da yawu ta wuce, tana bankaɗar mutanen da suka fara cika gidan gurin kallon faɗa.
_____________________________________
Me kuke tunanin ze faru a shafi na gaba?
Anya Asim zai dawo? Da gaske Mahaifiyar Asim bata san inda yake ba?
Ya rayuwar Amira da Uzair akan kuskuren da sukayi? Me zai faru da Namra?
Masu ziyarta shafina, a ƙasan blog ɗin zaku ga gurin subscribe, a nan zaku saka email address ɗin ku ta yadda da nayi sabon updated zaku samu notification, na kan fara sauke post ɗina a can kamin na kawo shi whatsapp.
Ina son ku duka fisabilliah 😘
Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa-14.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
*PAGE - 14*
Sai da aka kwana biyu sannan Maryam ta labarta ma Anty Amarya da Namra yadda suka yi da Maman Asim.
Ran Anty Amarya ya ɓace sosai, daga ita har Namra basu jidaɗin abunda Maryam tayi ba.
“Ke ke Maryam ba wata ba, Allah ya sauwaƙe miki bakin mutane, kullum ana miki magana amman kamar ba'a yi, rashin kunya an faɗa miki abun ƙwarai ne? Ai gashi nan baki mutane akan ki Wallahi Allah ya sauwaƙe miki wannan rayuwa”
Maryam ta ɓata rai sosai, daman tasan za'a rina dan tasan sai Anty Amarya tayi mata faɗa, tun da bata taɓa yaba ma masifar ta ba.
Anty Amarya kam sai harararta take tana jin kamar ta dake ta.
“Aure dai zakiyi kuma mace kike Wallahi ki canja rayuwa dan baki san inda zaki faɗa ba”
“Naji Anty yi haƙuri kin san ni yarinya ce har yanzu”
Namra tayi mata wani kallo
“Kece yarinyar?”
Sai kawai tasa dariya ita da Aisha. Anty Amarya ta ɗauke kai tana amsa sallamar da Ammy tayi.
Cikin tashin hankali ta doso inda Anty Amarya take gyalenta ma a bai-bai ta yafashi.
“Hajiya Amina lafiya na ganki haka?”
Ta zauna saman kujera tana kuka.
“Wallahi ba lafiya ba, Amira ce tun jiya ba mu ganta ba, ba musan inda take ba”
Gaban Namra da Anty Amarya ya faɗi. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Shine abunda yake fitowa a bakin su. Namra tace
“Amman an bincika ko ina? Kuma bata ga inda zata ba?”
“Bata ce ba, tun ranar data fita tace min nan zata zo inda kike ban sake sata a ido ba sai da safe, ko na na shiga ta tarar tana ta kuka wai kanta ke mata ciwo, sai ce min take tana jin tsoro, na bata magani ta sha sai tayi bachi, ko da na sake leƙawa ɗakin na dubata sai naga bata ciki, na duba ban ga jakarta ba da wayarta, sai na ɗauka ko tazo nan ne, har dare shiru, sai da Abbah ta ya dawo muka yi ta nemanta ba mu ganta ba idan an kira wayarta kuma kashe, haka muka kwana cikin tashin hankali”
Da kuka sosai ta ƙarasa maganar. Sai hawaye suka silalo daga idon Namra a take ta fasa kuka. Anty Amarya tace
“Wallahi rabonta da gidan nan tun shekaran jiya ranar laraba, ban sake sata a ido ba, Allah ya a gaji wannan yarinya ko ina ta shiga?”
Namra ta share hawayen idonta
“Ammy baku mata komai ba? Ba faɗa tayi da wani ba? Kuma babu wanda yayi mata sallama ko da a waje?”
“Wallahi bamu mata komai ba, kuma ni dai ban san wani yayi mata sallama ba, amman dai Babanta ya kai ma ƴan sanda report ko Allah ze sa a gane inda take, amman ke Namra baki san inda Amira zata iya zuwa ba?”
“Wallahi ban sani ba, ranar ma data bar gidan nan naga kamar anyi mata saƙo sai tace min wai kece ba kida lafiya bari tafi gida, washen garin ranar ne ma nace Maryam taje ta duba ki, sai tace min ai sun haɗu da Amira tace mata kin ji sauki”
“Wallahi ni ban yi wani ciwo ba lafiya ta ƙalau, na shiga uku yau ina Amira ta shiga?”
Da kuka ta tashi ta nufi ƙofa. Anty Amarya na bata haƙura har gurin har gurin gate.
Lokacin data dawo ne Hajiya Barau ta tare ta tana tambayar lafiya. Itama salati tasa lokacin tada ji abunda ya faru, suna cikin maganar sai ga Namra ta fito sanye Hijab tana hawaye.
Tana ƙarasowa kusa da su Anty Amarya tace
“Namra ina zaki ?”
“Anty zama be gan ni ba, tun da Amira ta ɓata”
Hajiya Barau ta riƙota
“Wallahi babu inda zaki, kije nemanta kema a ɗauke ki, ko kin manta abunda ya faru ne? Allah dai yasa ba Asim ɗin ne ya sace ba itama”
Namra tayi saurin girgiza kai.
“Wallahi Hajiya ba shi bane, Asim ba ze haka ba, Asim ma baya garin nan gaba ɗaya”
“Uhmm Aifa sai kiyi kuma, irin abunda aka miki ne za a mata, Inshallah mutun ɗaya ne yake muku wannan abun”
“Wallahi ba wanda zuciyarki take zargi bane, Asim baya garin nan”
“Toh a ina yake?”
Hajiya ta tambaya tana mata wani makirin kallo.
“Nima ban sani ba, amman dai ba shi bane”
Anty Amarya ta kasa mata tsawa
“Ai sai ki tsaya nan kina gardama da uwarki akan abunda baki da tabbaci, wuce ki koma ciki babu inda zaki je”
Ba dan taso ba, ta juya ta koma ciki tana kuka. Anty Amarya ta rufa mata baya tana ta mata faɗa wai tana gardama da Hajiya kamar ma uwarta.
Hajiya Barau ta tsire baki ta shige part ɗinta zuciyarta na raya mata Namra ta san inda Amira take.
Bedroom ɗinta ta shige ta ɗauki waya ta kira Uzair tana labarta masa abunda ya faru. Ya kaɗu matuƙa shi kansa ya kwana biyu yana kiran wayar Amira amman baya samu. Sai dai wani ɓangaren hankalinshi ya kwanta ganin kamar asirin kan Amira ya koma ba kansa ba.
Bayan ya gama waya da Hajiya ya kira Najeeb ya labarta masa ɓatan Amira.
“Kaga abunda nake faɗa maka ko? Ai daman nacw maka aikin ba akan ka ze dawo ba akan Amira ze koma”
“Ban sani ba ko nawa na nan tafe Najeeb, amman ina cikin tashin hankali”
“Ka kwantar da hankalinka babu abunda ze faru, amman kuma ka rufe wannan maganar”
“Ya za'ayi ma an faɗa, Allah dai ya sauwaƙe, Ni wallahi ba zan sake irin wannan abun ba”
Najeeb yasa dariya.
“Uzair ka cika tsoro da yawa, shiyasa ka yi sake har waɗannan abubuwan suka faru”
“Ni dai naji”
Daga haka ya kashe wayar, ya nufi ɗakin matarsa.
Hajiya na gama waya da Uzair sai ta kira wata ƙawarta wace take taubashiyar Ammy. Bugu ɗaya zuwa huɗu ta ɗauka.
“Assalamu Alaikum”
“Wa'alaikissalam Hajiya yanzu nake labarin ki, nace ko kina da labarin abun da ya faru?”
“Wallahi bani da labari sai yanzu nake jin abunda ya faru, shima fa dan Ammy tazo da kanta ne dan Wallahi sam ni Amarya bata faɗa min ba”
“Au kina nufin sai yanzu kika ji?”
“Wallahi sai yanzu shiyasa ma nakira ki, Namra ta ɗaki ƙasa ta rantse ita ba Asim bane ya sace Amira”
“Wanene Asim kuma?”
“Ina wani tsohon Saurayin Namra wanda na taɓa baki labari nace miki mahaifinta ya mata miji amman tacw bata so sai shi ko kin manta?”
“A'a na tuna ɗan makarantar su ko?”
“Allah ya bar ki, shi ne fa, toh ai kinsan shine ya sace Namra kwanakin baya har shiyasa ma mijin da zai aureta yace ya fasa”
“Ke ya sace fa kika ce?”
“Wallahi ya sace ko kuma ta bishi ba, kuma kinga ita Amira ta faɗa tace shine yazo ya tafi da Namra ɗin kuma duk nan mutane unguwa sun shedi haka dan sunce sunji lokacin da yake magana, har fa iskanci yayi da ita”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un toh wai ko sha ya sace Amirar?”
“Nima dai shi nake zargi, kuma magana ta gaskiya Namra tasan inda Amira take saboda tasan inda shi Asim ɗin yake, saboda ɗazu take take ƙoƙarin kare shi wai baya garin nan me me magana babu kai babu gindi”
“Amman wannan magana ai bata kyalewa bace, indai har haka ne dole ne a nemi Namra ɗin kuma ita da kanta Ammy tace min Namra ce mutum na ƙarshe da Amira ta gani”
“Ai ke dai bari ƙawayen zamani ai sai a hankali, Allah dai ya bayyana ta”
“Amin bari na kira Ammy yanzu”
Hajiya Barau tayi saurin cewa.
“Dan Allah karki ce gare ni kika ji, kinsan halin Alhaji balle kuma baka kake iko da gida ba, sai ace kayi ma ɗan kishi shaeri”
“Haba dai Hajiya sai kace wata ƙaramar yarinya da zanje nace ke kika faɗa? Ai babu wannan tsakanin mu”
“Toh na gode sai na jiki”
Daga haka ta kashe wayar.
KALSOOM POV.
Kwata-kwata Hilal be yi zuwa huɗu ba Daddy yace ya turo iyayensa. Shi kuma daman haka yake son yaji, satin daya zagawo iyayen Hilal suka neman auren Kalsoom, farin ciki gurin mahaifiyar Hilal kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha.
Iyayen basu bar gurin ba har sai da Daddy da ƴan'uwansa suka yanka musu sadakinta dubu saba'in suka biya sai Daddy yasa musu rana dan ba so yake aja abun da nisa ba, shirin da biyar ga watan huɗu. Cikin farinciki da jindaɗi suka bar gidan.
A ranar Rashida bata yi bachi ba saboda baƙinciki, kwana tayi kuka Hilal na rarrashinta. Washen garin ranar da akayi abun Kalsoom taje aiki sai suka riƙa taya ta murna suna ce mata amarya. Tayi mamakin inda suka