Showing 234001 words to 237000 words out of 281103 words
Chapter 79 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
uwar banza ba da na baka shawarar rabuwa da yarinyar nan...”
Ta ƙarasa tana kallon Hilal. Shi kan uffan be ce ba sai kallon pop yake abun duniya ya taru ya tsaya masa, idan ya shiga wannan ya shiga wannan. Miƙewa ya yi tsaye ya fice cikin rashin daɗin rai.
Bayan fitarsa Hajiya ta miƙe ta fita, ta bar Teema na kuka, Rashida kuma na hawaye. Bata yi minti talatin da fita ba Rashida ta tashi ta fice, a lokacin ne Teema ta kalli Kalsoom ta ce.
“Zan taimaka miki ki haihu, nasan hanyoyin da zan bi ki haihu, wannan cikin na ki yanzu shekarar ɗaya da wata huɗu cikin na biyar, amman idan kika taimaka min kika hana Hilal ya sake ni, ina son ki saka baki a lamarin auren mu domin a yanzu na fuskanci kina da ƙima a gurinsa da kuma mahaifiyarsa fiye da ni”
Ido kawai Kalsoom ta sakar mata tana kallon ikon Allah, ta ya zata ce ta kaita wani gurin bayan yanzu aka gama rigimar tana bin bokaye, ita bata ma tsoron wani ya ji. Kamar daga sama suka ji muryar Hilal da ke tsaye bakin ƙofa rumgume da hannayesa a ƙirji yana kallonsu, dan sam basu san da shigowarsa ba.
“Kalsoom bata iya shige-shige irin na ku ba, kuma idan lokacin haihuwarta yayi zata haihu, ke ai naga haihuwar kike nema miya hanaki bin bokayen su baki haihuwa?”
Ta miƙe tsaye yana kallonshi.
“Haihuwar da na ke so Hilal saboda kai nake son ta, ina son na haihu da kai saboda ina ƙaunar ka ne, yanzun kuma abunda nake ƙoƙarin yi ma saboda ina ƙaunarka ne Hilal, miyasa ka kasa ganin haka? Tun kana mijin Rashida na ke mafarki miji irin ka saboda kana kula da ita yadda ya dace, ashe ma Allah yayi sai na kasance ɗaya daga cikin matan ka, ka tausaya min Hilal, zan iya yi maka alƙawarin ba zan sake bin ko wane malami ba indai wannan ce kawai matsalar...”
Ta ƙarasa tare da risinawa kamar mai neman gafara.
“Ba wannan ce kawai matsalar ba, ko na zauna da ke ba zan aminta da ke ba, kuma mai hali baya fasa halinsa, ai yanzu aka gama wannan rigimar amman kika ɗaga ido kika kalli Kalsoom har kina neman ki taimaketa, dan ta saka kar na sake ke, kin manta ita da ke duka a ƙarƙashin kulawata kuke? Hajiya ma dake gindaya min sharaɗi yin abu ko hani ta bani umarnin idan na ga dama na sake ki, tun dan me zaki dawo gurin Mamata kina neman ta taimake akan abunda zan iya yanke hukuncinsa yanzu?”
Kalsoom ta girgiza masa kai.
“Saboda ta san zan iya saka ka yi ne...”
“Kalsoom karki saka bakin ki cikin wannan maganar please”
Teema ta hasala ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai da zafin zuciya.
“Ka daɗe baka sake ni ba Hilal, ni wannan wuƙancin da Rashida take ɗauka ni bana ɗaukarsa, sai kace kai ne kaɗai na miji ana magana kana ƙara butsewa, ka sake mana ai ni tafi nono fari, zaman gidanka ko zaman wahala haka kawai za ku ɗauko ni wani kula da yara wato ga ƴar aiki kenan ko saboda an maida ni shim mai ruwa uku sha-sha-sha, da ƙurciyata na lalata kaina gurin gina rayuwar ƴaƴan wata nawa ko zuwa duniya ba su yi ba”
“Shiyasa kike cutar da su? To Allah ya toni asirin ki, kuma ki je na sake ki saki ɗaya...!”
“Ai ni da uku ka yi da ka fi burgeni”
“Ɗayan dai zan miki ƙyaji da shi”
“Tafi nono fari, ai ba kai ne autan maza ba”
“Na sani shiyasa na sake ki saboda ki samu damar auren wani”
“Aiko zaka gani dan sai kasan kayi hasarar mace irina”
Ta kaɓe masa Hijab ɗinta ta fice kamar zata tashi sama.
“Hakan be dace ba Hilal kana wasa da saki, daga wannan maganar zaka ce ka saketa kuma kana ganin yadda take ta lallaɓaka akan ka barta ɗakinta...”
“Na faɗa miki babu ruwanki da irin maganganun nan, kin cika salo da saka kanki cikin irin lamurran nan shiyasa komai aka yi sai a kin saka bakin ki shiyasa komai ake ɗora miki laifi”
“Amman....”
“Na ce ki min shiru ko?”
Uffan bata sake cewa ba sai ta cigaba da wasa da kan Ezzah shi kuma ya juya ya fice.
UZAIR POV.
Gaba ɗaya jikinsa yayi nauyi ji yake kamar idan ya motsa jikinsa zai rabu biyu, idonsa kawai yake iya zagaye ɗakin da su. Hakan ya bashi damar ganin mutanen da ke ciki a ɗakin ciki har da Abbah.
“Sannu Uzair, Sannu Allah ya baka lafiya”
Shine abunda kowa yake faɗa, sai dai shi abunda be gane ba, miya ke damunsa! Abunda zai iya tunawa kawai yaji abu ya tsikare shi sai ya faɗi, daga nan be iya tuna abunda ya faru.
Be iya amsa musu da komai ba in banda ido da yake binsu da su da kallo, har suka masa sannu suka fice cike da tausayawa. Abbah ne ya zauna kusa da shi sannan Mahaifiyarsa.
“Uzair ka ɗauki abunda ya faru da kai matsayin ƙaddara komai yana zuwa ne daga abunda Allah ya rubuta maka, kuma haƙuri shi ne zai kai ka ga har kaga ka ci riba ka samu a nan ka samu a acan”
“Wai mi yake faruwa da ni ne?”
Sai a lokacin ya samu damar tambaya.
“Uzair ka haɗu da matsala ne a ƙashinka na baya da kuma ƙashinka na ƙafarka, you wouldn't be able to walk again”
“Taya taya za a ce mun haka bayan ba haɗri na yi ba, ba wani ciwo na ji ba haka nan kawai za a ce mun na samu matsala”
“Nima abunda ya ba ni mamaki kenan, za a fitar da kai waje a duba lafiyarka”
“Abbah mi yake faruwa da ni ne?”
“Muma ba mu sani ba, likitan da ya duba ka ya tambaye ni wai ko ka taɓa haɗarin mota nace masa aa, ko ka taɓa yi baka faɗa ba?”
Hawaye suka fara masa zuba.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Wannan wane irin bala'i ne? Miya faru da ni ne haka, Hajiya ko dai mafarki na ke yi? Allah kasa na farka Allah wayyo ni Allah na”
Haka ƴa ɗinga maganganu Abbah sai kallonsa yake cike da tausayawa, suna haka sai ga wasu friends nasa sun shigo duba shi ciki har da Dr Tahir, da wasu abokanin sha-shancinsu na Abuja. Abbah suka fara tambaya ya mai jiki ya amsa musu da sauƙi sannan suka gaishe da Hajiya dake ta sharar hawaye, suka matsa kusa da Uzair suka tsaya suna masa ya jiki.
Amsa musu kawai yake amman kana ganinsa kasan ya rikice, ba fita hanyyacinsa yayi ba, amman wannan ƙaddarar da ta faɗo masa ya gaza yarda da ita, ta ya zai zama haka mutumen da ke tafiya lafiyarsa ƙalau shi ba faɗowa yayi ba shi ba haɗari ba ace ya haɗu da wannan matsalar, ta ya haka zai faru?
Sun aje masa kuɗi mai yawa ban cin siyayyar da suka masa, Abbah na yayi musu godiya, suka kama hanya suna Allah ya sauwaƙe, sai kawai Uzair ya ƙwalawa Tahir kira, cikin sauri ya juyo ya nufo inda yake su kuma sauran abokan suka fice.
“Ina son mu yi magana da kai Abbah dan Allah ku ɗan ba mu guri”
Daga Hajiya har Abbah tashi suka yi suka fita, sai Tahir ya zauna a kujerar da Abbah ya tashi yana fuskantar Uzair ya ce.
“Na je gida na samu baka nan, matar ka ce kawai, naje na saboda na ta buga wayarka ban samu ba, kuma naje guest house ɗin ka baka nan, babu abunda matarka bata faɗa min ba, har ɗan wuta ta kira ni, daman ta san kana wannan harkar ne?”
“Shekaran jiya ta gano, lokacin da na Amira ta aiko min da saƙo, ni zargin nake ma ko ita ce ta yi min wannan asirin na koma haka ne? Da wannan daga gani lamarin iska ne aljanu ne”
“Ko kuma Amira ba saboda ta dawo na samu labarin gurin Yayanta”
“Lallai zata iya min asiri, yarinyar nan muguwace”
“Zata maka ko kuma zai dawo kan ka idan na jikinta ya kare? Kasan fa bokan nan yace maka idan be kama Namra ba, zai dawo gun ka ne, sai gashi ya kama Amira yanzu kuma Amira ta dawo ina tunanin kai zai dawoma”
“Dan Allah Tahir kaje gurin bokan nan ka faɗa nasa halin da muke ciki, idan ma wani ne yayi min ya san yadda zai yi ya kare shi, idan kuma wannan aikin ne ya kare shi dan Allah Tahir”
Tahir ya dafa shi.
“Zanje karka samu damuwa zan je har can na masa magana duk yadda aka yi zuwa yamma zan dawo na faɗa maka”
“Tahir ba sai yamma ba, kaje yanzu baka ganin halin da nake ciki...?”
Ya ƙarasa cikin kuka mai ban tausayi.
“Okay zanje yanzu Allah ya baka lafiya”
“Na gode”
Ya faɗa hawaye na zuba a idonsa. Jikin sanyin jiki Tahir ya fice yana mamakin lamarin Uzair.
ASIM POV.
Yayi rama sosai a ƴan kwanakin nan da aka yi na amsar gaisuwa, Ranar da aka kwana ɗaya da rasuwar Ƴan gidansu Mardiya suka zo har da Mardiyar gurin gaisuwa, a nan ne yake nunawa wasu ita yana cewar ita ce matar da yake son aure.
Bayan an yi addu'ah uku ya ɗaure ya ƙara kwana biyu saboda masu zuwa ƙara masa gaisuwa. A ranar ne Mama Inno ta raba yaran ta ɗauki Hajara da ƙanenta biyu wasu daga ɓangaren mahaifinsu suka raba sauran ƴaƴan, abun gwanin tausayi, ranar Asim ya ci kuka kamar zai haɗiye zuciya ya mutu dan baƙin ciki, ashe Mama bata da rabon ta shiga gidan da yake da niyar sai mata, be taɓa baƙin cikin haɗuwa da Hajiya Sadiya ba sai yau, ji yayi kamar ace tana kusa da shi ya kamata yayi mata gunduwa-gunduwa, gashi ita kuma sai damunsa take da kira, yana ce mata bashi da lafiya.
Be yarda ya labartawa Nably abunda ya faru ba, amman yana faɗa mata bashi da lafiya kuma tace zata zo ganinsa ya hana, ita kuma duk hankalinta ya tashi hakan ya hanata komawa Abuja, dan ya faɗa mata ranar da zai dawo.
Ranar da bar sokoto sai da yayi kamar zai kashe kansa, gudu ya riƙayi da motar yana kuka kamar zai tashi sama. Da wuri ya isa Katsina saboda ya tashi tun asuba ne, ɗan kawai kar Hajiya ta gane halin da yake ciki ne yasa ya sauka nasarawa, dan yin wanka ya shirya ya canja tufafi. Daga wankan har shirin be ɗauke shi minti talatin ba, yana gamawa ya fito ya nufi gurin da motarsa take. Juyowa ya yi yana kallon gidan.
Be taɓa jin yayi missing ɗin Namra ba sai yau, haka kawai yau da ya tuna ta sai ya ji babu daɗi, daya tuna mamarsa sai Namra ta faɗo masa a rai, jikin rashin daɗin rai ya nufi gidan Hajiya Sadiya.
Sai da ya kama hanyar gidan sannan ya kira ya faɗa mata gashi nan ya shigo katsina har ma ya iso gidan.
“Okay okay galni nan zuwa”
Ko minti goma sha biyar ba'ayi ba, sai gata ta iso. Yayita ƙoƙarin danne damuwarsa ya nuna mata mara rashin lafiya ne kawai matsalarsa, bayan sun zauna a falo yake labarta masa yadda rashin lafiyar ta fara da fever kwanansa biyu asibiti.
“Gaskiya ka ji jiki sosai, ka rame Allah ya ƙara lafiya”
Da Amin ya amsa yana mata wani irin kallo wanda shi kaɗai yasan Manufarsa da kuma abinda yake ji a ransa a tare da shi. Ta shi tayi ta shiga ɗaki dan ɗauko masa apple ɗin, shi kuma ya fidɗo wayarsa ya aikawa Nably saƙo.
_Ki same ni a Dahir Exclusive Restaurant, yanzu ina gurin_
In few minutes ta masa reply.
_Okay on my way_
Ya aika mata da saƙon ne a yanzu dan ya samu ta fita gidan kamin Hajiya ta san wani abu kai, dan yasan ba zata bari ta fita ba.
Ta daɗe a ɗakin sannan ta fito riƙe da farin ƙyale da kuma jika ƙarama mai kamar hand bag, jakar ta fara jefa masa.
“Miliyan biyar ne a ciki, dan Allah Asim ka tabbatar ba a samu matsala irin waccan karon ba, ka ɗauki abun nan da muhimmanci sosai”
“Ba za a samu matsala ba wannan karon na miki alƙawari”
Ya faɗa kamar da gaske. Sannan ya miƙa mata hannu, ta bashi apple ɗin ya ɗauki jakar ya fice zuciyarsa har mazari take ya isa gurin da yake zaton Nably ta isa. Yana shiga mota tana kiransa tace masa gata nan gakin gate.
“Gani nan zuwa yanzu”
Ya kashe wayar, a hanya ya tsaya ya siye wani Apple green, sannan ya ƙarasa restaurant ɗin, yana fakin motarsa ya hangota tsaye jikin wata mota da yake zaton ta tace. Tana hangoshi ta ƙaraso kusa da shi idonta tab da ƙwalla, ji tayi kamar ta rumgume shi dan har ga Allah ta yi missing ɗinsa kuma tana son Asim sosai.
“Ya jikinka?”
“Alhamdullah”
Tare suka shiga ciki suka kama tebur, sai yasa aka kawo musu plate da ƴar ƙaramar wuƙa sai fork. Apple ɗin ya fiɗo ya za a mata ɗaya ya ɗauki ɗayan mai green.
“Wannan ita ce tsaraba ta zuciyata na baki ita har abada, wannan kuma ki ɗauke ta a matsayin zuciyarki ce Asim zai cinye”
Dariya ta yi mai cike da shauƙi da kuma so da ƙauna.
“Ai ka daɗe da cinye zuciyata, har ma da ganganjikina gaba ɗaya”
Ya kalli wayarta yana murmushi.
“Ki kashe wayarki kar wani ya dame mu da kira”
Ba musu ta kashe wayar, shi kuma tsoron yake kar Hajiya ta kirata.
“Bana son ki raga komai daga zuciyata. I love you”
“I love you too”
Ta faɗa sannan ta fara hanya apple ɗin ta tasoma ci kamar yadda shi ma ya fara cin nasa, sai fira yake mata kamar gaske ita kuma sai faman murmushi tana faɗa masa irin yadda ta yi missing ɗinsa.
Sai da suka gama cin apple ɗin sannan ya haɗa ma wayarsa alarm ɗin ƙarya ta yadda zai yi kamar an kira shi.
“Ko na miki oder abinci...?”
“A'a na ƙoshi wannan zuciyar taka ba zata bar ni na ci komai ba”
Ya fiddo wayarsa dake saman cinyarsa, yana faɗin.
“Kai Ogaba na kirana”
Yayi picking cikin ladabi kamar gaske.
“Okay to gani zuwa”
Ya sauke wayar tare da miƙewa tsaye.
“Am so sorry Dear Wallahi ana nema Urgent, amman idan kin min izinin tafiya”
“Ba komai daman ni dai burina na ganka, kuma na ganka, take care of yourself”
“I will my love, ke ma ki kula min da kan ki, bari ma saukeki gida ko?”
“No da mota na na zo”
Sai da yaje ya biya kuɗi sannan suka jero suka fito tare, har gurin motarta ya rakata ta kama hannunta ya riƙa ya ɗan murza, yana mai jin tausayinta a ransa, sai dai kuma idan ta tuna Mama sai yaji babu wani tausayi a zuciyarsa. Sai da ta kama hanya sannan ya nufi motarsa ya shiga.
SORRY MY FAN'S🙏
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *84*
*Shafin na ku ne ƴan ZAGON ƘASA CONVERSATION I HEART YOU ALL*
Wani irin taku Abdallah yake mai ɗaukar hankali da burge duk wata mace mai kallonsa. Ko da wasa be kalli gurin da Lamido yake ba, yayi kamar ma be san da shi a gurin ba.
“Surprise...”
Namra ta faɗa tana tare hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata. Ɗaya daga cikin murmushinsa mai tsadar nan ya ɗauka ya miƙa mata, yana kallonta cike da shauƙi dan ta masa kyau sosai.
“Surprise is better than disappointed, haka naji turawa na faɗa, faɗa min wanda ya saka idon nan nawa kumbura, na hukuntasa”
Ya faɗa dai-dai lokacin da ya ɗoro ƙafarsa saman matattakar balcony ɗin da suke tsaye. Kallon mamaki na musamman Namra ta yi masa.
“Idon ka ko nawa?”
“Idon ki ai nawa ne”
Ya bata amsa kai tsaye, and yana acting like akwai wani abu a tsakaninsu. Saurin kawar da maganar tare da cewa.
“Meet my Brother. Lamido meet Abdallah”
Lamido ya danne abunda ke zuciyarsa, na kalaman da ya ji Abdallah yayi a yanzu, ya miƙa masa hannu.
“Am Aliyu Adam Lamido”
Wani kallo Abdallah ya watsa masa irin like sai a yanzu ma ya lura da shi, sai kuma ya tsaya kallon hannun kamar mai karantar abu a jikin hannun. Sai kawai ya zuba hannayensa duka biyu a aljihunsa yana ɗaga masa.
“Nice to meet you Lamido”
Ɗan murmushin ƙarfin hali Lamido yayi ya janye hannunsa, abunda be yi ma Namra daɗi ba.
“Baka ga ne shi ba ne? Lamido ne fa wanda...”
“Na gane shi *ABNAM* let talk something important”
New name ɗin da Abdool ya bata ya bata mamaki yana abu kamar su ɗin daman can masoyana, a ɗayan ɓangaren kuma bata jidaɗin kalmarsa ta ƙarshe da ya furta akan Lamido ba. Sai kawai ta kalli Lamido ta ce
“Zan kawo maka keys ɗin kaje ka duba”
Kai kawai ya iya ɗaga mata, fuskarsa na nuna rashin jindaɗin da ke zuciyarsa. Saukowa ta yi saman balcony ɗin ita da Abdool suka nufi ɓangare Abbah gurin da yake sauke baƙinsa.
“Faɗa abunda yasa ki kuka mana Abnan”
“Abun farinciki ne da tsoro da mamaki a lokaci ɗaya”
“Kamar...”
Ajiyar zuciyarta ta sauke ta kai hannu ta tura ƙofar falon.
“Bismillah”
“Thank you”
Ya faɗa sannan ya saka ƙafafunsa cikin falon, sai da ya shiga sannan ita ta shiga ta maida ƙofar ta rufe, sai ta nufi wata ƙofar da zata sadata da part Anty Amarya.
Bata samu kowa a falon Anty ba, sai kawai ta nufi ɗakinta dan labarta mata zuwan Abdallah nan ma sai ta samu bata nan, ɗakin Aisha ta shiga.
“Ke Anty ta shigo nan?”
Ko kallonta Aisha bata yi hankalinta yana kan computer ta, ta kaɗa mata biro alamar no. Namra ta janyo ƙofar ɗakin, ta nufi freezer tana ta tunanin abunda zata haɗa masa, ya zo mata a bazata, bata shirya masa komai ba, Lamido ma bata masa komai ba, su biyu ɗin sun zame mata ƴan uwa babu na wulaƙantawa a cikinsu. Hannu tasa ta dafe kanta kamin ta kai hannu ta buɗe firiza ta ɗauko fruits ta haɗa masa fruit salad, sannan ta haɗa tea da coffee ko wane one cup sai kuma ta ɗauki ƙaton ture ta ɗora kayan sama. Wani tunani ya zo mata na ta canja tufafin da ke jikinta, kar kuma ya ɗauka dan ta ganshi ta canja kaya he may think otherwise. Kai ta girgiza sai kawai ta ɗauki turen ta nufi part ɗin Abbah.
Zaune ta same shi