Showing 90001 words to 93000 words out of 281103 words

Chapter 31 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61240

saboda kar kace na yaudare ka. Na sadaukarda komai nawa saboda kai, amman duk ban tsira ba? Irin kallon da kake min kenan? Nice ya kamata ace na zarge ka tun lokacin da na ji abunda kuke magana kai da Mama amman na taushe zuciyata ina ƙoƙarin yaƙi da ita akan ka, ka kan nuna son iyayena su taimaka kama amman duk be sa na zarge ka ba, miyasa baka tausayina ne? Yanzu na gano dalilin rashin son da Mama take min, kuna min kallon wawuya wacce bata san ciwon kanta ba.


Son ka ne Asim shine ya rufe min ido na kasa ganin laifin ka, babu irin furucin da ba amin ba akan ka, amman na dage sai na aureka, a tunani na kana min irin son da nake maka ne”


Ta ƙarasa maganar murya ƙasa-ƙasa irin kifi musulmim nama, tana hawaye. Shi kam tsire baki yayi ya kalleta


“Kowa ya sani ba tsakani da Allah kika aure ni ba, sai da wanda zai aureki yace ya fasa sannan aka nemo ni, yanzu kuma kina son yin amfani da damar da kike da ita na rashin lafiya ki kula wasu mazan a waje”


“Me kake nufi?”


“Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, waya kawo ki yanzu cikin asibitin nan? Ina kallon yadda ya rako ki ya koma, ko kin maidani mahaukaci ne, talauci ba yin kaina bane Namra, dan ina talaka ba zaki wulaƙanta ni a banza ba”


Ta miƙe tsaye tana masa kallon mamaki, har kofin ruwan dake hannunta ya zube.


“Ka zarge ni da komai, amman ban da Zina, dan ban sha nono ba, mahaifina be yi da ƴar wasu ba, dan haka ba za'ayi da ni ba, ban aikata zina ina budurwa ba, ba zan aikata da aurena ba. Kai butulu ne Asim wanda be san hallaci ba, ɗan bushiya mai soke uwar goyonsa a baya....”


Tasss ya watsa mata yatsunsa biyar a gefen fuskarsa, a zaune da yake, sai wani zanzana yake kamar ya riƙota yayi ta dukanta.


“Kim fita da ainahin kalar ki Namra, daman kin min duk abunda kika min ne dan wata rana ki min gori? To mina samu a auren naki? In banda baƙar ƙaddara miye ke bi na?”


Dafe kuncinta tayi ta juya a guje tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, ta fice ɗaga ɗakin.






RASHIDA POV.


Kukanta ne ya shigo da su Momy a ɗakin. Duk tambayar da suka mata kasa amsawa tayi sai kuka take kamar wace aka cirewa rai.

“Ya sake ni Momy ya sake ni! Na shiga uku na lalace na ba ni Momy mutuwa zan yi, Wayyo Allah na”


“Me kika masa?”


Momy ta tambaya hankali a tashe. Ta kardar kawai ta iya nunawa Momy tana kuka sosai.
Da sauri Momy ta ɗauki takardar ta buɗe.


“Ni Hilal a yau na saki Rashida saki ɗaya”


Momy na gama karantawa ta rufe takardar tana faɗin


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Sai ta riƙata, ta zaunar saman gado tana girgizata, ganin tana ƙoƙarin fita hayyacinta.


“Ke Rashida kwantar da hankalin ki zan sa ya maida ke kin ji?”


Ta rirriƙe Momy gamgam tana zare ido.


“Da gaske Momy?”


“Da gaske mana, ki kwantar da hankalin ki kinji? Zan yi magana da shi”


“Toh”


Tayi zurun kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kallon Ummu Faisak take wace ta shigo yanzu.


“Lafiya miya same ta?”


Ta ƙarasa da sauri tana tambaya. Momy bata iya faɗa mata komai ba ta fita ta kira likita, yayi mata allura, cikin ƙanƙanen lokaci ta samu bachi.
Sai da suka fito sannan Momy take labarta mata abunda ya faru cikin yanayin damuwa.


“Af ai da sauƙi tun da sakinta kawai yayi be kashe ta ba, ai a yanayin yadda ya bar gida na ɗauka yana zuwa zai kashe ne ma, kin ga yadda yake ji da matar nan? Hmmm”


“Aiko idan ka ganta kamar ta ƙwarai, ƙo dai wani abun ne ya haɗa su?”


“Ai haka ƴan matan zamani suke, suyi miki laflaf su kwace miki miji sannan su koreki, ai wannan saki daga gani bana banza bane mace na ciwon zubar ciki kuma asibiti gurin iyayenta? Hmmm”


“Ai yanzu sai an bincika za a ji ko minene, bari na faɗa ma Daddyn”


Cikin yanayin damuwa da ɗaurewar kai Momy take maganar.


Hilal ko da ya koma gida ya tarar yaransa sun dawo, daga gidan Hajiya, ko wanne fuskarsa babu walwala sun saka Kalsoom gaba, kamar su mata kuka.


“Hey kids”


Ya faɗa yana ƙokarin zaunawa sound so cool and funny. Sai duk suka nufo shi suna faɗar.


“Daddy wai Hajiya tace mana Ammyn mu ba lafiya tana asibiti”


Ya ɗan sosa kansa, sam ya manta yace kar Hajiya ta faɗa musu. Kalsoom dake ɗauke Rafiq ta nufo shi tana faɗin


“I try to explain but.. ”


Da ido yayi mata alama da tayi shiru yaja hannunta ya zaunar da ita kusa da shi, ya kalli yaran.


“Listen kids Maman ku ta ji sauƙi sosai, har ma tace na gaishe ku”


“Daddy ina son na ganta”


“Ba zaki ganta yanzu ba, amman ajima zan kira miki ita a waya ku gaisa”


“Tau”


Ulfah ce ta wayance, jin ance taji sauƙi, Ezzah kam ƙin sakewa tayi sai ƙoƙarin kuka take.


“Duk sun ci abinci, amman ita ta ƙi ta ci”


Ƙalsoom ta faɗa tana kallon Ezzah. Hilal ya kai hannu ya riƙo hannunta.


“Sweetheart ki ci abinci kin ji? Mamanki tana nan lafiya”


Kai kawai ta ɗaga masa ta share hawayen da suka zubo mata, ta nufi ɗakinsu.


******
Rashida bata farka ba sai dare, tea aka bata ta sha sannan ta kora da magani. Yanzu nen abunda ya faru ɗazu yake dawo mata, a ƙwaƙwalwa, da sannu-sannu take tuna komai, sai ta gane ashe ba mafarki ne take ba.
A hankali hawaye masu zafi suka fara sauko mata, zuciyarta na ƙona kamar garwashi.


Taya zata juye rayuwa babu Hilal? Taya zata bar ƴaƴanta a hannun Kalsoom? Yanzu me zata faɗawa iyayenta? Ga kuma ciwon dake jikinta, da wannen zata ji? Wani irin kuka take irin kukan nan na baƙinciki da baka son kowa ya ji.


Wayarta ta janyo ta buɗe password ɗin, kamin ta taɓa komai sai ga saƙwanin sun taso sama, na mutane da kuma mtn.
Na number Amira ta fara buɗewa, cikin ƙarfin hali ta ƙaranta, ta yi reply sannan ta aje wayar gefe tana kallon ƙanwarta Sa'adatu take bata haƙuri.


“Momy tace zatayi ma Daddy magana sai su yi magana da Hilal ɗin”


“A'a bana da buƙata nice nace ya sake ni, karki bari Momy ta kira shi, kije kice nace karta kira shi”


“Amman Adda...”


“Kawai ki faɗa mata, nice nace ya sake ni, kije ki faɗawa Momy”


Sa'adatu ta tashi ta fice tana hawayen tausayin ƴar'uwarta. Rashida ta share hawayen da suka zubo kata tana kallon wayarta dake ringing.
Number Hilal ta gani, har tayi kamar karta ɗauka, sai kuma ta danna picking ta kara a kunne, muryar Ulfah ta ji tana mata ya jiki kamin Ezzah ta karɓa.


“Ammyn wai kin ji sauƙi?”


Cikin yanayin damuwa Ezzah ta tambaya, sai kawai Rashida ta fashe da kuka.


“Na ji sauƙi Ezzah, amman ba zaki sake ganina gidan ku ba, Abbahn ku ya sake ni ya zaɓi Antyn ku a kaina, yace baya so na Antyn ku yake so, ita zata zama mamanku daga yanzu, Abban ku yace kar na sake shigo masa gida....!”


Hilal be san me Rashida take ce nata ba, amman hawayen da ya ga suna zuba a idon Ezzah y tabbatar masa ba lafiya ba. Da sauri ya ƙarɓe wayar ya kashe, yana kallon ƴarsa dake wani irin ɗaukar numfashi tana kuka.
Kamin yace wani abu kiran Hajiya ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka.


“Hello Hajiya”


“Ka zo yanzu ina neman ka”


Bata tsaya jiran abunda zai ce ba, ta kashe wayar, hakan ya tabbatar masa da ranta a ɓace yake.




MARDIYA POV.


Tana suɗar yatsun hannunta ta kalli Inna tace


“Wai Inna baki san wata addu'ah da ake karantawa ba, wallahi sai nayi ta mafarki wuta na bina, kullum sai na farka a firgice”


“To ni wata addu'ah na sani, kawai ki riƙa anbaton Allah dai idan kika firgita, kina fa cikin maƙiya, kowa ya saki gaba, ko wannan yarinyar Namratu ba ta iya miki sheri ba”


“Hmmm Wallahi ta Allah ba ta su ba, kuma abun duk ba a so sai gan shi gare ni wallahi, kuma Wallahi tallahi indai ina numfashi, sai na rama abunda Namra tayi min, sai na ɗasa mata baƙincikin da har ta mutu ba zata manta da ni”


“Ai ko ita zata so ki haukace, ni wallahi kin baɓ mamaki karma wace aka ɗaurewa baki kin ki shiru tana ta cin zarafin a gaban mutane,
Kuma ko abunta kika ɗauka ai dole ki ɗauka mace sai rowar tsiyar, ko gobarar da tayi ai zakkace ta fita, sai ƙaryar banza wai ita ƴar masu kuɗi ce ƴar masu kuɗi zata zauna nan a wulaƙance”


“Ƙaryar banza ce kawai ba wani ƴar mai kuɗi, ni ko cikin nan nata sai naga kamar zubar da shi tayi wallahi”


“Saboda me? To ko bana mijin ba ne”


“Waya sani, daga maƙota ta ɗauki ƙiyayah ta ɗora min, ai ko abunta na ɗauka be dace ta ci min mutunci cikin mutane ba”


“Ke ai wauta kika yi da ace tun lokacin kinje kin siyar ya za'ayi ta gani”


“Toh ai ina jin tsoro ne kar naje siyarwa asiri ya tono”


“To ai yanzu kin tonawa kan ki asirin”


“Uhmm”


Mardiya ta unƙura ta tashi ta fice riƙe da kwanon. Inna ta bita da kallon tana tsakin abun haushi.




*🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺*


*© Khadeeja Candy*


ATTENTION 👇🏻
*Duk waccce take ganin ta biya kuɗi an saka ta grp na Zogon ƙasa ina son ta san da wannan. Baki da damar sharing pages ɗina dan kin biya kuɗi har sai book ɗin ya kammala, idan na kai ƙarshe na ƙare book ɗin gaba ɗaya a lokacin ya zama mallakinki kina da damar ki ba duk wanda kike so aro, amman yanzu labari ne mai tafiya, kuma ke kuɗin littafi kika biya, ashe ko idan hakan ne sai ki jira har labari ya kammala gaba ɗaya, sannan ki bawa wanda kike so aro. Amman fitar da pages ɗin a yanxu yana nufi karyama mai yinsa gwuiwa ne da kuma kasuwa, hakan kuma shiga haƙƙi ne!*


*Har a bada ba zan yi ma kowa Allah ya isa ba akan littafi, wannan alkwari ne Wallahi ba zan yi ba. Amman idan har ku na min haka ne da wata manufa ta cuta Allah yana kallon ku. Dan yasan abunda ke zuciyar ko wane bawa, sannan ina son kusan cewa alamomin munafuƙi guda uku ne 1. In yayi zance sai yayi karya. 2. In yayi Alkhawari saiya sab'a. 3. In aka bashi Amana sai yayi ha'inci. Duk wanda ta shigo cikin gidan nan ta shigo ne bisa yarda da sharaɗin da aka gindaya na gidan, dan haka idan kin fitar min da littafi ba tare da na kammalashi ba, to kin ci amana ta kuma kin shiga cikin waɗancan mutane da Annabi ya faɗa*


*Duk wacce take fitar min da littafi dan karya min kasuwa ko dan rai na ya ɓace ko kuma dan ƙeta, to ta sani akwai shari'ah ni da ita gobe! Kina da damar ki bayar aro ne, idan na gama littafin gaba ɗaya, sai ki tattara pages ɗin ki turawa duk wanda kike so ta karanta. Amman tura pages ɗin a lokacin da labarin yake tafiya, shiga haƙƙi ne kuma abu ne da ba zan taɓa yafewa ba!*


_Allah ka ɗora mu a dai-dai, ka tunatar da mu abunda muka manta, kuma ka yafe mana abunda muka yi akan kuskure ko ganganci._


*PAGE - 41*


NOT EDITED ⚠


Wani kallo Ezzah take yi ma Kalsoom tana hawaye, maganganun mamanta na mata yawo aƙwaƙwalwa. Daga Hilal har Kalsoom ɗin kallonta suke, ba sun dalilin kukan nata ba, amman sun san ba abun ƙwarai ne Rashida ta faɗa mata ba. Doc ya kai hannunshi ya dafa sai kawai ta ƙwaɓe hannu ta juya da gudu ta nufi ɗakinsu.


“Daddy ƙyale ta Mama tace ta ji sauƙi fa”


Ulfah ta faɗa tana lanƙwamo wuyan Kalsoom da Hilal. Ɗan murmushi Kalsoom tayi tana riƙa hannunta.


“Na sani ta ji haushi ne ba a kai ta ta ga Mama ba”


Hilal ya miƙe tsaye zuciyarsa na raya masa akwai abunda Rashida tacewa ƴarsa.


“Bari naje gurin Hajiya tace tana nema na”


“Okay Allah ya kiyaye bari nayi magana da Ezzah”


“No karki yi magana da ita yanzu, bari sai da safe”


“Okay Allah ya tsare”


“Daddy Allah ya tsare”


Ulfah ta faɗa tana tsalle.


“Amin Sweetheart sai na dawo”


Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fice. Cikin ƴan mintuna ya isa gidan Hajiyarsa, ba tare da fargabar komai ba ya fito mota ya shiga cikin gidan.
Yana shiga falon ƙannensa da ƴaƴan ƴan'uwansa da suke gidan suka soma gaidashi suna masa sannu da zuwa, sai da ya gama gaisawa da su sannan ya nufi ɗakin Hajiya.


Da sallama ya shiga, ta amsa masa ba tare da ta kalleshi ba, sai sarƙoƙin dake gabanta take gyarawa, har ya zauna ƙasan Carpet yana ɗan kallon yanayinta.


“Hajiya ga ni Allah yasa ba laifi na yi ba”


“Au ashe ka san kayi laifi? Yanzu abun da kayi ma yarinyar nan dai-dai ne? Ban samu naje ganinta ba sai da yamman nan ina zuwa suka ce min wai ka sake ta, duk kunya ya kamani”


Ya ɗan shafa kansa.


“Ayyah Hajiya sorry ban nemi shawarar ki ba, nima a kai tsaye sakin ya zo min, kuma bana da wata mafita sai ta sakin ne”


“Amman fisabillillahi baka tashi sakinta ba sai da tayi ɓari? Kai baka ma tsoron ace Kalsoom ce? Na san kana haƙuri da ita, dan kai ne kaɗai zaka iya ɗaukar abunda Rashida take maka, amman ai tuni ya kamata ka yi haka ba yanzu ba”


“Hajiya idan na sake ta a lokacin da Kalsoom bata nan wa zai kula da yaran? Kuma lokacin ba zan iya sakin ta ba saboda bata min komai ba”


“To me ta maka yanzu? Tun tun tun baka gano illarta ba sai yanzu? Hilal bana son ka zama cikin irin mutanen fa”


Yayi ƙasa da muryarsa yana son faɗa mata gaskiyar lamari.


“Hajiya ba zan iya ɓoye miki ba, Rashida tana da Hiv kuma ni da Kalsoom da ƴaƴana duka ba mu da shi sai ita, kuma ta hanyar sex ta samr shi”


Wani abu Hajiya tayi da hannu irin na ƙyama da tsoro idan sun zo ma mutum a lokaci ɗaya.


“Kana nufin Rashida tana bin maza a waje kenan?”


“Ba wai ina nufi bane, haka ɗin ne, tun da ga alamu ya nuna kuma ta tura ma likitan da na ba jininta ya auna kuɗi dan ya ɓoye yace ba haka ba ne”


“Idan ko har haka ne, ba kayi laifi ba Hilal dan irin wannan matar babu mai son ta zamo uwar ƴaƴansa, ni dama can yarinyar nan bata min, ai ƙara ma daka sake ta taje can ta ƙarata ita da uban nata daya tsaya mata”


“Amman Hajiya dan Allah karki faɗawa kowa saboda rayuwar ƴarana, zasu iya shiga wani hali kuma duk wanda ya ji zai riƙa mana wani kallo ne”


“Haba Hilal ai wannan sirri ne tsakanin ɗa da uwa, babu wanda zai ji har abada, amman me zaka faɗawa iyayenta ne?”


“Zam ce ta zubar min da ciki ne shiyasa na sake ta, ai nasan ba zata taɓa faɗa musu gaskiya ba”


“Allah ya kyauta, Mahaifin ka ma be sani ba, dan ban faɗa masa ba, nima haka zance masa. Ai Allah ba azzalumin kowa bane shiyasa asirinta ya tono tun wuri da sai duk ta laƙa muku shi sannan a gano”


“Kwata-kwata matar nan ta fita rai na wallahi, babu abunda bana mata, babu irin haƙurin da bana yi da ita akan zamantakewar mu, akan me zata je ta bi wani a waje? Idan akwai abunda nake mata wanda bata so ko kuma be gamsar da ita ba ai sai ta faɗa min ai tattauna aƙe so zamantakewar aure da fahimtar juna, dan me zata watsar da yaranta taje ta aikata wannan mummunan abu? Allah kaɗai ya san iya tsawon lokacin data ɗauka tana aikatawa, nayi nadamar zama da ita Hajiya.


Da nasan haka zata zama da tun farko ban aureta ba, kuma ban sa laifin kowa ba kamar na mahaifinta dan shine ya tsaya kai da fata akan dole sai ta yi aiki, saboda kawai baya son aurna da ita, yanzu ai sai ya aura mata wanda yake so ”


“Ƙaddarori ne idan Allah ya kawo sai haƙuri, Allah dai ya ƙara tsarewa”


“Amin ni zan wuce”


“To Allah ya tashe mu lafiya, akwai waina a kula idan zaka ci”


“A'a bana son komai yau sai da safe”


Daga haka ya fice, Hajiya na kallonsa cike da tausayawa.
Koda ya koma gida Ulfah da Rafiq sun yi bachi, Kalsoom ce kawai a falo, ta ƙurawa tv ido, duk da hankalinta ba nan yake ba.
Shigowarsa yasa ta ɗago kai ta kalleshi fuskarta da yanayin damuwa.


“Har ka dawo?”


“Eh ke kaɗai ce a falon?”


“Eh me Hajiya tace maka?”


“Tace idan na zo na cire miki kunne guda na kai mata”


Ya faɗa yana jan kunnenta har sai da tayi ƴar ƙara


“Ouuchhh nima tace na kai mata hancin ka”


Taja masa hanci ta tashi da sauri daga gurin. Ƙyalƙyalewa yayi da dariya, yana kallon kunkurunta.


“Kalsoom zo nan”


“No no no”


“Please?”


“No no”


Ta nufi ɗakinta da sauri, sai ya bita yana dariya.


******
Washe gari da wuri Kalsoom ta tashi kamar yada ta saba, sai da ta ciro musu uniform ta ɗora musu saman kujera sannan ta nufi kitchen ta haɗa musu breakfast, har ta gama haɗa breakfast ɗin tunanin Rashida take, tana ganin kamar Hilal be kyauta ba idan be barta taje ta ganta ba.


Sai da ta zuba musu abincin a kula sannan ta shiga ɗakinsu ta tashe su, Ulfah ta fara tayarwa t miƙar da ita tsaye tana girgizata, sannan ta shiga tashin Ezzah


“Ezzah tashi ku yi shirin makaranta na gama muku abinci”


“Ki ƙyale ni ni ba zan je ba!”


Ta faɗa a tsawace tana jan bargota ta ƙara rufa, Kalsoom bata sake taɓa ta sai kawai ta shiga da Ulfah ta haɗa mata ruwan wanka ta fito ta nufi ɗakin Doc.
Zaune ta tararda shi yana karanta saƙon da Rashida ta aiko masa. Daga bakin ƙofa Kalsoom ta tsaya tace


“Doc Ezzah tana ta fushi har yanzu”


Ya ɗago ya kalleta


“Kamar ya me tace?”


“Wai ba zata je makaranta ba”


“What! Ba zata je makaranta ba as how? I hate nonsense”


Ya aje


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login