Showing 102001 words to 105000 words out of 281103 words
Chapter 35 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
dan jin kanun labarai, ko wannen baya son a bashi labari.
Sai dai sojojin da ke zagaye da asibitin basu ba su damar shiga ciki ba, balle har su ɗauki rahoto ko kuma video abunda yake kan faruwa ba.
A bakin kofa Abdallah ya tsaya yana kai da kawo har sai aka fito da ita ɗakin tiyata, bayan an cire mata albarushin.
“Doc is she live?”
Shine abinda Abdallah ya fara tambaya ganin an fito da ita daga ɗakin galalla kamar wanda bata numfashi, a kife take saman gadon asibitin dan a bayanta ne suka mata aikin cirar albarushin.
“She survived, but she's unconscious now and she will take 28 -32 hours before she wake up”
Likitan na faɗar haka ya suka wuce da ita wani ɗakin, tare da wasu Nurses. Da kallo Abdool ya bita sai da duka shige da ita ɗakin sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shafa kansa. Sannan ya zauna a kujerar dake gurin ya lumshe ido yana sauraren wayarsa da ke ringing.
Kira ne kan kira yake shigowa, tun wayar tana ringing da vibration ita kaɗai har cinyarsa ta gara amsawa, saboda yawan kira. Shi dai yasan ba zai iya ɗaukar kira kowa a yanzu ba, dan yasan ba zai wuce masu son jin lafiyarsa ba, abu ɗaya yaji zai iya, magana da ƴan jarida dan tabbatar musu da lafiyarsa. Hakan yasa ya miƙe tsaye ya ciro wayar ya miƙa PA ɗinsa dake tsaye kusa da shi.
Wani ɓangare na asibitin ya nufa, inda sauran sojojin suke. Yayi magana da su akan a canja ma Amira asibiti zuwa asibitin sojoji da ke Abuja. Cikin sirri suka kawo wata mota ya shiga yaje gida ya tsimtsa ya canja tufafin jikinsa dan duk sun ɓace da jini.
Army uniform ya saka ya shiga wata motar ya koma asibitin. Ko da ya isa har an canjawa Amira asibiti zuwa asibitin daya buƙata, wajen asibitin ya fito yayi magana da ƴan jarida ya tabbatar musu da abunda ya faru, sannan ya juya ya koma cikin asibiti shima aka soma duba lafiyarsa duk da sun san albarushin be same shi ba.
“Sir Hajiya ta matsa sai ta yi magana da kai, Mai Martaba ma ya kira tun ɗazu kusan sau biyar”
Ya faɗa bayan ya tsare masa ya maƙe guri ɗaya kamar irin ya sha jinin jikinsa ɗin nan.
Sai da aka cire masa abun awan jini sannan ya karɓi wayar. Number Mai maitaba ce wannan karon hakan yasa shi murmushi.
“My Royal Highness”
“Babana kana lafiya?”
“Ina nan ƙalau Mai martaba”
“Babana karka ɓoye min komai”
“Wallahi Babu abunda ya same ni, sai dai yarinya ita sun same ta”
“Ga mu nan gida duk sun rikice sai koke-koke suke, Ummin ka ma ta kirani wai nayi waya da kai? Ta kira ba kai ka ɗauka ba, tana jin dai ko sun same ka bata san halin da kake ciki ba”
“i'm fyn Mai martaba, yanzu nan ma nayi magana da ƴan jarida, da kun kalli news za ku gani ai”
“Wai ya abun ya faru? Kuma su wanene?”
“Wallahi ban san su ba, amman dukan an kashe su, ni ina fito daga restaurant ne kawai sai naga yarinya tana gudu ta doso inda nake, shine sai kawai naga wani ya fito a wata mota dake can nesa da mu, amman haka be hana bingdigar samunta da yake Allah ya rubuto, sai duk muka faɗi, sai na kira boys ɗin mu dake nan gida na faɗa musu sannan na kira head quarter na faɗa musu, kamin su bar gurin sai da suka harbi mutum biyu, kuma duk sun mutu. Sai dai dikansu basu tsira ba sai akayi musu ƙofar rago suna ganin haka sai suka fara buɗawa boys ɗin mu wuta, suma sai suka buɗa musu. Anyi nasara akan su dan an kashe su duka, sai dai suma sun kashe mana soldiers biyu”
“Subhanallah Allah ya tsare gaba, amman ita yarinya ba tare take da su ba?”
“Bana jin haka da ba zasu harbe ta ba, kuma ta zo da wata takardar hannunta an rubuta, wai nayi taka tsan-tsan akwai masu son kashe ni suna bibiyar sawuna, ba zasu min komai a garin Abuja ba har sai na isa katsina saboda sasu akayi”
“Amman ya akayi ita yarinyar ta san da wannan? Anya ba haɗin kai ba ne?”
“Tunanin hakan yasa aka bincika bullet ɗin dan a tabbatar na ƙwarai ne ko roba, an bincika bullet ɗin na ƙwarai ne irin wannan ne da ake shigo da shi ta waje, ta ɓarauniyar hanya, yanzu dai duk wasu tambayoyi sai idan ta farka zamu mata”
“Allah ya tsare gaba, a riƙa taka tsantsan Babana kana wasa da rayuwarka fa”
“Kar hakan ya dame ka Mai martaba, ɗan Adam baya wuce ƙaddararsa, kuma abunda Allah ya kawo babu mahani”
“Haka ne, amman gobe zaka dawo ko?”
Yayi dariya yana mai miƙewa tsaye ya nufi window gurin.
“Gobe kuma? Ai bamu gama meeting ba, akwai wanda za muyi gobe da jibi kamin na dawo”
“Kai ni wannan aiki naka Babana yana tsorata ni”
“To ya muka iya? Dole ne mu saiyardar rayuwarmu dan wasu su rayu”
“Toh Allah ya kyauta. Ga Mamanka zaku gaisa”
Haka Abdool ya bisu ɗaya bayan ɗaya yana gaisawa da matan uban masa da ƙannensa da ƴan'uwansa da suke gidan.
Yana katse kiran Mai martaba ya kira Ummi, ringing ɗaya ta ɗauka tana kuka.
“Son...”
“Ummi I'm fine Wallahi babu abunda ya same ni”
“Ban yarda da kai ba, ai ba zaka faɗa min gaskiya ba, naso na biyo mota saboda babu jirgi yanzu amman gobe da safe zan zo”
“Ummi you don't have to, Wallahi babu abunda ya same ni, yarinyar data tare min bullet ɗin ita aka samu, kuma an yi nasarar kashe su duka”
“I don't trust you”
“If you don't trust me, you should trust yourself, believe yourself remember how you treated your Son he will never ever lied to you”
“You started it”
“No I'm just show it”
“Whatever ni dai gobe zan zo”
“To Allah ya kai mu”
“Amin. Ga sisters naka za ku gaisa sun ta kiran wayarka sai wani ya ɗauka”
Ɗaya bayan ɗaya ya gaisa da su sannan Ummi ta karɓa.
“Ka kira Mai Martaba ɗazu na kira shi yace shi ma hankalinsa a tashe yake be same ka ba”
“Yanzu muka gama waya da shi”
“Okay, Son su waye ne suka maka haka?”
“Nima ban san su ba maƙiya ne kawai”
“Amman ita yarinya ta rayu? Ka santa ne? Ina ka haɗu da ita”
“Na fito ne kawai sai na ganta tana gudu ta doso inda na ke, shine suka buɗe mata wuta, tana da rai amman tana buƙatar addu'ah dan tana cikin mawuyacin hali”
“Allah ya tashi kafaɗunta, ko dan na mata godiya for what she did to our family”
“Ni kaina ina son ta tashi dan akwai tambayoyin da na ke son ta amsa min”
“Allah ya bata lafiya gobe zan zo”
“Ummi”
“Don't!”
Ya riƙe bakinsa kamar tana gabansa.
“To Allah kawo ki lafiya”
Daga haka ya kashe wayar ya juya ya fice daga ɗakin. Ba shi ya bar asibitin ba sai da ya karɓa waya ta fi a ƙirga ɗuk masu tambayar lafiyarsa ne ƴan'uwa da kuma abokan arziki.
NAMRA POV.
Tun da Yasmin ta bar gidan bata fito ko bakin ƙofa ba, balle har ta fito falo, Gwaggo Kulu bata takurata ba, dan tasan halin Namra daman can ba mai son surutu bace balle yanzu data fuskanci kamar tana cikin damuwa.
Duk wainar da ake toyawa a falon Namra bata sani ba, dan hankalinta ma kwata-kwata baya jikinta yana can wata duniyar tana tunanin lamarin rayuwa, yadda ta sauya mata a lokaci ɗaya. Turo ƙofar da Hindatu tayi ne yasa ta dawo hayyacinta har ta ɗan tsorota.
“Anty Namra”
Ta rumgune ta zumuɗi ita da Aisha. Ƴar far'ah tayi irin far'ar nan data zame maka dole tun da tasan ba zuwan daɗi ne ta yi ba.
Sai daga baya Maryam ta shigo dan tun shigowarta tana can gurin Gwaggo tanan mata faɗa akan rashin son zumunci, wai rabonta da gidan har ta manta.
A bakin ƙofa ta tsaya tana murmushi.
“Ta so muje ƴar Anty Abbah yace mu zo muje da ke”
“Da gaske?”
Namra ta tambaya tana zaro ido, irin mamakin ɗin nan da rashin yarda da zancen Maryam. Sai Aisha ta karɓa mata.
“Wallahi kuwa, da gaske shine ma ya kira ki a waya yace muje mu ɗauko ki”
“Ko dai wani abun ai min?”
Ta faɗa da muryar tausayi tana kallonsu, dan bata gamsu Abbah zai ce aje a zo da ita hakan nan kawai ba.
“Babu abunda zai miki baya ma gidan yanzu na fita, Anty ce ta buɗe masa wuta shiyasa ya yarda”
Shiru ta ɗan yi tana tunani, kamin ta miƙe tsaye ta ɗauki jakarta ta rayata, ta kalli Maryam.
“Dan Allah Abbah ne yace na zo?”
Maryam ta dafe kanta.
“Kai ni Allah na, Namra nawa zaki biya ni ne da zan miki ƙarya”
“Ina jin tsoro ne”
“Daman ai kullum cikin tsoro kike”
Ta juya ta fice tana mai jin haushin lamarin Namra. Cikin rashin kuzari ta fito ɗakin tana riƙe da hannun Aisha ta zo ta risina gaban Gwaggo dake zaune falon tana mata sallama kamar wanda bata son zuwa.
Gwaggo na kallon idonta ta kalli Maryam tace
“Duk aka haɗa baki da ke aka yi ma Namra wani abu ko? Heeeee Wallahi sai kin raina kan ki”
Maryam ta ɗora hannu saman kai tana dariya
“Oh Ni na shiga uku, wai fuskata tayi kama da mugaye ne hala?”
“Na dai san halin ki, shegen karanbani da iyayi, kuma na faɗa miki, wallahi ran ki sai ya fi na kowa ɓaci duk aka haɗa baki da ke”
Da dariya ta fita falon. Har gurin Mota Gwaggo ta raka su, tana yi Maryam jan kunne ta daina tuƙin dare kuma ta kula da hanya ban da gudu.
Har suka isa gida gaban Namra be daina dakan uku-uku ba, saboda tsoro da tunanin abunda Abbah zai mata. Lokacin da Namra ta fito motar sai ta ɗaga kanta sama ta kalli gid, idonta ya cika da hawaye, tuna rayuwar da tayi a ciki, da hawaye shaɓe-shaɓe Hindatu taja hannunta suka shiga falo.
Tsaye suka same Anty Amarya tana tsumayinsu, duk wani kunya da take na Namra yau cireshi tayi sai ta zo da sauri gurin ƙofa ta rumgume ƴarta idonta cike da hawaye, haƙiƙa tayi farincikin ganin Namra, sai dai kuma bata jidaɗin ganin yadda ta lalace ba, kamar wance ta shekara tana ciwo.
Maryam ne da Aisha suka ɗauko mata abinci da sha suka jera saman center table. Namra ta kallesu da murmushi.
“Thank you Sisters amman ni ba na cin komai”
“Saboda me? ”
Anty Amarya ta tambaya.
“Namra kamar akwai abunda yake damun ki?”
Shiru ta ɗan yi tana nazarin abunda zata cewa Anty Amarya, dan bata jin zata iya faɗa mata abunda Asim.yayi mata, ta san ba zai mata daɗi ba kuma ba zata ƙyale ba, bayan kuma koma minene itace ta jawa kanta.
“Babu abunda yake damuna, na riga na ci abinci gidan Gwaggo ne, har wanka ma nayi ina shirin bachi suka zo”
“Amman duk da haka Namra kina da damuwa be kamata ki ɓoye min ba, dan nasan wannan zuwan bana banza bane, babu yadda za ayi ki tsallake Asim ki zo nan bayan kin san yana gadon asibiti kwance”
“A...an sallame shi ai, yana gida Mamanshi take jinyarsa shine yace na zo saboda na sha kai da maganar gida ne, nima kwana biyu zan yi na koma”
Anty tayi murmushi, dan tasan ba gaskiya Namra ta faɗa mata ba.
Hajiya Barau ce ta shigo da Sallama tana faɗin maraba da baƙi.
“Yau garin mu? Ina ji maƙi baƙi”
Anty Amarya tayi dariya ta tashi ta shige ɗakinta. A ɗayan kujerar da Namra take zaune Hajiya Barau ta zauna tana satar kallonta, sai fira suke sama-sama tana tambayar labarin Katsina. Sai nanata mata rashin jindaɗin zuwa ganin Asim da Abbah be barta taje ba.
Sai da dare ya raba sannan tayi mata sallama ta tashi ta fice, zuciyarta cike da gulma.
Bayan fitarta Hajiya Barau, Aisha take labartama Namra wanda zai auri Maryam da Hindatu duk sun zo sun gaida Abbah, kuma sun turo iyayensu, dan tsayar da magana.
Namra ta kallesu tana dariya.
“Eyyyye Amare”
Hindatu ce ta ji kunya har ta rufe ido, Maryam kan dariya ta riƙayi sai ta tashi ta bar falon kasancewar tana waya da angon ne.
“Saura ke”
Namra ta faɗa tana wasa da hannun Aisha, sai Aisha tayi mata wani kallo.
“Ni Anty no da na ss2”
“Ƴar jss ma anyi ma aure balle ss”
Dariya Aisha tayi ta rufe fuskarta. Dammm gaban Namra ya yanke ya faɗi, jin ƙarar tsayawar Mota, zuciyarta na nasalta mata Abbah ne ya dawo, ji take idan ya shigo rufeta zai yi da ruwan masifa. Da sauri ta tashi ta nufi ɗakin Anty Amarya gabanta na ci gaba da faɗuwa.
Tsaye ta tararda Anty Amarya tana gyara tufafin da suke wardrobe ɗinta, kallo ɗaya tayi ma Namra ta ɗauke kai tana murmushi, kamar ta san abunda Namra ta jo ma gudu.
“Ai shine yace aje a zo da ke”
“Amman be ce komai ba?”
“Be ce ba, dan shi kansa yana san kina cikin matsala akwai abunda yake damun ki”
“Babu abunda yake damuna Anty”
Anty ta bar tufafin ta zo ta zauna kusa da Namra
“Farinciki da baƙin ciki abubuwa ne da basa iya ɓoye kan su Namra, jikin ki ma ya nuna haka, dubi kiga yadda kika lalace kika rame kamar ba ke ba, Namra karki ɓoye min damuwarki, ni Mahaifiyar ki ce babu wanda ya dace ya ji matsalar ki sai ni”
“Anty babu abunda yake damu na, kawai na zo na gan ku ne”
“Namra dubi kam ki? Kin ga yadda kika lalace?”
“Ba ni da lafiya ne”
“Me ke damun ki?”
“A nan ƙasan marana iya jin ciwo ne, sai kuma ciwon kai da nake fama da shi, ga zafin jiki”
Duk abubuwan data faɗa gaskiya ne tana jin su sai dai bata jin wata matsala ne ko kuma ciwo, yanzu kuma tayi ma Anty ƙarya ne dan ta ƙyale ta.
“To gobe za muje asibiti likita ya duba ki”
“Allah ya kai mu”
“Amin”
Ta faɗa tana janye blanket ɗin dake saman gadonta.
“Ki kwanta a nan ni part ɗin Abbah ku zan kwana, idan kuma ba zaki iya kwana nan ba ki koma ɗakin Maryam”
“A'a nan zan kwana”
Ta faɗa tana kwantawa saman gadon.
Sai da Anty ta gama gyara komai na ɗakin sannan ta ɗauki wasu abubuwa ta yi ma Namra sai da safe ta fice.
ASIM POV.
Bayan ya gama shan koko Mama ta kalleshi tace
“Yau fa kwana biyu yarinyar nan bata leƙo asibitin nan ba”
“Ai ba zata zo ba”
Ya faɗa yana goge bakinshi
“Saboda me?”
“Faɗa muka yi da ita har ma mareta kuma na faɗa mata maganganu”
“Miya haɗa ku”
“Wani na gani ya rako ta, shine wai nayi magana tace ina zarginta, har da wani wai ta ji maganar da muke ɓoyewa na kuɗin a dashe”
Mama ta riƙe baki.
“Mai kaza aljihu baya jimirin ass, daga magana sai kuma tace ana zarginta? Daman tasan abunda take kenan, ni kai na wallahi naga yarinyar da wani amman ban faɗa ba saboda kar na ɓata muku zama, daman ai na faɗa maka ba da zuciya ɗaya take zaune da kai ba”
“Ai yanzu na gane halinta, dan yi mata magana shine har ta min jawabi wai ba na da komai ta aure na lalata mata rayuwa na rabata da karatun ta”
“Amman Ibrahim ka yi wauta, ai kamata yayi ka sa mata ido ka ga iya gudun ruwanta, kuma yanzu idan ma gidan su ta tafi ai sai tace ka ci amanarta kuma ka zarge ka koreta, kuma kai yanzu ko sallamarka akayi ba itace zata yi hidima da kai ba? Ni fa gida zan koma tun da can ma akwai yara ga sana'a na baro kasan idan ba dole ba babu abunda zai zaunar da nan, tunanin hakan tasa Wallahi ban faɗa maka ba.
Yanzu zuwa kaiwai zata yi ta ɓata maka suna, sannan idan ka rabu da ita a yanzu kana da halin auren wata ne? Ai dole kayi haƙuri da ita har Allah ya nuna maka kaji sauƙi sosai ka warke kayi kuɗi, ka auro wata sannan idan ita rabuwa zaka yi da ita sai ka yi, daman sun saba yaba maka rashin mutunci, kawai ka bata haƙuri kace kayi nadama, ai Allah ma ba zai barta ba ace da aurenka kana zina haba abun ai yayi muni, daman can ba ƴar tarbiya bace shiyasa ta bi mutumen aka riƙa cewa kai ne ka ɗauke ta, har ɗan'uwanta ya fasa aurenta kai aka ƙaƙaba maka ƙaya”
Ajiyar zuciya ya sauke wani irin ɓacin rai me ke ziyartarsa.
“Amman Wallahi Yarinyar nan ta ci amanata sosai”
“Haƙuri dai za kayi, ai babu yadda ban yi ba akan karka aureta amman ka tsaya kai da fata sai ka aureta”
“Nayi tunanin aurenta zai zame min alheri ne shiyasa na yi”
“Ka kirata dai yanzu kace ta dawo, kar taje ta shafa maka kashin kaji gurin matsiyacin uban nan nata mai dukiyar likudi (Kuɗin da ba'a iya ci)”
“Bana jin tana garin nan fa”
“Shiyasa na ce ai ka kirata ba kana da number uwarta ba? Sai ka kirata ka bata haƙuri tun dai lafiya ta samu an kusa sallamar ka, idan ka kira karka nuna musu wani abun ne ya haɗa ku, idan sun ce tace kayi mata wani abu kace kai ƙarya take maka, sai idan ta gaji da auren ka ne, karka yarda ka nuna wani abun ne ya haɗa ku”
Kwantawa yayi saman gadon zuciyarsa cike da baƙinciki abunda Namra ta masa, har yana jin kamar ba zai iya kiranta ba, dan ta ci zalinsa da yawa.
“Baka da wata mafita sai wannan, idan kuma kana ganin akwai wata hanya mai fiddaka sai ka yi”
Ta faɗa tana ɗaukar ledar ƙosai da robar koko ta fice.
RASHIDA POV
Mataki uku ake bi gurin gwajin jinin dan a tabbatar da mutum yana ɗauke da cutar, idan an yi na farko ba a tsallake ba sai ayi na biyu idan shima ba a tsallake ba sai ayi na uku.
Duka an yi ma Rashida kuma results ɗaya ya bada cewar tana ɗauke da cutar, tun a cikin asibitin ta fara kuka, har ta iso gurin motarta. Nadamar taraiya da Alh. Bashir take taraiyarta da shi be haifa mata ɗa mai ido ba, be sata komai ba sai baƙinnciki da da na sani.
Tunanin yadda zata faɗawa Momy take, mutuƙar da faɗa mata gaskiya ta san ita ma gudunta za ta yi, mu'alamarta