Showing 66001 words to 69000 words out of 281103 words
Chapter 23 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
ɗakin da shirinsa na zuwa office.
Robar fitsarin ya ta bashi, ya karɓa yayi mata kiss, sannan ya fice. Ɗakin Kalsoom ya shiga, tana jin motsinta ta lafe kamar tana bachi, itama kiss ɗin yayi mata sannan ya fice.
Rashida na jin tashin motarsa ta janyo wayarta ta danna number Asmee, ringing huɗu tayi sannan ta ɗauka.
“Asmee an tashi lafiya?”
“Lafiya ƙalau ya gidan?”
Ya amsa mata muryarta da alamar damuwa.
“Asmee yau ba zan samu fita ba, bana jindaɗi, sai dai kr kije idan da hali”
“Me ke damun ki?”
“Abubuwa da yawa ga jikin duk ya min nauyi”
“Ko dai ciki ne?”
“Haka nake tunani nima”
“Allah ya raba lafiya”
Jin ta faɗa ba da wani jindaɗi ba yasa Rashida Tambaya.
“Ya naji muryar ki ba daɗi?”
“Ba komai, nima bana jindaɗin ne, amman zan daure a haka naje”
“Yauwa na gode sosai, kin ce dai yana aiki sosai ko?”
“Sosai Wallahi kamar yan kan wuƙa, duk yadda mu kayi zan faɗa miki”
“Okay na gode”
Rashida na kashe wayar Asmee ta fashe da kuka.
‘Allah kasa ba gaske bane Allah, idan har da gaske ne ya ci amanata, tun da yasan yana da shi kuma ya nemi ya kwana da ni, Wallahi dana sani ni dama ban je gunsa neman magani ba, mugun Malami kawai’
Abunda take ta tunani a zuciyarta kenan, a fili kam kuka kawai take, kamar ta cire idonta.
_________________________________________
Kuyi Haƙuri da wannan idan Allah ya bani iko zan kara muku wani anjima.
BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY 😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*
Website
www.khadeejacandy.com.ng
Godiya marar iyaka gareki Daughter, na gode na gode I really did not expect this awesome surprise from your side
Allah ya kara arziki 😘
*PAGE - 31*
NOT EDITED ⚠️
Ƴan seconds ya rage wayar ta fara ringing sai kawai ta kashe, tana tunanin yadda za fallasawa kanta asiri idan har ta yarda ta faɗa masa danuwarta, ba duka ɗan'uwane yake taimako dan Allah ba, ballanta shi data san dole ne ya faɗawa Hajiya Barau, ita kuma fitar da maganar zata yi, sai a fara cewa tana roƙon dangi.
Juyowa tayi ta nufo gurin da Hajara take zaune, ita ma ta zauna tana miƙa mata wayar.
“Har kin kira?”
“A'a ban kira ba na fasa ne”
Ta faɗa tana murmushi, isowar Mama yasa ta sadda kanta ƙasa tana watsa da yatsun hannunta.
“Wai gida za mu koma yanzu”
Daga Hajara har Namra kallonta suka yi
“Gida kuma? Ina ba dai sokoto ba ko?”
Namra ta tambaya cike da mamaki.
“Can fa, wai so nake muje yanzu kamin yamma mun isa sai da gobe kuma mu juyo”
“Amman zuwa lafiya ne?”
Mama ta ɗan yi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce mata.
“A'a wai kuɗi zan je na ranto idan har Allah yasa an samu sai a siye maganin da likita ya rubuta ta, tun da naga alamun sauƙi a jikinsa amman kumburin nan na kansa yana bani tsoro. Kuma ina son naje na ɗauko wasu tufafin gashi mai son Hajara shi ma ya damu yaushe za mu dawo”
Namra ta sauke ajiyar zuciya cike da tausayawa, ji take kamar ace tana da mafitar su ta ɗauka ta bada, ba sai taje neman rance ba.
“Amman Mama da zaki yi haƙuri har gobe, saboda yanzu rana yayi sosai, kuma zaku iya zuwa ku tarar da jira a tasha, ƙara ki haƙura har da safe sai ki tafi, amman tafiyar dare ba kyau, musamman lokacin nan na muke cikin matsalar tsaro”
Mama ta ɗan yi shiru, tana nazarin maganganun Namra.
“Nima haka nake gani, ƙara na haƙura har zuwa goben”
Ta faɗa daga tsayen da take tana gyara ɗaurin zanenta, sai kuma ta juya ta koma dan faɗawa Asim zancen canjin tafiyar.
Sai da wuce sannan Hajara ta kalli Namra tace
“Tafiya yanzu sai kace waɗanda aka kora daga gari”
“Nima ai shi na gani, ƙara dai a haƙura har da safe, yau da gobe a duk ɗaya ne wajen Allah”
Namra ta faɗa tana ƙoƙarin tashi
“Lallai kam, nima bana son tafiya irin wannan”
Murmushi kawai tayi ta nufi ward ɗin da nufin ƙara tausasa Mama ta haƙura da tafiyar har gobe.
A bakin ƙofar ta tsaya cak! Tana sauraren muryar Mama da kunnuwanta suke sato mata.
“Na ce amman ai dubu ɗari sun isa ko? Kar mu karɓo kuɗin duka ya zama ba muna da komai gurin mai dashen”
“A'a Mama ki karɓo gaba ɗaya, kin san dole ne mu siye abinci, kuma wata ƙila ba wannan maganin kawai za a siya ba”
“Amman Ibrahim idan muka karɓi kuɗin duka mun fita daga adashen kenan fa, abinci idan har taga babu shi ai dole ta faɗa ma iyayen nata, ni ina mamakin ace ƴarka ta yi wuta irin haka ka kasa taimaka mata, anya wai ƴar su ce tagaske kuwa? Ni bana ganin a kashe kuɗi dika fa”
“Haba Mama lafiya na kama da me? Idan har Allah yasa na ji sauƙi, ai sai a samo wasu a ake shiga kuma”
“Ina za'a samu wasu Ibrahim? Kana ganin yadda suka juya maka baya, Wallahi bana tunanin zaka samu wani abu a auren nan, duba kaga ko fa ƴar garar nan da ake ba su maka ba, yanzu dubi halin da kake ciki ai ko basu fitar da kai waje ba, sa maka iya ƙoƙarin su amman suja ƙyale ka”
Wani dogon numfashi Asim.yaja ya sauke zuciyarsa cike da jin zafin abunda iyayen Namra suka masa.
“Allah dai ya bani lafiya, idan kiɗa ya canja rawa ma dole ta canja, idan su yi dan Allah ba sa yi dan ƴar su”
Kamar an jefar da gilass a ƙasa ya tarwatse haka taji a zuciyarta, lokacin da maganganun Asim suka daki dodon kunnenta.
Da sauri tayi baya tana maida numfashi, tare da haɗiye yawu a lokaci ɗaya. Wani irin mamaki take tana girgiza kai, kamin tayi haramar barin gurin.
Da sauri-sauri take tafiya kamar zata haɗa da gudu, ji take kamar tayi tsalle ta ganta a wani wajen, ta kasa yarda da kunnuwanta sun ji abunda Asim da Mahaifiyarsa suke faɗa.
Ta tari mai Napep tana haƙi kamar wanda aka janye wa numfashi.
“Nasarawa zaka kai”
“To ɗari da Hansi, kuma sai na bi ta Yarima Estate na sauke wannan matar”
Kai kawai Namra ɗaga masa, ta shiga Napep ɗin ba dan hankalinta yana jikinta ba. Yarinyar dake kusa da ita taja wani dogon tsaki, tana matsawa can gefe irin tana ƙyaƙyamin Namra ɗin nan.
“Mtswww ni dama zaka sauke ta, ta nemi wani sai na biya ka kuɗin duka”
“A a haƙura dai zaki yi Hajiya, ai da kamin a ɗauke ta kika ce haka, amman yanzu na riga na ɗauko ta kyayi wannan maganar kuma”
Mai Napep ɗin ya faɗa, yana mai cigaba da tuƙinsa. Sai a lokacin Namra ta kalle ta da kyau.
“A'a ka sauke ni mana ka kaita ita kaɗai saboda ni ba mutum bace, ko kuma Napep ɗin ta gidan ku ce, idan har kin isa miyasa ba'a siya miki mota ba? Ko kuma ayi miki direba na ki na kan ki? Wallahi ƙaryar arziki kike tun da har kika iya shigo Napep”
Ƙasa-ƙasa ta kalli Namra tana wani yamutsa fuska, ita har ga Allah ƙyaƙƙyamin Namra take. Wayarta dake jaka tayi ringing, tayi saurin fidɗo purse ɗin dake cikin jakar ta cire wayar tare da yin picking ta kara a kunne.
“Hello Dude”
Ta ɗan yi shiru kamin ta sake cewa.
“Ni na baro motar can, Ummy ce na faɗa mata, wai bata turo direba tun da ban faɗa mata zan fita ba”
“Eh ina kam Napep n kusa isa, okay bye safe trip Dude”
Ta kashe wayar kamar ta fasa kuka, kamin a isa Estate ɗin nasu har ta tsawala.
Har bakin gate ɗin gidansu ya sauke ta, ta ciro 1k ta miƙa masa, bata tsaya karɓar canji ba ta nufi gidan, da sojoji suke gadi, da sauri suka buɗe mata gate shige cikin, sai ƙyaƙƙyamin kanta take.
Kai kawai mai Napep ɗin ya kaɗa ya wuce da Namra Nasarawa road.
A ƙofar gidan su Mardiya tace a sauke ta, ta ciro ɗari biyu ta miƙa masa ya karɓa ya bata canji sannan ta juya ta nufi cikin gidan, zuciyarta na dawo da maganganun da kunnuwanta suka joyo mata.
A zauren gidan ta tsaya, ta jingina da ginin gurin ta lumshe.
‘Miyasa Asim yake ƙoƙarin ɓoye min sirrin sa? Me suke shiryawa shi da mahaifiyarsa? Kar zancen Anty ya zama gaskiya, kar dai ace rayuwar Asim ta canja, da biyu ya aure ni kenan? Soyayyar daya nuna min a baya ta ƙarya ce?’
Hawaye ya silalo daga idonta, dake lumshe, sai kuma ta girgiza kai tana cigaba da zancen zuci.
‘Amman ya so ni a baya kuma so na gaskiya, miyasa yanzu zai canja? Na juyawa kowa baya saboda shi, ba zai min haka ba, what if i choose the wrong person? No no no it's Asim mutumen da yake son ki so na haƙiƙa mutumen da yace min miki ba dukiyarki ce a gabansa ba’
Ta buɗe ido tana share hawayenta.
“Amman mi yake nufi da idan ba suyi dan Allah sa yi dan ni? Me yake nufi da idan rawa ta canja, Allah ka fahimtar da ni, Allah ka amintar da ni, Allah kar ka saka zancen Anty ya zama gaskiya, Allah kar kasa Asim ya zama cikin mutanen da za su min Zagon Ƙasa, Allah kar kasa ayi ma auren nan na mu dariya”
A fili tayi furucin tana kuka, zuciyarta a karye, tana ji a jikinta ranar nadamar ta tana daf ta ita.
Ganin wata zata fito daga cikin gidan yasa tayi saurin ɓoye kukanta.
“Namra ce a nan tsaye?”
“Eh yanzu na shigo ina wuni?”
“Ya jikin mai gidan na ki?”
“Da sauƙi sosai”
“Allah ya ƙara sauke, har yanzu dai ba mu samu mun koma mu ƙara dubashi ba”
“Ba komai ai, kuna ta sana'ah ba zama”
“Ba zama fa Allah dai ya ɗauƙe Wahala”
“Amin”
Namra ta kunna kai cikin gidan, ita kuma ta fice tana gyara hijabinta.
HILAL POV.
Yau one day da gwajin da ya kai ayi ma Rashida, dan haka yana buƙatar karɓo result ɗin dan tabbatar da zarginsa, duk da alamu sun nuna cikin ne amman ya fi son ya ƙara tabbatarwa.
Lokacin daya gama duba Patients ɗinsa sai ya nufi lab dan karɓar sakamakon.
To his surprise ba abunda yake zato ba kawai ya gani, a cikin result ɗin akwai symptom ɗin HIV. Haka ya riƙa karanta result ɗin ba daɗi, but still abu ɗaya yake gani da biyu yake gani.
Ciki da kuma symptom.
Ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi, kar mutanen da suke gurin su zargi wani abu. Cikin rashin kuzari ya dawo office ɗinsa, har ya zauna sai kuma ya tashi tsaye, sai karanta takardar yake numfashinsa na yawo, wani zafi ya riƙa jin yana masa yawo tun daga cikin cikinsa zuwa ƙwaƙwalwarsa.
“Ko dai mistake suka yi? How could this happen?”
Ya kasa yarda, mamaki yake har yanzu, shi dai yasan yana yawan gwada kansa every 6 months da kuma iyalansa, kuma lokacin da aka auna jinin Kalsoom be nuna haka ba, why Rashida?
Gani yake mistake ne suka yi, sai dai baya jin zai iya koma ya tambayesu, abunda kawai zai iya, shine ya sake ɗibar jinin nata, da na ƴaƴansa da kuma na Kalsoom ya kai ward ɗin da ake gwajin cutar, dan tabbatar da zarginsa, idan har da gaske ne ai zai nuna yadda ta samu ciwon da kuma daɗewarsa a jikinta.
Be iya ƙarasa aikin ba ya haɗa kayansa ya ɗauki ƙaramin box ɗinsa ya cire labcoat ya riƙe a hannu ya fice, ba tare daya tsaya kulle office ɗin ba.
Ko da ya isa gida kansa har wani zafi yake kamar an kunna masa wuta, gaba ɗaya kalar idonsa, da fuskarsa ta canja irin kana kallonsa kasan yana cikin damuwa.
Rashida na zaune falo riƙe da plate tana cin abinci, ba laifi yanzu kan ta ɗan samu sauƙi dan ita ma tayi girkin sa kanta. A bakin ƙofar falon ya tsaya yana kallonta wani tausayinta yaji ya lulluɓe shi har idonsa suka cika da ƙwallah.
Ita kuma ta ɗan kalle shi kaɗan ta kauce kai, ba dan bata son kallon nasa ba, sai dan baƙin kishi daya rufe mata ido, gani take yanzu ai ba ita kaɗai ce da shi ba.
Yana sako ƙafarsa a first step ɗin falon, sai ta tashi ta nufi ɗakinta. Shi kuma ya tsaya a gurin ya bita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta.
______________________________________________
Assalamu alaikum Habibaties 🌺
Ina fatar kuna cikin koshin lafiya? Allah yasa haka Amin
My dear readers idan Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya, idan na yi page 35 tau ZAGON ƘASA na Khadeeja Candy ya koma na siyarwa, daga bakin Page 35 har zuwa karshe na kudi ne, daga page 1 zuwa 35 free ne. Nasan zaku ga chanji yazo muku ba ta yadda kuka zata ba, ku yi hakuri ku min uzuri, haka sauyin ya zo. Kuma ina fatar zaku goya min baya, fiye da yadda kuke min a da, soyayyar ku da haɗin kan ku, shi na ke fata a kullum, Allah yasa ku min kyakkyawar fahimta. 😊👌
Ga waɗanda suke sha'awa. Naira ɗari biyu ₦200 zaku turo ta wannan account ɗin 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.
Ga wanɗanda basa da account kuma za su iya turo katin waya na line mtn na dari biyu da hansin ₦250 ta wannan number 08036126660
Idan kun tura. Sai ku turo da shaidar biyan kudin wato screenshot ta wannan number 08036126660.
NA GODE 😊
BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*
Website
www.khadeejacandy.com.ng
*PAGE - 32*
NOT EDITED ⚠️
Ɗakinsa ya wuce ya aje kayan da suke hannunsa, sannan ya fito ya shiga ɗakinta. Zaune ya same tana taunar naman abincin data gama ci, kusa da ita ya zauna yayi mata ƙuri da ido, kamar mai tunanin abunda zai faɗa mata.
“What?”
Ta tambaya shi sam be san ta lura da kallon da yake mata ba har sai da tayi magana.
“Bana da ikon kallon ki ne?”
Ya faɗa yana murmushin ƙarfin hali.
“Kallo na nawa kuma, ai na gaji da kallon nawa ne shiyasa kaje ka ɗauko wata, kuma ni ka faɗa mata ta daina zuwa min yawo da yara karta lalata su”
“Uhmm, Pyar ki daina sawo zance Kalsoom a gurin da muhallinta ba, ke da ita duka ɗaya kuke a guna, wani abun da kike faɗa akanta ba daɗe yake min ba, and you know what ita bata taɓa wani mugun furuci akan ki ba, balle kuma akan ki ba, sannan tana kula da ƴaƴanki”
Ta taɓe baki ta aje plate ɗin ƙasa.
“Wallahi duk son ƙarya ne, babu kishiyar data zata so ƴaƴan kishiryarta, wannan duk Zagon ƙasa ne”
Ya kai hannu ya riƙo hannunta.
“Naji pyar faɗa min when last nayi miki gwajin jini?”
“I can't remember, ba kai kake min ba?”
Ya ɗanyi shiru.
“Ina ganin anyi shekara biyu yanzu, saboda ba samun zama nake ba, miya faru?”
“Ba komai, zan sake ɗibar wani ne, wacan a mota ya ɓata fitsarin kawai na auna”
“Okay amman yau zaka ɗiba, dan gobe zan je aiki”
“Daga jin sauƙi sai kuma zuwa aiki?”
“Kasan matsalar banki tun yau ma aka so na koma”
Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta.
“Pyar i love you so much ki sa wannan a zuciyarki, mijinki yana son ki sosai”
“Yana son mu dai point of correction”
Ta faɗa tana wani yatsina fuska, shi kuma yayi murmushin da be kai zuci ba, ya tashi tsaye.
“Bari na yi wanka”
“As you wish”
Bayansa ta bi da kallo zuciyarta na mugun tafarfasa, duk yadda take so mijinta idan ta tuna da ba ita kaɗai yake so ba, sai ranta ya ɓace.
Sai da yamma lis sannan Kalsoom ta dawo, dan yau gidan su ta wuni ita da yara, daman duk ranar da ba'a zuwa makarantan ilamiya, ta kan yi amfani da lokacin ta koyar da su wani abu na rayuwa ko kuma addini, sai ya kasance yau kan tana buƙatar zuwa gida gaida du Momy, shiyasa ta kwashi yaran duka suka je gidan.
Tayi mamakin ganin Rashida tayi abinci a yau bayan kuma jiya ta gama koken bata da lafiya, kusan kwana biyu nan ma har cewa take ita ba zata iya cin komai ba.
Ta san yau Doc ba a ɗakinta yake ba, hakan yasa bata damu da dole sai ta ganshi, dan ko da suka dawo, baya gidan Rashida ce kawai, kuma har dare be dawo ba.
Da wuri yaran suka yi bachi saboda gajiya, sai ya rage ita kaɗaice a falon sai tv tada tisa a gaba tana kallo. Saman kanta Rashida ta zo ta tsaya sai wani yauƙi take kamar ance mata Doc ne a gurin zaune.
“Ammyn Rafiq ya idan zaki fita da yara ki riƙa faɗawa Dadyn su, yazo nan yana ta min faɗa wai shi baya son yawo kar a lalata masa yara”
Kalsoom ta ɗago kai ta kalleta tana murmushi
“Ai ni kaina ban fita ba, sai da na nemi izininsa, balle kuma na ƴaƴansa, I'm friendly Rashida feel free to tell me baki son ina fita da yaran ki, is okay sai na tura su duk inda nake so”
Bata tsaya jiran abunda zata sake cewa ba, ta aje remote ɗin dake hannunta, ta tashi ta bar mata falon.
Da wani mugun kallo Rashida ta bita ji take kamar ta tashi taje ta maƙareta, bata san tana kishinta ba ma sai a yanzu data kwana biyu nan a gida, ita dai gani take Kalsoom ta tare mata guri.
‘Ni ban ga abunda matar nan ta fini da shi ba, yaje ya kwaso ta, mace sai baƙin munafurci, Wallahi kin yi kuskuren auren mijina dan mijina mijin Rashida ne ƙadai ba dawata macen ba’
Ƙwafa tayi tana wani huci kamar maciji, ta juya ta koma ɗakinta. Saman gado ta zauna tana sauraren yadda zuciyarta take mata zafi, kishin Mijinta take ji sosai, sai a yanzu take gane abunda wasu ƴan grps nata na whatsapp suke faɗa mata akan kishiya, ya karɓe mata ƴaƴa, yanzu