Showing 126001 words to 129000 words out of 281103 words

Chapter 43 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61228

riƙa yi ita kaɗai tana jiran fitowar Hilal ko kuma wasu daga cikin, amman shiru har kusan mintuna arba'in da takwas.
Sannan wasu Nurser suk fito daga ɗakin, ita kuma ta zura kai sai leƙo take ko zata ga wani halin da Rafiq yake cikin.


Hilal ne ya fito, sai ya janyo ƙofar ya kulle. Fuska babu annuri ya nufi office ɗinsa, ba tare da kula ta ba, balle ma ya bata amsar tambayar da take masa.
Binsa tayi a baya tama tambayarsa amman be kula ta ba har sai da ya shiga office ɗin. Ita kuma duk hakalinta ya tashi a tunaninta ko Rafiq ya rasu ne.


“Me kika ma Rafiq ? Ya aka yi ya ci guba?”


Itace tambayar da Hilal ya fara mata suna shiga office ɗin. Ras ras ras gabanta ya faɗi har jakar dake hannunta ta faɗi idonta na kan Hilal tana kallonsa hawaye sai zuba suke mata ba tare data sani ba.


“Gu....Ba....Bah...”


Ta maimaita cikin rawar muryar tana mamakin furucin daya fito a bakin Hilal. Shi kuma sai kallonta yake fuska babu annuri.


“Eh guba, ya aka yi ya ci guba?”


“Wallahi ban sani ba, amman Rafiq ko abinci safe be ci ba, bachi ma yake, sai kawai na ji ƙyalowarsa ina shiga ɗakin na tararda shi a ƙasa yana fusge-fisge”


“Be ci komai ba guba zata zo ta shiga jikinsa ne? Ni dai a sanina indai ba batir ɗin remote ba mu da wani abu mai guba, da Rafiq zai yi saurin ɗauka ya saka a baki”


“Ban gane ba me kake nufi?”


“Ina baki damar da nake baki ne Kalsoom dan ki samu damar zama uwa a gurin ƴaƴana, kuma dukansu kamar marayu suke a gare ki tun da babu uwarsu a tare da su, babu abinda Ezzah bata faɗa min amman bana kulawa saboda na ɗaukeki a mtsayin uwar data haife su, a tunani ba zaki taɓa musu abinda be kamata ba but wannan yayi yawa, idan ba shi akayi ba taya kamar Rafiq zai ɗauki guba ya ci?”


Ta yi shiru ta kasa magana, sai idonta ne suke magana. Jikinta ya mutu lis har ji take kamar ta zube a gurin. Ba ita ce ta bashi gubar ba, bata da tabbacin gubar ce ma yaci tun da tasan be karya ba, sai dai kuma bata da abinda zata wanke kanta, dan tage gun da kalaman Hilal suka dosa.


“Idan na cutar da Izzah na kashe Rafiq me zan ji?”


“Nima ban sani ba Kalsoom, ban sani ba, wata ƙila ba ki son zama da su ne ko kuma kin gaji da su, amman ni ina son ƴaƴana fiye da yadda nake son rayuwata, kuma zan iya barin komai a kan ƴaƴana, dan sune zasu zauna da ni ko a wane hali nake ciki ina ta avoiding abinda kike ma yaran nan Kalsoom but you cross your limit”


Bata ce masa komai ba, tasa hannun hijabinta ta goge hawayenta, ta duƙa ta ɗauki jakarta ta juya jiki ba gwari ta fice. Binta yayi dan zuciyarsa na raya masa ɗakin da Rafiq yake zata je. Hanyar da zai kai mutum ward ɗin ta nufa ga dukan alamu can ta nufa, tun da ga hanyar fita harabar asibitin nan ta bari. Daga inda yake ya ɗaga muryarsa ta yadda zata iya jiyosa yace


“Kalsoom don't, we don't need you for now”


Tsayawa tayi cak! Kamin ta juyo ta soma takowa ta dawo inda yake. Sai da ta kawo daf da shi sannan ta ɗaga muryar cikin zafin rai ta ce.


“Thank you, thank you so much”


Ta faɗa in low voice sannan ta juya, hawaye na cigaba da zuba a fuskarta ta nufi hanyar data zai fitar da ita harabar asibitin.




NAMRA POV.


Tun faɗan da suka yi da Asim ya fita bata sake saka shi a ido ba sai washe gari, ita kaɗai ta kwana a gidan, tana aikin data saba na kuka, bayan ta faɗa ma Allah buƙatarta.


Sai da safen ta gurka sabon abinci dan kwata-kwata jiya bata yi girki ba, saboda bata cikin ɗaɗin rai. Bayan ta gama, ta gyara gidan, ta ɗora ruwa tayi wanka sannan ta zuba abincin ta zauna ta ci sai kawai ta fashe da kuka, haka ta riƙa rera kuka har tayi ya isheta sannan ta share hawayenta ta ɗauki abinci ta mayar. Dan bata iya ci. Har zata kwanta sai wasu yara suka shigo siyen magi da manja, sai da ta sallame su sannan ta shimfiɗa tabarma waje ta ɗauko matashin kai zata kwanta kenan sai ga Asimya shigo.


Sai da tayi kamar kar ta masa magana ganin be shigo da sallama ba, kuma be kalli inda take ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, ko ba komai mijinta ne dole ta yi haƙuri ta zauna da shi a haka.
Binsa ta yi cikin ɗakin, sai ta same shi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa. Yana ganinta ya wani kawar da fuska, ya ƙara haɗe rai.


“Sannu da zuwa. Jiya baka kwana a gida ba lafiya?”


Ya tsaya daga cire wandon da yake ya kalleta


“Uwata ce da zan sanar miki dole? Ke kike iko da ni ko kuma ni nake iko da ke?”


“Ba ni bace amman ina da haƙƙi, Asim mi yasa kake min haka ne? Ina ta ƙoƙarin taushe zuciyata dan na zauna da kai lafiya amman baka so, look at me, haka nake a da duk na bi na canja saboda kai har kunya nake ji wani ya gani a halin da na ke, kana cin amanata Asim kana zalumtana”


Ya nuna kansa.


“Nine azzalumin?”


Baya baya tayi ta girgiza masa kai, dan ta san dukanta zai yi.


“Yi haƙuri dan Allah”


“Bakin ki ya saba da furta kalami mai daɗi a gare ni ko kuma jikinki ya faɗa miki”


Ɗaga kai tayi ta kalleshi da idonta dake zubar da hawaye, Asim ɗin baya take hangowa Asim ɗin da yake ce mata idan babu ita a duniya ba zai iya rayuwa ba, wanda yake ce mata zai iya sadaukarda komai na sa danta, zai iya bata dik abinda take so, Asim ɗin data watsar da kowa a kansa, wanda ta bijerewa Abbah saboda, wanda Maryam da Anty suka yi ta tunantar da ita akansa amman idonta ya rufe, yau shine yake gargaɗinta. Wani baƙin abu ne mai kamar ƙaho taji ya tsaya mata a zuciya har ƙafafunta suka kasa ɗaukarta ta zube ƙasa tana yaƙi da baƙincikin dake neman numfashimta.


“Kur wallahi kurwata kur sai dai ki ci kan ki”


Ya faɗa yana yatsine ganin kallon da take masa ɗazu. Lumshe ido tayi, ta rarafa ta ƙarasa saman katifar ta kwanta, tana sauraren ciwon zuciyar daya game ilahirin jikinta. Nan take jikinta ya ɗau rawar fever sai kuma zafin jiki. Bedsheet taja ta lulluɓa dan tsanyi take ji ya baibayeta.


Asim kan ko a jikinsa, fita ma yayi daga ɗakin yaje yayi wanka ya dawo ya saka wasu tufafin ya mata waɗanda ya cire a tsakar ɗaki yayi lafiyarsa.


Gurin aikinsa ya koma, daman yayi da abokan aikin nasa zasu je gurin Hajiya Sadiya gyaran gate. Dan haka yana isa suka wuce.
Shine yayi musu jagora a cikin gidan har suka yi aikin suka gama, sannan ya koma ciki ya sanar mata da sun kammala aikin sai ta ɗauko 30k ta bashi akan aikin da be wuce 8k ba. Hannu biyu yasa ya karɓa yana mata godiya.


“Allah ya saka da alheri Hajiya Allah ya ƙara arziki, wallahi halin ki na musaman ne”


Ta yi dariyar jindaɗi.


“Na ce ka iya mota kuwa?”


“Eh na iya mota Hajiya”


Ya amsa da sauri jikinsa har rawa yake.


“Idan ba damuwa, ina son ka riƙa jana a mota dan yanzu bana da direbe, kuma kaga gidan nan yayi min girma da yawa dole akwai buƙatar wanda za a aika a duk lokacin da aka tashi da kuma mai ban ruwan fulawowi da sauran ayuka”


“Wallahi Hajiya duka zan iya, wallahi komai kika sani zan iya”


“To idan ka shirya sai ka min magana, idan ban takurawa aikin ka ba”


“A'a ai aiki ina yi dan na samu na taɓawa, ai ko a yanzu ai na tashi”


“A'a kaje dai kayi shawara dan ni a gidana zaka dawo idan har ka fara aikin”


“Ba matsala Hajiya, zan iya zama a gidan ki”


“Yanzu dai idan ka kimtsa sai mu yi waya”


“Toh Hajiya na gode Allah ya saka miki da aljannah”


Da murmushi ta amsa nasa ba tare data ce amin ba. Sai ya juya ya fito baki har kunne zuciya kuma fal da farinciki.
A bakin ƙofar ya tsaya ya cire 20k ya saka a ɗayan aljihunsa, ya ƙarasa da 10k ya miƙa musu yace su ta bashi. Su kansu sun yaba da 10k ɗin sai kowa ya cire na abin hawan da ya hawo suka komawa Ƙanen Babansa da sauran kuɗin sai ya miƙawa kowa nasa. Duk da 20k dake aljihun Asim be hana shi sa hannu ya karɓi abinda Ƙanen mahaifin na sa ya bashi ba.
Basu tashi aikin ba sai 6 kamar yadda suka ba, sannan suka rufe kayan aikin na su. Sai dai ba su bar gurin ba sai da suka yi sallah magariba.
Sannan yayi sallama da su ya nufo gida, ba kuma gida kai tsaye ba, unguwarsu dai dan be shiga gida ba sai da 10pm. Babu abinda yake ransa sai saƙe-saƙen tunanin yadda zai sarrafa 20k tare da sauran kuɗin da yake ajiya su zame masa millions.


Yana ganin halin da take yasan vata da lafiya, dan tun fitarsa da zazzaɓin ya rufeta bata tashi daga inda take sai idan sallah zatayi, maganin ciwon kai ma sai da wata mai siyen magi ta shigo sannan ta aike ta ta siyo mata ta sha. Amman saboda ƙarfi hali yaƙi yace mata sannu balle tambayarta abinda yake damunta.
Haka ya kwaɓe tufafin jikinsa ya saka ɗan guntun wando data wanke masa jiya ta farar falmara, ya je ya ɗibi abinci ya ci sannan yaje ya rufe gidan, yazo bayanta ya kwanta yana lallubarta. Tabbas bata da lafiya dan yaji jikinta da zafi sosai. Cikin ƙarfin hali ta ɗaga kai ta kalleshi.


“Haba Asim bana jindaɗi”


“Ai na ji Allah ya sauwaƙe ya baki lafiya”


Sai dai hakan be sanya shi daina abinda yake da niyar yi ba....






AMIRA POV.


Tare suka yi breakfast da sukan ƴan matan Ummi, da kuma Ummi ita kanta. Yadda Ummi take ƴaƴanta ya burge Amira ainun hakan yasa ta kwaɗayin shiga cikim familyn dan ita ta zama ɗaya daga ciki. Suna gama cin abincin safe Abdool ya kira Ummi ya gaishe ta, bata iya jin abinda yake cewa duk da taso haka ganin fuskar Ummi da Murmushi alamun wata magana ce yake mata mai daɗi mai kuma muhimmanci.


Tsakaninta da Ummi akwai tazara sosai, dan tana ɓangaren falon ne ita da Haleema. Ummi kuma tana ɗayan ɓangaren ne. sai dai hakan be hanata kashe kunne ta jiyo abinda Ummi take faɗa masa ba.


“Good son haka na ke son ka zama”


“Allah ya kai mu me za a girka maka?”


“To yayi kyau ɗan Mai Martaba kuma Babansa”


Ƙyalƙyalewa Ummi tayi da dariya, ga dukan alama ita ma wani abin yace mata. Haka kawai Amira ta samu kan ta cikin farin ciki, ta san ko ba komai yanzu Abdool.yana can cikin walwalah da farinciki.

Farincikin dake zuciyarta ne yasa ta kai hannu ta riƙo hannun Amal dake shirin aje school bag ɗin a doguwar kujerar da Amira take zaune.


Wani irin ƙyalowa Amal tayi tana yarfarda hannu alamar ƙyaƙyami ta nufi bathroom ɗin falo dan wanke hannunta.


Haleema ta girgiza kai.


“Haka take, ƙyanƙyamin mutane take, Amal ƴar iskar yarinya ce, sai kin yi haƙuri da ita”


Amira tayi murmushi tana nuna abinda a Amal tayi be dame ta ba ko ɗan.


“Ba komai ai wata rana zata daina”


“Yeah amman Amal will never change, bari na koma ciki zan yi bachi”


“Ba ku da class ne?”


“Muna da amman sai da yamma”


“Okay sleep tight”




“I will thanks”


Ta wuce ɗakinta tana rangaji irin na ji da kai ɗin nan. Da Ido Amira ta bita har ta shige sannan ta ƙara mai da hankalinta gurin Ummi dake faɗawa Shukura abinda za a girka musu. Sai da Ummi ta tashi sannan Amira ta bi bayan shukura kitchen ta karɓi girkin ta girka musu white rice and pepper soup. Ummi bata san Amira tayi girkin ba har sai da taga tana jerawa a dinning. Ita kuma tana saukowa daga stairs.


“Shukura...”


Ummi ta ƙwala mata kira. Sai gaba da gudu tazo gaban Ummi ta tsaya.


“Ya kika barta tana jera kaya? Aiki aka ce miki ta zo yi ne?”


“A'a Wullahi Haseya sene yase zse girka ni in tafee”


Ummi tayi murmushin jindaɗi da kuma yabawa da halin Amira.


“To je ki taya ta jera kayan”


Da sauri shukura taje tana taya Amira har suka gama.


YASMIN POV.


Tun da ta dawo tunanin Namra take damunta, tana ganin idan har bata faɗawa Anty halin da Namra take ciki ba bata kyauta ba. Sai dai kuma tana tsoron faɗa musu kar ya zama tayi ma Namra kashin aure ko kuma ita Namra ɗin taga laifinta.
Dan Uzair ya gargaɗe ta akan karta faɗa tun lokacin data faɗa masa a irin halin data samu Namra.
Yau ma nanata mata yake kamar kullum.


“Babu ruwanki da matsalarta idan abin ya dame ta ai ita zata faɗa da kan ta, ba ita ta zaɓe shi ba, kin manta irin cin mutuncin da yarinyar nan tayi min?”


“Komai tayi maka Uzair be kamata mu ƙyaleta a halin da take ciki ba, wallahi baka gan ta abin tausayi, har dukanta yake duk ta canja kala”


“Ina ruwanki da canja kalar ta? Ba auren soyayyah tayi ba? To taje can su ci soyayarsu, wallahi Yasmin idan baki fitar da maganar nan daga ran ki ba, sai mun samu matsala da ke, kiji da cikin da yake jikinki dan Allah”


“Amman Uzair ni lauyace kuma..”


Ya taso ta haɗe bakinsa da nata......








DEDICATED THIS CHAPTER TO ZAGON K'ASA PAID GROUP MEMBERS. I LOVE YOU ALL 💖💖💖
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *53*


KALSOOM POV.


Haka ta fito asibitin hawaye na bin fuskarta amman bata damu ba, kamar ma bata san suna zuba ba. Bata iya gani sosai saboda hawayen daya cika idonta, sai dai hakan be hana ta tsayar da Mai a daidaita ba.
Tana shiga be sauke ta ko ina ba sai unguwar su Salma mai Napep ɗin ya sauketa, ɗari biyar ta miƙa masa bata tsaya karɓar canji ba ta smtura gate ɗin gidan ta shiga hawaye na bin fuskarta.
Ganin motar mijin salma yasa ta tsayawa a bakin ƙofar falon ta share hawayenta ta gyara tsayuwar hijabinta sannan ta tura ƙofar ta shiga tana sallama da muryar kuka.


Babu kowa a falon kasancewar yau monday ce yara basu dawo scul ba kuma ita da mijinta suna ɗaki. Saman kujera Kalsoom ta xauna ta dafe kanta tana sauraren hawayen da suke son zubo mata. Ta ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da biyar a haka sannan Salma ta fito daga ɗakin mijinta tana dariya. Ganin Kalsoom ya razanata, dan da farko ta zata ko ba ita bace sai daga baya ta yarda Kalsoom ɗin ce jin sheshshekar kukanta. Ƙarasawa tayi ta dafata


“Ke miya same ki”


A maimakon ta yi magana sai kawai ta ƙara fashewa da kuka. Hakan yasa hankalin salma ya tashi sosai, har zauna kusa da ita tana girgiza ta


“Dan Allah ki yi magana ko wane ni ya mutu”


Daker ta samu natsuwar sai ta kanta sannan ta kalli salma ta soma mata bayani ba tare da hawayen sun daina mata zuba ba.
Salma ta girgiza da jin labarin har ta rasa yadda zata fassarashi tun da Kalsoom tace be ci guba ba.


“Kalsoom ko dai ya ci baki sani ba?”


“Wallahi be ci ba, bachi ma yake yi”


“Dole ne ya zarge ki Kalsoom ni kaina zan iya aikata kwatankwacin abinda Hilalya aikata, ba ze iya banbance ƙarya da gaskiya ba a yanzu, wata ƙila ya ci gubar ne ba tare da kin sani ba”


“Ba mu da abinda Rafiq zai yi saurin ɗauka ya ci a yanzu, he's just three years old, ni kuma ba zan dauka abu mai cuta na bashi ba, wallahi ban masa komai ba”


“Ba za ki masa ba Kalsoom ba halin ki ba ne, amman taya haka ta faru”


“Ban sani ba Salma wallahi ban sani ba”


Ta faɗa cikin wani irin kuka mai ban tausayi. Salma ta dafa ƙawarta tana hawaye ita tace


“Rashida bata zo gidan ba?”


“Bata zo ba, tun ranar daya sallameta bata sake zuwa gidan ba, kayanta ma sai daga baya ta turo ƙannenta suka ɗibi wasu”


“Allah kaɗai ya san ko mienen wannan abin. Amman abin akwai ban mamaki”


“Amman dai ɗazu na ji ana kirana a muryar Hilal lokacin dana leƙa ban ga kowa ba, har sau uku, a lokacin ne na ji ƙyalowar Rafiq”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah yasa ba lamarin iska ba ne, kar ace ke aka jefa ya faɗa kan yaron ko kuma tayi ma yaron jifa dan ya mutu ace ke ce”


Kalsoom ta kalleta da sauri


“Ɗan ta ne fa”


“Ko ɗan ta ne fa? Ai zata iya aikatawa, idan zuciyar mutum bata da imani komai zai iya aikatawa”


“Na ji ni zata iya yin amman ba zata iya yi ma ɗanta ba, mu riƙa kyuatata zato Salma”


“Hmmm Allah dai ya kyauta, yanzu ina zaki je?”


“Ni ban sani ba, idan naje gida ban san me zan faɗa musu ba, ba lalle bane suma su yarda da ni”


“Kar ma kije gida a yanzu ki koma ɗakin mijinki”


“Amman yace min basa buƙata a yanzu”


“Komai yace miki tun da be ce kije gida ba karki je, idan kin koma gidan ki sa masa ido shi da yaransa babu ruwanki da sha'aninsu, har sai idan ya saki, amman yanzu idan kika koma gida zai ƙara jin haushin ki ne, ki bashi lokaci ya huce ya fahimci komai shi da kansa zai dawo yayi miki magana”


“Idan kuma na koma gidan ya wulaƙanta ni fa?”


“Ki jira har ya wulaƙanta ki ɗin amman yanzu gaskiya ban baki shawarar zuwa gida ba, Kalsoom ki koma ɗakin mijinki”


“Da nasan haka aure yake da ban yi ba, tun da na shiga gidan kullum da matsalar da take buɗe min sabon shafi, idan kuma ka zauna ba kayi auren ba jama'ah su zage ka, idan kuma auren ya mutu ace ka kaso auro ka dawo ma zaman gida, ba su san matsalar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login