Showing 9001 words to 12000 words out of 281103 words

Chapter 4 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61215

shirinsa na zuwa office, be damu da breakfast ba ya fito ya nufi ɗakin da Yasmin take, yana taɓa ƙofar ya ji ta kulle, be tsaya komai ba ya sauko downstairs ya buɗe Fridge ya ɗauko ruwa ya sha, sannan ya fice.


Ba tare da fargabar komai ba ya nufo gidan Abbah, tun da yayi parking ya sauya yanayinsa zuwa na damuwa da ɓacin ciki.
Part ɗin Hajiya Barau ya fara shiga har wani sauke ajiyar zuciya yake. Murya ƙasa-ƙasa yayi sallama, Jikokinta suka amsa masa. Be yarda ya zauna ba dan be ga alamun Hajiya a falon ba.


“Ina Hajiya?”


Sai duk suka haɗa bakin gurin amsa masa


“Tana part ɗin Abbah”


Be tsaya komai ba ya juya ya nufi part ɗin Abbah yana ƙoƙarin ƙirƙiro ƙwalla. Ƙwanƙwasa ƙofar ya fara yi sai da aka amsa masa daga can ciki sannan ya tura ƙofar ya shiga da sallama.


Guri ya samu ya zauna ya natsu, yana sauko da kalaman da suke ƙwaƙwalwarsa zuwa bakinsa.
Ya kusan minti biyar zaune sannan Hajiya Barau ta fito, tayi mamakin ganin Uzair da wannan safiyar, a zatonta ma ko cikin yaran gida ne suka zo karɓa wani abu hannun Abbah, zaunawa tayi tana kallon yadda damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa ƙarara.


“Uzair lafiya kuwa?”


“Hajiya lafiya ba ƙalau ba”


“Toh mi ya faru?”


“Abbah yana nan?”


“Yana nan”


“Dan Allah ki kira min wata magana nake son mu yi”


Ba musu Hajiya ta tashi ta nufi ɗakin Abbah. Bata ɗauki wani dogon lokaci ba sai gata ta fito tare da shi. Guri Abbah ya samu ya zauna yana amsa gaisuwar da Uzair yake masa


“Lafiya ƙalau, lafiya dai kayi mana sammakon nan?”


Jimmm yayi kamin ya ɗago kai ya kalle Abbah ya ce


“Abbah ka gafarce ni, kuma ka fahimci dan Allah”


“Mi ya faru?”


“Abbah...”


Sai kuma yayi shiru, kamar mai jin nauyin furta, har sai da Abbah ya ce


“Am... Uzair ni mahaifinka ne, kuma ina tunanin kasan da hakan, so ka faɗa min damuwarka kawai let your voice out”


“Abbah akan maganar dana aiko Hajiya ne na neman auren Namra, shine nake son a yanje...”


Wani kallo Abbah yayi masa yana karantar yanayinsa.


“Daman kace kana son ta dan ka dawo daga baya kace ka janye?”


“Ko kaɗan babu hakan a raina Abbah, kawai na lura kamar bata so nane kamar akwai wanda take so”


Abbah ya kalli Hajiya.


“Ke kika faɗa masa akwai wanda take so?”


“A'a Wallahi mi zai sa nayi haka?”


Cewar Hajiya tana ƙoƙarin kare kanta. Sai Abbah ya kalli Uzair ya ce


“Waya faɗa maka haka?”


“Abbah jiya ta kira ni da dare, gaban Yasmin tana min kalamai da basu dace ba, babu irin zagin da bata min ba, sannan tayi min barazanar ɓata min suna matuƙar ban janye maganar aurena da ita ba, tace min Asim take so kuma shi zata aura”


Abbah yayi murmushi yana gingina kai.


“Kurciya ho, ai Khadija ba ita zata aurar da kanta ta ba, kar wannan ya ɗaga naka hankali, sai dai ina son ka tabbatar min da zancen ka, shin har yanzu kana nan akan kuɗirinka na aurenta?”


Ɗagowa yayi ya kalli Abbah ido cikin ido.


“Abbah da bana son ta babu abunda zai sa na nemi aurenta, idan har zata amince da aure zan fi kowa farinciki, sai dai idan bata so kar a cilastata gudun abunda zai je ya dawo”


Abbah ya tashi tsaye yana faɗin


“Kar ka damu Uzair, kawai kaje ka fara shawarar date ɗin da kake so a saka musu na aure”


Murmushi Uzair yayi ya sauka ɗaga kan kujera ya ɗuka yana yima Abbah godiya.


“Abbah na gode sosai Allah ya ƙara rufa asiri yaja nisan kwana”


Sannan ya kalli Hajiya yana faɗin


“Hajiya a taya ni godiya”


“Ba komai Uzair, ai kai ɗan mu ne”


Cewar Hajiya. Cikin farinciki yayi ma Abbah sallama. Uzair na ficewa Hajiya ta kalli Abbah tace


“Amman ita kam Namra mi yasa tayi hakaɓ”


Abbah be ce mata komai ba ya kaɓe rigarsa ya nufi part ɗin Anty Amarya a fuce.
Haka ya shiga falo babu ko sallama sai sunan Namra yake kira iya ƙarfinsa. Duk fitowa suka yi har Hindatu dake kitchen da Maryam da Aisha, Anty Amarya ta nufo shi tana tambayar lafiya.


Wata harara ya watsa ma Namra sai da ta haɗe yawu da ƙarfi tayi ƙasa da kanta.


“Ni zaki watsawa ƙasa a ido? Ni zaki tozarta? Ɗan ƴar'uwata zaki kira ki ciwa mutunci dan kawai yace yana son ki?”


Kasa magana tayi sai kawai ta fara kuka. Anty Amarya ta girgiza ta


“Namra kin kira shi ne?”


Kai ta ɗaga. Anty Amarya ta shiga salati. Cikin kuka Namra tace


“Wallahi bana son sa ne, na zan iya auren sa ba, haba Abbah da wane ido zan kalli Anty Yasmin idan na aure shi”


“Da idon da kika kalle ni kika ce min kina son Asim”


Abbah ya faɗa a fusace yana zare mata ido. Anty Amarya tace


“Amman Namra ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, Uzair ɗin ne kike faɗin ba zaki iya aurensa ba? Da me kika fishi toh?”


Karkato fuskarta tayi ta kalli Anty Amarya tana kuka


“Wallahi Uzair ba mutumen kirki bane, yace yana so na ne da wata manufa”


Anty Amarya ta nuna ta da yatsa


“Ke ai mutuniyar kirkice tun da Mahaifinki ya shimfiɗa miki tabarma, kika naɗe kika jefar”


“Wallahi Uzair ɗan homo ne Abbah, maza ya ke nema ƴan'uwansa”


Lokaci ɗaya ta ji ɗaukewar wutar cikin kanta, wanda hakan ya haddasa mata ganin waɗansu ƙananan taurari sakamakon wani irin mari da Abbah yayi mata, bata ankaro ba ya ƙara mata wani, be tsaya komai ba ya sake marinta, kamin kace kwabo sai ga jini ya gangaro ta hancinta kamar mai haɓo.






____________________


#Blog
#Comment
#Share
#Three-family
#Three-Team


http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa05.html




🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated




*PAGE - 5*


NAMRA POV.


Cikin takaici da jin haushi, Abbah ya nuna ta da tsaya.


“Ke baki isa kisa nayi magana ta tashi ba, a duk cikin ƴaƴana babu tsagerarra irin ki, bari kuma kiji na faɗa miki weather you like or not sai kin auri Uzair, idan kin haihu ranar da aka ɗaura miki aure da Uzair ki kashe kan ki”


A fusace ya juya ya fice. Anty Amarya ban da hawaye babu abunda take, sam bata ga laifin Abbah ba, dan tana ganin duk abunda yayi mata ita taja, ita ma kanta kwatankwacin abunda zata iya yi mata kenan, dan bata ga dalilin aibanta Uzair ba dan kawai bata son sa, kasa cewa komai ta yi ta juya cike da baƙinciki ta nufi ɗakinta.
Namra kan na risine gurin tana kuka, Maryam da Aisha na bata haƙuri.


Babu wanda zai fahimce ta saboda babu wanda yaga abunda ta gani, kuma bata da wata sheda da zata nuna.
Hajiya Barau ce ta ɗauki zancen tana yayatawa, wai Namra ta yi ma Uzair ƙazafi dan kawai bata son ta aure shi. Cikin sati maganar ta zagaye familyn su. Wasu kan sun yarda duba da irin kuɗin da suka taso masa lokaci ɗaya, sai dai kyakkyawan halinsa da mutane ke gani ya shafe wacan baƙin fentin da wasu suke ganin Namra ta shafa masa.
Hakan da Namra tayi ba ƙaramin sosa ran Uzair yayi ba, ko ba komai ta ɓata masa suna ta wani ɓangare, ga kuma rashin jutuwa daya samu da Matarsa Yasmin.
A ƴan kwana kin nan sai shiga cikin dangi yayi masa wuya, gani yake kamar sun yarda da abunda Namra ta faɗa, a waya wasu ke kiransa suna nuna masa abunda Namra ta yi bata kyauta ba, wasu har da yi mata Allah ya isa. Amman ita kan Yasmin ko a jikinta, sai ma sha'aninta take kamar abun be dame ta ba.


Babu irin faɗan da mahaifiyarsa bata masa akan ya janye maganar auren nan, amman ya ƙi saboda Abbah yaƙi bashi damar hakan.


“Uzairu ka janye zancen auren nan, ka faɗa maka, duk fa mutumin da yayi maka haka toh ko kashe ka zai iya yi, wannan ƙazafin data maka zai iya shafar har aikinka, ni ban taɓa ganin maƙiyiyi kamar Namra ba, ace ɗan'uwanka,
Aiko kama da gaske ne ka rufa masa asiri”


“Babu komai Umma Allah zai saka min, sai ta ga abunta inshallah”


“Allah dai ya isar maka, amman abun nan ya ɓata min rai matuƙa Wallahi, kai ma dai da hange-hange kake mi Namra take da shi daya fi na Yasmin har kake son aurenta”


“Wallahi Umma tun lokacin dana auri Yasmin ina jin son Namra, kuma wannan walimar da akayi na haddatan ƙur'ane kin san har da ita ciki, shiyasa naji na kwaɗaitu da zama mijinta dan na samu mai bawa ƴaƴana tarbiya, tun da ni da Yasmin ba wani dogon ilmin Islama ne da mu ba, sam ban tsammaci abun zai zama haka ba”


“Toh ai ko ilminta ya zama na banza tun da har ta iya yi ma ɗan'uwanta wannan ƙazafin”


Haka dai suka yi ta hirar Namra Hajiya Binta na tsine mata har aka kira Azahar.
A masallacin gidan yayi sallah, sannan ya koma ciki yayi ma mahaifiyarsa sallama ya fice. Babu abunda yake ji a ransa sai tsanar Namra, ji yake ko kashe ta yayi ba zai huce abunda tayi masa ba.


A dai-dai gate ɗin gidan su Amira yayi parking, sai ya fita ya taka da ƙafa, ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin. Mai gadi ne ya leƙo yana tambayar.


“Wanene?”


“Dan Allah Amira na ciki?”


“Eh tana ciki”


“Dan Allah yi min sallama da ita”


“Toh wa zan ce mata?”


“Ce mata manager ne”


Daga haka ya juyo ya dawo gurin motarsa, ya ciro wayarsa yana ƴan danne-danne. Ba a ɗauki dogon lokaci ba sai ga Mai gadin ya dawo yana faɗin


“Wai tace tana zuwa”


Tsayuwarsa ya gyara, yana kallon ƙofar gidan har ta fito.
Cikin rangwaɗa da isa take tafiya har ta ƙaraso kusa da shi da sallama.


“Maraba da sarauniyar kyau, gimbiyar mata, kuma adon mata, nasan ba ki san ni ba amman ni na san ki”


“Na sanka mana, ba kai bane Cousin ɗin Namra”


“I'm glad you remember”


“So what brought you here?”


“Ke ai ba sai kin tambaya ba, mace kyakkyawa irin ki mai hankalin da tarbiya, ai dole ne ta riƙa samun masu ziyartar ta a duk lokaci, son ki ne ya kawo ni, zuciyata ta kasa haƙura da ke na kasa haɗeye yawuna a kan ki, shiyasa kika gan ni a ƙofar gidan ku”


Cikin salon jan hankali yake maganar yana murmushi. Ita kuma sai wani yauƙi take abun ka da mata.


“Na ji matashin darasin ne kawai amman ban fahimcin karatun da yake cikinsa ba”


“Zan miki bita, na kuma fassara miki inda baki gane ba idan har mafaraucin zai samun ganin Gimbiya anjima?”


Shiru tayi tana fari da ido.


“Sai ka shigo, kuma idan ka zo karka tsaya a waje ka shiga harabar gidan, kar ka wuce ƙarfe tara”


“Consider it done my lady”


Buɗe motarsa yayi ya ɗauko bandur ɗin 1k ya miƙa mata.


“Ki shiga da wannan, zan yi farinciki”


A yadda ya karanceta be yi zaton zata karɓa ba, a take murmushi ya bayyana a fuskarta, tasa hannun biyu ta karɓa tana masa godiya


“Na gode sosai”


“Never mention it again, my regards to mom please”


Fari ta ƙara masa da ido


“Sure”


Ta juya ta shige. Wani shu'umin murmushi yayi ya buɗe motarsa ya shiga.






KALSOOM POV.


SIX MONTHS LATER.... Tun da ta dawo daga Seminar take bachin gajiya, ta taje aiki ta dawo sai bachi. Ga kuma ɓacin ran dake tare da ita, da tunani, dan ko ranar da zata tafi seminar ɗin sai da Dad yayi mata jan kunne akan ta kame kanta, ya sake maimata mata irin zagin da ake masa na yaƙi aurar da ita ya barta tana aiki sai yawa take gare gare, Babu kuma yadda zai hana ƴarsa aiki, dan da shi take yima kanta wasu laluraron ba dan kuma ya kasa ɗaukar nauyinta ba, sai dan rashin auren da bata tayi ba, idan har yace zai hanata aiki sai yaga kamar be mata adalci ba, kuma zai tauye mata haƙƙi damuwa zata mata yawa.
Sai dai burin iyaye ne suga sun aurar da ƴarsu sai idan hakan be samu ba, yadda zamani ya lalace komai girman ɗan ka dole ne kasa mishi ido gudun kar ɓata gari su lalata maka shi, musamman ƴa mace.
Ita kanta wani lokancin ba son zuwa seminer take ba, sai dai babu yadda ta iya tun da haka kamfamin MTN ya tsarawa ma'aikatansa.
A ɗayan ɓangare kuma tana ganin kamar iyayenta ba su yarda da ita bane, shiyasa suke takura mata da da yawan tambihi a duk lokacin da zata nisanta da su.
Tana ji a ranta har yanzu iyayenta ba su gama karantar ta bane, dan ta ɗaukarwa kanta alƙwarin duk irin sha'awar dake damunta da son auren da take ba zata taɓa aikata zina ba.


Da yamma ta tashi bachi, bayan ta ci abinci ta koma ɗakinta ta buɗe system tana duba wasu abubuwan. A ɗakin Momy ta same ta tana labarta mata hukuncin da mahaifinta ya yankena haɗata aure da Cousin ɗin ta Abubakar.


Gabanta ya faɗi, duk yadda take son aure bata jin zata iya auren Abubakar, mutumen da duk a familynsu an buga masa tambarin neman matan banza, neman mata kawai yasa ma gaba shiyasa auren ma kwata-kwata baya gabansa gashi yanzu har ya girmi tazurai, ba dan kuma ya rasa matar aure ba.
A cikin yanayin damuwa ta kalli Momy tace


“Amman Momy mi yasa ba'a nemi shawara na ba, kamin ku yanke wannan hukuncin?”




“Yayi hakan ne dan yasan ba zaki bashi kunya ba, kuma ba mahaifinki bane yayi masa magana, mahaifinsa na yayi ma Abbanki magana da amincewar Abubakar ɗin”


Girgiza kai tayi


“Gaskiya ni ba zan iya aurensa ba”


Wannan maganar da Kalsoom tayi ta fusata Momy har tasa ta canja fuska.


“Haba Kalsoom ana son a samu kiyi aure sai kuma kice ba zaki iya aurensa ba? Toh idan ba shi ba kina da wani wanda zaki iya fitarwa a yanzu ne? Ba zaki bar ruwan idon nan ba ko?”


Hannu biyu tasa ta dafe kanta. Sai yaushe Momy zata fahimcin matsalarta ne? Kullum cewa take tana ruwan ido, taƙi ta tsayar da miji, alhalin ba ruwan ido bane, duk mazajen babu na aure ko wanne da tasa matsalar.
Dagowa tayi ta kalli Momy tace


“Yanzu dan kawai ina son aure sai ace duk wanda ya zo min sai na aura? Abunda nake it not calling ruwan ido it calling carefully planning for the future”


Momy ta taɓe baki


“Yanzu dai idan kunya zaki bawa mahaifinki sai kiyi, naji ma yana faɗar baya son aja abun da nisa ina jin ba zaki wuce wata biyu a gida ba idan har kin yarda, kuma ni ban san Abubakar da wani mugun hali ba, yana da rufi asiri yana da kyau kuma baya shaye-shaye, neman mata ne kawai shi ma kuma bamu tabbatar ba tun da bamu taɓa kama shi yana yi ba,
Kuma yanzu ai da wahala ace maza basu san mace ba, ko kuma basu taɓa aikata zina ba, wata ƙila ma idan ya aure ki zai daina”


Idon Kalsoom ya cika da ƙwallah, ganin yadda Momy take gyara Abubakar dan kawai ta aure shi.


“Idan kuma be daina ba, ƴarki zata cutu, Momy kisa wannan a zuciyarki”


Momy ta dafata


“Kiyi auren dan ibada Kalsoom, kuma ki auri Abubakar da zuciya ɗaya”


Tashi Momy tayi ta fice, ta bar Kalsoom cikin tunani da neman zaɓin Allah.




____________________________


Masu karantawa a blogger ina ganin ku fa, amman baku comments, sometimes zan samu mutum 200+ sun leƙa website ɗin amman ba ku comments. Yadda kuka ga Wattpad haka Blogger yake zai nuna masu karantawa, amman babu Comments, ina fatar zaku gyara.
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa06.html




🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*


Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


Ƴan Taskar Khadeeja Candy wannan shafi na ku ne. Ina jindaɗin Comments ɗin ku keep it up.🌺


*PAGE - 6*


NAMRA POV.


Har yanzu Asim baya ɗaukar wayarta, ta masa text ya fi a ƙirga, amman ba reply, kuma tun ranar da suka samu matsala bata sake saka shi a idonta ba, scul ma ya daina zuwa.
Hakan yasa ta yanke shawarar jan ƙawarta Amira su je gidan iyayensa, dan dubasa.
Haka kuwa akayi bayan an gama lacca, sun fito ita da classmates ɗin su, sai ta riƙa hannun Amira ta nufi hanyar library da ita.
Amira biye kawai take da ita, amman hankalinta na can wani gurin, sai tunani take.
Saman balcony suka zauna, kamin Namra ta yi magana sai Amira ta fara yi mata tambayar da ke cikin ranta.


“Namra kin ce da Uzair aka sa muku rana ko? Kuma kin ce baki son sa right?”


“Uhm”


“Ba taimakon ki zai yi ba?”


Namra ta yi mata kallon rashin fahimta


“Taimako kamar ya?”


“Haka dai na ji ana faɗa wai taimakon ki zai yi, dan Abbah ya bari ki auri wanda kike so”


“Kowa ya faɗa miki haka ƙarya ne, idan har zan nemi taimakon wani toh ke ce zaki riga kowa sani”


“Amman miyasa baki son sa?”


Shiru tayi, tana tunanin faɗa mata gaskiyar lamarin, sai dai tana jin har yanzu Amira bata kai matsayi da zata san sirrin gidan su ba, wannan matsalar ta cikin gida ce kawai, kuma ba komai bane zaka faɗawa ƙawa, dan ba kowa bane zai iya riƙe maka sirrinka, wani kuma zai yi kallon ka da abun ne, duk kuwa da amincin da ke tsakaninku.


“Amira so na ke ki raka ni gidan su Asim”


Ta ɗauko mata zancen ne, dan samun damar kawarda wancan tambayar da tayi mata.
Ajiyar zuciya Amira ta sauke, har yanzu kan ta kulle yake ta rasa dalilin da yasa Uzair ya yi mata ƙaryar yana son ta, kuma ya ƙulla alƙawarin zai aureta, lalai akwai wani abu a ƙasa.


“Zan raka ki mana, kwana biyu ya daina zuwa makaranta,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login