Showing 51001 words to 54000 words out of 281103 words
Chapter 18 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
samo kuɗin da za'ayi masa aiki, har kuma ta gama bata samarwa kanta wata mafita ta bayan ta siyar da wayarta.
Mayafinta ta ɗauka ya saka ta fita ta nufi gidansu Mardiya. Da sallamarta ta shiga, mataɓ gidan suka amsa mata, suna mata ya mai jiki. Sai da ta gama gaisawa da su sannan ta wuce ɓangaren su Mardiya, kasancewar gudan irin tsohon gidan nan ne da ake na dangi mai ɗakuna da yawa.
Bata tararda Mamarta ba, sai Mardiya dake sallah. Zaunawa tayi saman simintin ɗakin tana jira ta gama. Bayan ta sallame ta juyo ta kalli Namra.
“Namra har kin yi wanka?”
“Tun ɗazu, dan Allah so nake ki kai ma Mama abinci da wasu abubuwan da za su buƙata, kuma dan Allah idan kin san inda ake fansar da waya ki kai ni ina son siyar da wayar ne”
“Kai yanzu kam sun tashi kin ga har tara ta gota fa, sai dai gobe, sai na rakaki ki kai”
“Abincin fa?”
“Muje na kai musu”
Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. Tare suka fito gidan. Tun da suka fito Mardiya take abu kamar mai jin kunya, har suka shiga cikin gidan. Namra ta bata kayan ta ɗauko sauran canjin dake jakarta ta miƙa mata wai tayi na okada da su.
Bayan ta wuce, Namra ta sake buɗe jakarta ta ɗauko waya, sai taga wayam, babu waya babu alamunta, a nan fa hankalinta ya tashi, sai ta zazzage jakar gaba ɗaya, bata ga wayar ba.
Jikinta be bata ta jefar da wayar a cikin gidan ba, amman haka tabi ta yamutse gidan tana neman wayar.
Har Mardiya ta dawo bata ganta ba, idonta duk ya rine tana jin kamar tayi kuka ba hawaye.
Ita kanta ta lura da yadda Namra ta ƙara firgicewa.
“Na kai musu, tace wai na faɗa miki likita ya sake zuwa”
Hannu Namra ta ɗora saman kai ta fashe da kuka
“Kai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kin ga wayar ma da nake son saidawa ban ganta ba, ko kin ga inda na jefar”
Wani irin dakan ƙirji Mardiya tayi
“Baki gani ba? Wallahi ban ga inda kika jefar ba, kuma tun da na karɓi jakarki ban ma buɗeta ba, yau ko na shiga uku, da wayar mutane”
A take tasa kuka. Sai Namra ta share hawayenta tana faɗin
“Ƙila ko na jefar a motar matar nan ne ban sani ba”
“Lallai ba zai wuce can ba, amman ni ban ɗaukar miki waya ba Wallahi, sai idan kuma a asibiti kika jefar”
“Bana zargin ki Mardiya, da zan samu rancen kuɗi da sai naje gida ta yanzu, dan hankalina ba a kwance yake ba”
“Amman yanzu dare ne, da kin haƙura har da safe, kin ga ma baki san gidanta ba”
“Ai ta bani addireshinta, dan Allah ki ara min ko ɗari biyu ne naje na duba, kin ga halin da mijina yake ciki”
“Ina da wasu ɗari takwas da aka bani ajiya sai idan sun zan aro miki”
“Aro min dan Allah”
“Bari na ɗauko miki ɗari biyar”
Tashi tayi ta fita, bata daɗe ba ta dawo, ta kawo mata kuɗin. Sai Namra ta ɗauki Hijabita ta saka.
“Dan Allah Mardiya ki zauna nan har na dawo, ina son ki taya ni kwana”
“Tau ba komai Allah ya tsare”
Ta ɗauki katin ta fice, hankalita a tashe. Napep ta tara ta shiga. Su kusan tafiyar rabin awa sannan suka isa unguwar GRA ring.
Gidajen gurin duk masu kyau ne da ɗaukar hankali, abun ka da wanda hankali ba kwance ba haka suka kai ƙarshen unguwar bata gane gidan ba, dan numbobin gidajen sun ɓace mata. Har sai da suka yi tambaya, saɓnan aka nuna musu gidan Hajiya Saratu.
Sai ta da buga ƙofaɗ gate ɗin mai gadin ya buɗe mata, ta tambaya yace mata gidan nan sannan ta sallami mai napep ɗin, shi ma ɗaker ya karɓi ɗari biyu da hansin.
A bakin gate ɗin ta tsaya sai da mai gadin yaje ya faɗawa Hajiyar sannan yayi mata iso.
Tana saka ƙafarta cikin falon ƙashin turare ya fara mata marhabun.
Haka tayi ta doka sallama amman ba a amsa mata ba, sai ta samu guri ta zauna, zuciyarta sam bata natsu da gidan ba.
ta ɗauki tsowon lokaci sannan matar ta fito cikin wata rigar yadi mai shara-shara, kusan ana ganin underwears ɗinta.
Tun da Namra ta kalleta sau ɗaya ta sadda kai bata sake kallonta ba, duk gaisuwar da suka yi idon Namra na ƙasa.
Cikin wani irin karairaiya taje ta ɗauko ma Namra lemu da snack ta kawo mata. Namra bata ci dan basu ne a gabanta ba, kuma ta kasa ɗaga ido ta kalli Matar. Ganin hakan yasa matar ya taso ta dawo kusa da Namra ta zauna, ta kai hannunta dafa Namra tana shafa bayanta duk da kasancewar Namra na cikin Hijabi ne.
“Ki kwantar da hankalin ki miji zai samu sauƙi nayi miki alƙawarin duk abunda tmya dace ayi masa za a masa, dan ya samu lafiya, yanzu me likitocin suka ce ne? Dan daga ganin ki akwai wani a ƙasa”
“Na gode sosai, yanzu sun ce sai an biya kuɗin aiki dana magani, kuma suna buƙatar jini gora uku, shine naso na siyar da wayana na duba ban gani ba, nace ko na manta a motar ki ne”
Wani ƙasaitattacen murmushi tayi, ta girgiza mata kai.
“Baki jefar da komai a mota na ba, amman bari na baki keys ki duba, saboda cire kwankwanto”
Bata jira komai ba, ta tashi ta shiga ɗaki ta ɗauko mata keys ɗin ta miƙa mata.
“Muje ki duba, amman na faɗa miki ba dole sai kin siyar da wayarki zaki iya taimakon mijinki ba”
Namra ta karɓi keys ɗin tana faɗin
“Ba ni da wata mafitar ne sai wannan”
“Kina da mafitoci ba ma ɗaya ba”
Ta faɗa yayinda suke fitowa daga cikin falon suka nufi gurin motocin da suke gidan. Ita da kanta ta nuna mata motar da suka shigo, cikin rawar jiki Namra ta nufi motar ta buɗe tana dubawa. Zuwa Hajiyar tayi bayan Namra ta tsaya tana shafa mata duwawu, tare da faɗin
“Duba da kyau ki gani, amman ni bana tunanin kin bar wani abu a gurin”
Da sauri Namra ta juyo ta fito da jikinta cikin motar tana yima matar wani mugun kallo.
“Miye haka? Ya zaki riƙa taɓa min jiki kamar wata karuwa, ko an faɗa miki ni irin waɗannan mata nan”
Murmushi Hajiyar tayi kamar bata ji zafin kalaman Namra ba.
“Ɓana nufi komai da ke sai Alheri, kina da kyau da duk mace data kalle ki sai tayi sha'awarki, balle kuma namiji, dan haka kiyi amfani da damarki ki taimaki kan ki”
“Ke kuma haka kike? Tirrr da ke daman taimakon da kika min ba dan Allah kika min ba? Saboda wani mugu nufi naki? Toh Allah ya fiki, jikina bana mata irin ki bane, ba kuma na wasu mazan bane, na mijina ne shi kaɗai halalina”
“Hmmm kije kiyi tunani Namra, matuƙar kika amince da buƙata zan miki duk abunda kike so a duniyar nan, idan ma waje ya dace a fitar da mijinki zan sa a fitar da shi”
Namra ta girgiza mata kai.
“Dukiyarki bata burge ni, arzikin gidan mu ya ninka naki sau dubu, ƴan'uwana ne suka juya min baya shiyasa kika ganin a halin da kika tsince ni”
Hawayen ya gangaro daga idon Namra. Hajiyar ta matsa kusa da Namra tana ƙoƙarin dafata.
“Kaicon ki, haƙiƙa ina tausayin rayuwarki, wallahi wata mace bata taɓa burge ni ba kamar ki”
“Ba nice a abun tausayi ba, kece a abar tausayi a ranar da zaki yi nadamar da bata da amfani”
Namra ta buge mata hannu ta juya ta fice daga gidan tana hawaye. Ta daɗe tana tafiya a estates ɗin kamin ta samu Napep. Har ta iso gida hawaye take zuciyarta a cakushe.
Ɗari biyun da hasin da suka yi saura ta miƙawa mai Napep ɗin, ya so yayi magana, sai dai hawayen daya gani a idonta yasa shi tausayinta, ya kaɗa napep ɗinsa yayi gaba.
Mardiya na gani hawaye a fuskar Namra, hankalinta ya tashi, da sauri ta riƙa ta suka zauna saman kujera.
“Lafiya ? Ba acan kika jefar da wayar ba?”
Sai kawai Namra ta fashe da kuka tana riƙe Mardiya kamar ta shige cikin jikinta.
*** *** ***
Ganin dare ya lula Namra bata dawo ba, yasa Mama har zuƙa sosai, a ganinta abun kamar be damu Namra ba. Tun da tana da hanyoyin da zata iya biyan wannan kuɗin. Ita ganin take kamar ma da haɗin kai aka yi masa wani abu yayi haɗari motar, so that idan ya mutu sai ta auri wanda take so.
“Mama ko kuɗin adashe zamu karɓo a biya ina ganin fa kamar bata da kuɗin nan”
Cewar Hajaru, Mama ta kai mata wani mugun zungura
“Duk naji bakin ki yayi maganar adashen nan sai na kusa halaka ki, taya zata ba mu kuɗi bayan mun riga mun zuba, kina ganin kullum zogaron kuɗin zubi take mana. Ai ita ta fimu sanin hanyoyin samo kuɗi, ta nemo ta biya a itace silar komai tun da tasan be wani iya mota ba, tasa ya jawo ta tun daga sokoto har katsina dan kawai su ga bayan shi.
Ni Wallahi ɗana ko mutuwa yayi sai nayi ƙararsu”
Hajaru dai tayi shiru bata sake cewa komai ba, Mama kam sai cika take tana barsewa, ita mai ɗa.
KALSOOM POV.
Babu abunda ta ɓoye Salma na zamantakewar auren da suke yanzu da Hilal.
Ita tafi raja'a akan Hilal baya son haihuwa, daman Asmee takan nuna mata alamun hakan tun lokacin data shigo cikin gidan. Sai dai tunaninta ya sha banban lokacin da Salma take nusar da ita akan wasu abubuwan data manta.
“Haba Kalsoom ke kan ki yanzu ba zaki iya gane wani abu a tare da shi ba? Taya za ace dan kin yi ciki sai ya sauya miki? Baya son haihuwa zai bar matarsa ta haifi yara uku kuma tana aiki?Sherin kishiya yana da yawa Kalsoom musamman na zamanin nan”
“Naga sauyi a ɓangarenta dan duk wani kishi data ɗauka yanzu ta aje shi, bana da matsala da ita”
“Wannan ma kaɗai ya isa ya nuna miki akwai abun da tayi, ki bita a sannu kuma ki yi taka tsantsan da ita. Sannan a duk lokacin da mijinki yake fushi yana hawa sama karki tanka shi, kisa mishi ido, saboda maganar zai iya zama miki illah.
Cigaba da addu'ah, idan zaki iya kiyi alwala a zama ɗaya ki karanta Yasin ƙafa goma sha biyar, ki roƙi Allah, ko kuma ki karanta ayatul kursiyu ɗari uku da sha uku Wallahi duk kika roƙi Allah sai ya amsa miki, ki daure kiyi na tsawon sati acikin kwana uku Allah zai biya miki buƙarta ki.
Sannan ki samu ruwa mai kyau ki watsa a saman rufin ɗaki, idan ya gangaro ki tara abu ya zuba a ciki, ki taceshi ki sha ki wanke kanki, Wallahi indan Asirine akayi miki sai ya karya kuma sai Allah ya nuna miki wanda yayi miki haka a bachin ki, maƙukar kika yi har sau uku”
“Na gode sosai Salma, Allah ya bar zumunci”
“Amin Allah ya baku zama lafiya”
Daga haka ta aje wayar, ta jingina da gadonta tana sauke ajiyar zuciya.
“Kai kayi auren baka huta ba, idan kuma baka yi baka huta ba, da wannen zaka ji”
Yadda ya turo ƙofar ɗakin ya shigo ne yasa ta zabura ta tashi zaune, tana kallon yanayinsa.
“Ina kuɗina dake cikin closet?”
Wani kallon mamaki tayi masa.
“Kuɗi kuma? Ni ban ɗauki kuɗin ka Doc, ban ma san ka aje kuɗi a gurin ba”
“Babu wanda zai ɗaukar min kuɗi bayan ke, dan ke kaɗai kike goge gurin”
“Amman ai ba ni kaɗai bace a gidan nan”
“Mata ta bata taɓa min sata ba, ƴara na kuma basu ɗaukar min kuɗi, sannan basa da wayon da zasu iya ɗaukar dubu ɗari uku da hansi”
Hawaye ya silala a idonta. Ta nuna kanta
“Ni kake zargi kenan, ni na ɗaukar maka kuɗin ko? Haba Doc taya zan ɗaukar maka kuɗi abunda ban taɓa yi ba”
Ƙara haɗe fuska yayi kamar an aiko masa da mutuwa, ya ɗaki mirror ta yana ƙara jadadda mata.
“Bari kiji na faɗa miki, ko ki nemo dubu ɗari uku da hansi ko kuma a bakin auren ki!”
Bata san lokacin data kwantar da kanta gefe tana masa kallon da ita kanta bata san tana masa ba, ta kasa tantancewa shi ne ko ba shine ba.? Fuuuu ya bar ɗakin kamar walƙiya yana wani irin huci.
________________________________
I need more and more comments. 🙌
Bari na ga suwa suke son nayi long chapter gobe 🤔
BEST REGARDS 💖
Khadeeja Candy 😘🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*
Website
www.khadeejacandy.com.ng
Masu Tambayar Labarin Uzair da Amira zai zo muku a gaba, tare da nasu Zagon ƙasa. Just keep moving komai zai zo daki-daki.
*PAGE - 25*
NOT EDITED ⚠️
KALSOOM POV.
Ta daɗe a gurin tsaye duniyarta na juya mata, kunnuwanta sun kas ɗaukar abunda suka ji Hilal ya faɗa mata, idonuwanta kuma sun kasa yarda da ba mafarki take ba.
Makomar aurenta take tunani, yadda zamanta a gidan zai kasance yake mata yawo a ƙwaƙwalwa, taya zata biya abunda bata ɗauka ba? Akan me zai nuna dubu ɗari uku sun fi aurenta daraja a gareshi? Dan me idonsa zai rufe har yayi mata wannan furucin?
Ta kasa zaɓa tsakanin igiyar aurenta da kuɗin da idan har ta bashi zai iya tabbatar masa da lallai ita ɗin ce ta ɗauka.
Hawayen dake idonta ta share, ta tashi ta ɗauko akwati ta buɗe wardrobe ta ɗauko tufafinta ta saka aciki, ta ɗauki jakarta ta saka wayarta da duk wasu abubuwa da tasan zatayi saurin buƙata, ta zari mayafin ta yafa ta jayo akwati ta fito. A lokacin Hilal yana zaune falon ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya.
“Ina zaki je?”
“Gidan mu, ba kace na kawo kuɗi ba ko kuma a bakin aure na? Ni ba zan iya biyan abunda nasan ban ɗauka ba, amman Allah yana nan baya bachi baya angaje zai bayyana gaskiya, amman ni ba ɓarauniya bace”
Tasowa yayi ya ƙaraso kusa da ita.
“Look Kalsoom ...”
Sai kuma yayi shiru ya kasa magana, ya kuma kasa kallonta. Ganin hakan yasa t share hawayenta ta cigaba da jan akwatin. Sai ya riƙe ya kai hannu ya riƙota, kuma ya kasa mata magana, shi dai ji yake babu daɗi ya rasa abunda ke damunsa, sai yanzu yake jin nadamar furucin da yayi mata, mamakin yake yadda ya alaƙanta sakinta da kuɗin da basu taka kara sun karya ba a gurinsa, bayan kuma baya da tabbacin ita ɗin ce ta ɗauka.
“Ban aureka dan dukiyarka ba, balle har ya kai ni ga yi maka sata, nayi tunanin kasan darajar aure, ashe na yi kuskure, daman an faɗa min baka son haihuwa kana son kayi amfani da wannan damar ne ka wulaƙanta ni ko? Zan bar maka gidan ka sai ka zauna da wanɗanda ba ɓarayi ba!”
Kalamanta sun harzuƙa shi matuƙa, sai kawai y saki hannun nata.
“Kije duk inda zaki je, amman bari na faɗa miki duk wani abu ya samu cikin nan na ki, Wallahi sai kin yabawa aya zaƙinta”
Cikin wani irin ɓacin rai ya nufi ɗakinsa, ita kuma ta bishi da wani kallo na takaici na baƙinciki, kamin ta saka kai ta fice.
Ɗakinsa ya koma ya zauna, rasa yayi abund ke masa daɗi, dawowar da yayi ɗaukar kuɗi sai ya kasa komawa. Ba shi ya fito ɗakin ba sai da lokacin ɗauko yaransa daga makaranta yayi har ya gota, sannan ya fito daga ɗakin.
Kukan Rafiq yaji da yaji yasa shi ya nufi ɗakin Kalsoom dan shi sam ya manta da Fariq na bachi.
Ɗaukarsa yayi ya ɗora a kafaɗa yana jijjigashi, ya fito ya buɗe motarsa ya saka shi gidan gaban, sannan ya zagaya ya shiga ya tashi motar.
Ko da ya isa ɗaukarsu duk sun ƙosa, ga Rafiq sai kuka yake masa, har suka dawo gida.
Da gudu suka shiga falon, sai suka tsaya a gurin da Kalsoom ta saba nuna musu su aje safunan su suka aje sannan suka nufi ɗakinta suna rigangan.
Ganin bata ɗakin yasa suka fito suka nufo kitchen da gudu, nan ma basu ganta ba, sai suka nufo dinning gurin da Hilal yake tsaye yana haɗawa Rafiq madara.
“Daddy ina Anty?”
Yi yayi kamar be ji su ba, har sai da suka ƙara tambaya sannan ya kalli Ezzah kasancewar ita ce babba.
“Anty ku taje unguwa”
“Yaushe zata dawo?”
Ulfah ta tambaya. Sai da ya sawa Rafiq madara a baki sannan ya amsa musu.
“Ni ma bata faɗa min ba”
“Daddy ta dafa mana abinci?”
“A'a bari Rafiq ya gama zan muku takeaway yanzu”
“Anty tace mu daina cin takeaway sai abincin gida”
Kallonta Ezzah yayi da kyau.
“Amman yau Anty ki bata nan na ce zaku ci takeaway”
“Daddy ka dafa mana Indomie”
Ulfah dake ƙoƙarin cire uniform ɗinta ta turo baki tace
“Ba za mu ci indomie ba ai da safe Indomie muka ci, Daddy ayi mana takeaway”
Ezzah ta nufo a fusace tana faɗin
“Allah kuwa duk Anty ta dawo sai na faɗ mata nace kin ci takeaway”
Ita kuma sai ta taɓa hannayenta alamar ma shiryawa masifar.
“Nima na faɗa mata na ce kin yi faɗa da wata a makaranta, ai ta ce ki daina faɗa a makaranta”
Hannu Ezzah ta kai zata daketa sai Hilal ya katsa mata tsawa.
“Ezzah karki dake ta, zan dafa miki indomie, ke kuma zan miki takeaway is that okay?”
Duk suka haɗa baki gurin amsa masa.
“Yes Daddy”
“Come and take your brother”
Ezzah ce taje ta karɓe shi, sannan ya nufi ɗakinsa kansa na masa wani mugun zafi.
NAMRA POV.
Tare suk kwana a gidan ita da Mardiya. Sai dai ita batayi bachi ba, har safe Asim take tunani da halin da yake ciki.
Tasan ita kaɗaice a duniyar nan zata iya taimakonsa, idan kuma har bata masa ba waye zai masa, tun da mahaifiyarsa bata da hali.
Babu abunda ya fi ɓata mata rai kamar abunda Anty Amarya da Maryam suka mata, kuma bayan su bata tunanin akwai inda zata iya zuwa ta kai kukanta.
Tun da tayi sallah asuba ta shiga kitchen ta haɗ ma Mama abun kari,