Showing 198001 words to 201000 words out of 281103 words

Chapter 67 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61295

kawo yace a ba Alhaji wai hannuna hannunsa”


Karɓa ta yi tana faɗin.


“Okay, wanene?”


“Wallahi ban san shi ba. Ya wuce dai”


Tana karɓa, ya juya ya fice. Ita kuma ta kalli yar aikinta.


“Abincin be yi ba ne?”


“Saura kaɗan”


Juyawa ta yi ta nufi ɗakinta, cike da son jin maganar da Adnan ya soma tsaƙura mata.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *75*


Ko da sha ɗaya na safe ta yi Abbah da Anty Amarya suna katsina, amman basu samu ganin Mai Martaba sai da aka sauko daga sallar azahar, duk da haka kuma be ba da izinin a shigo da su ba sai da ya kira Abdool dan ya sanar da shi. Sai dai yasa an masu masauƙi a gefen sauƙar baƙi, duk abunda ya kamata a yi musu, an musu, abinci ma kusan kala biyar aka jera musu shi drinks, ba a maganarsa.


Mai Martaba be fito ba sai da Abdool ya iso. Sannan suka fito fada tare, ɗaya daga cikin dogarai aka aika ya yi musu iso.
Daga Anty Amarya har Abbah faɗuwa gabansu yake, dukansu zuciyarsu ɗauke take da fargabar kiran da Mai Martaba yake musu. Tun daga ƙofar faɗar Abbah ya tada kai yana kallon irin dukiyar da aka narka a gurin, daman tun farkon shigowarsa gudan ya koma baƙauye, dan duk kuɗin Abbah wasu abubuwan be taɓa ganinsu ba, sai a gidan Mai Martaba, wata ƙila saboda yana sarki ne, shine abunda ya fi ayyanawa a ransa, ga uban sojojin da aka zube a gidan sun matuƙar burgesa, ko ina na gidan cctv cameras ne.


Be ƙara raina kansa ba, sai da aka walgale masa ƙofar faɗa ya shiga. Komai na faɗar ruwan zinari ne, daga kan kujerun har center carpet, da fankar tsaye da ta sama hatta da maɓallin wutar faɗar golden color ne, ga bangon gurin an masa kwalli da wani abu mai kamar zinari, ga wani ƙaton agogon gmt na zinari a gefen faɗar. Alkyabar Mai Martaba ma yau golden ya saka, kamar takalminsa, sai farin rawani da ke kansa. Yarima Abdool na zaune gefensa, cikin shiga ta farar shadda, ya ɗora baƙar hula a kansa, fuskarsa sai wani sheƙi take kamar ango.
Kallo ɗaya Abbah yayi ma Mai Martaba ya yi saurin sadda kansa, saboda wani kwarjini da Mai Martaba ya yi masa, sai gashi ya zube ƙasa yana kwasar gaisuwa, kamar wani ƙaramin talaka.
Mai Martaba be amsa ba sai dai dogaransa ne suke amsa, kamin ya ɗaga musu hannu, ya muku musu izinin fita ba tare da yaƴi magana ba. Tsif ɗakin yai sai sanyi ac dake tsara jikinsu, Abbah dai be sake cewa komai ba, balle kuma Anty Amarya da ko ɗaga kai ba ta yi ba tun da suka shigo.


Tun daga shigowarsu, Abdool ya fahimci Anty Amarya ce mahaifiyar Namra, dan ga kamanin Namra nan shinfiɗe a fuskarta. Mai Martaba yai gyaran murya, wanda hakan ya tatttaro hankalin Abdool ya dawo gurinsa, dan jin shinfiɗar da Mai Martaba zai yi.


“Kai ne mahaifin Namra?”


Da sauri Abbah ya amsa gabansa na faɗuwa, tare da ɗaga hannunsa ɗaya yana bawa Mai Martaba girma.


“Allah ya taimake ka Ni ne”


Mai Martaba ya ɗauki daƙiƙu ashiri da uku kamin ya ɗora da...


“Amman kamaninka da yanayinka be nuna zaka iya aikata abunda ka aikata ba, sam ba kayi kama da mutumen da ya kori ƴarsa saboda ta zaɓi wanda take so ba”


Anty Amarya ta ɗan ɗago kaɗan ta kalli Mai Martaba da kuma Abdool, da take ganin kamar ta san shi.


“Ko kana da dalilin yanke wannan ɗanyin hukuncin?”


Abdool ya tambaya, cike da son jin labarin ta ɓangaren Abbah, wata ƙila ya sha banban da na Namra, idan kuma ya zo ɗaya, Namra ta faɗa masa gaskiya daman be zaci zata masa ƙarya ba, sai dai yana tunanin zata iya ɓoye mata wani abu daga labarinta, ko kuma laifin da ta yi ma Abbah ta.


“Ta zaɓi son ranta ne, bayan kuma na yi mata zaɓi, sannan ina ganin kamar wanda ta zaɓa be dace da ita ba, ta ɓata taraiyyata da mahaifiyar yaron, kuma ta watsa min ƙasa a ido cikin family mu shiyasa na sallama masa ita gaba ɗaya.”


Mai Martaba ya rausayar da kai, tare da kallon ɗansa kaɗan ya ɗauke kai ya mayar gurin Abbah.


“Idan ta kasance kai ne kake son mata fa? Sai kuma iyayenta suka hana ka aurenta har ya zama ka aure ta sai su yi fushi da kai, ya kake tunanin rayuwarka zata kasance?”


“Allah ya taimaki Mai Martaba, ba zan jidaɗi ba”


“Miyasa ka auna ƴarka a muhallinka ba? Kai fa uba ne, ban yi tunanin zaka iya aikata abu kamar wannan, ka kai matsayin da idan wani ya aikata ka kirashi ka yi masa faɗa. Ƴarka ba ƙarar ta kawo a nan ba, kaga yaro gashi nan shi ya ji abunda ya faru ya gurgiza da lamarin har yasa muka kira ka anan”


Mai Martaba na ajewa Abdool ya ɗora.


“Mijin da take aure ya sake ta, saboda ya ce a zubar da ciki ta ƙi, yanzu haka bata cikin garin katsina tana Kaduna, gidan wasu rakuɓe, ba abincin kirki babu abun sha na ƙwarai, kuma kullum kuka take, tana tunanin yadda za tayi ta koma gida har ka karɓe”


Tun da Abdool ya soma magana Anty Amarya ta ɗago tana kallonsa, hawaye sai bin fuskarta suke, daman kullum cikin kukan rashin sanin Halin da Namra take ciki take.
Sai dai zancen sakin da Abdool ya labarta mata ya sanyaya mata rai, hankalinta ya kwanta sosai lokacin data ji dalilin kiran da Mai Martaba yake musu, daman da daɗi tana addu'ah sai yanzu Allah zai amsa mata.


“Kasan abunda nake so da kai?”


Abbah ya girgiza kai tareda ɗaga hannu sama.


“A'a Allah ya taimake ka”


“Ina son ka yafe mata abunda ta yi maka, ko da ba zaka zauna da ita ba, ni zan zauna da ita a matsayin ƴata, daman ni gida na gidan ƴaƴa ne, amman idan ka yafe mata kuma ka saka mata albarka zata ga haske a rayuwarta”


Abbah ya sauke ajiyar zuciya.


“Allah ya taimake ka, ba wai bana son Namra ba ne, kawai ta aikata min abunda ban taɓa mafarkin zata aikata min ba ne, ta zaɓi wani sama da ni, ta bar karatun ta da danginta saboda shi...”


“Wallahi ta yi nadama yanzu, abunda kawai Mai Martaba yake so ka yafe mata mu zamu zauna da ita”


Abdool ya faɗa yana mai saukowa ƙasa ya zauna kusa da Abbah. Anty Amarya ta ɗago ta kalli Abdool.


“Idan har ya yafe mata, ni na fi kowa cancantar na zauna da ƴa ta”


Abbah ya data kai ya kalli Anty Amarya sannan ya kalli Mai Martaba.


“Mamana ta shiga rigarka ta samu alfarmarka, duk da yake ina jiran zuwan wannan ranar da Mamana zata gane kuskure da kuma gangancin abunda ta aikata, na sani wata zata dawo a gareni ko da kuwa mijinta be wulaƙanta ba, nasani wata rana zata gane muhimmancin iyaye, da kuma irin gudumawar da suke badawa a rayuwa, ko da babu saki na sani akwai ciwo, ba fata nake mata ba, amman nasan wata rana zai iya kamata ba duk miji bane yake zama da mace mai wani ciwo, sam bana son na mutu na bar Mamana a cikin halin da ta zaɓi kasancewa a ciki, na sani wata rana zata ratu ba ni, sai dai bana son ta rayu a cikin halin ina fushi da ita, dan nasan ba zata ga dai-dai, ina son Mamana sosai, kuma na yafe mata duniya da lahira”


Mai Martaba yayi murmushin ƙasaita irin nasu na manya.


“Lallai kana son ƙulla abota da ni”


Abdool ma yayi dariya mai cike da farinciki da har suka bayyana haƙoransa da kuma dimples ɗinsa ya ce


“Ni da Mai Martaba muna godiya”


Anty Amarya ta share hawayen idonta tana murmushi.


“Dan Allah idan tana cikin gidan nan ku faɗa mata Mahaifinta ya yafe mata, ta fito mu ganta”


“Bata tare da mu, tana can a Kaduna a wani gida rakuɓe, bata san Mai Martaba ya aika maka ba, ni ne kawai na ga tana cikin matsala kuma na san irin matsalar da rashin zama kusa da iyaye yake haifarwa”


“Allah ya maka albarka Allah ya raya maka iyalanka, ya cika maka burinka, ya taimake ka akan dukan lamurranka, na gode sosai yadda ki yi wannan jihadin Allah ya baka abunda kake so”


Ya amsa da “Amin” Yana wani sunsun da kai, shi ala dole ga surukin da ba san da shi ba 😂.


Mai Martaba ya miƙawa Abbah hannu yana murmushi.


“Yanzu kam zamu yi gaisuwar mutunci da kai, kaga har ƙoƙarin raba uwa da ƴa kake.”


Mai Martaba ya faɗa yana miƙewa tsaye. Da sauri Abbah ya miƙe tsaye, da hannunsa biyu ya riƙa hannun Mai Martaba yana dariya.


“Tuba na ke ranka ya daɗe, Allah yaja kwanan ka”


Juyawa Mai Martaba ya juya Abdool ya miƙe tsaye da sauri ya take masa baya. Har turakarsa Abdool ya rakashi farincike shinfiɗe a fuskarsa, Mai Martaba na shiga Babban falonsa Abdool ya riƙa alƙyabarsa ya cire masa ya jingine, sannan Mai Martaba ya cire rawaninsa da kansa ya aje a gefe, da sauri Abdool ya ɗauki rawanin ya aje a muhalinsa. Sannan ya zo ya zauna ƙasan carpet ya dafa ƙafafun Mai Martaba yana dariya.


“Na gode sosai da karamcin da Mai Martaba yayi min, ba zan taɓa manta wannan ba, Allah ya ja zamanin ka”


Murmushi yayi sai da aka ɗauki daƙiƙu sannan Mai Martaba ya amsa da


“Amin. Nan da minti talatin zamu je ɗan dime ƙaddamar da zakka, idan da hali sai ka shirya muje”


“...A...”


Sai kuma yayi shiru. Kallonsa kawai Mai Martaba yayi hakan ya cilastashi ƙarasa maganar.


“Da naso naje ne can Kaduna na kai su inda take”


Mai Martaba ya sake kallon ɗansa, irin kallon nan na akwai wani abu a ƙasa.


“Babana be kamata kana saka kanka a cikin irin wannan rayuwarba, karka manta kai ɗan sarki ne, kuma nan gaba kaɗan kai Sarki ne, sannan kai mutun ne mai babban muƙami a nigeria, be kamata ana ganin fuskarka a ko'ina ba, wani gurin kamata yayi ka aika, ko kasa ayi. Shi babban mutum ba ko ina ake son yana kasancewa ba, musamman ƴaƴan sarakuna, yana janyo raini, wani gurin ma yakan zubar da mutumcin mutum, amman kai sai naga kamar baka damu da hakan ba”


Yayi ƙasa da kansa, dan yasan Mai Martaba ya faɗi gaskiya, sai dai shi kan har ga Allah yana son ya zama na farko da zai fara yi ma Namra wannan albishir ɗin ko ba komai zai ƙara kwarjini a idonta.


“Amman Mai Martaba ina son na kasance nina zan yi ma yarinyar nan Albishir, idan mun kama hanyar Kaduna yanzu kasan kamin yamma mun isa”


Mai Martaba ya shafa fuskarsa.


“Idan har ganinta kake son yi, zaka iya aikawa a taho da ita”


“She's so stubborn ba lallai bane ta zo, kuma abun zai fi burgewa idan iyayenta da kan su sukaje suka ɗauko ta”


Kallon tsab Mai Martaba yayi ma Abdool sai ya ɗauke kansa, tare da ɗaga masa hannu, alamar go ahead.


*** **** ****


Fitar da Mai Martaba da Abdool suka yi ne, yaba Anty Amarya damar data kai ta ƙare ma Faɗar kallo. Manyan hotuna da ta gani na Abdool ɗaya a cikin kayan sarauta ɗaya kuma a cikin kakin soja, yanzu kan sarai ta tuna waye Abdool. Mutumen da ya taɓa taimaka mata lokacin da motarsu ta lalace ana ruwan sama.


“Gaskiya yana da kirki, matar ka da ƴaƴanka sun yi dacen uba na gari”


Ta faɗa idonta kan hoton Abdool. Abbah dai be ce komai ba, sai fama idonsa abinci yake yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi faɗar.


Fitowar Abdool ne yasa duk suka maida dubansu gurinsa. Wata shigar ce a jikinsa bata ɗazun ba, wannan ma ta fitar da kyausa, da kuma annurin fuskarsa. Zuwa yayi ya risina gabansu, ya yi ƙasa da muryarsa sosai.


“Idan kun shirya zamu je Kaduna yanzu sai na nuna muku inda Namra take”


“Abunda muke jira kenan”


Anty Amarya ta yi saurin amsawa.


“Mai Martaba yana shiri ne, idan ya fita muma zamu kama hanya”


Ya faɗa yana kallon fuskar Abbah dan yaji me zai ce. Murmushi kawai Abbah yayi ya ɗaga masa kai, yana masa kallon mutum mai hankali da natsuwa.


NAMRA POV.


Murmushi kawai take, sai ɗaga kai tana maidawa, duk firar da ake, bata saka baki saboda itama nata ya isheta, su kansu suna firar ne ɗan kawai su rage mata kewa. Amman ta ƙi ta sake, sai dai a kan yi murmushi ko ɗaga kai, gudun kar suce ta ƙyale su, tun da Abdool ya takalo mata maganar gida sai ta koma wata irin, tunanin rayuwar jindaɗin da take ciki ta baya ta riƙa dawo mata, da kuma tunanin halin da Asim ya jefata, ga halin ko in kula da ya nuna mata, da kuma ƙin son haɗa jini da ita, ace duk tsawon wannan lokacin be neme ta, da gaske baya da buƙatar ta kenan? A ɗayan ɓangare kuma tana tunanin yadda zata shirya da iyayenta har ta koma ta zauna a tare da su wanda take ganin abu ne mai matuƙar wahala yin haka.


Duk dariya suka sa lokacin da Lamido yake bada wani labari na ban dariya, ita kam Namra sai ta saka kuka tana mai ɗaga murya dan damuwarta tasa ta manta da agaban jama'ah take, babu wanda hankalinsa ya fi tashi kamar Lamido, dan ya tsani ganin Namra cikin damuwa balle kuma zubar hawayenta. Sai da taga hankalin kowa ya dawo kanta sannan ta sassauta kukan da take ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Ajiyar zuciya Lamido ya sauke cike da rashin daɗin rai ya ce


“Yarinyar tana cikin damuwa, ni ko bana son ganin ta cikin wannan halin, dan zai ƙara mata damuwar ne kawai, babu abunda yake raina a yanzu kamar na maza sanadiyar farincikinta, zan yi iya yadda zan iya na ganin na cire ta cikin wannan halin inshallah”


Neina ta miƙe ƙafafunta tana kallon ɗanta cike da son sa da kuma tausayinsa ta ce


“Cire yarinyar nan a damuwa abu ne mai wahala Lamido, ga dukan alamu ƴar babban mutunce, shiga irin lamarin gidan su sai yi wahala gareka tun da kai ba ɗan kowa ba ne”


Ɗauke kansa ya yi ya maida gurin ƙofar da Namra take. Sai da Neina ta tashi sannan ya miƙe tsaye yana ɗan ɗingishi ya nufi ɗakin. Zaune ya same ta kusa da ƙofa tana raira kukanta mai ban tausayi da taɓa zuciya.


“Namra kukan nan da zai miki magani da tuni yayi miki, kina ƙara saka kan ki ne cikin damuwa ne kawai”


Ɗago kai ta yi ta kalleshi.


“Idan ban yi kuka ba mi zanyi? Kana tsammanin mace data shiga cikin halin da nake ciki zata yi abota da dariya ko farinciki? Ba zaka gane abunda nake ji ba”


“Nasan kin shiga rayuwa kala-kala amman kuka ba zai miki magani ba, ki taimaka min ki tausaya min ki daina wannan kukan Namra, saboda gani nake kamar nine silar zubar hawayenki, ina damuwa sosai”


Hannayenta biyu tasa ta share hawayenta, sannan ta miƙe tsaye ta nufi gurin katifa ta zauna, ta yo ƙoƙarin tsayardar kukanta ne kawai dan ta lura da damuwar da Lamido yake idan tana kukan, balle kuma har ya kai ga yi mata magana, ita kanta tasan ba kowa ne zai juri zama da ita ta dinga masa kuka kamar ƙaramar yarinya.
Ajiyar zuciya Lamido ya sauke ya shafa fuskarsa sannan ya juya ya fice. Ba tayi minti talatin da zaman ba, taji yaro ya doko sallama wai Abdallah daga Katsina yana sallama da Namra. Wani baƙin haushi ta ji ya turniƙe ta, yau kuma da wacce ya zo? Me yake nema a gareta ne? Ba zai barta da damuwarta ba! Tana jin motsin shigowar Neina ta yi saurin kwantawa saman katifar ta lafe sosai kamar ta yi bachi.


“Na san ba bachi kike ba Namra, kuma kon ji lokacin da aka ce ana sallama da ke a waje, ki rufa mana asiri ki tashi kije”


Neina ta faɗa zuciyarta Fal da tsoro, dan ita tun da taji ance ɗan sarki ne, duk fargaba da tsoro suka kama ta, kullum zulluminta ɗaya kar yasa ayi musu wani abu.
Sosai Namra ta so tayi pretending like tayi bachi amman jin yadda muryar Neina take mata magana kamar mai magiya, yasa ta motsa har ta buɗe ido ta kalle


“Neina ban san me mutumen yake nufi da ni ba, me zai zo yayi min a yanzu?”


“Kije dai Allah, ko ma minene zaki ji, kin rufa mana asiri Namra, kin ga mu talakawa ne bayin Allah, karki ja mana abun ba zamu iya ɗauka ba”


“Bana nufin janyo muku komai Neina, amman kamar ba ki fahimci abunda nake nufi ba”


“Na fahimta, kawai ki tashi ki tafi, idan kuma har baki jin tafiyar, ni zan iya bashi izinin ya shigo nan yayi magana da ke, wata ƙila ma carpet ɗinsa da daya manta shekaranjiya ya zo karɓa”


Kamin ta Namra ƙara yin magana. Lamido ya ɗaga labulen ɗakin ya kunno kai yana faɗin.


“Neina kina tsoron masu milki da yawa”


“Dole na tsoraci masu milki Lamido, kafi kowa sanin sune sanadin shigar mu wannan halin”


Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Shi ma Lamido juyawa yayi ya fice cikin rashin daɗin rai, yakan samu kansa a cikin rashin jindaɗi a duk lokacin da Yarima ya tsaya ƙofar gidansu da sunan kiran Namra.
Namra bata motsa daga inda take ba, sai ga Neina ta dawo ɗakin riƙe da carpet ɗin ta miƙa mata.


“Tashi kije ki kai masa, ko ba komai wulaƙanta ɗan Adam babu kyau, balle babban mutun kamarsa”


Wannan karon Namra bata yi mata musu, ta tashi ta karɓi carpet ɗin ta miƙe tsaye, already tana da hijab ɗinta sanye, sai kawai ta bi bayan Neina suka fice tare, takalminta ta zura, ta nufi ƙofar fita.


As usual gurin daya saba tsayuwa ya tsaya, tana tunkara inda yake tsaye gabanta ya soma faɗuwa, ta rasa dalilin daya saka yake mata kwarjini, tana isa kusa da shi ta miƙa masa carpet ɗin ta ce


“Ga carpet ɗin ka dan nasan ita ka dawo ƙarɓa”


Be ɗago ya kalleta ba, balle ta gane maganarta ta ratsa kunnensa, sai sha'aninsa yake da wayarsa, kamar be san da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login