Showing 30001 words to 33000 words out of 281103 words

Chapter 11 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61287

samu labarin tun dai ita ban da ƙawarta Salma bata san ta faɗawa kowa ba, da Momy tace mata ƙara kawai mutane suji za'a ɗaura mata aure.


Sai daga baya suka faɗa mata ai Asma'u ce ta faɗa musu. Kalsoom ta kalli Asma'u tana dariya


“Asmee ina kika ji?”


“Abun sheri ma be ɓoyu ba balle na alheri”


“Ni ina mamakin ta ina kika ji”


“Ai tuni ni na sani dan har a wayar mijin naga hoton ki, ido na sa miki dan naga indan zaki faɗa”


Sai duk suka sa dariya. Suka mata barka da Allah yasa alheri.
Bayan ta wuce office ɗin ta Asmee ta bita tana zolayarta


“Amaryar mu amarya mu”


Kalsoom ta ɗora jakarta saman tebur tana dariya.


“Wai daman Hilal ɗan'uwan ku ne?”


“A'a unkuwar mu ɗaya dai da shi, kuma mijina abokin shi ne”


“Allah sarki ke haka unguwarku daya ba”


“Amman Wallahi kin yi dacen miji, gaskiya Hilal yana da mutunci sosai, gashi bawon mata sai yadda kika yi dashi, matarsa ma ba daɗinta yake ji ba amman sai juya shi take”


“Kin san matarsa kenan?”


“Sosai ma, amman wallahi ƴar banza ce sai kin shirya zama da ita hmmm amman aje aikinki zakiyi ko?”


“Haka yace wai baya son aiki”


“Ai saboda aikin matarsa zai ƙara aure dan ya son ya hanata aiki amman ba dama”


“Saboda me?”


“Ai ma'aikaciyar banki ce ƴar gidan su Dr. Ayuba matsayi, kin san ai ƴaƴan gidan ba daga baya ba, haka ake cewa wai aba a musu kishiya, uwarsu ma duk masifar Uban sai tun da ya aure mui”


Ta ƙarasa tana shafa baki. Ganin yadda Kalsoom ke kallonta yasa ta tsargu sai ta tashi daga saman kujerar da take zaune tana dariya tace


“Bari na koma gurin zamana kar MD ya tararda ni a nan ina tsiyaya”


Nan ma Kalsoom murmushi kawai tayi. Sai ta nufi ƙofa tana faɗin


“Mu dai ayi auren nan da wuri aje ayi mana rainon ƴan ɗiyan mu, Allah ya sanya alheri”


Da Amin Kalsoom ta amsa ta bita da kallo tana nazarin maganganunta.




NAMRA POV.


Wuni Namra tayi addu'ah tana ba Allah cigiyar inda Amira take. Duk hankalinta ya tashi ji take kamar ita ce ta ɓata, abu ɗaya zuciyarta ke ayyana mata wato Uzair, sai dai ta kan tambayi kanta da kanta ma zai haɗa alaƙa tsakanin Uzair da Amira.


Kiran da taji Maryam tana mata yasa ta tashi daga saman sallayar da take ta nufi falo.
Tsatsaye ta tararda su Anty Amarya da wasu police biyu mata tsaye a falo. Gaban Namra ya faɗi, da sauri ta ƙaraso kusa da su.


“Lafiya?”


Sai ɗaya daga cikin ƴan sandar ta nuna mata id cart ɗinta.


“From Marna Police station, Muna zargin da a hannu gurin kidnapping ɗin Amira, abokan aikin mu suna waje, zamu je da ke a station”


Ba shiri Namra ta daki ƙirgi tana nuna kanta.


“Ni....?”


Da sauri Maryam ta nufi part ɗin Abbah tana kuka. Anty Amarya ma kuka take ita da Aisha. Kamar an jefo Hajiya Barau sai gata cikin ɗakin tana salati da sallami.




____________________________________


THERE WORDS FOR THIS CHAPTER...!
WHAT DO YOU EXPECT NEXT?
LOVE YOU ALL FISABILLIAH 😘💖🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa12.html


🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*


Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


NOT EDITED ⚠️


*PAGE - 15*


Suna fitowa waje Abbah na kawowa. Sai ya tsayar da ƴan sanda yana tambayarsu.


“Miya faru haka?”


“Sir muna tuhumar Namra ne da sa hannu a gurin sace Amira”


Abbah yayi ma Namra wani kallo. Sannan ya kalli ƴan sanda yace


“Ɗaya daga cikin ku zata biyo ni muje cikin motana”


Ba su musa masa ba, ɗaya daga cikin police ɗin ta bi Abbah suka shiga mota ita da Namra baya, Anty Amarya a front seat.
In banda kuka babu abunda Namra take har aka isa station ɗin. Sannan Abbah ya fita suka shiga cikin station ɗin. Ammy da ƙanwarta na tsaye a gurin idonta A kumbure.
A take wani police ya karanto masa abunda ake zargin Namra da shi, sannan yayi musu jaga zuwa office ɗin dpo. Sai da ya gama da wasu cases sannan ya su Namra suka iso gurin ya gaisa da Abbah cikin mutumci yana girmama shi.


“Ranka ya daɗe Ashe kai ne”


“Nine Wallahi ya aiki ya kwana biyu”


Abbah ya faɗa ba dan ya waye shi, sai dai shi ɗin yasan Abbah kasancewarshi sanannen ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa.


Bayan Abbah ya zauna, Namra ta zauna a kujera dake kusa da Abbah, sai Ammy ta zauna a kujarar dake gefen Namra ita da ƙanwarta.
DPO ya kalli ya dubi takarda take gabansa ya kalli Namra yace


“Amm Namra Usman ana zargin ki dasa hannu gurin ɓatan ƙawarki Amira...”


Kasa magana Namra tayi sai kuka take. Abbah ya katsa mata tsawa.


“Ki buɗe baki kiyi magana mana”


Sai kawai ta ƙara rushewa da kuka kamar zata tsuƙe. Anty Amarya tace


“Taya zata iya magana? Bayan irin ƙazafin da aka mata, a rasa wanda za'a zarga sai ita, lokacin da Namra ta ɓata miyasa bamu zargi Amira ba, ko ita Namra ba ƴa bace? Ko kuma ni ban san zafin ta ba? Faɗa min ɗa ya fi ɗa ne? Wallahi Allah sai ya saka mata shikenan dan anga yarinya bata magana komai aka kwaso sai a dire a kanta, dan kin rikice akan neman ƴarki sai ki ɗauka ki ɗorawa wani, me kuke da shi da har Namra zata sa a ɗauke Amira, wallahi ke kinsan Namra ta fi ƙarfin Amira nesa ba kusa ba...”


Dpo ya miƙe tsaye yana ɗaga ma Anty Amarya hannu.


“Dan Allah Hajiya ki saurara, an zo nan dan a sasanta ba dan faɗa ba”


Bayan ya zauna ya kalli Namra yace


“Ki kwantar da hankalin ki ba wani za'a miki ba, nan guri ne na...”


Ƙwanƙwasa ƙofar da akayi ne ya hana Dpo ƙarasa maganarsa.


“Yes come in”


Wani ɗan sanda ne ya shigo ya sare masa sannan yace


“Sir Alhaji Haruna is here to see you”


“Let him in”


“Yes Sir”


Ya sake sare masa sannan ya juya ya fice. Sai ga Abbah Amira ya shigo cikin ɓacin rai, idonsa be sauka ko ina ba sai akan Ammy, nunata yayi da yatsa.


“Amman Wallahi Asiya baki jin magana, yanzu duk maganar da na miki baki ji ba, sai da kika aikata? Yanzu miye amfanin haka? Ki zubar da kanki mutuncin kawai”


Ya ƙarasa yana miƙawa dpo hannu suka gaisa.


“Wannan maganar bata ma kamata ta fito bakin ki ba, dpo ban kawo maka rahoton ɓatan yarinyar nan ba? Babu inda ban kai rahoton nan ba”


Dpo ya ɗaga masa kai yana murmushi. Abban Amira ya miƙa Abbah hannu suka gaisa


“Alhaji Usman, yau dai mun yi zumunci dole, mata sun haɗa mu”


Abbah yayi dariya.


“Kasan sha'anin mata sai haƙuri, ba tunani suke ba idan zasu yi abu”


“Wallahi basa tunani yanzu miye amfanin wannan abun? Yanzu haka sai da aka kira ni daga gwuiwa station aka ce min ance anga Amira a tashar mota amman basu san motar data shiga ba”


Ammy ta fashe da kuka.


“Wallahi babu abunda ze sa Amira ta gudu tun da ba wani abu muka mata ba”


“Toh aljana ce aka gani kenan? Ko kuma ƙarya suke, tashi ki wuce gida bana son maganganun banza”


Cewar Alhaji Haruna Abban Amira. Abbah yace


“Karka ga laifin ta duk haka muke fama dasu inda mata ne sai haƙuri”


“Magana ce da bata da toshe balle makama ban san inda ma wannan maganar ta fito ba”


Cikim kuka tace Ammy tace.


“Hajiya Barau ce ta faɗa kuma ai ba zata yi ƙarya ba”


Abban Amira ya nuna ta da hannu yana kallon Abbah.


“Kaji ko? Jita-jita ne kawai”


Abbah yayi shiru yana motsa baki alamar nazari. Alhaji Haruna ya kalli Ammy da Ƙanwarta yace


“Ku tashi muke gida”


Da kuka Ammy ta tashi ta fice, sannan ya kalli dpo ya ciro wasu ƴan kudaɗe a aljihunsa ya aje gaban teburin dpo


“Dan Allah aka kashe maganar nan dpo, matsala ta cikin gida ayi haƙuri”


“Ba matsala, muma ai mun fi son haka”


Tare da Abbah suka fito. Anty Amarya na riƙe da Namra har suka fito harabar station ɗin. Sun ɗan daɗe suna fira da Alhaji Haruna sannan sukayi sallama cikin mutunci ya wuce Abbah kuma ya nufi Motarsa.
Har Abbah ya iso gida Anty Amarya masifa take, tana kiran Hajiya Barau da munafuka.


“Ai itama ta haifi ƴaƴa mata, zata jidaɗi idan aka mata haka? Me Namra ta tare mata ne? Ai Wallahi duk mace data ɗuka ta haifi mace tace wata macen ba zata jidaɗi ba sai Allah ya gwada mata akan ƴaƴanta”


Sai da Abbah yayi parking sannan ya kalli Anty Amarya yace


“Bana son ƙananan maganganu, ki wuce part ɗin ki ki bar ni da ita kawai”


Bata sake cewa komai ba, dan tasan halin Abbah zai iya juyarda faɗan akanta. Sai kawai ta buɗe ta fita ita da Namra suka nufi part ɗinta Abbah kuma ya nufi part ɗin Hajiya Barau.


Tana ganin Abbah hankalinta yayi mugun tashin, kamar tasan asirinta ya tono, ko da yake ta karanci yanayinsa shiyasa zuciyarta ta ayyana mata lallai akwai laifin da tayi masa.


Abbah be kula jikokinta da suke falon ba ya hauta da faɗa, daman haka yake idan ya tashi matsifa babu ruwanshi da wanda yake zaune. Ta inda Hajiya barau take shiga bata nan take fita ba, tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta kai ga fasa kuka tana faɗin


“Ni Wallahi ba da wata niya nayi ba, kuma tun da daɗewa mukayi wannan maganar fa”


“Ni dai na faɗa miki, ki iya bakin ki ko kuma duk abunda ya same ki ke kika ja, Namra dai kin kusa jikanya da ita, dan haka ba dai-dai bane ki zauna kina faɗan mugaye kalamai akan ƴarki”


Kuka take sosai tana faɗar wai ƙazafi aka mata, har jikokinta suka dafata suna bata haƙuri. Sannan Abbah ya tashi ya nufi part ɗinsa.


Namra na kwance jikin Anty Amarya tana sauke ajiyar zuciya Maryam tace


“Wallahi Allah sai ya saka miki daga Ammy har tsohuwar makirar can Hajiya”


Anty Amarya ta katsa mata tsawa.


“Ke matar uwanki zaki cewa makira ko dan darajar tsufanta kya ce mata haka, balle tana auren uban? Kin gani ina ja miki kunne akan rashin kunyar nan kina ƙarawa ko? Wallahi kika kai ni ƙul sai na ɓata miki rai”


Miƙewa tayi tsaye cikin fushi ta miƙawa Namra takardar dake hannunta.


“Ke ni dai karɓi, Asim ya zo baki nan yace a baki”


Da sauri Namra ta ɗago ta kai hannu ta karɓi takardar, sai ta share hawayenta ta tashi ta nufi ɗakinta, zuciyarta cike da zazzanar son sanin abunda takardar ta ƙumsa.




__________________________


Wannan shafi na ƴan TASKAR KHADEEJA CANDY ne, da CLASSIC LADIES, tare da NAMRA FANS GROUP. I really appreciate your comments 💖💖💖
https://chat.whatsapp.com/LHd6gwdQQWZKNeHU9z4qf0


Masu tambayan grp ga link nan. Amman ban da maza ❌


🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*


Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


NOT EDITED ⚠️




*PAGE - 16*


Natsuwa tayi sosai ta tattara dukan hankalinta ta mai da gurin takardar, sannan ta buɗe ta soma karantawa.


_SALAM_
MY DEAR NAMRA.


Na zo gidan ku ance min baki nan, na kira wayarki ban samu ba, mahaifiyata kuma ta shaida min kina nema ma, ban san ta yadda zan iya ganin ki ba amman ga sabon number waya na ki kira ni dan Allah.


Urs ASIM.


Wani dogon ajiyar zuciya ta sauke, ta rumgume takardar a ƙirjinta ta lumshe ido, tana sauraren bugun zuciyarta.
Ta ɗauki daƙiƙa goma zuwa shabiyar kamin ta buɗe idon, ta tashi ta nufi ɗakin Maryam.
Dariya ta tararda Maryam na ƙyalƙyala kamar wata sabuwar mahaukaciya, har ta zauna kusa da ita bata san ta zauna ba, tana taɓa ta ta zabura.


“Wayyo Allah na”


“Ke lafiyan ki?”


“Wallahi wani littafi ne nake karantawa mai shegen dariya”


“Littafi kuma ai ke Allah be raba ki da karatun littafai ba”


“Wallahi Anty Namra yayi daɗi kamar me, da zaki karanta kema da kin sha dariya”


“Idan na samu time zan karanta, meye sunan littafin?”


“Noor na Khadeeja Candy”


“Okay ni dai ara min wayarki wani abu”


“Ke dai ce zaki kira Asim ba wai kiyi wani abu ba”


“Naji ni dai bani”


Sai da tayi saving ɗin page ɗin, sannan ta miƙa mata wayar tana zolayarta. Namra dai bata ce mata komai ba ta tashi ta fice tana faɗin.


“Ina fatar da Akwai kuɗi a ciki”


“Kai kaji ki da wata magana, manyan Babe's irin zasu zauna waya ba kati, taf mune tare da manyan samarin garin nan fa, kin san ko dan karya dole a saka mana manyan kati ”


Da dariya Namra ta fice, ta koma ɗakinta. Takardar ta ɗauko ta saka Number ta danna kira. Ringing biyu zuwa uku yayi picking da sallama.
Sai da ta lumshe ido ta buɗe da murmushi sannan ta amsa masa.


“Wa'alaikassalam. Asim”


“Namra...”


Daga cikin wayar tana jin lokacin daya sauke ajiyar zuciya, sannan yace


“Namra wai Abban ki ya yarda na aure ki?”


Kai ta ɗaga masa kamar yana gabanta, hawaye suka silalo mata.


“Ya yarda Asim, shiyasa na neme ka”


“Alhamdulillah”


“Ina kaje Asim? Ashe zaka iya tafiya wani guri ka bar ni?”


“Namra idan mun haɗu zamu yi magana”


“Yaushe zaka zo?”


“Ba zan iya zuwa gidan ku da sunan hira ba, sai dai mu haɗa ta layin su Azeema”


“Okay gobe da ƙarfe tara dan Allah”


“Allah ya kai mu I Love You”


“I Love You More”


Daga haka ya kashe wayar. Sai ta rumgume phone ɗin tana murmushi tare da hawaye.


KALSOOM POV.


Kusan kullum sai Doc. Hilal ya kirata a waya sun gaisa, sai dai fira ce be cika zuwa ba sai jefi-jefi. Sau biyu ya taɓa kawo mata ƴaƴansa suka gaisheta ita kuma tayi musu goma na arziki.
Ana sauran sati biyu biki Doc. Hilal ya nemi ta bashi list ɗin abubuwan da zata yi na biki. Bata rubuta wasu abubuwa masu yawa ba, bayan abubuwan da al'ada ta tana da.


Batayi wata hidima ba duk da kasancewar ƙannenta sun so tayi, amman bata biye musu ba, wai ita ta girmi wannan yanzu.
Kala kusan arba'in da huɗu yayi mata, duk masu kyau da ɗaukar hankali, kowa ya gani sai ya yaba, wasu na faɗin haƙurin da tayi yanzu zata ci riba.


Ranar laraba aka saka amarya lalle a daren ranar akayi wankin amarya, washegari alhamis akayi ƙunshi da kitso, friday akayi walima, Assabar aka ɗaura aure Kalsoom da Doc Hilal.
Daddy yayi mata nasiha mai ratsa jiki, gwaggwanin suka mata jan kunne akan rayuwar gidan aure kamin Momy ta ɗora da nata. Kuka sosai Kalsoom tayi a lokacin da aka fito da ita za a saka ta mota zuwa gidan mijinta. Duk wanda ya gani zai yi zaton bata son auren ne.


Da ƙafar dama ta shiga gidan aurenta tana ƙorar shedan kamar yadda Momy ta faɗa mata. Sai da aka zaunar da ita a saman gadon aurenta sannan ta tsagaita kukan.
Batayi zaman minti ashirin ba abokan ango suka shigo tare da ango, sai zolayarsa suke, anyi siyen baki da wasu abubuwa da al'ada ta tanada sannan suka yi musu addu'ar zama lafiya.
Har gurin ƙofa Hilal ya raka abokansa, yayi ma ƴan'uwan amarya da wasu daga abokanta sallama sannan ya rufe ƙofar.


A maimakon ya koma ɗakin Kalsoom, sai ya nufi ɗakin Rashida dan duba halin da take ciki.
Zaune ya tararda ita ƙasan carpet tana wani irin kuka kamar ranta ze cire, wata cousin ɗinta na kusa da ita tana bata haƙuri.


“Habiba ɗan bamu waje”


Ya ƙarasa faɗar yayinda yake zaunawa kusa da ita, janta yayi izuwa ƙirjinsa ya rumgume ta sosai.


“Shiiiiiiiii. Wannan hawayen ban ga dalilin zubar da su ba Ammyn Rafiq, kin san ba ɗan bana son ki bane yasa nayi aure sai dan sauwaƙe miki wasu abubuwan, a maimakon kiyi farin ciki sai kuma kiyi kuka?”


“Ina son Hilal ina kishin naga wata a tare da kai, zan iya mutuwa Hilal”


Ta faɗa tana ƙara narke masa a jiki. Saman kanta ya shafa ya sumbanci shi sannan yace


“Allah ya sassauta miki wannan kishin Pyar, I Love You so much amman ina son ki so abunda nake so”


Kuka tayi sosai har sai da maƙoshinta ya bushe sannan ta sassautama kanta, har kuma lokacin Hilal na rumgume da ita yana rarrashinta.


“Pyar”


Ta ɗago kai ta kalleshi da kumburarin idanuwanta.


“Karki sa damuwa a ranki kin ji? Mijinki yana son ki matuƙa, kuma baya da niyar cutar da ke”


Ta ɗaga daga jikinsa.


“Tashi kaje kar na shiga mata haƙƙi”


“Zanje amman sai kin yi min alƙawarin zakiyi bachi!”


“Zan yi”


Babbar rigarsa ya cire, da ita ya gyara mata fuskarta, ya goge majinar data ɓata mata gaban riga sannan ya kai bakinsa cikin nata yana kiss.


Ya ɗauki lokaci mai tsawo yana kiss ɗinta da shafa wani ɓangare na jikinta, har sai da ya tabbatar ya kashe mata jiki, sannan ya ɗaga ya kalleta.


“Good night Pyar”


“Good night”


Sai ya sumbaci goshinta.


“Dream me i love you”


Ɗan murmushi ta sakar masa kaɗan. Sannan ta sake shi ya tashi, ya baro mata ɗakin zuciyarsa cike da zumuɗin zuwa gurin Amaryarshi.


Da sallama ya shiga ɗakin yana murmushi, sai ya zauna kusa da ita ya kai hannu ya yaye lulluɓin dake kanta.


“Wannan Amaryan bakinta da tsada yake, har ta kasa amsa sallamar angonta”


Hawayen daya gani a fuskarta ya tada hankalinsa. Dan be yi zaton macen data kai kamar Kalsoom idan anyi mata aure a zamanin nan zatayi kuka ba.


“Wannan hawayen na minene My Queen? Ashe yau ba ranar farincikin mu bace? Ai kamata yayi mu gode Allah ko?”


Ita kanta bata san hawayen minene take ba, na farincikin yau Allah ya gwada mata aurenta, ko kuma na yanayin da take ciki na baƙincikin rabuwa da iyayenta.
Matsawa yayi daf da ita sai ya kai tattausan hannunsa ya share mata hawayen, ya kwantar da ita jikinasa, yasa babban yatsansa da mai bi mata yana mata saƙa a jiki.


“Ranar yau ba ranar kuka bace ranar murna ne, ranace da zaki gode Allah kuma ki shirya karɓar angonki da kyakkyawar tarba”


Notse kanta tayi cikin ƙirjinsa, jikinta na amsa saƙon da ƴan yatsunsa suke kai mata. Tana jin wasan ya canja salo sai ta zame jikinta, idonta cike da nauyin kallonsa.


Murmushi yayi yana wani lumshe ido yana buɗe, sannan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login