Showing 168001 words to 171000 words out of 281103 words

Chapter 57 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61277

da ke, ba ki yi kama da mugayen mutane ba, kuma na san ba zaki cutar da mu ba”


“Na gode”


Namra ta faɗa cikin muryar kuka.


“Uwani zuba mata ruwa ta yi salla”


Lamido ya faɗa cikin halshen fulatancin yayinda yake ƙoƙarin miƙewa tsaye ya jefar da ledar kifin dake hannunsa. Cikin ladabi ta tashi ya ɗauko mata buta ta miƙe mata sannan ta nuna mata banɗaki. Kamin namra ta yi alwala har ta shinfiɗa mata tabarma ta ɗosa mata sallaya sama ta aje mata carbi. Sannan ya ɗauko ɗayar tabarmar ta shimfiɗa mata gefe ɗaya ta ɗauko zanen gado ta shimfiɗa mata ta aje mata matashin kai. Sai ta dawo ta ɗauki abincin taje can kusa da tabarma ta aje mata.


Namra bata tashi daga saman sallayar ba sai da tayi salla insha'i sannan ta ƙara faɗawa Allah buƙatarta ta sai ta tashi ta koma inda Uwani tayi mata shimfiɗa ta kwanta. Babu abunda ya zo mata a rai sai gidan su, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna irin abunda Asim yayi mata sai ta ji kamar zuciyarta zata rabe biyu tsabar baƙinciki.
Kusa da ita Uwanin ta zo tayi shimfiɗa, ta kwanta, sauran yaran gidan kam sai da dare ƴa raba sannan suka nemi guri suka kwanta. Juyi Namra ta yi ta yi har safe ba yi bachi ba, abun nan da take jin ya tsaya mata a ƙahon zuciya yaƙi saukar mata har yanzu numfashinta ma daker take yinsa.
Bata san kan gidan ba amman haka be hanata tashi da wuri ba dan gabatar da salla azuba, sai duk sakkon tashin da tayi sai ta hango Lamido a ƙofar ɗayan ɗakin 6ana salla nafila, kallo ɗaƴa tayi masa ta ɗauke kai. Sai da tayi alwala tana daf da gamawa sai ga Neina ta tashi sai ta tashi dukan sauran yaran gidan har da waɗanda ba su wuce shekara bakwai ba zuwa takwas.


Bayan sun yi alwala dukan mazan sai suka tafi masallaci su kuma suka yi nasu salla a gida. Tun da Neina ta maida gabanta gaban bata juyo ba sai ta ta gama lazumin da take. Uwani ma ta maida gabanta gabas tana nata karatun ƙur'ane, ɗayar ma da tsawon su zai iya zuwa ɗaya da uwani ita karatun take, duk yaran masu ɗan tsawo da wayo kowa ya kama surar da yake yana karantawa. Ƙananen kawai suka koma bachi, sai ita kuma ta jingina jikin icecen dake tsakar gidan tana tasbihi da hannu. A hankali ta karkata kanta tana kallon Lamido take can ƙofar wani ɗaki yana nashi karatun cikin natsuwa da ƙira'ah mai daɗin saurara.


Hakan ya karantar ita irin tsantsar natsuwa da kuma ilmin da ƴaƴan gidan suke da shi, tun daga yaran su har ƙanana, ta samu kanta da ɗan sakewar zuciya tun bayan daga irin karatun ƙur'anen ta suke, daman sauraren karatun ƙur'ane yana saukar da natsuwa karanta shi kuma yana sa kwanciyar hankali da walwalah.


Bayan duk sun gama sai suka duk suka zo suka gaishe ta, ta amsa musu da far'ah sannan ta gaishe da Neina, kamin ta kalli Uwani dake mata murmushi ta ce.


“Ina kwana?”


“Lafiya ƙalau ai daman na ce sai dai ki gaishe ni, ba dai ni na gaishe ki ba, dan nayi ƙanwa da ke”


“Ni...?”


“Eh mana Lamido da kike gani ni nake binsa kin ga kuwa ni yayarki ce”


“Gaskiya ban yarda ba”


“Ta girme ki ƴar nan, jikin ne haka ba'a gane girman ta, yaran nan da kika gani duka ƴaƴanta ne”


Neina ta saka baki a maganar su da Namra tana murmushi. Namra tayi mata kallon mamaki.


“Amman ba za a ce ke ce kika haifesu ba, dube ki fa”


“Kowa haka yake cewa sai wanda ya sani, kin san jikin fulani”


“Allah sarki Allah ya shirya miki su”


“Amin. Maryam tashi ki ɗumama mana tuwon can”


Da sauri Namra ta kalli wacce uwani ta kira da Maryam ɗin tana murmushi.


“Marƴam sunan ƙanwata kenan, amman ita kam uwar masifa ce”


“Hmm wannan ma ai ba baya ba, ga shegen rashin kunya da kauɗi ɗuk ta tara kamar ya kashe ta”


Neina tayi dariya tana ƙoƙarin tashin tana faɗin.


“Maryam bar ni na gyara abu na da kai na, karki je ki min ƙire-ƙire da shi”


Uwani ta kalli Namra.


“Ke kan sai dai asiyo miki koko ko shayi ko? Naga ko jiya ba ki ci komai ba”


“A'a kawai bana jin cin abincin ne”


“Saboda me?”


“Damuwar da ke raina ba zata bar ni na ci abinci ba”


“Hmm idan kika ce zaki saka damuwa a ranki zaki samu matsala, kin gan ni nan damuwar da take rai na mai yawa ce, amman a haka na ke sakewa ina walwalah kamar komai”


“Wata ƙila damuwar ki bata kai tawa ba”


“Ko kuma ke na ce damuwarki bata kai tawa ba, kin ki yaran can? Ubansu yana nan da ransa amman babu ruwansa da mu, saboda mahaifiyarsa bata so na tun ina auren fari, sai take ganin kamar na mallake mata ɗa, kullum kalar masiba daban har na haifi yara biyar ina da cikin na shida can ne tasa ya sake ni, kuma tun daga lokacin babu ruwansa da cin mu da sham mu, balle sutura yau tsawon shekara biyu kenan, Lamido ne da Neina kawai suke hidima da mu, sai kuma ƴar sana'ar da na ke. Kin ga kuwa damuwarki bata kai tawa ba”


“Kowa dai irin ƙaddararsa, amman miyasa ba ku sashi kotu ba? Ai kamata yayi ace an karɓa muku haƙƙin ku”


Daga can gaban murhu da Neine take ta amsa ma Namra tambayar da tayi ma uwani


“Muna kotu yanzu haka, amman shari'ar ta zama wani iri saboda mu talakawa ne, shi kuma yana da rufin asirin da zai tsaya masa a ko'ina, duk da yakr matsalar daga gurin muguwar uwarsa ne”


Namra ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina lamarin.


“Rayuwa kenan! Kows da kalar ƙaddararsa, kowa da yadda aka rubuta masa tasa, wani matsalar daga gurin mijin ne, wani uwar miji wa su ƴan'uwan miji wasu kuma ahaɗa musu duka”


“Haka ne kowa ai baya wuce ƙaddararsa, shiyasa idan kaga ta wani sai ka gode Allah da ta ka”


Cewar Neina tana ƙalla itace yana sakawa cikin murhu. Lamido dai yana daga jikin ƙofar ɗakin yana dannar shakiɗin ka baƙauyensa kamar baya jin firar da suke.


“Kin ga tawa ƙaddarar ta so tayi yanayi da taki, nima saboda ciki dake jikina mijina ya sake ni, kuma saboda ya san babu inda zanje tun da na riga da na ɓata da mahaifina”


Dukasu kallonta suka yi, except Lamido, kowane cike da mamaki da kuma shauƙin son jin labarin nata. Sai dai duk da haka Lamido be ɗago ba balle ya nuna hankalinsa yana kan labarinta sai dannar wayarsa yake alhalin kuma dukan hankalinsa da jinsa ya tattara ya koma gindin iccen mangoro da Namra take zaune.


Babu abunda Namra ta ɓoye su, tun daga neman aurenta da Asim da irin gwagwarmayar da suka sha, kamin auren da kuma irin abubuwan da suka biyo bayan auren da irin wulaƙancin da Asim yayi mata har i zuwa jiya da ya sake ta.
Sun tausaya mata. iya tausayawa ganin yadda tayi sadaukarwa amman ace ya ci amanarta, duk da basu sanshi ba hakan be hana su tsine masa ba tare da roƙon Allah ya isar mata.
Kuka take sosai duk da irin haƙurin da suke bata be hana ta zubar da hawayen baƙinciki ba. Wannan karon idon Lamido yana kan Namra, be ce uffan akam labarinta amman yana jinjina irin cin amanar da Asim yayi mata, a ransa yake ƙyama da kuma mamakin irin mazan nan da suke auren ƴaƴan masu kuɗi dan su gina nasu rayuwa, ya daɗe yana jin irin wannan labarin na auren jari yau kuma sai Allah ya haɗa shi da wace aka yi ma.
Haƙiƙa rayuwar Namra abar tausayince,duba da irin rayuwar da zatayi da kuma wacce tayi, ga kuma tunanin makomar abunda tafi nanata musu a labarin na ɓatawar da mahaifinta yayi da ita. Saukowa yayi daga saman banrandar da yake ya saka takalminsa ya nufo gindin bushiyar ya ciro ɗari biyu ya miƙawa Maryam


“Karɓi ki amso mata tea da bire a waje”


Sai da Maryam ta karɓa ta fita sannan ya kallin saman kan Namra yace


“Kuka baya magani abunda Allah ya rubutawa ma bawa, haƙuri ya kamata ki yi, Allah zai bi miki haƙƙin ki, abunda ya fi akwai kiyi ƙoƙarin shiryawa da iyayen ki babu kamar iyaye duniya komai kika zama a duniya idan babu albarka iyaye sai kin lalace kuma komai kika lalace idan akwai albarkar iyaye sai kin kai inda baki zato”


Ɗagowa tayi ta kalleshi ido cikin ido.


“Ta ya zan shirya da su? Na je gida da cikin wanda suka hana na aura? Bayan mahaifina ya yi min gargadi? Naje na faɗa mu su Asim ya sake ni? Ya kake ganin za su karɓe ni?”


Ɗauke kai yayi daga kallonta saboda zubar hawayen da take, ya samu kansa a tausayinta. Hannayensa ya zuba cikin aljihu ya nufi ƙofar fita gidan zuciyarsa nata raya masa abubuwa da dama.


Tea kawai ta sha, sai Neina tasa ta shiga ɗakinta ta kwanta, ganin an kawo musu wutar safe wai ko ta samu ɗan bachi. Lamido kuma ya dawo yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin yayi ma mahaifiyarsa sallama ya fita zuwa gurin a neman halalinsa.




KALSOOM POV.


“Ba zaunawa za kayi ba sakin ta nace ka yi ko baka ji ba?”


Hajiya ta faɗa a tsawace tana kallon Hilal. Gaba ɗaya sai hankalin Rashida ya tattara ya koma gurin da zancen da Hajiya tayi duk da bata san wainar da ake toyawa ba, hakan be hanata karantar akan mutuwar Rafiq ba ne, sai kawai ta ƙara narkewa ta fashe da kuka tana faɗin.


“Ina gawar ɗa na? Hilal ina ɗa na ya ke”


“Yana waje a motar Doc Noor”


Durƙushewa tayi a gurin wani kukan gasken ya zo mata. Sai ta Ummu Faisak ta shigo tare da wasu ƙanenen Rashida ciki har da Safiya.


“Da gaske ya rasu kenan? Kalsoom kin ci amana ta, kin kashe min ɗa sauran ƴaƴa ma na bar miki suma ki kashe”


Rashida na kaiwa nan ta tashi ta fice tana wani irin kuka. Ummu Faisak ya nuna Kalsoom da yatsa.


“Wallahi baki da imani Kalsoom kin kashe shi kin huta, yanzu sai ki zuba ruwa ƙasa ki sha, kin ƙori ƴar'uwarmu kin kashe ɗan ta hankalinki ya kwanta ko? Tam congratulations”


Ita ma ficewa ta yi tana kuka, tare da sauran ƴan'uwan. Kai kawai Kalsoom take girgizawa alamar a'a dan bata iya magana saboda kukan daya ci ƙarfinta.
Hilal har cikin ransa yake jin kukan Kalsoom cos shi kam he believe ba ita ta aikata ba.


“Hajiya kar mu aiakata abunda za mu zo muna nadama, wallahi ba ita bace ta rantse min”


“Iyyye nadama? Ah lallai Hilal yau kai da kan ka kake faɗin haka? Kasan hukumcin wanda ya aiakata kisan kai kuwa? Tafa kashe maka ɗa har lahira amman kake wannan maganar kamar wanda baya cikin hankalin kansa, ka sake fa nace ko kuma wallahi na tsine maka a yanzu”


Kalsoom ta matsa ta kama ƙafafun Hilal tana kuka tana girhiza shi


“Sake ni Hilal, ka sake ni a yau karka sallaaƙe maganar mahaifiyarka, ka sake ni dan girman Allah Hilal”


Kallonta yake kamin ya ɗaga kai ya kalli Hajiya idonsa da hawaye.


“Haba Hajiya da wanne zan ji? Rashin ɗa na ko kuma wannan matsalar? Ki bari komai ya laɓa za'a gano gaskiya”


“Da uwarka zaka ji, wawa kawai marar hankali, a yau fa sai ka zaɓa ni ko ita”


Ya maida dubansa akan Kalsoom da fatar fuskarta ta soma ja saboda kuka. Cike da nauyin baki ya ce


“Na sake ki saki ɗaya...”


Wani irin abu taji ya ratsata tun daga saman kanta har zuwa ƙasan ƙafafunta, wani sanyi ya ratsa gefen jikinta.


“Tashi ka yi ma ɗan ka sutura akai shi makwancinsa”


Ba musu ya tashi ya shiga ciki. Ya ɗan ɗauki lokaci kamin ya fito ya nufi waje. Da kansa yayi masa wanka daman yasan wanka gawa kamar yadda ake wankan tsarki ake yinsa, banbanci shine wannan ana saka masa magarya da kuma turare, sai kuma na mata daya ɓanɓanta dan shi akan tufke kan mace gida uku ne sannan a yarfar da shi a bayanta saboda hadisin Ummu Aɗiyya wajen siffanta wankan gawar ƴar Annabi S. A. W tace sai muka kitse gashin kanta tufka uku muka yarfa shi a bayanta _Bukhari da muslim ne suka ruwaito shi_ sai kuma inda take cewa na kasance cikim waɗanda suka yi wa Ummu Kulsum ƴar Manzo Allah s.a.w wanka lokacin data rasu farkon abinda Manzon Allah ya fara ba mu shine gyautonsa, sannan taguwa, sannan mayafin ka, sannan mayafin jiki sannan aka lulluɓe baki ɗayan jikinta da wata tufar. _Ahmad da abu Dawud suka ruwaito shi_ (Amman yanzu duk yadda aka samu yi ma mamaci ake indai ba an haɗu da masu illimi a gurin wankan gawar ba, Allah kasa mu cika da imani kasa ayi mana kamar yadda ma'aiki ya koyar)


A cikin gidan akayi masa salla, duk da yake gidan mai faɗi ne kuma ƙaramin yaro ne amman hakan be hana mutane da dama halartar zina'izar ba, wasu saboda Hilal wasu kuma saboda Hajiya wasu na ɓangaren Rashida ne wasu kuma dan gulma ne, saboda labari ya ishesu ɗan da kishiyar uwarsa tasa masa guba ya rasu, so that su samu damar bada labarin ai da su ma akayi salla yaron. Har da masu ɗaukar hoton gawar suna ɗorawa status duk da kasancewar wasu ƴan'uwane amman hakan be hana su yaɗa abunda suke ganin ya zame musu wajibi ba. Kan kace kwasi.har labarin mutuwar Rafiq ya cika social media, kowa sai faɗin albarkacin bakinsa ya ke, alhalin wasu basu sam komai akai ba.


Bayan sun tafi kai Rafiq ne maƙota mata suka shio cikin gidan, suka zazzauna tare da Rashida dake ta kuka kamar ranta zai fita suka bata haƙuri wasu kuma a ransu suke tsine mata suna faɗin wai kuna munafurci ne, daman wasu ganin fuskarta ya kawo su cikin har da Asmee Aminiyar Rashida.


Bayan sun dawo daga kai shi ne, mutane suka soma yi ma yi ma Kalsoom da Hilal gaisuwa. Tashi Kalsoom tayi ta shige ɗakinta ta bar su Hajiya falo dan duk sai ta tsargu da zaman Hajiya a falon.
Aikaws Hajiya tayi aka kira mata Hilal sai ta koma can ƙarshen falon ita da shi ta faɗa masa wai a maida zaman makokin a gidanta zai fi, shi dai to kawai ya amsa mata, dan ransa baya masa daɗi.


“To ita wannan yarinyar fa?”


“Hajiya a nan zata zauna ai kinsan Musulumcin ya yarda mace ta yi idda a gidan mijinta”


“Ikon Allah anya Hilal kana cikin hankalin kan ka? Wai wace hujja kake da ita ne na yarinyar nan ba ita ta aikata ba?”


Ajiyar zuciya ya sauke, dan har ga Allah be da abunda zai nunawa Hajiya a matsayin dalilinsa na ba ita ta aikata ba, shi dai a rantsuwar da tayi masa ya gamsu, kuma jikinsa na bashi ba ita ce ta aikata ba, wata ƙila dan yana sonta ne.
Ganin be ce komai ba yasa ta ce


“Zamu wuce can, idan ka gama lelenta sai ka kaita gidan su”


Juyawa ta yi ta koma gurin mutanen da suke zaune falon, shi kuma ya nufi ɗakin Kalsoom jiki a sanyaye.




ASIM POV.


Har yanzu bashi da damuwa akan abunda yayi ma Namra, shi yana nan yana jiran ta kira shi ko kuma ta aiko masa da saƙon ban haƙuri. Yana yawan waya da Nabila Nably da kuma Mardiya, a ɗan kwana ɗayan nan har ya saba da Nably kusan kullum sai sun yi waya sau biyar ko fiye da haka. Ya tura mata hotunsa ita ta turo masa, sai yaba kyawunta yake yana faɗin nan gaba kaɗan zai zo Abuja dan ta kawai.




Yau ya tashi da nishaɗin ɗaya kwana da shi tun jiya da dare da Hajiya Sadiya ta labarta masa zuwan baƙonsa. Yasan saɓon Allah ne zai aikata amman zuciyarsa a wanke take saboda burin samun kuɗin da Hajiya ta faɗa masa zai samu idan har ya sake jiki da mutumen. Suna breakfast ta ke ƙara nanata masa yadda zai masa da kuma irin shigar da zaiyi, already ta siya amsa turaruka masu kyau da tsada da zai saka.

A gida ya wuni duk da kasancewar ta yi nata bakin amman a ɗakinsa dan ta faɗa masa iɗan har tana da baƙi bata da buƙatar ya shigo gurinta idan ba wani babban dalili ba. A gida yyai Salla magariba bayan yayi isha'i ya shiga yayi wanka ya cuɗa jikinsa sosai kamar zai cire fatan, sannan ya fito jikinsa sai ƙamshin sabulan wankan yake kamar wanda ya saka turare, saboda tsadarsu, wasu ma ayau ya fara amfani da su.


Gaban madubi ya zo ya xauna kamar wani mace yana kallon jikinsa, tare da gyara gashin kansa. Mayuka masu kyau da saka laushin jiki ya shafa sannan ya bi jikin nasa da humra na maza sannan ya shafa wasu turarukan masu tafiya da imanin mutum ya shafe duka jikinsa. Sannan ya ɗauki wani baƙin jean ya saka da farar riga mai kyau, sannan ya ɗauki facing cap baƙa ya saka ya ɗauki wani turaren ya feshe jikinsa, da shi ya ɗauki lipstick ya shafa a bakinsa ka ɗan, sai kuma ya ɗauki baƙin madubin ido ya saka. Tsayawa yayi gaban madubi yana duba kansa da kansa, shi kansa yasan ya yi kyau mashallah, hakan yasa shi murmushi tare da ɗaukar kansa hoto.


Shigowar Hajiya Sadiya ne yasa ƴa ɗan natsu ya rage murmushin da yake.


“Wow...... Gaskiya Asim kana da kyau, kaga kan ka kuwa”


Ta taɓa masa gemu tana murmushin jindaɗin ganin yadda yayi kyau, har ya ɗauki hankalinta.


“Lallai za a je da kai Asim, wannan ƙamshi haka hhmnn ka iya business, to sai ka fito ga mota can ya aiko da dareba a ɗauke ka”


“To Hajiya”


Ya faɗa kamar a kumyace, sai kuma ya samu kansa da faɗuwar gaba. Ita kanta ta lura da yanayinsa na alamar tsoro ko kuma fargaba da ke cikinsa.


“Ka kwantar da hankalinka ka sake jiki ka ci arziki babu abunda zai faru, jeka mota na jiran ka”


“Okay”


Ya faɗa kana ya ɗauki agogon hannunsa ya saka, bayan ya ƙara fesa turare, ya nufu ƙofar fita. Ita kuma ta bishi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login