Showing 138001 words to 141000 words out of 281103 words
Chapter 47 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
ka sake ni a yau, irin sakin da aure ba zai sake shiga tsakanin mu ba, irin sakin da ko na so na yi tunanin zuciya zata hanani, irin sakin da zan manta da wanzuwarka a doron ƙasa, irin sakin da zai sa na cire ka a zuciya.
Ina roƙon ka Hilal karka horar da ni da irin horon da zan cutu, karka saka zuciyata cikin ramen da ba zata iya fita ba”
Tun da take maganar hawaye take, irin hawayen nan dake hana sautin kuka fita. Miƙewa tayi tsaye ta ɗauko takarda da biro dake gefen gadon ta zo gabansa ta aje masa gabansa, ta miƙe tsaye ta bar ɗakin.
Notebook ɗin ya tsurawa ido yana nazarin kalamanta.
Wanka yai ya shirya cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da turare, sannan ya ƙaraso gurin gadon ya ɗauki takardar yayi mata rubutu, ya naɗe ya ɗauki kayansa ya fito.
Ɗakin Kalsoom ya shiga, sai ya same ta zaune ƙasan gado tana rusar kuka. Tsayawa yai cak yana sauraren kuka nata dake shiga har cikin zuciyarsa, be san dalili ba duk da abinda Kalsoom ta aikata masa still yana son a zuciyarsa, har yanzu natsuwarta da yadda take gudanar da al'amuranta burgeshi ya ke. Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ƙarasa cikin ɗakin ya miƙa mata takardar.Idonsa na shiga cikin nata gabansa yayi mugun faɗuwa, ta rame sosai kamar ba ita ba, ga wani ja da idonta yai, kamar ta saka garwashi a ciki, a take tausayinta ya rufe shi. Ita kuma ta sakarwar takardar ido sai kallo take tana tsoron karɓa, ta haɗe yawu ya fi a ƙirga kamin ta miƙa hannunta dake ɓari ta karɓi takardar.
“Na gode Allah ya haɗa ka da mata ta gari..”
Cikin sarƙewar murya ta faɗa bayan ta karɓi takardar. Har ya buɗe baki yai magana, sai kuma ya fasa ya juya ya fice.
A jikim mota ya tarar da yaransa suna jiransa. Yana shiga suma suka shiga, har suka isa scul ɗin Ulfah bata daina tambayarsa ina Rafiq ba, sai dai be amsa mata ba dan be san me zai ce mata ba, Hilal irin mutanen nan da idan matsala ta shiga tsakaninsa da iyalansa baya son kowa ya ji, har yaransa, dan aganinsa ba muhallinsu ba ne.
Ƴan canji ya zaro a aljihunsa ya miƙa musu, sannan ya kama hanyar asibiti yana neman number Rashida daya saka a blacklist ya kira ta. Ta daɗe tana ringing kamin ta ɗauka, dan sai da ta tabbatar ta tantance cewar number Hilal ɗin ce sannan tai picking.
“Ki janye maganar kotu nan”
Shine abinda ya fara faɗa mata, a tunaninta zai bata haƙuri ne ko kuma yai mata wata maganar ta daban.
“Ba zan janye ba, ba za a dake ni a hana ni kuka ba, ba zaka cutar da ɗana kuma ni ka hanani ɗaukar mataki ba”
“Ɗan ki ko ɗa na? Bakin ki yana kurkure gurin faɗar kalmar nan”
“Ai da ɗan ka ne da baka ce za ka goyi bayan ta ba, wai har ka kace zaka tsaya mata bayan ita ce take ƙoƙarin aika ɗan ka lahira, dan kawai ta mallake ka”
Ya taka burki.
“Kar ki soma faɗa min maganar banza, ni ba wawa ba ne irin ki, kuma na faɗa miki ki janye zancen kotunan ko kuma na faɗawa duniya dalilin sakin ki da na yi kuma try me ki gani”
Be tsaya jiran abinda zata ce ba, ya kashe wayar. Sai ya kira wayar Alh Bashir sai da yai masa two missing calls sannan ya ɗaga, Hilal be tsaya jiran komai ya ce
“Idan kana son shiga cikin maneman Rashida ka shiga kawai ba sai ka riƙa ɗaukar maganar da muka yi ba ka kai mata, wannan ba girman ka ba ne”
Ya katse wayar ya jefar a front seat yana wani huci da bugu sitarin motar.
*RASHIDA POV*
Mamaki ya isheta, yadda Hilal ya juye ya zama maƙiyinta, mutumen da ko a mafarki aka ce zai mata zata musa, balle kuma a fili.
“Lallai na yi sake da har na bar ka ka auri wata ban mallake ka a lokacin ba, Kalsoom ki biya bokan ki haƙiƙa ya iya aiki. Zan janye maganar kotu, amman kuma dukan ku sai kun ƙwamace kiɗa da karatu...! Wallahi wasan yanzu aka fara, Hilal sai ka zo da kan ka ka nemi yafiya ta, Wallahi zan aikata ko minene matuƙar buƙatana zata biya... Sai na banbance muku aya da tsakkuwa”
Tashi tai tsaye ta cigaba da shirin zuwa office da take zuciyarta a dake irin na masara imani ɗin nan, dan a yanzu babu imani a kusa da inda take ma balle ace kusa da ita.
Sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauki jakarta da keys ɗin mota ta fito falo, already tai breakfast tun 6:30. Ɓangaren Mahaifinta ta nufa dan har Momy tana can. Cikin ladabi ta shiga ta samu guri ta xauna ta gashe su sannan ta ɗora da..
“Daddy zan janye maganar kotu nan, mu barta kawai da Allah”
“Wallahi kin yi tunani Rashida, nima abunda naga yafi kenan, indai cin amana ne baya taɓa ɗaurewa, Allah zai nuna mata sakamakonta tun duniya”
Momy ta faɗa cike da jindaɗin hukumcin da Rashida ta yanke. Dady yaja dogon tsaki.
“Ku kan Allah ya waddaran zuciyarku komai sai a ace a bari ga Allah? Ai musulucin ya ce idan an yi maka cuta ka rama gwargwadon abunda aka yi maka idan ba zaka iya yafewa ba, sannan irin wannan abun bw kamata ace a ba ga Allah ba, sai fa anje lahira kenan fa? Haba ai ƙara ayi mata tun duniya ta kunyata dan Wallahi idan yai wasa har shi sai nasa an kulle”
“A'a Alhaji ya kake magana kamar ba mai tunani ba? Haka sam be dace ba, hukuncin data yanke shine dai-dai”
Ya kawarda fuskarsa daga ta Momy ya kalli Rashida dan a tunaninsa ko Momy ce tayi mata wannan shawarar.
“Ke kina son abi miki kadin yaron ki?”
Ta girgiza kai.
“A'a Abbah na janye, na barta da Allah”
“Akan me?”
“Kawai haka naga ya fi”
“To ni zan bi kadin jika na (grandson) idan ku baku san abunda ake kira da humanity ba, ni na sani... Tashi kije office Allah ya kiyaye hanya”
Ba zata iya musawa Dady ba kar ya zargi wani abu, sai dai zuciyarta bata so haka ba, dan babu banbanci mahaifinta ne yasa ba ita ba. Tasan Hilal zai iya cewa wani sabon salo ne ta mayardar shari'ar gurin Mahaifinta.
A hanyar ta zuwa office ta kira Mom Shuraim, bayan sun gaisa take faɗa mata idan ta tashi daga aiki zata biyo ta gidanta, akwai magana mai muhimmanci da zata yi da ita.har da narke murya tana faɗin wai tana cikin matsala, amman dai sai tazo zata ji komai.
*ABDOOL POV*
Sai ten ya tashi bachi, dan yana yin sallah azuba ya koma bachin gajiya, farkawar da yayi ma a yanzu ba dan ya gaji da bachi bane, sai dan son zuwa gurin da Ummi tayi masa magana ne jiya. Be fito part ɗinsa ba sai da yayi wanka bugaggar shadda mai tsana blue color, ta fito da shi sosai kasancewar fari sol, ga ɓaƙar hulal da ya ɗora akansa kamar wani sabon balarabe,baƙaƙen takalmi ya saka sannan ya feshe jikinsa da turare, ya fito daga part ɗinsa ya nufo part ɗin Ummi shaddar har amsawa take a jikinsa, ga wani maiƙo da take kamar an zuba mata mai.
Ita kanta Ummi sai da tayi murmushi ganin yadda ɗan nata ya fito mashallah kamar ta cinye abunta.
“Ina fatar ka yi addu'ah”
“Addu'ah me?”
“Idan mutum yayi kwaliya ya dubu kansa a madubi yana kyau yace Mashallahu laƙuwwati illa billah, to ko wani yayi maka baki (kanbun baka) Ba zai kama ka ba, idan ma zaka ita ka riƙa karantawa da safe kullum sau uku”
Dariya yayi yana kallon cucumber da Ummi take yankewa ya ɗauki ɗaya ya ci.
“To ni da ba mace ba miye na wani kanbu zai kama ni, amman dai zan riƙa yi”
“It better”
Ya faɗa tana cigaba da yanka cucumber take. Shi kuma ya zauna kusa da ita yana tambayarta yaje yanzu ko sai anjima.
Ƙamshim turarensa ne ya isarwa da Amira saƙon isowarsa a falon. Ras! ras!! ras!!! Ga banta ya faɗi kamar yadda ya basa mata a duk lokacin da ta ji ƙamshin turarensa. Da sauri ta walƙato ta sauko daga saman gadon da take ta nufo falon idonta cike da maitar ganin Abdool kamar bata taɓa ganinsa ba.
Cikin wata irin siga take tafiya, takalmin dake ƙafarta plate ne amman hakan be hana su amsa amon gurin ba saboda yadda take buga da tiles ɗin gurin. Ummi ce kawai ta ɗago ta kalleta wanda kuma ita bata so haka ba. Abdool kam ƙin ɗagowa yayi dan sarai zuciyarsa ta raya masa Amira ce, dan yasan by this time duka ƙanensa suna makaranta.
“Ina kwana”
Ta gaishe shi cikin ladabi har tana son risina masa.
“Lafiya”
A kaikaice ya amsa, yana mai miƙewa tsaye. Wanda hakan be ma Ummi dadi ba,sai kawai ta kada baki ta ce.
“Amira shiga ciki ki ɗauko mayafin ki ki rana yayanki unguwa”
Ta fasa zaman da zata yi ta miƙe ta nufi ɗakin data fito. Sai da ta shige sannan Abdool.ya kalli Ummi yana ware hannayensa ya ce
“Haba Sweet Mom ya za ki min haka? Kin san fa ni Allah be haɗa jinina da mata ba, kuma it so annoying naje da ita unguwa”
Wani Kallo Ummi ta masa.
“Abdool... Karka soma halin Amal, tun da yarinyar nan ta zo kullum tana ciki gida bata fita ita ma ai ƙara ta ga gari ko?”
Be ƙara cewa komai ba ganin Amira ta fito, sai kawai ya jiya ya nufi kowa yana wani shan ƙamshi.
Ko da ta isa har ya tashi motar ita kawao yake jira su wuce. Tana shiga ya fisgi motar kamar baya son ransa har sai da Amira ta tsorata.
Bata ce masa ba, shi ma be ce mata ba haka suka yi ta tafiya har suka isa nasarawa. A bakin gate ɗin gidan yayi parking ya fito yana ƙarewa gidan kallom ganin yadda ya kone.
Yana rufe gambun motar Amira ta buɗe ta fito, sai ya kalleta ya ce
“Ba daɗewa zan yi ba, kina iya zama a cikin kamin na dawo”
Ba musu ta koma cikin motar ta zauna, zuciyarta cike da tunani kala-kala.
Baya tunanin akwai mutane a gidan dan Ummi bata faɗa masa ba, hakan yasa be yi sallama ba ya tura kofar gate ɗin kawai ya shiga ciki. Gaban gidan ya fara dubawa kamin ya zagaya baya, tana nan ya hango mace tana girki a BQ. Hannayensa yasa aljihu ya nufi bq ɗin yana sallamar da kusan shi kaɗai ne zai iya jinta, sai kuma wanda yaga bakinsa ya motsa.
Namra na ganin mutum tayi saurin komawa ciki ta ɗauko hijabinta ta saka sannan ta fito. Ko da ta fito har ya ƙaraso bq ɗin yana ƙare ma bq ɗin kallo dan ita bata yi komai ba.
“Haba Malam waye kai zaka shigo babu sallama”
Dago da dubansa yayi gurin mai maganar. Ganin Namra yasa numfashinsa hijira daga jikinsa ma ɗan wasu daƙiƙu, sannan ya dawo. Be ɗauke idonsa daga gareta ba be kuma kyafta ba, haka ya ƙafe da ido kamar wani hoto. Nan da nan zuciyarsa ta soma rabawa jijiyoyin jikinsa jini da ƙarfi.
Rassss rassss rassss gabansa yake faɗuwa, sai dai kuma ba irin wacan faɗuwar ba, ta tsoro ko fargaba, faɗuwar gaba ne da shi kansa ba zai iya fassara na minene ba.
Ita sai yanzu ta gane ko wanene shi, daman tun ɗazu ta ga ganin kamar fuskar sani, mutume daya bita asibiti. Ƙamshin turaresan ya haddasa mata ciwon kan da bata yi zato ba, daman tun jiya bata cikin daɗin rai.
“Subhanallah malam wannan kallo ya haramta a musulumci”
Daɗin sautinsa yasa shi lumshe ido yana murmushi.
‘A'uzubillahi minal sheidanin rajin’
Ya furta a zuciyarsa yana ƙoƙarin da abunda sheiɗan yake son masa, sannan ya buɗe ido ya haɗe fuska kamar be taba dariya ba.
“Su waye ku?”
“Mu ne waɗanda suka kama hanyar wannan gidan”
Ta amsa masa a gautse.
“Bq kuka kama ko Main house”
“Main house muna ciki aka yi gobara sai muka dawo nan da zama”
“Ina mijin ki?”
“Baya nan ya tafi kasuwa”
“To idan ya zo ki ce an baku one week ku tashi za ayi gyaran gidan”
Gabanta yayi mummunan faɗuwa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi dan Allah ku gyara babban gidan sai ku bar mana BQ ɗin wallahi ba mu da gurin zuwa idan muka bar nan, dan Allah ku taimaka mana”
Ta haɗe hannayenta idonta na son cika da ƙwalla.
“Da yaushe ake tarar da mijin ki?”
“Da safe ko kuma da dare guraren goma”
“Okay zan zo na yi magana da shi gobe”
“Allah ya kai mu na gode”
Be sake cewa wani abu ba, ya juyo hannayensa zube a aljihu ya fito gidan. Har lokacin Amira na cikin mota zaune tana jiransa, yana shiga motar yayi mata key suka juya. Wannan karon ita ce ta ke ɗan jansa da fira shi kuma jikinsa duk ya mutu baya ma iya amsa mata. yawancin tambayarta akan gidan ne da kuma unguwar, sai kuma yaba garin Katsina da take. Shi dai har suka isa gida sai dai ya ɗaga mata kai kawai.
Ta rigashi fita daga motar, dan yau ranta fes yake ta ta fita tare da sahibinta. Bata tsaya a falo ba sai kawai ya wuce ɗakinta tana ƙoƙarin ɓoye nishaɗinta. Shi kuma ya zauna a falo, kusa da Ummi da take zaune a inda ya barta ɗazu, sai dai wannan karon ita da Shukura ne kuma carrots take gyarawa.
“Har kun dawo?”
“Yeah ai ba wani nisa”
“Kaga gidan ko?”
“Eh duk ya lalace idan aka ce za a gyara shi sai anci kuɗi kam ”
“ Ai dole a gyara shi tun da gidan marainiya ce, a ciro kuɗinta ayi mata gyaran, daman kasan Amal bata da daɗi ta matsa min tuni kamar ni ce na ƙone gidan.Yanzu sai ci nawa idan za a gyara shi?”
“A lot, nawa kika siya mata shi?”
“Ba da kai aka yi cinikin ba, da Alhaji Ƙasimu da Mansur”
“Kai ai bana iya tunawa kin san abu da yawa”
“Nine million aka siye shi”
“Na siya 15 million”
Ummi tayi saurin dubansa.
“Joking abii?”
“I'm serious wallahi na siya”
“Ba zamu siyar ba”
“Saboda me?”
“Muka sani ko zinari aka gani a gidan zaka mana wayo”
Ta faɗa tana tashi ta nufi kitchen, dan ga dukan alamu yai da kanta zata yi girki. Dariya Abdool yayi ya cire hular kansa ya jingina da kujera yana faɗin
“Indai Amal ce ai abu mai sauƙi ne”
Lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya. Babu wacce yake gani sai Namra, da sauri ya buɗe ido ya tashi ta nufi Gardem.
FIVE READ MORE.....🙌🏻
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *57*
Bata taɓa sanin haka jikin da zuciya suke ba idan wani abu marar daɗi ya faru da mutum sai yau. Duk tashin hankalin da ta shiga lokacin da Rafiq ya kamu da ciwo be kai wanda take ciki ba yanzu.
Wannan karon kuka ma yayi ƙaura daga idonta duniyarta sai juya mata take. Gani take kamar mafarki take ba da gaske ba ne Hilal ya miƙa mata wannan takardar.
Miƙewa tayi tsaye sai gata ta dawo xaune saboda rashin ƙarfin jiki, ga wani sanyi da take jin ƙafafunta sun mata.
Wani abu taji yayi mata tsaye a zuciya, hango kanta take a bazarawa, irin rayuwar da tayi ta budurci kuma yanzu ace aurenta ya mutu bayan bata daɗe gidan mijin ba. Takardar ta ƙurawa ido tana auna yadda Mominta zata ji.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi tai ta maimatawa sannan ta samu ƙarfin jiki, har ta unƙura ta tashi. Durowarta ta buɗe ta ɗauki canjin da yake ciki da Atm ta saka a jikarta tare da takardar ta saka hijabin ta fito falo. Saman kujera ta zauna tana maida numfashi kamar wanda tayi gudun fanfalaƙi. Hannu ta kai ta rufe bakinta saboda kukan daya zo mata gadan-gadan.
Sai dai hakan be hana hawayenta zuba ba, ashe da gaske hawaye suna da zafi, sai a yau ta tabbatar dan yau ta ji hawayenta kamar ruwan zafi.
“Me yasa zan yi kuka akan abunda ba zai sauyu ba? Miyasa zan kuka akan mutumen daya zaɓi rabuwa da ni? Anya Hilal ya cancanci hawaye na?”
Sune tambayoyin da tayi ma kanta a fili, sai dai har ta tashi ta kai bakin ƙofar falon bata samu amsarsu ba. Kamin ta ƙarasa gate ta gyara fuskarta, ta goge idonta da Hijabin gudun kar wani ya gani ya zargi wani abu.
Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, sai da ta shiga sannan ta faɗa masa inda zai kai ta. Har suka isa estate ɗin su idanuwanta basu daina cika da ƙwallah ba.
Tana biyan Mai Napep ɗin ta shiga gida hawaye na bin fuskarta. Bata samu kowa a falon ba, daman by this time ba zata samu kowa a gidan b Sai Momynta. A saman kujera ta zauna ta haɗe kai da gwuiwa tana kuka. Sautin kukanta ne tashi daga bachi da take ta fito da sauri falo. Ganin Kalsoom ya tashi hankalinta, tasan da maganar kotu da Rashida ta sata amman bata zaton shine zai sa Kalsoom wannan kukan bayan ko kotun ba'a shiga ba. Kusa da ita ta zauna tana ƙoƙarin ɗago kanta.
“Ke miya same ki?”
Ɗagowa tayi cikin kukan ta rumgume Mominta. Girgiza Momi tayi
“Ke ki min magana mana, waya mutu? Ko Rafiq ɗin ne ya mutu?”
“Ni ce Momi Hilal ya sake ni...!”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me kika masa?”
Kasa magana tayi sai kuka take kamar zata shuɗe, Momi ma hawaye take, ita kanta bata jidaɗin maganar da Kalsoom ta faɗa mata ba, babu mace da zata so auren ƴarta ya mutu sai dole, balle Kalsoom da aka samu aka yi auren daker.
“Ya isa bari kuka, aure rai ne da shi idan lokacin yin sa yayi sai an yi, idan kuma mutuwarsa yayi dole ya mutu, ki kwantar da hankalinki”
Ta faɗa tana share mata hawaye, sai dai kuma ita na ta hawayen ba su daina zuba ba. Daker Momi ta lalaɓa Kalsoom tayi shiru, har ta shiga ɗakin Momi ta kwanta, kanta sai sarawa yake, ga wani ɗan banzan nauyi da yayi mata kamar an ɗora mata dutse, idonta kuma har ji take kamar ƙasa ce a ciki.
Momi kan cikin rashin kuzari