Showing 171001 words to 174000 words out of 281103 words
Chapter 58 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
da kallo tana murmushin jindaɗi.
ABDOOL POV.
Da wuri yyi breakfast gurin Ummi saboda tafiyar data zame masa ta dole, dan tun cikin dare Mai Martaba ya kira shi ya faɗa masa ya tura tawarga da za su je tare tun da rana, shi kuma zai bi jirgin safe ya sauka kaduna, dan da ƙarshe biyu za a ɗaura aure, so zai sauka da wuri dan ya samu ya huta ta kuma kimtsa cikin lokaci.
Duk cin abincin da yake idon Amira na kansa, irin kallon take masa na rasa yadda zan yi da kai. Sai dai bata bari ya ganta ko kuma Ummi ta ganta duk kallon da take ƙasa ƙasa take masa shi wanda ba kasafai mutum zai kula ba.
“Dude za ma zaka je da ni”
Amal ta faɗa tana ƴar dariya tare da kallon Ummi.
“Yaje dake ya aje ki ina? Shi da zai je ɗaurin aure kuma”
“To yau Assabar ba aiki”
“Ba shi na ke magana ba, yau zai je yau zai dawo”
Ummi ta amsa tana cin wainar ƙwai. Daman duk weekend sune suke rigan karyawa, sauran ƴan matan gidan duk sai dai su yi ta kwanan gajiya.
Agogon hannunsa ya kalla sai yayi saurin miƙewa tsaye yana dire kofin tea ya ce
“Ummi ayi mana addu'ah”
“To Allah ya tsare ya kiyaye hanya”
“Amin ya rabb, dude sai na dawo ko?”
“To Allah ya tsare”
Ta ɗaga masa hannu. Har ya juya sai Amira ta kira shi.
“Ya Abdool”
Yana juyowa ta miƙa masa tissue paper dan ya goge bakinsa. Hannu ya kai ya karɓa yana murmushi.
“Thank you. Sai na dawo”
“Allah ya tsare”
Ta faɗa tana murmushi kamin ta biyo sawunsa tare da Ummi suka raka shumi har gurin mota. Sai da ya bar gidan sannan suka koma ciki.
Goma da rabi na safe ya sauka kaduna, daga airport motocin Mai Martaba suka tarbosa, dukansu dagarawa ne cikin jajayen kaya sai bashi girma suke suna masa kirara, abunda ya tsana a rayuwarsa, shiyasa ya fi ƙaunar ya zo da a cikin motar Army's.
Yana shiga motar suka kama hanyar masaukin Mai Martaba da ke kaduna, dan acan zai huta sannan ya shirya su ɗauki hanyar Zaria. Jaridar dake cikin motar ya ɗauka yana duba, sababin labarai ne a cikin. Akwai labaruka kala-kala na abubuwan da suke faruwa a nigeria da kuma na ban aljabi.
Kerrrrr motar dake gabansu ta taka burki, sai direban dake jan Abdool ya tsayar da motar da suke ciki. Abdool be damu daya tambaye dalilin tsayawar motar ba, shi dai hankalinsa gaba ɗaya ya tattara ya koma kan jaridar.
Ɗaya ɗaga cikin dogaran da suke motar gaba ne ya zo ya ƙwanƙwasa ma direban dake tuƙa Abdool da kuma dogarin da ke front seat. Zuƙe gilashin motar dogarin yayi yana sauraren abunda ɗayan dogarin yake ce masa.
“Subhanallahi”
Kalmar da diriban motar yayi ne ya ɗago da hankali Abdool a izuwa gare shi.
“Ran Yareema ya daɗe, wani mai Napep ne aka kaɗe”
Dogarin dake front seat ya faɗa 6ana ɗaga ma Abdool hannu irin girmamawa nan.
“Garin yaya?”
Dogarin dake tsaye jikin motar ne ya amsawa Abdool.
“Allah ya taimaki Yarima Kutse yayi mana, yyai aron hannu ne mu kuma zo da gudu. Amman za'a wuce da kai gida ne mu sai mu ji da da shi”
Uffan Abdool be ce ba, sai kawai ya aje jaridar dake hannunsa ya buɗe motar zai fita, da saurin sauran dogaran duk suka yo kansa, na gaban yayi sauri buɗe gambun motar wa Abdool yana mai girmamashi.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *65 NOT EDITED⚠️*
*ASIM, AMIRA, MARDIYA, UZAIR, RASHIDA. Duk suna muku barka da sallah 😂*
Da ƙarfi take cije bakinta, tana mulmula saman tabarma dake ɗakin, sai faman rumtse ido take tana buɗewa, ita kaɗai tasan irin zugin da take ji.
Hawaye ne ya fara mata zuba, lokacin da ta ji abu mai ɗumi ya fara bin ƙafafunta, bata buƙatar a faɗa mata abunda yake shirin faruwa da ita, tasan abunda yake cikinta yake ƙoƙarin rabuwa da ita, sai dai ita kam har ga Allah bata shirya rabuwa da shi ba, dan tana jin kamar shi kaɗai ne mafita a gareta, ko ba komai bata son ta mutu bata bar abunda za a kalla a riƙa tuna ta ba. Babu banbanci tsakanin wacan ciwon da ta ji da kuma wannan, sai ma jin da take kamar wannan ya fi tsananta masa.
“Innalillahi wa'inna ilaihi”
Shi ta samu ta furta da ƙarfi tana ƙoƙarin fita hayyacinta. Kana ganin yadda take yaƙi da numfashinta, kasan tana da buƙatar ratuwarta, wata ƙila saboda wasu dalilai na ta na karan kanta, ko kuma saboda cika wasu kuɗirinrika da suke gabanta.
Lokaci zuwa lokaci numfashinta yake barin jikinta, sai ta yi hanzarin dawowa da shi tana sauke ajiyar zuciya da ƙarfi.
Uwani ce ta shigo ɗakin da sauri tana tambayar.
“Lafiya Namra?”
A yanayin yadda ta ga Namra yasa ita ma ta furta innalillahi tana riƙa ta.
“Inna waurei”
Ta faɗa da yaren fulatanta tana mai ɗaga murƴa ta yadda Neina zata ji ta. Aiko sai ga Neina cikin ɗakin da gudunta har da ɗayar maƙociyarsu mai ganin sanin abunda yake faruwa, Maryam ma tana bayansu tare da ƙanenta maza.
Neina na ganin halin da Namra take ciki ta yi saurin kora Maryam da ƙanenta da kuma maƙociyar waje, ta sauke ƙyauren ɗakin.
cikin ƙarfin hali ta riƙa Namra, tana ƙoƙarin zame mata uwa a wannan lokacin, aiko nan Namra ta kama hannun Neina ta riƙe gam tana hawaye.
“Sannu ƴata sannu Allah kawo miki sauƙi, uwani ki je ki ɗibo mana lafiya dubu da wasu itatatuwan gidan su Mama a'i”
Neina ta faɗawa Uwani tana kallon Namra cike da tausayawa. Cikin sauri uwani ta tashi ta fita, bata ɗauki lokaci ba sai gata ta shigo da ruwa a kwano daga ta dire gaban Neina daga bisani ta miƙa mata ganyayyakin. A cikin ruwan Neina ta mirza su, ta miƙawa Namra, daker ta ɗan kurɓa kaɗan, sannan Neina ta shafa mata lafiya dubu a goshi, sai ta maida kwanon ta aje gefe da taimakon Uwani suka riƙa ta ta miƙe tsaye.
“Tashi muje banɗaki”
Tana fara takawa jiri ya ɗibeta sai ta rafke a gurin ta faɗi ƙasa. Hakan yasa Neina ta tura ƙofar ɗakin, ta rufe gudun kar wani ya shigo.
Gaba ɗaya idonsa da hankalinsa ya tattara ya koma kan ƙofar ɗakin, baya buƙatar a faɗa masa komai tun shi ba ƙaramin yaro ba ne, tun daga yanayin ihun Namra da ya ji da kuma gayyen da ga Uwani ta samo, yasan abunda yake faruwa. Wani irin tausayinta Namra ne ya lulluɓe masa zuciya, gaba ɗaya ya manta da nasa ciwon, he feel her pain, masu shigo suna masa sannu ma ba jinsu yake ba, sai dai ya amsa masu sama-sama, dan gaba ɗaya hankalinsa yana can, ga masu shigowa sai tambayar Neina suke daga shi har su Maryam babu wanda ya iya furta ga inda take, sai duk suka yi kamar bata cikin gidan. Hankalinsa ya fara tashi ganin an ɗauki lokaci, daga Neina har uwsni babu wanda ya sake leƙowa, ya san duk wani abu da Neina zata mata ba zai kai na asibiti ba.
“Maryam zaki iya zuwa bank ki ciro kuɗi?”
Ya faɗa yana kallon Maryam ɗin dake zaune kusa da shi. Kai ta girgiza masa alamar a'a.
“Okay je gidan su Mustafa ki ga idan yana nan ki ce masa ya je ya samo mota kuma ya ciro min wannan kuɗin sai a kaita asibiti”
Ya miƙa masa takardar kuɗin da Yarima ya bashi na one million. Zuwa tayi ta karɓa sannan ta sakata cikin hijabin dake jikinta ta nufi ƙofar fita. Bata ɗauki lokaci ba sai gata ta dawo sai faman sauri take.
“Baya gida”
“Aro min wayar uwani na aro wayarta na kira shi”
Miƙa masa takardar ta yi sannan ta nufi ɗakin tana buga ƙofar.
Daga can cikin ɗakin Neina ta tambayi waye, sai Maryam ta amsa da.
“Ya Lamido yace Uwani ta aro masa wayarta zai kira mustafa a kai Namra asibiti”
“Ai ba sai anje asibiti ba, Allah ya kawo mata sauƙi”
Buɗe ƙofar Neina ta yi, sai ga Namra tana takawa a hankali Uwani na riƙe da ita an ɗaura mata zane saman wani zane suka fito. Kallo ɗaya Lamido ya yi mata ya ɗauke kai be sake kallon inda take ba, har suka shige banɗaki.
Har cikin ransa yake aiyana irin zafin da Namra ta ji, a take wani irin tausayinta ya lulluɓe masa zuciya, idan kuma ya tuna irin rayuwar da ta fito ciki sai yaji kamar ya zubar mata da ƙwalla.
Uwani ce ta taimaka mata wajen gyara jikinta, sannan ta fito ta ɗauki kuɗi cikin jakar Namra ya aika Maryam ta siyo mata Pad, sai ta bi ta gidan maƙotansu ta karɓo mata bashin pant guda huɗu hannu Sadiya mai haja.
Neina ta gyara ɗakin sam kamar ba ayi komai ba, sannan taje ta ɗora mata ruwan wanka masu ɗan ɗumi ta kai mata banɗakin ki. A nan ne uwani ta bar mata banɗakin dan ta yi wanka.
Ta ɗan samu ƙarfin jikinta lokacin da ta yi wanka ta saka pad sannan ta ɗauki zanen da Uwani ta ɗora mata saman ƙofar banɗakin ta ɗaura ta saka hujabi, ta ɗan ɗauki lokaci zaune a banɗakin sannan ta unƙura ta fito. Da sauri uwani ta zo ta riƙa ta suka nufi ɗayan ɗakin da su Maryam suke kwana.
Saman katifar ta kwanta idonta tab da hawaye, tausayin kanta take ji irin ƙaddarar dake faɗa mata ɗaya bayan ɗaya, idan ta fita wannan sai kuma wannan. Bata da tabbacin cikin ya zube gaba ɗaya amman a yadda taga tsare tsaren jini bata zaton akwai abunda ya yi saura a cikinta. Bata bari Uwani taga hawayen da suka zubo mata ba, har sai da ta fita sannan tasa hannu ta shafa cikinta, tana tuna dalilin barin gidan Asim saboda cikin da yanzu babu shi, kuma bata da madafa, dan ba zai yiyu ta zo ta zauna musu a gida haka nan kawai ba, sai dai har yanzu tana tsoron komawa gurin Abbah, to tace masa me? Mutumen daya ce kar tayo fushi ma balle kuma saki ya shiga tsakaninta da Asim.
“Ba adili ba ne”
Ta furta a fili zuciyarta cike da ƙololon baƙinciki, tana tuna irin hallacin da tayi masa yayi mata wannan sakamakon.
Kai kawai take iya girgizawa tana tuna yadda ta rabu komai nata saboda shi, shi kuma a yau ya butulce mata. Dafata da Maryam tayi ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da take.
“Ki yi haƙuri Allah zai sake baki wani”
Kai ta ɗaga mata, tana mata kallon wacan Maryam ɗin ƙanwarta.
“Haka ne, babu abunda bata faɗa min ba, amman na ƙi na yarda na riƙa ƙaryata ta, yau gashi na ga komai daman duk wanda ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba”
Da kuka ta ƙarasa maganar kamar wanda bata cikin hayyacinta. Maryam ta girgiza ta.
“Namra lafiya kike kuwa?”
Da sauri ta ɗaga mata kai tana ƙoƙarin share hawayanta.
“Lafiya ta ƙalau”
“Tau ga Maltina nan Ya yace ki sha da madara, mustafa zai karɓo kuɗi a kai ki asibiti”
Ta faɗa tana dire mata gwangwanin maltina guda biyu da madara.
“Ba sai an kai ni asibiti ba, na gode sosai Allah ya saka muku da alheri”
“Amin”
Maryam ɗin ta miƙe tsaye ta bar mata ɗakin. Dawowa tayi gurin da Neina take zaune da Uwani da Lamido, suke zaune ta zauna tana faɗin.
“Tace wai ba sai an kaita asibiti ba, ta gode Allah ya saka mana”
“A'a ba za'a barta haka ba kam, bari dai mustafa ya dawo”
“Ai taji sauƙi Lamido ko ba a kai ta ba, ko minene a cikinta be nina ba”
Neina ta faɗa, Lamido ya kaɗa kai.
“Ƙara dai aje asibiti nan ba zasu rasa abunda zasu mata ba”
“Kuɗin zaka ɗauka ka kashe kuma? Lamido kana ganin Napep ɗin nan taka ta lalace an baka ka siya wani ka samu na jari sai kuma ka ce zaka kashe”
“Haba ai kuɗin yayi yawan da ba zan iya kashesu duka a maganin baiwar Allah nan ba, kuma ko duka za a kashe mata wallahi zan iya badawa, kai ko Napep ɗin ce zan iya siyarwa dan nemaw yarinyar nan lafiya, wallahi mugun tausayi take ba ni”
Daga Uwani har Neina kallon juna suke da mamaki. Maryam ce ma tayi ƙoƙarin magana.
“Lallai Yaya kana tausayin yarinyar nan, Allah dai yasa labarin gaskiya ta ba mu dan kasan duniya yanzu yadda take”
“Amman ta miki kama da wacce zata baki labarin ƙarya? Haba Mairo ki duba yanayinta mana”
Har Neina zata yi magana sai ga Mustafa ya shigo, sai kawai ta sauya maganar da amsa masa sallamarsa. Kusa da abokinsa ya zauna yana bashi labarin yadda suka yi a bank.
“Wallahi akwai layi sosai, kuma naga rashin lafiya ne shiyasa sai nace bari na dawo sai ayi amfani da abunda yake aljihuna in yado idan aka ciro kuɗin sai na ɗauka, kuma kasan manyan kuɗi ne ba zan iya zuwa ni kaɗai ba, kar abiyo ni”
Duk da Lamido baya jin dariya hakan be hana shi darawa ba.
“Wallahi kai dai Mustafa kamar baka yi boko ba, ko da yake karatun naka iya diploma ya tsaya, amman miliyan ɗaya indai ƴan dubu dubu ne ai ba wasu kuɗi ba ne”
Neina ta girgiza kai.
“A a nan Alhaji Isa ba dubu ɗari ya zo dasu gida akan haka aka kashe shi balle mai miliyan ɗaya, ni tun ranar da Allah ya yi ni ban taɓa ganin dubu ɗari biyar a idona ba, balle kuma miliyan ɗaya”
Mustafa ya amsa.
“Wallahi fa ai zamani ne ya riga da ya lalace shiyasa komai sai an yi kafa kafa da shi”
“Allah dai ya shirya mana, ko bana ma son ana faɗar an fashi kuɗi har haka da yawa”
Cewar Neina tana miƙewa tsaye. Uwani ta ce
“Ai babu wanda ya sani idan ba mustafa ba, tun da ba mu faɗawa kowa ba”
“Allah dai ya tsare mu”
Duk suka amsa da Amin har Maryam dake ƙoƙarin tashi ita da Uwani su basu guri.
Bayan sun wuce Mustafa ya kalli Lamido.
“Wallahi babu wanda ya faɗa min haɗarin nan da ka yi in ba dan daka kira ni ba”
“Toh ai ba wani abun daɗi ba ne balle a riƙa yayatawa, kuma ba a daɗe da yin abun ba, Allah ma dai ya tsare”
“Allah ya ƙara tsarewa, amman dai wannan ɗan sarki ko sarki zan ce Allah be yi shi da rowa ba har miliyan ɗaya! Kamar wanda be san zafin kuɗi ba”
“Ya za'ayi ya san zafin kuɗi? Iyayensu suna kawashe kuɗin ƙasa, yanzu dai idan ka fita ka biya ka biya bilya kuɗin maltina da madara na aika am karɓo mata”
“Okay maganar asibitin fa?”
“Tace ba sai an jibe kuma naga kamar Neina bata son aje, ƙara mu ɗan saurara tukuna”
“Okay yayi Allah bata lafiya, amman ƴar'uwar ku ce ko? Naga kamar baƙuwar fuska ce”
Shiru ya ɗan yi yana tunanin faɗawa abokinsa nasa, sai dai baya jin zai iya ɓoyewa mustafa komai, kamar yadda mustafan baya ɓoye masa, kuma yasan idan ma be faɗa masa yanzu ba zai faɗa masa gaba, ko kuma ƴan gulma su tsegunta masa.
Hakan yasa be ɓoye masa komai daga haɗuwarsa da Namra da kuma labarin da Namra ta ba su nata.
Shi kansa Mustafa ya girgiza kuma ya tausayawa Namra matuƙa. Babu ma abunda yafi taɓa shi kamar rabuwa da tayi da iyayinta.
“Ai kaji matsalar mata suna da ƙaramar ƙwaƙwalwa, dan me zaka rabu da uwayen ka kan saurayi?”
Lamido ya numfasa.
“Ai mutum baya iya tsallake ƙaddararsa, sannan mu kan mu maza muna da matsala, da yawa sai ki ga dan kuɗin gidansu yarinya ake son ta, ni ina mamakin irin mazan nan wallahi, haka kawai abun wani ya tsune maka ido, ni dai Allah be sa min irin wannan rayuwar ba wallahi”
“Ai irin ka irin ka kaɗan ne Lamido, ni ma nan idan na ga arziki ba zan ƙi bi ba, masu arzikin nan suke kawai suke watayawa, ka duba kaga tun yaushe ka gama digiri ka yo bautar ƙasa, amman aiki ya gagareka, yanzu da kai ɗan wani mai kuɗi ne, da yanzu kana can Abuja kana hanawa kana aiki a wani babban kamfani”
Ajiyar zuciyar Lamido ya sauke.
“Muma Allah be manta da mu ba, kuma kaga wannan sana'ar Napep ɗin da nake? Ni ta wadarta da ni kamin Allah ya buɗo min wata hanyar kuma”
“Allah ya tabbatar mana da alheri, amman babu wanda ya ƙi kuɗi”
“Ita yanzu kallo ɗaya zata yi ma duka mazan takalawa alhalin ba haka muke ba, dan bamu taru muka zama ɗaya ba”
“Uhm, rayuwar ce sai a hankali, Allah ya bata wani na gari, ya shirya tsakaninta da iyayenta”
“Amin Amin”
*ABDOOL POV*
```Yana tsaye jikin wani upstairs, ya hango ta tana wani irin gudu kamar zata faɗi, kare na biye da ita a baya yana mata haushi, da alama karen take ma gudun, bata ankara da ƙaton ramen dake gabanta sai kawai ta faɗa cikin kamar an jefata. Daga can cikin ramen ta ɗagowa Abdool hannu tana son ya taimake ta sai kuma take, shi kuma ya yi tsaye yana kallonta kamar zai je, kamar ba zai je ba.```
Firgigit ya farka daga ɗan kajeren bachin daya kwashe shi yanzu-yanzu.
Haƙi yake sosai yana maida numfashi, jin yake kamar a zahiri ne abun ya faru. kyakkyawan askin kansa ya shafa, ya lumshe ido ya buɗe yana kallon agogon ɗakin.
“Mtsssss mi zai sa ba zan yi mafarkinta ba? Bayan na kwanta da ita a raina? Why this? Miyasa na zurfafa akan yarinyar nan ne? I'm totally mad”
Ya unƙura ya tashi ya nufi bathroom, zuciyarsa na raya masa ba zai yi mafarkinta haka nan kawai ba, shi kumasai yaƙar zuciyar tasa yake yana ƙaryata ta, dan ganin yake idan har ya yarda da ita to zata kai shi ga hallaka ne kawai.
Sai faman faɗa yake ma kansa kamar wani taɓaɓɓe. Har yayi wanka ya fito mafarkin be daina tsaya masa a rai ba. Haka ya shirya cikin tufafi na alfarma, wata musulmar shadda ya saka har wani maiƙo take tana shining daya ya motsa sai shadda ta amsa amo, shaddar ta karɓesa sosai, ta zauna a jikinsa kasancewarta sky blue, shi kansa da ya kalli kansa a madubi sai da yayi murmushi.
Wayarsa ya