Showing 33001 words to 36000 words out of 281103 words
Chapter 12 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
janyo ledar dake gefensu ya buɗe ya ɓalle lemun dake cikin kwali ya ɗauko cup ya zuba mata. Duk yadda taso ta ci da kanta ƙin yarda yayi a dole ta haƙura yayi feeding ɗinta, ba dan tana jindaɗin yadda yake bata ba, abun ka da wanda be saba ba.
Bayan sun gama, ya riƙa hannun tana mursa lallen dake hannu tare da yaba.
“Amman wanda tayi miki lallen nan ta iya lalle gaskiya, yayi kyau sosai”
Yadda yake taɓa hannun nata yasa tsigar jikinta tashi. Duka hannayensa yasa yana luddar hannun nata, a ɗan space ɗin dake tsakanin fingers ɗinta yasa one finger ɗinsa yana mata tafiyar tsusa, sai kallon yanayinta yake, gaba ɗaya idonsa sun koma kamar ba nashi ba.
Janye hannunta tayi ta miƙe tsaye.
“Bari mu tashi mu yi sallah”
Murmushi yayi ya dantsi bakinsa, sannan ya tashi ya nufi bathroom ɗin.
Tun da sunayi sallah godiya be yarda ya kai hannunshi ya sake taɓa jikinta ba, in banda kayan bachi daya ciro a closet ya miƙa mata sai shima ya saka nasa. Sannan ya hau saman gadon ya kwanta ya bata baya, be juyo ba sai asuba.
Bayan sun yi Sallah, ta hau gado ta kwanta, shi kuma ya fita dan duba uwargidansa.
A kitchen yaji motsinta, hakan ba ƙaramin bashi mamaki yayi ba, da sauri ya nufi kitchen ɗin ba dan zuciyarsa ta yarda da ita ɗince a kitchen ba.
“Wow Pyar me kike yi?”
Ta juyo ta kalleshi da murmushi, fuskarta acan-acan da kwalliya kamar ita ce amaryar.
“Breakfast nake haɗa muku”
Ya zagaye ƙugunta da hannayensa, zuciyarta cike da jindaɗi.
“Seriously Pyar? Amman gaskiya kin kyau mana, so faɗa min jiya kin yi bachi?”
“Nayi bachi mana, ai nasawa rai na zan iya ne”
“Good girl”
Yaja hancinta, wanda hakan yasa ta dariya.
“Amman ni dai Doc Ina jin tsoro, kar yarinyar nan ta amshe min kai, wasu ba aure Allah suke ba burinsu kawai su fitar da matar gida su maye gidan da ƴaƴanta”
“No no no, wannan yarinyar ba irinta na auro miki ba, tana da tarbiya fiye da tunanin ki”
“Allah yasa”
“Amin”
Sai ta ɗago kai ta miƙa masa bakinta sukayi kiss, sannan ya rumgume ta a kafaɗa kamar wani ƙaramin yaro.
Har ta gama soya dankalin rumgune yake da ita ta baya, sai da ta fara jera kayan abincin sannan ya sake ta da nufin zuwa ya tashi Kalsoom.
Har lokacin bachi take hankalinta kwance. Da murmushi ya ƙarasa kusa da ita, zanen bachinta ya fara yayewa, yasa hannunshi ta ƙasan wandon bachinta ya soma shafa ƙafarta zuwa cinya.
Wani yarrr taji, sai tayi saurin buɗe ido ta tashi tana kallonsa. Murmushi yayi ya hau saman gadon ya ɗora kansa saman wuyanta.
“Good morning Queen ina fatar kin tashi lafiya?”
Kamin ta amsa ya zira halshensa yana lasar wuyanta, ya kai hannunshi saman ƙirjinta, ya soma murza breast ɗinta a hankali, lumshe ido tayi zuciyarta cike da ƙyamar abunda yake mata. Tana jin ya fara ƙoƙarin ɓalle bottom ɗin rigar bachinta tayi saurin riƙe hannunsa, ta buɗe ido ta tashi.
Sai shima ya miƙe tsaye yana murmushi.
“Je kiyi brush zamu ci abinci”
Bata tace komai sai kawai tayi murmushi, ta nufi bathroom, shi kuma ya fice ya nufi nashi ɗakin dan wanke bakinsa.
Bayan ta fito ta ɗauki mayafinta na jiya ta rufa a jikinta sannan ta nufi falon. A lokacin Hilal har ya hallara a dinning yana riƙe da hannun uwar gidansa.
Yadda taji abu ya soki zuciyarta sai taji kamar karta ƙarasa kusa da dinning ɗin, sai dai tayi ƙarfin halin ƙirƙirar murmushi ta ƙarasa tana gaisawa da Rashida.
Rashida da kanta ta zuba ma Hilal abinci sannan ta zuba ma Kalsoom, sai ta zuba ma kanta.
“Ina Ezzah?”
Ƙalsoom ta tambaya. Sai Rashida tayi murmushi tace
“Suna bachi around tara da rabi zasu je islamiya, idan na tashe su yanzu zasu dame mu ne kawai”
Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin zaunawa, zamanta keda wuya sai hawaye ya gangaro ta idonta ya wanke mata fuska, da sauri ta tashi.
“Am sorry”
Sai ta nufi ɗakinta. Sai Hilal yayi saurin tashi ya rufa mata baya. A take yanayin Kalsoon ya canja har ta haɗiye wasu yawu da ƙarfi, ta sauke ajiyar zuciya tana kallon yadda abincin ya fita ranta.
NAMRA POV.
Tara saura mintuna Namra ta saci jiki, ta nufi gidansu Azeema. Sai da ta kusa ƙarasa sannan wani tunanin yazo mata.
Sai ta yanke tafiyar ta dawo gida, a lokacin an buɗewa Abban gate zai fita, taji kunyar ganinsa sosai sai dai sa'arta ɗaya dawowa ne tayi ba fita ba da fita ne da me zata ce masa?
Lokacin data kawo kusa da shi ya zuƙe gilashin motarsa yana mata wani kallo.
“Daga Ina mike?”
Ta ɗanyi jikiri gurin bashi amsa saboda tunanin ƙaryar da zata masa.
“Az- Azeema ce bata da lafiya shine yaje na dubata”
“Da izinin wa?”
“Anty”
“To kar na sake ganin kin fita ke kaɗai”
Be jira amsar ba ta ya ɗagarda gilashin motarsa, direba ya jashi yayi suka yi gaba.
Ta hanyar kitchen ta biyo ta shigo falo, sai rabon ido take idan wani be ganta ba.
Al-hamdulillah falon ba kowa hakan ya sata jindaɗi, cikin natsuwa ta nufi ɗakin Anty Amarya.
“Wa'alaikissalam”
Ta amsa sallamar Namra a yayinda ta aje kofin tea dake hannunta saman bedside drawer.
Kusa da ita Namra ta zauna tana tauna maganar da zata mata.
“Anty kin ga jiya ai Maryam ta bani wasiƙa ko?”
“Uhm”
“Asim ne ya bar min ita wai yazo be same ni ba, shine ya rubuta min number wayarsa, sai na kira da wayar Maryam, yace min mu haɗu a gefen gidansu Azeema”
Anty Amarya ta girgiza mata kai
“A'a ke yanzu girman ki ne a ganki a ƙofar gidan wa su kina fira? Yazo gidan ku mana, sai kace wani baƙo”
“Wai shi yana jin ba daɗi idan yazo nan gidan”
“Cinye shi zamuyi? Ai ko yanka namansa ake dole ne yazo nan indai yana son ki”
Shiru Namra tayi tana nazari. Anty Amarya ta mire baki.
“Uhm- Allah dai yasa kina son Asim ɗin nan yana son ki kamar yadda kike son sa”
Murmushi kawai Namra tayi, ta kai hannu ta ɗauki wayar Anty Amarya dake gefenta.
“Bari na kira shi”
Sai ta tashi ta fita. Ɗakinta ta dawo ta sake ɗauko takardar ta saka number ta kira. Ringing tayi har ta katse be ɗauka ba, sai da ta ƙara kiransa sannan yayi picking.
Tana yin sallama ya gane ta.
“Namra gani a gurin ban gan ki ba”
“Ina gida Anty tace ba sai dai kazo gida”
“Namra ina jin tsoro, bana son zuwa gidan nan naku kallon wulaƙanci ake min”
“Kazo mana babu koma ma, Hajiya tana part ɗinta, Maryam da Hindatu sun tafi makaranta, Abbah ma ya fita”
“To gani nan zuwa”
“Gidan ka shigo kaje gurin Garden”
Daga haka ta kashe wayar, ta mayarwa Anty Amarya.
“Anty ga wayarki na gode”
“Ke kin hallaka taki wayar ko?”
Murmushi tayi, ta juya ta fice. Firjin ta buɗe ta ɗauki lemu da kofuna, sannan ta nufi garden zuciyarta cike da zumuɗin son ganin masoyinta.
A-ƙalla ya ɗauki mintuna goma shabiyar, sannan ya iso, da faɗuwar gaba ya buga ƙofar gate ɗin. Sai mai gaɗinsu ya buɗe masa yana tambayar wanene.
“Nine ko Namra na ciki?”
“Eh tana ciki”
Mai gadin ya buɗe masa ƙofa, yana mamakin ganinsa.
Gidan ba baƙonsa bane, dan haka be sha wahala ba gurin ɗaukar hanyar da zata sadashi da garden ɗin. Namra na hango shi ta miƙe tsaye ta rumgume tana murmushi, ta hannayenta, idonta ya cika da ƙwallah.
Shima murmushin yayi yana kallon yadda ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba.
“Namra ashe zan ƙara ganin ki?”
Bata bashi amsa ba sai kawai ta nuna masa kujerar dake facing ɗin nata. Bayan ya zauna sai ta zauna tana share hawayenta.
“Asim ina ka tafi?”
“Katsina naje gurin wani Ƙanen Mahaifina ina riƙa masa aikin jima da yake yi”
“Haba Asim shi kenan sai ka gudu ka bar ni kana ganin kamin adalci kenan?”
“Namra idan kika aure wani ba niba, mutane zasu min dariya, ban san da wane ido zan ɗaga kai na kalli mutane ba”
“Matuƙar kace zaka biye ma dariyar mutane ba zaka iya aikata komai ba Asim. Nima dana biye dariyar mutane da ban yarda na aure ka ba, yanzu ka watsar da karatun ka, abunda nake da yaƙinin shine zai taimaki rayuwarka”
“Ba karatu ne a gaba ba yanzu, faɗa min da gaske mahaifinki ya yarda muyi aure?”
“Ya yarda shiyasa yace na nemo ka, kuma ina jin ba zai sa mana date da nisa ba”
“Al-hamdulillah Allah mun gode maka, amman Namra kina ganin zaki iya zama da ni?”
“Ba zan iya zama da kai ba na amince zan aure ka? Ya kake wannan maganar kamar ba Namra ce a gaban ka ba?”
“Ina ganin kamar yanayi na da naki ba ɗaya bane”
“Ba mu da banbanci ai duk mutane ne. Asim Amira ta ɓata”
“Haka naji kuma ni ake zargi da sace ta ko? Kamar yadda aka zarge ni da sace ki”
Ta share hawayenta.
“Waya faɗa maka?”
“Ai abun duniya baya ɓoyuwa Namra, kuma kin san akwai munafukai da yawa a duniyar nan. Shiyasa na yanke shawarar barin garin gaba ɗaya, ko da mun yi aure a Katsina zamu zauna tun da ban da gurin aje ki a nan, amman can family house ne akwai ɗakuna da yawa, sai dai na ƙasa ne”
“Amman Asim kana ganin zaman mu a can zai yiyu? Karatun ka fa?”
“Na riga na yafe karatu Namra. Kuma zaman mua can zai fi, saboda har ga Allah nan bana da gurin aje ki, kuma kin ga nan idan mun ci za'a gani, idan ba mu ci ba ma za'a gani, kuma abu kaɗan za a zo gidan ku a faɗa, can kuma babu wanda ya san ki, kuma kin ga ɗan zuwan nan da nayi, ina kama masa aikin jima nima ina samun nawa, kin ga ko dashi zamu iya cin abinci kamin Allah yayi mana wata hanyar”
“Amman Asim shi yace zai baka gida a can? Ni dai zan fi jindaɗi mu zauna nan”
A take ya canja fuska.
“Ko be yarda ba ni zan roƙe shi ya bamu gurin zama, kuma ni a tunani na Namra ko a ciki wuta nace ki zauna zaki iya zama in har kina so na”
“Ina son ka Asim, kuma zan zauna a duk inda ka aje ni, yanzu kaje ka samu magabatan ka suzo su ga Abba”
Murmushi yayi ya sauke ajiyar zuciya.
“Zan yi haka Inshallahu, na gode sosai”
Ba suyi wata doguwar hira ba suka yi sallama, ko lemun da ta kawo masa be sha ba.
Cikin rashin jindaɗi ta nufi shiga falo, har ta nufi kitchen ta aje lemu na ɗauke da kalaman da Asim yayi mata. Idan tace ba zata iya zama a can ba zai zargeta, sai dai har ga Allah bata jin zamanta acan ɗin zai fi.
Bata yarda ta labarta ma Anty Amarya komai ba, sai kawai ta shige ɗakinta tana shawarta zucuciyarta, da nema musu mafita.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa17.html
🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺
Wattpad @
KHADEEJA CANDY
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
Wannan shafin sadaukarwa ce ga SANAH S MATAZU. Namra da Kalsoom sun ce a gaishe ki😘
NOT EDITED ⚠️
*PAGE - 17*
KALSOOM POV.
Sun ɗauki dogon lokaci kamin su fito. Ko da suka fito har Kalsoom tayi nisa da cin abincinta.
“Sorry mun bar ki kina cin abinci ke kaɗai”
Rashida ta faɗa tana ƙoƙarin zama. Kallonta kawai Kalsoom tayi ta cigaba da cin abincinta. Hilal ya lura da yadda yanayin Kalsoom ya canja hakan yasa ya zauna a kujerar dake daf da ita ya ɗauki abincin ya mai da agurin.
Sosai da sosai hakan ya sosa ran Rashida, for the first time in history jikin mijinta yana gugar jikin wata mace. Wasa da riƙayi da abinci ta kasa ci. Hilal ya lura da yanayinta amman be kulata ba har ya gama cin abinci tare da Rashida. Tashi Rashida tayi zata kwashe kwanukan sai ya riƙe mata hannu.
“Bar su kawai je ki shirya kan ki zan kwashe kayan, nima na iya aikin ai, amman kamin nan zauna zamu yi wata magana”
Ba musu ta koma ta zauna. Sai da yaja dogon numfashi sannan yace
“Rashida Kalsoom ina son ku bani aron hankalinku, Ban auri Kalsoom ba dan na wulaƙanta Rashida, kuma ban auri Kalsoom ba dan bana son Rashida ba, yanzu nauyin ku duk ya hau kai na, dan haka ina fatar zaku taya ni sauke nauyin da Allah ya ɗora min, ba wai ku tada min hankaliba, zan fu kowa jindaɗi idan kuka haɗa kanku.
Zan iya zama abun kwatance idan kuka kwantar min da hankali, ba zan iya gane wace tafi so na ba sai ta sai ta hanyar kwantar min da hankali da kuma kyautatawa. Bana son wani rashin jituwa ya shiga tsakanin ku, kuma ban da ɗauka anyi ance duk wanda take ganin ba ayi mata dai-dai ba zata iya magana”
Kalsoom ce ta fara magana bayan ya kai aya.
“Inshallah zaka same me mai biyayyah, ni ɗai indai gefe na inshallah ba za a taɓa samun matsala ba, kuma ina fatar wasu abubuwan da zanyi a cikin rashin sani Ammyn Rafiq zata tunatar da ni”
“Inshallah ina fatar nima zaki tunatar da ni Allah ya bamu haƙuri zama da juna, sai dai sai kin yi haƙuri dasu Ezzah saboda basa jin magana”
Rashida ta faɗa tana mai jin sassauti a zuciyarta.
“Ba komai Ai yara na kowa ne, yaran ki ai nawa ne”
Hilal ya jidaɗin yadda yaga sun ɗan sake da juna, yasan nan gaba komai ze wuce kishi ne kawai wanda ba a rasa ba.
Bayan sun ɗan yi fira ta tashi ta nufi ɗakinta, Rashida kuma ta nufi ɗakin yaranta, dan ta tashesu.
Shigar da tayi a ɗakin ya bata damar kallon irin dukiyar da mahaifinta ya zuba mata, ta jidaɗi matuƙa sai da ta ƙare ma ɗakin kallo sannan ta ɗaga hannu sama tayi ma Allah godiya. Sannan ta nufi bathroom ɗinta tayi wanka, cikin koriyar atamfa ta shirya ta tsaɓa ado. Sannan ta ɗauki wayarta ta kira Momy da Daddy ta gaishe su.
Guraren biyu da rabi Salma tazo gidan, aiko Kalsoom kamar ta haɗeye ta, sai duk taji kamar ta daɗe bata ganta ba.
Ɗakinta ta kaita ta kawo mata abinci da abun sha. Sai da Salma ta ci ta ƙoshi sannan ta kalli Kalsoom tana dariya tace.
“Komai mai lokaci, yau dai gashi na ci abincin gidan Kalsoom”
Kalsoom tayi dariya. Salma tace
“Ya dai zaman ku babu wani matsala dai ko?”
“Eh toh babu matsala zuwa yanzu, ban sani ba dai ko gaba. Amman a yadda na lura kamar yana son matarsa da yawa”
Salma ta saki baki.
“Kalsoom kenan ke kin fi son ki auri mijin da zai riƙa wulaƙanta uwargidansa? Irin wannan mijin ai ba mijin aure bane, idan ya gama da ita akan ki zai yo.
Kuma Hilal ai dole ya so matarsa tun da matarsa ta gina masa sonta a zuciyarsa, kema ki gina naki mana, yana son matarsa cikin bata bashi lokacinta bata kula da gidanta a yadda ya dace, me kike tunani idan ke kika masa duk abunda yake so?
Aure ba abun wasa bane Kalsoom sai kin kai zuciyarki nesa, babu ruwanki da sashenta indai ba har ta kama bane, wani abu da gangan zata yi dan ki gani amman ki riƙa kauda idonki dan samawa kanki masalaha.
Ban da nuna masa ke maki son matarsa, wallahi komai take miki karki nuna masa baki son matarsa balle kuma ƴaƴansa, sai dai idan tayi miki wani abun na laifi ki nuna ɓace ranki ki yi magana dan ƙwatar yancin ki. Karki kuskura zagin matarsa gaban idonsa, kina ida kina haka ko da ita ta nuna masa bata son ki ita zai riƙe da abun a zuciya ba ke ba
Kuma ki kama ƴaƴansa ki riƙe kamar naki, babu ruwanki da ƴan anyi ance, ban da ɗaukar zancen maƙota, ban da biye son zuciya, duk wani kishi da zaki ji ki danneshi ki sawa ran ki sassauci, ban da faɗin sirrin miji, musamman na al'amarin auratayya. A duk lokacin daya buƙace ke ki nuna masa kin fisa buƙatarsa, ki sake jikinki ki yiwa mijinki duk abunda yake so. Ke ai baki da matsala da wannan matar tun da bata da lokacin kanta ma, yara kuma kullum suna islamiya da boko kin ga ai gidan ma kusan naki ne ke ɗaya
Ƴan uwansa ki kama ki riƙe ki maida su kamar naki, ki girmama mahaifansa, ki girmama abokansa, ki tarbi kowa da far'ah idan kina da abun basu ki basu, ki zama mai yawan alheri, gidan ki ya kasance mai ƙamshi da tsafta, abincin ki ko yaushe a ready.
Kin ga waɗannan abubuwan da na faɗa miki? Sune mallaka na musamman wanda mu mata basu san da ita ba, idan kina wannan wata mace ba zata iya gane kan mijinki ba, sai dai kiji ana ta mallake shi ai baya da magana sai nata”
Kalsoom tayi dariya tana mamakin yadda Salma take jero mata waɗannan bayanan kamar wata tsohuwar mace.
“Salma.yaushe kika ɗauki wannan karatun?”
“To ai ke sabuwace mu kuwa mun tsufa a lamarin, ke bari na baki wani sirrin, idan zaki bawa mijinki abinci ki laɓe a inda ba zai ganki ba ki riƙa karanta masa Bismillah kafa shirin da tara ko sha tara, ki tofa masa a ruwa ko wani abu kamar alawa haka ko dabino, a lemu ma zaki iya amman idan kin ƙanƙare, sannan ki karanta masa Hal'ata alal insanu har zuwa samin'an basira, sai maimaita sami'an basira sau bakwai ki tofa masa a abinci, ki yawaita lalle idan mijinki mai son lalle ne, ko kuma ki karanta ayatul kursiyo ki tufa masa a ruwa, kuma ko yawaita cin fruits da tsarki da ruwan ɗumi, ki riƙa masa shagwaɓa dan zama suna son shagwaɓa sosai, hmmm ƙawata sauran soyayyar ki nemeta gurin Allah kawai, amman sai kin ba labari”
Taɓawa sukayi, Salma ta ɗora
“Ai shiyasa bana da shakku akan mijina, nasan ko aure yayi ba dai wata ta ɗauke masa hankaƙi ba, sai dai ma ta rasa gane kansa”
Salma ta daɗe tana yi ma Kalsoom lacca har aka kira la'asar, bayan tayi sallah suka je tare a ɗakin Rashida Kalsoom ta gabatar mata da Salma sannan ta fito, har gurin gate Kalsoom ta raka ta.
NAMRA POV.
Washe garin ranar