Showing 15001 words to 18000 words out of 281103 words
Chapter 6 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
ba har sai anyi, haƙiƙa ina son Khadija matuƙa sai dai tayi tsalle ne da ɓata rawarta tun daga lokacin data tsaya kai da fata akan lalle ita sai wannan yaron,
na bata dama na fitar da wani ta ƙyale wannan yaron amman sai ta buga min ƙafa a ƙasa ita sai Asim, shiyasa kaga na fita lamarin ta, saboda so da yawa zaka abunda mu iyaye muke hangowa ba shi ƴaƴa ke hangowa ba, a tunanin ta na yi mata hakan ne dan na cutar da ita, tun da ta nuna bata so.
Nasan anbar auren dole a yanzu, amman duk abunda na yi ma Namra ita ta jawa kanta”
Abbah ya ɗaga kai ya sake kallon Uzair da kyau yana mai nuna masa abunda yake faɗi a bakinsa shine a zuciyarsa.
“Uzairu ina fatar zaka riƙa Khadija da amana, kuma zaka nuna mata so da kulawa, irin son da zata san lallai ta yi dacen mahaifinta be mata mugun zaɓi ba, ina son ka sani duk abunda ya samu Namra ni ya sama, kuma zai taɓa mahaifiyarta, ina addu'a wannan aure Allah ya sa masa albarka, ya baku haƙuri zama da junanku”
Jikin Uzair yayi san yi sosai da kalaman da Abbah yayi masa, sai yake jin kamar Abbah ya san abunda yake son aikatawa.
Cikin rashin kuzari ya yi ma Abbah sallama, ya tashi ya fice.
Har ya iso gurin motarsa tunanin kalaman Abbah yake.
‘Abunda duk ya sami Khadija ni ya sama’
Same shi ya fi tsaya masa a rai, tunani yake what if Abbah ya gane gaskiyar dalilinsa na neman aurenta? Shi kuma baya jin yana da wata mafita ta rufa ma kansa asiri bayan wannan, tun shi dai ba zai ce zai kashe Namra ba, gashi ta ce sai ta tona masa asiri.
Ya kwashe minti arba'in a gurin yana tunani, ba tare da ya sani ba. Can sai ya nufi gurin Mai gadin yayi masa magana kan ya shiga yayi masa sallama da Namra.
Cikin girmamawa mai gadin ya nufi part ɗin Anty Amarya, shi kuma ya dawo gurin Motarsa ya tsaya ransa a jagule.
In few minute Mai gadin ya dawo ya shaida masa ance gata nan zuwa. Chanji ya fiddo a aljihunsa ya miƙawa Mai gadin, sannan ya gyara tsayuwarsa yana jiran fitowarta.
Lokacin da Mai gadin ya shigo falon, Anty Amarya, na zaune tare da ƙannensa suna cin abinci, sai tace da Mai gadin yace tana zuwa, sannan ta tashi Maryam ta ce taje ta kirata ɗakinta.
Maryam ta aje littafin dake hannunta ta tashi ta nufi ɗakinta. Tana yin sallama Amira ta zabura kamar marar gaskiya.
“Anty Amira, ina Anty Namra?”
Shiru tayi tana dube-dube kamar mai neman abu, can kuma ta kalli Maryam tace
“Maryam idan na faɗa miki wani abu zaki fahimta ai ko?”
“Uhmm minene?”
“Namra ta fita ɗazu, Asim ne yayi mata texs wai yana son ta zo suyi sallama, shine ta fita tun ɗazu”
Gaban Maryam ya faɗi
“Amman kika barta taje ita kaɗai? Idan wani abun ya same ta fa?”
Shiru tayi tana tunanin ƙaryar da zata ƙaƙaro
“Ba yadda ban yi ba, amman tace ba zan bita ba, wai na tsaya kar a zo nemanta ba'a ga kowa ba, amman bari na kirata”
Cikin sauri ta shiga kiran wayar. Maryam bata tsaya ba, ta juya ta fita.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kiran Anty Amarya. Daker ta taso saboda abincin da suke ci da kuma firar da suke da ƴan'uwanta.
A tunaninta Maryam zata ce mata Namra taƙi zuwa ne, sai kawai taji wani labari banbaragwai. A take Anty Amarya ta ɗauko wayarta ta shiga kira amman ba a picking.
Sai duk hankalinsu ta tashi, Anty Amarya ta koma ɗakin Namra ta samu Amira zaune tana faman kiran waya.
Anty Amarya ta katsa mata tsawa.
“Ina tace miki zata?”
Jiki na rawa ta amsa ma Anty Amarya dan ta ga ranta ya ɓace sosai.
“Tace min nan bayan layi”
“Amman dai Anty Amira kin yi wawanci Wallahi, shine kika bar ta taje? Maimaiko ki hanata ko ki faɗawa Anty, kuma kika ƙi binta kuje tare”
Maryam ta faɗa tana hararar Amira. Anty Amarya tace
“Ita ma Namra ai da wayon ta”
“Ko da wayonta ai wani abun sai an nuna mata, tun da kinsan yadda Anty Namra take ko ni sai na fita wayo, waya sani ma ko da ke ya haɗa kai kika lallaɓa masa ita ta tafi”
Amira ta kalleta
“Haba Maryam wane irin magana kike haka ne? Kina tunanin ni zan iya cutar da Namra?”
“Waya sani abu a duhu, ƙawayen yanzu ai ba abun yarda bane, kuma Wallahi duk abunda ya samu Namra ki ƙaddara ke ya sama dan ba zan taɓa yafe miki ba”
Amaimakon Amira tayi magana sai kawai ta fashe da kuka, ta tashi ta ɗauki pose ɗinta ta fice tana kuka.
Anty Amarya sai ta hau Maryam da faɗa
“Wai Maryam ba zaki bar fitsarar nan ba ko? Kullum ina miki magana kan shegen bakin nan naki amman baki ji, yanzu miye na wannan furucin fisabillahi? Ita Namra ƙaramar yarinya ce da Amira zata ɗorata a layi ta hau?”
Maryam ta tunzure baki.
“Wallahi zata iya ɗora ta a layi wannan Amirar da kike gani shegen wayo ne da ita, kuma Wallahi tun ba yau na lura kamar tana hassadar Anty Namra, wani fa sam baya son yaga cigaba a gareka sai ci baya, kuma wani maƙiyi na ɓoye ba gane shi ake ba”
Anty Amarya ta katsa mata tsawa
“Zaki je kiyi magana da Uzair, ko tsayawa zaki yi, kina ƙara min ɓacin rai”
Juyawa tayi ta fita tana faɗin
“Wallahi duk wani abu ya samu Anty Namra Amira zan zarga”
Ɗakinta ta shiga ta ɗauki Hijabinta ta saka, sannan ta fito ta nufi harabar gidan gurin da Uzair yake, tana harararsa.
“Bata jindaɗi ba zata iya fitowa ba”
Ta faɗa ba tare data masa sallama ba, kuma bata tsaya jiran abunda zai ce ba ta juya tayi tafiyarta.
Wani kallo ya bita dashi, daman duk cikin Family Abbah Maryam tafi uban kowa tsageranci. Buɗe Motarsa ya yi ya shiga zuciyarsa cike da tunane-tunane, hannu yasa ya shafa kansa, sai ya ciro wayarsa ya nemo wata number ya danna mata kira.
Ana yin picking ya ce
“Tahir kana ina?”
Ban ji me aka ce masa ba, sai kawai yace
“Ok gani nan zuwa yanzu”
Daga haka ya kashe wayar, ya ƙarama gudu. Can kaɗai ne yake jin zai iya tafiya ya fayyace sirrinsa, tun da duk akan layi ɗaya suke.
Sai da ya yi tafiya mai nisa, sannan ya isa bakin wani ƙaton gate.
Horn yayi mai gaɗin ya buɗe masa sannan ya kunna kai cikin ƙaton guesthouse ɗin. Parking ya yi, ya fito ya nufi hanyar shiga gurin. Zazzaune ya tararda su, Tahir da Najeeb. Tun daga ganin yanayin shigowarsa sun san akwai wani abu a ƙasa. Tahir ne ya fara magana
“Lafiya kake Uzair?”
Bakinsa ya cika ma iska ya busar
“Wallahi ina cikin matsala”
“Matsalar me?”
Najeeb ya tambaya, cike da son sanin abunda ke damun amininsa.
Uzair be ɓoye aminansa komai ba, tun daga ganin da Namra tayi ma friends ɗinsa na Abuja har zuwa nemanta da yayi, kuma kalaman da Abbah yayi masa yanzu, sannan ya ɗora da sace ta da yayi.
Tahir ya girgiza kai
“Uzair you Fuck up, ai yin wannan abun da kanka matsala ne, mun riga mun san junan mu toh miye na ɓoyewa kasa kanka a matsala? Yanzu ka sace yarinyar mutane kana ganin asirinka ba ze tunu ba?”
“Nayi tunanin zan iya solved ɗin matsalar ne, da nayi nufin na riƙe ta ne har kwana biyu ta yadda za a yi tunanin ta gudu da bi saurayinta ne. Ga Yasmin ta juya min baya na rasa gane kanta, kuma yanzu idan ta dawo zata iya faɗa asirina ya tonu kuma kasan komai ze iya faruwa, family ni za a zaga kuma.mahaifinta ba zai ƙyale ni ba”
Tahir ya dawo kusa da shi ya dafa shi.
“Ka kwantar da hankalinka, irin wannan yarinyar ta dabara bata musu, kuma irin wannan sirrin ba a sake da shi”
Najeeb yace
“Lallai kam, irin wannan yarinyar malamai za a shiga da ita, fiussss an gama da ita”
Tahir yace
“Shine kawai, yanzu kaje kayi abunda zaka yi da ita, kasa a maida ita gida kamin asuba, zan rubuta maka wani magani ka bata tasha zata manta abunda ya faru, idan Jafar ya dawo zamu zauna mutattauna”
Murmushi jindaɗi yayi, yajin ya samu mafita gurin abokansa.
Cikin kuzari ya tashi bayan Doctor Tahir ya rubuta masa maganin a takarda, ya yi musu sallama ya fice.
__________________________
LOVE YOU ALL FISABILLIAH 💖😘🌺
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
NOT EDITED ⚠️
*PAGE - 8*
Yana cikin mota yana driving zuwa guesthouse ɗinsa, kiran Najeeb ta shigo wayarsa. Picking yayi ya kara a kunne sai ya mai da tuƙin da hannu ɗaya.
“Hello”
“Uzair kana ina? Ka isa gidan ne?”
“A'a gani dai kan hanyar zuwa siyen maganin”
“Karka siyo ka wuce gidan kawai, idan ka isa ka jira ni gani nan zuwa, kuma ka tabbatar bata farka ba, idan kuma ta riga ta farka, karka bari ta gan ka, ina ka aje ta?”
“A guesthouse ɗina”
Sai ya kashe wayar, ya ƙara ma Motarsa gudu. Yana isa, Najeeb na isa. Sai duk suka yi saurin fitowa Motar. Najeeb ya nufi shi yana faɗin
“Yanzu ya kamata mu mai da ita gida”
“Taya?”
Najeeb ya kalli ko ina na gurin, sannan yace
“Ni zan kaita, faɗa min inda ka ɗauke ta, zanje can na maidata, zamu saka mai gadin nan naka ya je a inda take ya riƙa ihu da neman taimako har mutane su taru su, su nuna masa gidansu, zai bamu haɗin kai dai ko?”
“Me zai hana indai an bashi kuɗi”
Uzair ya faɗa.
“Okay zan tsara masa yadda zai yi, miye sunan Saurayin nata?”
“Asim sunan shi Ibrahim, amman anfi saninsa da Asim”
“Good yanzu kira ɗaya daga cikin masu tsaronta ya duba mana idan bata farka ba”
A take Uzair ya ciro wayarsa. Najeeb kuma ya nufi gurin mai gadin.
Ɗaya daga cikin yaran ne suka shaida masa har yanzu bata farka ba. Shi kuma ya nufi Najeeb ɗin ya faɗa masa.
Sai da Najeeb ya gama tsarama mai gadi yadda zai yi, sannan ya juyo gurin Uzair.
“Good yanzu kasa su ɗauko ta, su saka ta a mota na, sai ka shiga taka motar ka nuna mana daidai inda ka ɗauke ta”
“Baba Audu zaka iya ko?”
“Ƙwarai Zan iya ranka ya daɗe ai wannan abu ne mai sauki, kuma taimako ne”
Baba Audu ya faɗa da kansa. Sai Najeeb yayi murmushi.
“Zamu baka dubu ɗari idan aiki yayi kyau, zamu baka wasu dubu ɗari na rufar sirri, ka tabbata dai ba'a samu matsala ba”
Har ƙasa Baba Audu ya risina yana godiya baki har kunne.
“Allah Ubangiji ya saka da alheri, ai ni ko baka bani komai ba, zan iya maka fiye da wannan”
Najeeb ya nuna masa Mota.
“Kaga Mota can je ka shiga gidan gaban”
Sai kuma ya kalli Uzair
“A fito da ita yanzu”
Cikin sauri Uzair ya nufi gurin, be daɗe ba ya fito, wani namiji na ɗauke da ita. Ita kuma ta langwaɓe kamar wacce ta mutu.
Najeeb da kansa ya bude Motar suka saka ta gidan baya. Sannan Najeeb ya shiga driver seat, Baba Audu ya shiga front seat, Uzair kuma ya shiga Motarsa, sai ya shiga gabansu dan nuna musu hanya.
Cikin mintuna suka isa gurin. Can nesa da gurin suka faka, sai Najeeb ya buɗe motar ya fito da ita. Uzair ya nuna dai-dai inda ya ɗauketa sai Najeeb ya ajeta a gurin, yasa car key ɗinsa ya ɓarke mata Hijabi, ya yagashi, ya barƙa rigar afamfar dake jikinta, har rabin breast ɗinta ya fito.
Sanna ya ɗago ya kalli Uzair
“Ta fito da waya?”
“Yes ga wayar ta nan hannu na”
Ya faɗa yana ƙoƙarin cirota daga aljihunsa. Najeeb ya miƙa masa hannu
“Wani wayar zan taka ta da mota, kuma ka bani layin da ka kira ta da shi”
“Why?”
Najeeb yayi masa wani kallo
“Haba Uzair ya kake abu kamar ba wayaye ba? Baka san za'a iya amfanin da wayar a gano sawon hannunka ba? Za a iya gano ka idan kana amfani da layi, kuma yanzu ai amfanin layin ya ƙare”
Kamin Uzair yayi magana, kiran Amira ya shigo wayarsa. Da sauri Najeeb ya tambaya.
“Who's calling?”
“Her Best friend”
“Did she know?”
“Yes tare da ita muka haɗa komai”
“Karka yi picking call ɗin nan it risk, let's go kar wani ya gan mu”
“Da wahala wani ya gan mu, baka ga yanayin gurin ba? Ko da rana ba a cika wucewa ba balle yanzu pass 11 fa”
Najeeb yayi murmushi, irin na har yau baka waye ba Uzair. Sai kuma ya kalli Baba Audu
“Da ka daina hango hasken Motar mu, zaka fara ihun”
“Toh ranka ya daɗe”
Cikin sauri suka nufi motocin su, Najeeb sai wage-wage yake kamar mai neman wani.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa09.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
*PAGE - 9*
A lokacin da Baba Audu ya daina hango su, sai ya buɗe dukanin muryarsa ya kwarara uban ihu yana neman taimako.
“Wayyo Allah jama'ah a taimaka mana, a ceto rai, jama'ah ku kawo agaji”
A yanayin gurin, ba kowa bane zai iya saurin fita, saboda yanayi na tsoro da ake ciki, gashi ta bayan layin unguwar ne ba mutane sosai.
Cikin ƙarfi hali da bugawar zuciya, Baba Audu yake ta kwarara ihun yana wage-wagen jiran wanda zai fito.
Tsinta-tsinta aka fara fitowa ana nufar gurinsa, sai tambayarsa suke lafiya. A nan ya soma ƙirƙiro hawayen ƙarfin hali yana faɗa musu abunda Najeeb ya tsara masa.
“Wallahi wasu mutane yanzu suka jefo da wannan yarinyar daga mota, kuma suka zo suna ƙoƙarin taɓa mata mutunci”
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Shine abunda kowa yake faɗa, dan makamacin wannan be taɓa faruwa a unguwar ba. Wani dattijo ya kai hannu ya gyara mata Hijabinta, ta yadda zai suturta mata breast ɗinta dake buɗe.
Waɗanda suka santa sun gane ta, sai dai kowa mamaki yake, yana tunanin suye ne suka mata haka? kuma a ina ta haɗu da su haka.
Wani saurayi ne ya kawo ruwa aka zuba mata, amman shiru bata farka ba, haka akayi ta zuba mata ruwan but still bata motsi. Anan mutane suka ce a ɗauke ta a kaita gidansu
*** *** *** ***
Babu irin kiran wayar da Anty Amarya bata yi ma Namra ba, tun tana ringing har aka kai ga kashe wayar.
A lokacin hankalinta ya tashi sosai, ita da Maryam har Aisha da Hindatu sai da hankalinsu ya tashi.
A take Anty Amarya ta fara kuka, tana tunanin abunda ze samu ƴarta, kuma tana tsoron kar Abbah yaji, sai duk tabi ta rikice ita da Maryam. Aisha da Hindatu suka ce zasu je bayan layi su duba ko Allah yasa zasu same ta.
Anty Amarya ta share hawayenta.
“Babu inda zaku je cikin daren nan, bayan layi da yake da duhu idan wani abun ya same ku fa, ban san abunda yasa Namra ta raina ni ba, ta ya zata saka ƙafa ta fita ba tare data faɗa min ba? Duk abunda ya same ta ita tajawa kanta”
Maryam ta ɓata fuska.
“Gaskiya Anty Namra bata kyauta ba, amman da kin bari munje mun duba ko zamu ganta”
“Babu inda za ku je, idan Abbah ku ya gani kuce masa me?”
“Abbah ba ze gani ba, tun da yana part ɗinsa, kuma ba daɗewa zamu yi ba, dubowa kawai zamu yi mu dawo”
“Babu inda za ku je yanzu goma ta wuce, inda har kuna jin magana ta, toh karku je ko ina nemanta, ai ita ta kai kanta, ina zaune falo tabi ta ƙofar kicin ta fita, ba dai-dai bane tasa ƙafa ta fita ba tare da sani ba”
Anty Amarya na gama faɗar hakan, ta tashi ta nufi falo tana hawaye. Yanzu kan babu abun ɓoyewa dole ta faɗa ma ƙannenta abunda yake faruwa, su kansu basu jidaɗi ba, sai laifin Namra suke gani, wai taya zatayi haka kamar wata ƙaramar yarinya.
Haka suka yi zaune jugum, kowa sai addu'ah yake, babu irin roƙon da Mama Zainab bata yi ma Anty Amarya ba akan ta bari suje su dubota, amman ta hana.
Har kusan shaɗaya babu wani labari, sai shabiyu saura kwata, suka soma jin hayaniya a habarar gidan, sai doko musu sallama ake da muryar maza.
Wani irin faɗuwa gaban Anty Amarya yayi, har sai da ta dafa zuciyarta ta lumshe ido. Mama Zainab da Hajiya Raliya ne suka riga fita, Aisha da Hindatu suka rufa musu baya.
Maryam kuma ta tsaya kusa da mahaifiyarta ganin halin da take ciki. Cikin ƙarfin hali Anty Amarya ta tashi, Maryam ta ɗauko mata hijabinta ta saka sannan suka nufi ƙofar fita.
Ko da suka fito har Hajiya Barau ta isa gurin, Abbah kuma ya fito daga part ɗinsa ya nufi gurin da mutane suke tsaye, riƙe da Hannun jikan Imam jikan Hajiya, da alama shi ya je ya faɗawa Abbah.
Cike da kasala Anty Amarya ta ƙasara gurin ita da Maryam. Tana ganin halin da Namra take cike gabanta ya ƙara faɗuwa, a take kasala ta sauki mata. A nan Maryam ta fara kuka ganin Namra kwance kamar matatta ga Hijabinta a yage.
Abbah ya kalli mutanen cikin tashin hankali.
“Miya faru? Ina kuka ɗauko Khadija?”
Kowa sai ya nuna Baba Audu yana faɗin shi ne san abunda ya faru, tun da yace musu a gaban idonsa akayi. Tun kamin Abbah ya tambaye shi ya shiga yi masa bayani.
“Na fito ne gidan ƙanena can baya, sai na hango wata ƙatuwar mota mai kamar ta ƴan makaranta ta tsaya, a gefen gurin sai aka jefo wannan yarinyar , sai kuma suka fito su huɗu suna ƙoƙarin cire mata tufafi, shine fa sai na fara