Showing 249001 words to 252000 words out of 281103 words

Chapter 84 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61302

da fita ranshi daman yanzu ba maxe ba burgeshi take ba, wannan ma da zai aureta dan kawai kariyar kai ne, kuma yana son ganin shi wutar take bi ko Mardiya.


Babu irin neman taimakon da ba ayi ba akan wannan matsalar, wani gurin ace aiki ne aka mata wasu kuma su ce iska ne yake mata, tana zuba kuɗi da yawa dan ganin ko za a dace amman babu wani sauƙi sai abunda ya cigaba.


A unguwa kuma sai gulma ake mata kowa da irin abunda yake faɗa, waɗanda suka san halinta suce amanace ciki har da masu cewa ai taci amanar Namra tun da ta aure mata miji....
[7/22, 10:00 PM] Khadeeja Candy♥: *87*


NAMRA POV.


Shiru-shiru bata ga Abdool ya dawo ba, hakan ya tabbatar mata da fushi yayi. Miƙewa tayi tsaye ta fita sai ta hangoshi jikin motarsa yana kallon ƙofar falon. Ƙarasa tayi cikin wani taku mai jan hankali da ƙasaita, ta rumgume hannayenta tana kallonshi.


“Ina da matsalar mahaifa ne Abdallah, ciki baya iya tsayawa tun ina gidan Asim, wannan matsalar ce tasa Dr Faruk ke kula da lafiyata”


Uffan be ce mata ba, sai kawai ya kawardar fuskarsa yana kallon part ɗin Abbah.


“Abdallah...”


“Abnam...”


Ya kira sunanta kamar yadda ta kira nashi, still be kalleta ba.


“Baka yarda da ni ba ko?”


“Babu rashin yarda a tsakani na da ke, sai dai zai fi idan muka bar maganar nan”


Murmushi tayi ta juya koma ciki. Haka ya tsaya a gurin har sai da yaji ya samu sassauci a zuciyarsa sannan ya nufi part ɗin Abbah. A falo ya samu Abbah daman yasan da zuwansa sun samu awa ɗaya suna tattauna akan rayuwa da abubuwan duniya sam ba zaka ce Abdallah ne yake neman auren ƴar Abbah ba, sam ba zaka ce surukinsa ba ne.




*ONE MONTHS LATER...*


Har yanzu jikinsa na nan a yadda yake, Umma yanzu na hausa take nema masa wai ko Allah zaisa a dace.
Bayan ya gama shan magani ya turo kekensa ya fito harabar gidan. Wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ya ciro ya kira Tahir.


“Bros ya ne, ya jikin naka ne?”


“Alhamdullah, ya aiki?”


“Mun gode Allah”


“Tahir tun ranar baka sake ce mun komai, ko baka kai mata ba ne?”


“Wallahi na kai mata, sai dai ban ji wata magana daga gareta ba, Uzair ina son na.baka shawara akan rayuwa, ka yi haƙuri ka rumgumi ƙaddara, wannan abun da ka gani na ishi kowa ishara ni kaina wannan ciwon naka yasa na zubar da duk wata muguwar da nake da ita, ba kai kaɗai ba, yawancin duk mai aikata irin wannan matsalar ce take faɗa musu, ka duba lamarinka Uzair ba haɗarin mota ka yi ba, ba kuma faɗowa kayi daga wani guri ba, haka kawai rana tsaka ance ka kamu da irin wannan ciwon, ita kanta Amira yanzu ta kanta take balle ka zargeta da aikata maka wani mummunan abu”


Tun da Tahir ya fara masa maganar jikinsa yayi sanyi, be san lokacin da hawaye suka zubo masa ba, lallai maso rai wawa, haƙiƙa yanzu Tahir ya lurar da shi abunda be kasa ganewa.


“Na gode”


Shine kawai abunda ya faɗa ya katse kiran. Hawaye na cigaba da masa zuba, tabbas wannan kawai ya isheshi ishara, a yanzu idan ba Mahaifiyarsa babu kowa a tare da shi, zai barwa ɗansa mumman tahirin da ba zai taɓa goguwa ba har a bada.


Kekenshi ya tura ya koma cikin falon, ƙanensa na zaune sai sha'aninsu suke ko kula da shi basu yi haka ya tura kansa ya shiga ɗakin da aka ware masa ya zamo kamar nasa. Farar takadarda da ya gani a saman gadonshi ya kai hannu ya ɗauka.


Sammaci ne daga kotun high court, ganin sunan Yasmin yasa shi murmushin da ya fi kuka ciwo, sannan ya sake tura kekena ya fito falon yana tambayar wanda ya kai masa wasiƙar.


“Ɗazu ne kana shan magani aka kawo, na shiga ban ganka ba shine na aje saman gadonka”


Ƙaramar ƙanwarsa ta faɗa. Sai kawai ya kaɗa keken ya nufi ɗakin Umma.






***


Hankalin Mai Martaba ya kwanta yanzu, har ma da na Ummi. Ganin an tsayarda magana, ranar da Mai Martaba ya aika aka yi maganar aure har da sadaka sai da yayi. Sai dai tun daga lokacin magana ta riƙa zuwa tana dawowa akan Abdallah zai auri bazawara, abun mamaki ne mutun kamar Abdallah ace zai auri bazawara kuma ɗan Sarkin Ƙatsina, wanda hakan sam be yi ma Mai Martaba daɗi ba, sai dai ya kan zuciyarsa nesa domin kawai ya farantawa ɗansa, domin yasan Annabi ma ya auri bazawara kuma yana sauranyinsa.


Ita kanta Ummi tana shan magana akan aure wasu su ce kar ta barshi wasu kuma su ce kamata yayi ya haɗa biyu. Sai dai duk wannan maganganun da ake be taɓa zuwa kunnen Abdool ba, ko da wasa ƴan'uwa da abokai basu taɓa masa wannan maganar ba, saboda sun san waye Abdool idan yana yin abu yana yi ne no matter what, ao faɗa mishi irin wannan maganar zai sa ya ɓata da kai ne kawai, ko kuma kai ma ya faɗa maka marar daɗi, sai dai abokai sun ka zolayeshi cikin wasa. Babu abunda yayi masa daɗi kamar auren da Abbah be yarda aka saka nesa ba, shi kansa da ansaka auren nesa zai roƙa a rage ne, domin ya matsu ya ɗauke Namra daga gidan. Ta ɓamgare ɗaya me yake jin zai iya zame masa matsala karatunta da take yanzu.






NAMRA POV...


Babu inda zance baikon Namra be kai ba cikin garin Sokoto da kewaye, a social media kan ba zaka iya lissafawa ba, babu abunda zai baka mamaki kamar ace bazawara ce aka yi ma wannan kayan, kuma duk da sunan an gani ana so abunda aka san budurwa ake yiwa. Kayan ƙwalah da maƙulashe ba zaka iya ƙigarsu ba, ga akwati goma da aka sako na tufafi har da zinari duk a cikin an gani ana so, kowa abunda yake faɗa to lefen me za'ayi?


Ba a gidan aka kawo kayan ba, daman haka Abbah yake duk lokacin da za a yanka ma ƴaƴansa sadaki ko a kai lefensu, gidan ƴaƴanshi yake turawa.


Ko da ake hidimar kai kayan Namra tana makaranta a lokacin duk da yake asabarce amman a ranar tana da darasin (lecture) da zata ɗauka a makaranta, bayan sun gama tayi sallama ta abokanta ta nufo gurin da tasan Lamido ya saba tsayawa ya jirata.
Ko da ta isa yana zaune cikin motar buɗewa kawai ta yi ta shiga ta zauna sai kawai taji ya ce


“Congratulations”


Tasan abunda yake nufi, yanayin muryarsa ya karantar da ita baya cikin daɗin rai.


“Na amince da auren Abdallah ne saboda mahaifina, kuma na san kai ma baka ƙi goya min baya ba wajen amincewa da hakan”


“Abdallah ya kasa ni, daman ya faɗa min zai kasa ni, ta tabba yanzu shi ne a zuciyarki ba kowa ba”


“Ya faɗa maka? Alfahari yayi, fariya yayi da zai kasa ka? Yaushe bakin ka ɗa nashi ya taɓa haɗuwa?”


Yayi ma motar key yana cigaba da magana a hankali.


“Bayan tafiyarki, abubuwa da tawa sun faru, ciki har da dalilin zuwa neman aurenki, da kuma neman zama direba a gidanku...”


Ta gyara zamanta a gidan bayan da take.


“Ban gane ba dan Allah ka ƙara min bayani, karka ɓoye min komai”


“Bayan kin bar Kaduna da kwana biyu, Yarima yasa aka ɗauko ni daga Kaduna aka kawo ni Katsina, mahaifata garin da ƙabarin ubana yake, kuma garin da nayi alƙawarin ba zan sake takawa ba.....”


Kamar wanda ya tuna abu sai kawai yayi shiru ya cigaba da driving ɗin da yake. Ita kuma gaba ɗaya natsuwarta ta bar jikinta hankalinta ya karkata kan labarin da Lamido ya fara bata...




IS BETTER THAN NONE... 😎 YI HAKURI DA SHORT CHAPTER 🙏
[7/23, 9:21 PM] Khadeeja Candy♥: *88*


“Ka tsayarda motar nan Lamido”


Ta faɗa a tsawace, umarninta yake bi tunda danta yake wannan aikin, a dole ya faka mota a gefen ti-ti, sai dai be juyo ya kelleta ba balle yace mata wani abu.


“Miyasa Abdallah ya sa aka kai Katsina? Miya ce maka? Miya faru bayan na baro Kaduna?”


“Faɗa miki abunda ya faru ba zai yi maganin komai ba”


“Wata ƙila zai yi wata ƙila kuma ba zai yi ba, amman faɗin shine mafi a'ala”


“Ni da Mahaifina asalin mu fulanin Katsina ne, mahaifiyata kuma ƴar asalin jihar kano ce, mahaifina ɗan kasuwa ne ya kan ɗauki kaya daga Katsina ya kai Kaduna idan ya siyar sai ya siyo na Kaduna ya kawo Katsina da hakan abun nasa ya girma, har ta kai ya kan ɗauka daga Katsina ya kai Nijar, a lokacin muna ƙanana, iya gata mahaifinmu ya nuna da kulawa mun taso cikin jindaɗi, arkizin mahaifinmu ya bunƙasa cikin ƙanƙanen lokaci, sai dai mahaifin mu be da amini irin Alhaji Mu'azu, ita kanta mahaifiya bata da ƙawa irin Hajiya Zuwaira, ba unguwar mu ɗaya ba, amman duk ranar weekend sai an kawo yaranta gidanmu su yi weekend, bana da wayo sosai a lokacin, amman ina jin yadda Mahaifina yake faɗin idan har ya haɗa wannan kuɗin ya tura aka turo masa kaya zai samu kuɗi sosai, haka ya tattara komai na shi ya haɗa kai da Aminsa ya tura kudaɗensa masu yawa sosai. Shiru-shiru babu kaya babu labarinsu, har ta kai mun fara shiga wani hali na ha'ila i, Alhaji Mu'azu ne yake aiko mana da cefane wani lokacin kuma har da ɗinkuna da wasu abubuwan na more rayuwa, ashe duk wannan yana masa ne a cikin kuɗin da yake binsa, wata ranar Assabar mahaifina yake labarta masa kayansa suna nan zuwa, har an kamo hanyar nigeria da su ta jirgin ruwa, haka muka ɗauki tsawon wata ɗaya muna jiran isowar jirgin, sai kawai dirar ƴan sanda muka gani a gidanmu, wai ana zarginsa da safarar muyagun ƙwayoyi, haka suka tisa ƙeyarsa a gaba suka tafi da shi, sau ɗaya suka bar mu muka ganshi tun daga lokacin ba mu sake ganinsa ba, sai dai abokinsa ya zo ya faɗa mana cewar ana nan za a sako shi, amman shiru har Allah ya karɓi ransa. Bayan rasuwarsa Alhaji Mu'azu yake faɗa mana cewar babu dukiyar Mahaifinmu ko taro a hannunsa, sanadin haka muka bar garin Katsina ni da Mahaifiyata, sai muka koma garin Kaduna da zama wato mahaifarta, a gidan data gada gurin mahaifinta, tun daga lokacin garin Katsina ya fita daga raina duk da kasancewar a nan mahaifar ubana take, sai sai bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya sake waiwayar mu a cikinsu”


Namra ta share hawaye idonta cike da tausayawa ta ce


“Ba shi na tambayeka, abunda Abdallah yayi maka na tambaye ka”


“Abdallah yasa an ɗauko ni daga garin Kaduna aka kawo ni Katsina saboda kawai yana ɗan sarauta kuma ɗan mai kuɗi yafi ƙarfin ya bar garinsa ya zo kaduna saboda ni”


“Har yanzu baka faɗa min dalilin ɗaukoa da yasa aka yi ba”


Shiru be sake ce mata komai ba, hara aka kira sallah la'asar, tasan ba zai faɗa mata ko minene a yanzu ba. Zata sake magana wayarta ta yi ƙara number Abbah ta gani cikin sauri ta yi picking.


“Gamu nan kan hanya”


Shine kawai abunda ta faɗa ta sauke wayar. Shi kuma ya tashi motar suka hau ti-ti. Ta madubin gaban mota take kallon yadda hawaye suke zuba daga idon Lamido.


Sai da suka kusa isa gida sannan ya ciro handkerchef ɗinsa ya share hawayensa. Yana faka motar ta buɗe ta fito sai shi ma ya buɗe ya fito ya miƙa mata keys ɗin motar.


“Aikina ya ƙare daga yau! Gobe zan kama hanyar garin mu”


“Ba a gurina ka karɓi keys ɗin motar ba, ba ni na ɗauke ka driving ba”


Tana bashi amsa ya gyara tsayuwar littafan da ke hannunta ta nufi hanyar falo.
Tana shiga Maryam da Wasu old friends ɗinta suka jo kanta suna mata murna da zolaya. A abubuwa biyu ta samu kanta, farincikin da akasinsa, ba data dalilin yin duka biyu ɗin, dan har ga Allah bata shirya aure a yanzu ba, sai dai babu yadda ta iya tun da Abbah ya nuna yana son ta yi, a ɗayan ɓangaren kuma idan ta tuna halin da Lamido yake ciki sai ta ji Abdool ya fita a ranta. Cikin ƙarfin hali take musu dariya tana nuna musu farincikinta sannan ta wuce ɗakinta. Littafanta ta jefar saman gado ta shiga banɗaki ta yi alwala, ko da ta fito wayarta na ringing, wasu kawayenta ne na makaranta hakan yasa bata ɗauka ba, tasan ba zai wuce su taya ta murna ba, ko kuma su faɗa mata yadda zancen engaged ɗin ta ya cika social media. Har ta saka Hijab ɗinta sai wayar ta sake ringing wannan karon Abdool ne, tana son magana da shi sosai hakan yasa tayi picking tana aika masa sallama.


Ya amsa mata yana ƙarantar saƙon dake cikin muryarta na ranshin daɗin rai.


“Tell me i'm wrong, amman kamin ki yanke hukunci ya kamata kisan duk abunda aka yi Mai Martaba ne yayi ba ni ba”


A tunaninsa ko akan kayan ta ya tura ne wani abun be mata daɗi ba, sai kawai yaji ta ɗauko masa wata magana ta daban.


“Miyasa kasa aka ɗauko Lamido daga Kaduna ka kawo shi Katsina? Mi kace masa?”


Yannu ya kai yana shafa dogon hancinsa, tare da maimaita sunan Lamido a zuciyarsa.


“Be faɗa miki abunda Yarima Abdallah yayi masa ba? Be faɗa miki gaskiyar abunda ya faru ba?”


“Be faɗa min ba, amman ga dukan alamu abunda ka yi masa babba ne, domin har hawaye na gani a idonshi”


Ƙafarsa ya ɗora ɗaya saman ɗaya yana imaging fuskar Namra a wannan lokacin duk da kuwa bata kusa da shi.


“You're crying...”


Sai kawai ta katse kiran ta share hawayen idonta ta miƙe tsaye ta kabbatar sallah. Har ga Allah tana jin son Abdool a zuciyarta sai dai bata fatar ta yi amfani da wannan damar ta cutar da Lamido, dan tana jin rashin kyautawa a abunda ta yi masa, sai dai bata da zaɓi bayan na Allah daman can shi ta miƙawa lamurarranta, har gobe roƙon Allah take idan har babu alheri a aurenta da Abdool Allah ya musanya mata.


Haka ta kwashe kwana biyu, babu wata magana mai daɗi dake shiga tsakaninta da Abdool, saboda tana ganin kamar yana amfani da saurautarsa da kuma kuɗinsa ne wajen nuna mata ƙarfin iko ya ita da Lamido, ga kuma farin jikin daya samu a tsakanin iyayenta wanda hakan ya hanata ko da wasa ta cewa Anty wani abu ya shiga tsakaninta da Abdool ba.


Har yanzu Lamido ne yake kaita makaranta, bata tambaye shi yadda yayi da Abbah ba, shi kuma be ce mata komai ba. Sai dai ta kan tsargu da abu ɗaya a yanzu, ya kan tsura mata ido ta madubi mota ko kuma idan tana waje kamar madubinshi.
Ita kuma a yanzu bata magana da shi saboda ya ƙi ya faɗa mata.




ABDOOL POV.


Tun da ya karanci halin da Namra ta sashi, sai ya ke ganin kamar Lamido ne yake masa zagon ƙasa, daman shi zuciyarsa bata natsu da zaman lamido a gidan ba, a duk lokacin da ya tuna sai yaji kamar zuciyarsa zata rabe biyu, musamman da yasan shi yake kaita makaranta ya ɗauko ta, tabbas yayi sake da yaba har tsawon wata takwas tana keɓancewa da Lamido, aiko dole ta so shi fiye da shi.


Kamar an masa allurar ƙarfi haka ya zabura ya miƙe tsaye be damu da saka hula ba duk da shaddace a jikinsa ya fito ya nufo part ɗin Ummi.


Be same ta a falon ba, sai Amal ya samu tana ta faman solved Maths.


“Dude Ina Ummi?”


“Tana Garden lalle ake musu, Dude na taso mu yi wannan assignment ɗin?”


“No bari sai na dawo fita zan yi”


Ya juya ya fice. A garden ya sameta zaune saman carpet ta jera ƙafafunta ana zizira mata lalle irin wannan na zamani.


Tsaye yiyi ya jingina da icen guava yana wasa da keys ɗin hannunsa.


“Ummi na canja shawara, zanje na ga Mai Martaba”


“Shawarar me?”


“Nan da One Months nake son a yi auren nan?”


Da mamaki Ummi ta kalleshi.


“saboda me?”


“Kawai ni nafi son haka ne”


“To su ƙanenka da aka saka date ɗin aurenku a tare fa?”


“Su a barsu sai lokacin ni kan gaskiya i can't wait, zan samu Mai Martaba mu yi magana”


“Amman zai zama kun yi magana biyu Abdallah, da ka yi haƙuri har lokacin nan da wata biyar a ba wani abu ba ne”


“Haƙuri ba zan iya ba Ummi, kawai ki min addu'a”


“Toh Allah yasa alheri, amman nasan Mai Martaba ba zai amince ba”




“Zai amince ki daina ƙwanƙwanton mahaifina akai na”


Hannu ta ɗaga masa.


“Tafi kai da kan ka zaka dawo ka ba ni labari”


Murmushi yayi ya juya ya bar Garden ɗin tana ta saƙe-saƙe a ranshi har ya isa faɗar Mai Martaba.
Be same shi a gida ba, saboda wani taro da taje, haka ya zauna a gidan har aka yi sallah magariba, bayan ya fito daga masallaci ne Mar Martaba ya dawo, dan shima sai da ya tsaya a can suka yi sallah sannan ya kamo hanyar gida.


Mai Martaba na gaba Yarima Abdool na biye faɗawa sai zuba masa kirari suke har aka shiga fada. Kai tsaye Mai Martaba ya wuce turakarsa Abdool ya rufa masa baya yana masa bangajiya. A saman fafaffaɗa kuma ƙasaitacciyar kujera Mai Martaba ya zauna ya cire rawaninsa ya miƙawa Abdool. Bayan ya aje rawanin ya dawo kusa da ƙafafun Mai Martaba ya zauna yana mai natsar da kai kasa kamar yana gaban sukurinsa, ya kan yi hakan a duk lokacin da da yake neman wata alfarma a gurin mai Martaba saboda kawai Mai Martaba yaji tausayinsa ya amince.


“Buɗe baki ka yi magana, Babana ni mahaifinka ne idan ban maka uzuri ba waye zai maka?”


“Allah ya taimaki Mai Martaba ya ƙara maka lafiya, daman magana ce na zo da ita akan auren mu, sai dai ban san ta fuskar da zaka kalli abun ba”


Mai Martaba ya jingina da kujera yana cigaba da kallon ɗansa. Abdool ya cigaba ba tare da ya ɗago ya kalli Mai Martaba ba.


“Idan har ka amince min, ina son ka roƙa mahaifin Namra akan ya rage lokacin da ya saka na aurenmu saboda yayi tsawo...”


Sai da aka ɗauki tsawon ɗakika talatin da huɗu wata kalma bata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login