Showing 18001 words to 21000 words out of 281103 words

Chapter 7 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61213

musu ihu suka gudu suka shige motar, bayan sun wuce ne, na ƙarasa inda take ina neman taimakon jama'ah ganin halin da take ciki, da jama'ah suka fito sai suka ce sun santa a nan gidan take, dan ni ba ɗan unguwar nan ba ne ban san ta ba Wallahi”


Wani irin abu ne ya taso ma Abbah, tun daga kan ɗan yatsan ƙafarsa zuwa ƙasan zuciyarsa, a take kalar idanunsa suka canja, wata jijiyar ɓacin rai ta taso masa, ta ratsa gefen wuyansa zuwa kansa, a hankaɗe ya kalli Anty Amarya.


“Yaushe ta fita?”


“Wallahi... Ban ...san ...ta fita ..ba ...”


Anty Amarya ta amsa murya na rawa. Abbah ya katsa mata tsawa




“Baki san ta fita ba kamar ya? Taya zata fita ba tare da kin sani ba?”


Kamin Anty Amarya ta ƙara bashi amsa, sai mama Zainab ta yi ɓaranɓarama, a ƙoƙarin kare Anty Amarya.


“Wallahi duk muna falo ta fita, babu wanda ya san da ita, ta hanyar kitchen ta bi, wai zata yi sallama da saurayinta”


Anty Amarya jin tayi kamar ta matse bakin Mama Zainab amman ba dama.


“Junaidu!”


Hajiya Barau ta ƙwalawa mai gadin kira. Da sauri ya amsa dan yana kusa da ita, yana kallon Namra dake kwance cike da mamaki.


“Ya aka yi Namra ta fita? Ba dokar gidan nan bace idan anyi magariba ba wanda ze fita?”


Jikinsa ya hau ɓari, yana ƙoƙarin ƙare kansa.


“Wallahi sai da na yi mata magana, sai tace wai saƙo zata karɓo nan kusa, ni sam na manta ma da bata dawo ba sai yanzu”


Abbah ya kalli Baba Audu


“Kasan mutanen ne? Zaka iya gane su?”


Baba Audu ya yi shiru kamar mai nazari.


“Gaskiya ba zan iya gane su ba, amman dai na ji suna faɗin Aasimu ko Ƙasimu, suna ce masa ya yi sauri su tafi”


“Asim..!”


Abbah ya amsa da ƙarfi. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli mutanen.


“Na gode sosai, Allah ya saka ma kowa da alheri”


Sai da suka masa Allah ya kyauta, sannan suka fita kowa bakinsa ƙunce da magana, wasu kuma mamakin fitar da ta yi suke, ga kuma ɓarin zancen da Mama Zainab ta yi.


Maryam ta nufe ta tana faɗin


“Abbah akai ta asibiti, duba fa bata motsi”


Juyawa Abbah ya yi ya nufi part ɗinsa rai a ɓace. Hajiya Barau ta ce


“Daga ta zan ɗauko mota akai ta, ai kisan halin Abban ku sai dai ta mutu a nan”


Hajiya Barau ce taja mota, da taimakon Hindatu da Mama Zainab suka sa Namra a mota, suka nufi asibitin dake kusa da su.
Suka bar Anty Amarya da Maryam suna aikin kuka, Hajiya Raliya na bata haƙuri, sai kawai Aisha ta yanke jiki ta faɗa iskokanta suka taso.




*** *** ***


Suna shiga Uduth, aka wuce da ita emergency, da sauri Nurses suka karɓe ta, aka ɗorata akan gado, suka shiga da ita wani ɗaki, taimakon gaggawa suka shiga bata kamin Likitoci su iso.


Ba a fi minti biyar ba, Doctor Hilal ya shigo cikin manyan kaya, hannayensa zube a aljihu, tare da wani likita, hankalin kwance ya ƙarasa inda take kamar ba marar lafiya ze duba ba.
Duk natsuwa Nurses ɗin suka yi suka ja da baya suka bashi guri. Hannu ya kai ya taɓa gefen wuyanta, yana kallon agogonsa hannunsa, sannan ya kalli drip ɗin da aka ɗora mata.


“Ku cire mata drip ɗin nan sai numfashinta ya dawo, ku kira Doctor Adamu ko wani likitan, da wannan ba aikin Likita ɗaya ba ne”


Yana kaiwa nan ya juya, sai Likitan da suka shigo tare ya yi saurin cewa.


“I'm sorry Doctor, Doctor Adamu is not around, that's why i call you”


Juyowa ya yi ya kallesa


“Wannan ba aiki na ba ne, and you know it, tiyata kawai na zo yi garin nan, ba kuma zan ɓata lokaci na akan abunda ba aiki na ba, jirgi zan bi na koma kaduna a can ma ina da aiki”


Yana kai wa nan ya fice. Da sauri wasu Nurses suka fita dan kiran wani likitan, shi kuma wannan likitan ya shiga bata taimako.




KALSOOM POV.


Tana tashi daga aiki, ta wuce gidan ƙawarta Salam dan labarta mata halin da take ciki.
Bayan Salma ta kawo mata abinci ta ci tayi sallah, sai take bata labarin abunda ya faru.
A maimakon ta ga ɓacin rai a fuskar Salma na taya ta baƙinciki irin mijin da zata aura, sai ta ga Salma na murmushi da yima Allah godiya


“Alhamdullah Allah mun gode maka, haba Kalsoom ko dan daɗewar nan da kika yi ba aure, be isa yasa kiyi haƙuri ki auri wannan ɗan'uwan naki a haka ba? Kina ji fa na faɗin da babbar budurwa ƙara ƙaramar bazawara, ƙannenki biyu a ɗaki ke kina nan, haba Kalsoom ki yi tunani mana”


“Ba auren ne bana so ba Salma, halin Sadiq ɗin ne na ke tsoro, ina gudun abunda ze je ya dawo, tun kamin tafi ake shawara ba sai an dawo ba, Wallahi na tsani mutum ne neman mata”


“Dan Allah ki daina faɗar wannan maganar, kar wani ya jiki ya san sirrinki, nema mata yanzu ya zamo ruwan dare, da wahala ki samu namiji me aure ko marar aure da baya neman mata, ko wace mace da kika gani a gidan mijinta tana da nata matsalar, no married friend of yours will ever tell you her marital problems,no woman will tell you her husband's fault amma karya take tace he is perfect,because no one is, dan Allah kiyi auren ki Kalsoom ke kaɗai ce a cikin kawayen mu kika rage baki yi aure ba”


Wani kallo Kalsoom ta yi mata, tana mamakin yadda ta kasa fahimtar ta.


“I have never blame myself for being single, i know I'm pretty, i'm well behaved, i'm Godly,and yet still single. Salma thats just how nature works, that is how Allah has designed it.
Idan duk a cikin ƙawaye na ni kaɗaice ban yi aure ba so what? Ni nayi kai na? Allah who created me differently and created them differently, surely made you destinies different. Komai lokaci ne Salma i don't want to rush into marriage with just any guy just because i want to be married, babu mai son ya je ya yi aure ya fito”


Salma ta dafa ta


“Haba Kalsoom zaki yi auren ne da niyar ki fito? Your idea is inside you Kalsoom, kiyi tunani me kyau, amman aure nan shi ya fi, kawai ki bawa Allah zaɓi”


Hawayen da suka zubo mata ta share ta ɗauki jakarta ta rataya.


“Na gode Salma zan yi tunani akai”


Har bakin gate Salma ta rakota, suka yi sallama sannan ta koma. Tafiya Kalsoom take tana tunani, sai taji ana mata horn, juyowar da zata yi sai taga wata hadaɗɗiyar mota mai kyau, tana binta a baya. sayawa tayi sai mai motar ya zo dai-dai ita ya tsaya, yana sauke gilashin motar.
Dattijo ne mai yalwatacciyar fuska da cikar kamala ta mai kuɗi.


“Shigo mana”


Ya faɗa yana buɗe mata front seat. Bata kawo komai a ranta ba, sai kawai ta buɗe motar ta shiga. Driving yake kaɗan-kaɗan yana gaisawa da ita.


“Ya kike ya gida?”


“Lafiya ƙalau”


“Ina zaki je ne haka?”


“Gida”


“Kuma kike tafiya a rana haka, kar fa rana ta taɓa min ke”


Ɗan murmushi tayi ta gyara yafin gyalenta.
Ba ko kunya ya kai hannu ya yaye mata gyalen


“Haba ke kuwa ya kiƙe ƙoƙarin rufe min kyau nan naki...”


Be karasa ba ta buge masa hannu tana masa wani kallo


“Sauke ni Malam, ni ba irin waɗannan matan bane”


“Haba kyakkawa daga magan...”


“Ka sauke ni nace!”


Ta faɗa a tsawace. Ba shiri ya ya faka motar ta buɗe ta fita tana tsaki.


“Ku ba za ku ce kuna son mace da aure ba sai lalata, duk Namijin da ka haɗu da shi abunda kawai yake ƙoƙari ya kai ga jikinka, ƴan iska kawai marar mutunci”


Haka tayi ta zaginsa, shi dai be bi ta kanta ba ya ƙaɗa motarsa yayi gaba.






_______________________________


Share it please, and drop your opinion. 🙌


Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa10.html


🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*


Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


*PAGE - 10*




UZAIR POV.


A guesthouse ɗin suka koma. Bayan Najeeb ya fito motarsa sai Uzair ya fito, suka nufi bayan motacin da suke gurin.
Ta inda suka san ba za'a gansu ba suka tsaya. Sai Najeeb ya kalle Uzair ya ce


“Uzair zaka janye maganar auren nan gobe gobe ba sai jibi ba, ka ce ka fahimcin tana da wanda take so, dan haka kai ka haƙura.
Sai idan ka yanje maganar ne sannan za mu je da kai gurin Malam gobe da nisa, dan ba za a yi mata magani kana auren ta ba”


“Amman idan mahaifinta yaƙi yarda fa?”


Najeeb ya yi masa wani kallo


“Ta ya zai ƙi yarda ? Shi ze aure ta ne? Ya kake abu Uzair kamar ba ɗan duniya ba? Sai wani ɓoye-ɓoye kake ai gashi nan ka jawa kan ka”


“Babu babbar matsala kamar ganin da tayi min, yanzu idan ta faɗa dame zan kare kaina”


“Sai kace ai ta saba maka ƙazafi, kai ma ai kasan kayi kuskure na bari ta ganka, kamata ya yi kasa a ɗauko maka ita”


Uzair ya yi shiru yana nazari, tashin hankali bayyane a fuskarsa. Kiran Amira tana ta shigo masa a waya amman yaƙi ɗagawa.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare kiran Baba Audu ya shigo wayar Najeeb. Cikin sauri ya ɗauka yasa hands-free.


“Hello Baba Audu ya ake ciki?”


Daga ɗayan ɓangaren Baba Audu ya amsa


“Na gama komai, na fito ina babban ti-ti, dai-dai inda kace na tsaya”


“Ina fatar anyi nasara?”


“Komai ya tafi yadda kake so”


“Toh ka jira ni, zan zo nan gurin na ɗauke ka”


Daga haka ya kashe wayar, ya kalli Uzair.


“Yanzu ka wuce gida kawai, ni zanje na ɗauko shi, idan ka taso aiki gobe mu haɗu a guesthouse ɗin Jafar, kuma ka tabbatar da ka sallami waɗannan mutane da suka ɗauko ta in case of”


Be jira abunda Uzair zai ce ba, ya nufi motarsa. Sai bayan ya fice sannan Uzair ya nufi cikin guesthouse. Be daɗe ba ya fito ya buɗe motarsa ya shiga, ya ɗauki hanyar da zata kai shi gidansa.


Tun kamin yana yin parking ya kashe wayarsa, sannan ya fito ya nufi hanyar falon.
Yasmin na zaune falo tana duba wasu takardu da system Uzair ya shigo da sallama.
Sai dai bata amsa masa sallamarba ma balle har ta ɗaga kai ta kalle. Kamar hakan be dame shi ba, sai kawai yazo ya zauna kusa da ita ya rufe system ɗin dake gabanta.
Yana ganin ta unƙurin zata tashi, sai yayi saurin riƙe ta ya zaunar, ya danneta da dukan ƙirjinsa ya ɗora mata nauyinsa, yana ƙoƙarin saka mata hannu ciki riga.


“Haba Bloody miyasa kike min haka ne? Dan kawai zan ƙara aure sai na zama maƙiyinki? Ai badan bana son ki zan ƙaro wata ba, sai dan rufin asirin mu”


A kaɗan-ƙaɗan ya raɗa mata haka, cikin wani irin siga na son tada mata hankali, sai numfashi yake sakar mata a kunne.
Ƙoƙarin ƙwatar kanta take amman ta kasa, ta ƙara haɗe rai sosai.


“Sake ni mana, Uzair bana son haka”


“Zan sake ki, amman sai kin faɗa min idan kin daina fushi da ni, idan kuma baki daina ba toh zan janye maganar auren”


“Maganar auren ka be dame ni ba, babu ruwana da lamarin auren ku, dan haka ka daina saka ni a ciki”


“Babu ruwanki da lamarin aure na kuma kike fushi da ni?”


“Amman dan zaka yi aure sai ka rasa wadda zaka aura sai Aminiyata, kuma ƴar'uwa ta”


“Nima ai ƴar'uwata ce, kuma naga kamar zaku fi zaman lafiya”


Wani dogon tsaki taja, tasa guiwar hannunta ta buge masa ciki. Ba shiri ya sake ta ya dafe cikin.


“Yasmin kashe ni zaki yi?”


Tsaki ta sake masa ta wuce ɗakinta, tana cika da batsewa. Da kallo Uzair ya bita yana murmushi, sai da ta shige ɗakinta sannan ya tashi ya nufi ɗakinsa.


Tun da asubar fari Hajiya Barau ta bugo masa waya ta faɗa masa abunda ya faru. Yi yayi kamar be sam komai ba, duk ya firgice yana nuna damuwa, sai tambayoyi yake zubo mata, yana nuna mata tashin hankalinsa kamar ance masa gata nan gabansa.


“Ban san miyasa Namra ta tsane ni har haka ba, ban san abunda na tsare mata ba, na rasa gane kanta”


“Uzair, inda har ba Allah yayi auren nan naku ba, bana jin zata zauna gidanka ko da ka aureta, kuma Wallahi a yadda zuciyar Namra take ko kashe ka zata iya yi ko kuma tayi maka wata illar, tun da bata son ka”


“Daman abunda Hajiyata take ta faɗa kenan, ni ina ganin gaskiya haƙura zan yi, ƙara taje ta auri wanda take so kawai”


“Da kam yafi maka, dan wannan auren ba zai yi ƙarƙo ba, sannan bana jin wannan yaron daya ɗauke ta ze barta haka nan, kar ayi maka kwashe-kashe”


“Barin ze fi tun da har zuciyarta wani take so, kuma duk macen da zata iya bin saurayinta kinsan ta girma”


“Ashe kai ma kana da tunani, fasa auren akam zai fiye maka”


Daga haka suka yi sallama. shi kuma ya sauka saman gadon ya nufi bathroom.
Sai tara da ƴan mintuna ya shirya, be damu da breakfast ya fito ya nufi parking space. Lokacin Yasmin har ta daɗe da barin gidan. Direct gidan Mahaifiyarsa ya nufa Hajiya Binta. A can ya yi breakfast yana labarta mata abunda ya faru, sai tace masa ai Hajiya Barau ta kira ta ta faɗa mata komai. Ta ji daɗin maganar da yayi ta basa auren Namra, ita daman zuciyarta bata natsu da aurensa da Namra ba, tun lokacin da tayi masa ƙazafi.




NAMRA POV.


Cikin ikon Allah numfashinta ya dawo, sai aka ɗaura mata drip,
Sai dai bata farka ba sai kusan Asuba, a lokacin Mama Zainab ce kawai a ɗakin, dan Hajiya da Hindatu tun cikin dare suka koma gida.
Kuma har garin Allah ya waye babu wanda ya leƙosu sai Amira, ita ma sai goma har da rabi sannan ta iso.


Namra na zaune jugummm tana tunani hawaye na bin fuskarta. Amira na shiga ta je da gudu ta rumgume Namra tana kuka.


“Wallahi da ba'a ganki ba Namra, da kashe kai na zan yi”


Namra ta share hawayenta, ta kalli Amira.


“Amira ina Asim yake?”


Gabanta ya faɗi, har sai da ta haɗiye yawun bakinta ta.


“Ina Asim yake Amira? Taya Asim ya zo gidan ku har ya baki wannan number?”


Nan ma kasa amsawa ta yi sai kukan munafurci take, zuciyarta na tsara mata irin ƙaryar da zata yi Namra dan kare kanta. kamin ta amkaro har Namra ta ƙara mata wata tambayar.


“Amira ki amsa min mana, ina Asim? Amira number da kika ba ni bata Asim ba ce, lokacin dana je ba Asim na gani ba Uzair na gani, faɗa min ta ya haka ya faru?”


Har lokacin Amira shiru take, bakinta sai rawa yake ta kasa magana. Hakan ya tabbatar ma Namra abunda take zargi.


“Uzair ya haɗa kai da ke an cuce ni”


Dam! Dam!! Dam!!! Zuciyar Amira take bugawa har cikin ƙwaƙwalwarta, ja ta yi da baya tana girgiza ma Namra kai hawaye na fita a idonta.


“Ki zargi kowa da cin amanarki, amman ban da ni, har a bada Amira ba zata taɓa cin amanar Namra ba”


Namra ta ɗaga mata kai tana hawaye.


“Asim ma ba zai iya cin amana ta ba, karki yaudari kanki wajen nuna min Asim yana so ya cuce ni. Amman ke Uzair zai iya siyen ki ya biya ki dan ya cimma burinshi, babu wanda ze fahimci ni, na ɓata ran kowa, ban san hali da Mahaifana suke ciki ba, sanadin ke da Uzair”


“Namra karki yanke hukuncin abunda baki sani ba, zan iya dafa miki qur'ane Namra, ban haɗa kai da Uzair ba dan na cuce ki.
Namra ta ya zan haɗa kai da wani ya wulaƙanta ki a titi? Har sai jama'ar unguwarku sun ɗaiko ki su kawo gidanku, Kuma su bada shaidar sun ji muryar Asim kuma sun ji an kira sunansa.


Namra tun da na bar gidan ku, ban rumtsa ba saboda tunanin da kukan rashin sanin halin da kike ciki, kina fita Maryam ta shigo ni ta ɗaurawa laifi tace ni ce silar komai, na yi tunani ke zaki bada shaida akaina ashe na yi kuskure.


Namra ki faɗa min dalili ɗaya, da zai sa na cuce ki, faɗa min Namra? Kinsan a iya zamantakewar mu da ke duk wanda ya ci amanar wani Allah sai ya fitar masa da haƙƙinsa”


Da wani irin kuka ta ƙarasa maganar kamar ta sheɗe. Kalamata sun sa jikin Namra sanyi, sai zargin da take mata ya soma raguwa, sai dai har yanzu bata ji zuciyarta ta natsu da Amira ba.
Kan ta ya kulle, ita dai tasan ba mafarki tayi ba, tabbas ta yi ido huɗu da Uzair kuma ya riƙa ta, sai dai bayan nan bata san wani abunda ya faru ba.


‘Taya Uzair yazo gurin? Miye dalilin da zai sa Uzair ya yi min haka? Taya Amira zata cu ni ta’


Sune tambayoyin da suka tsaya mata a rai, kuma suke ƙoƙari riƙita mata ƙwaƙwalwa.
Jin Amira ta dafa ta ya dawo da ita daga dogon tunanin da take.


“Namra kin fi kowa sanin ni wace ce...”


Bata ƙarasa Namra ta kai hannu ta riƙa hannunta.


“Ki yi haƙuri, kaina a kulle yake, a yanzu bana iya banbance gaskiya da ƙarya, bana iya tantance komai na rasa gane abunda yake faruwa da ni...”


Da kuka ta ƙarasa maganar, sai Amira ta rumgume ta suna kukan tare.
Shigowar Mama Zainab ne yasa suka tsagaita kukan, suka share hawayensu.


“Kuka fa ba zai muku ba, abunda ya faru ya riga ya faru sai dai a tari gaba. Likitan ya rubuta miki wani magani?”


Ta tambaya dan ɗazu Likitan daya shigo ne yasa ta fita, ta basu guri. Namra ta ɗauki takardar dake gefenta ta miƙa mata.


“Bai rubuta min komai ba, ya dai bani takardar sallama, yace bayan sati biyu na dawo”


Mama Zainab ta karɓa tana faɗin


“Masha Allah, sai ki tashi muyi harama,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login