Showing 63001 words to 66000 words out of 281103 words

Chapter 22 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61248

ba wayana ya faɗi ban sani ba ko ya kira”


“Har yanzu baki daina halin ki na sakarci ba ko? Ya faɗi ko dai kin siyar?”


“Wallahi faɗuwa yayi”


“Namra ki yi hankali da mutane, ba kowa ne yake son ya gan ka a cikin alheri ba, wani yana baƙincikin yaga kana jindaɗi, wasu fa hassadarsu ba ƙarama bace, kowa abunda yake ƙoƙarin yi ya ture ka daga jindaɗin shi ya shiga, ko kuma ya ture ka duk ku rasa, ba kowa bane zai so ki tsakani da Allah ba, idan kina da shi kowa naki ne, sai ranar da kika rasa komai zaki gane masu son ki da gaskiya


Wani ƙiyayyar tasa a ɓoye take ba zaki taɓa ganewa ba, haka zai ta miki zagon ƙasa har sai ya ga kin rasa komai sannan hankalinsa ya kwanta, dan haka kiyi tunani sosai da duniya, idan baki da hankali mutanen duniya za su miki shi, ki rage damuwa a ran ki ki sawa ran ki sassauci”


“Na gode Anty”


Ta faɗa har cikin ranta, kalaman Anty sun mata daɗi, sai dai tasan ba kowa Anty ke nuna mata ba, sai Asim dan tana tunanin kamar da biyu ya aureta, gani take har yanzu Anty bata yarda da Asim ba.


“Allah ya ƙara masa lafiya, na kira wayarki ban samu ba, shine Maryam ta karɓo min number Asim”


“Eh ai naga line Maryam ne, na gode sosai”


“Tau Sai anjima”


“Okay




Daga haka suka yi sallama. Wayar na yankewa wa Namra ta tsara text ta tura mata Anty Amarya a wayar Maryam.


“Maryam... Zo ki karɓi wayar ki”


“Na'am”


Ta aje system dake jikinta, ta taso ta nufo ɗayan ɓangaren inda Anty Amarya take. Tana karɓar wayar text na shigo, Anty Amarya bata kula ba, ta miƙa mata wayar ta nufi gurin sha'aninta.


_Anty ina cikin matsala, bana iya faɗa miki a waya nasan faɗa zaki min, dan Allah ki taimaka min da kuɗi ko kaɗan ne_


Maryam ya gama karanta saƙon taja wani dogon tsaki ta danna deleted ta goge saƙon.


“Ai fa kullum haka zai riƙa saki kina yi, tun da yaga be samu abunda yake so ba, kai mutanen duniya nan da abun haushi da mamaki suke, ala dole dan auri yar masu kuɗi kai sai kayi arziki, to sai kaje ka ci ubanka, ya mayar da ita saniyar tatsa”


Ta koma mazauninta tana mai jin haushi Namra da Asim ɗin.




KALSOOM POV.


Hilal na kallonta ta girgiza masa idonta da hawaye.


“Wallahi ban aikata ba, ban san wannan mutumen ba Wallahi”


Hannu Hilal ya kai ya ɗauki hotunan yana kallo. A-uzubillah hotunan babu kyau kallo, Kalsoom ce tsirara ita da wani, wani gurin yana kissing ɗinta wani gurin kuma tana kissing ɗinsa.
Ɗaya bayan ɗaya ya riƙa duba hotunan har ya gama sannan ya kalleta yace


“Kin san wannan mutumen”


“Wallahi ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba”


Ta faɗa da kuka.


“Daga ganin wannan ma ai haɗi ne, i trust my wife's ba zaki aikata irin wannan abun ba, duk yadda akayi wannan abun shirya sa akayi”


Ta ƙara fashewa da kuka


“Wallahi sheri ne kawai, na rantse da Allah ban taɓa ganin wannan mutumen ba”


Shiru Hilal yayi kamar mai nazari.


“Ina suka samu hoton ki?”


“Wallahi ban sani ba, dan Allah ka yarda da ni Wallahi sheri ne”


“Na yarda sheri ne, daga gani ma ai kasan haɗi ne, daɓ ga fatar fuskar ta banbanta dana jikin hoton, kuma miyasa ba a kawo lokacin da bana nan ba, sai da ina nan? za a iya haɗa irin wannan hoton a computer? But i can't believe is taya suka samu hoton ki?”




“Wallahi ban sani ba”


“Baki sani ba kamar ya? What kind of nonsense is this? Aljani za a turo ya ɗauki hoton ki ko me?”


Durƙushewa tayi ƙasa tana kuka.


“Wallahi ban sani ba Hilal na rantse da Allah ban aikata ba”


“Naji baki aikata ba, faɗa min ta ina suka aka samu hoton ki?”


Ya faɗa a tsawace irin zuciyarsa ta fara kawowa ɗin nan.


“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hotona ba”


Ɗuƙawa yayi a hasale ya kwashe hotunan ya nufi ɗakinsa da su. Wani irin zugi zuciyarsa ke masa, baƙin kishi ya taso masa.
Haka ya tiƙa duba hotunan kamar wanda zai haddace su, shi dai what he believe Kalsoom ba zata aikata haka ba, sai dai kuma kansa ya ɗaure har yana jin tunaninsa na ƙoƙarin canjawa.


Bedside drawer sa ya buɗe ya zuba hotunan ya rufe, sannan Shirya cikin ƙananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya ɗauki atms ɗinsa ya saka a aljihu da wasu ƴan canja, sannan ya ɗauki wayarsa da keys, ya fice daga ɗakin fuska babu annuri.


Sheshekar kukanta ya ɗago da hankalinsa i zuwa gareta, ashe duk tsawon lokacin tana a gurin tana aikin kuka, jikinsa ya mutu yaji ba daɗi ganin kamar shine silar hawayenta. Ƙarasawa yayi kusa da ita ya ɗafa ta


“Kalsoom Calm down, nima fa wayayyen mutum ne nasan za a iya haɗa wannan, amman kin ƙi ki bawa zuciyata damar yarda da hakan”


Ɗagowa tayi ta kalleshi tana kuka fuskarta da majina nashe-nashe.


“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hoto na ba”


“Kina da grp ɗin da kika chat da maza ko?”


Ta ɗanyi shiru tana tunani.


“Grp ɗaya ne, shima kuma na koyon sana'ah ne, kuma ban taɓa magana a grp ɗin ba Wallahi, Instagram ɗina da Facebook tun da nayi aure ban sake hawan ko ɗaya ba Wallahi”


“Good indeed, kina instagram ba? Kina facebook?”


“Amman tun da nayi aure ban sake shiga ba”


Zaunawa yayi kusa da ita yana cire password ɗin wayarsa.


“Ba ni handle ɗin ki”


“Kalsoom_Miss-Arewa”


Instagram ya shiga yayi searching sunanta, sai ga account ɗinta. Yadda ya riƙa ganin hotunan ta sai wani baƙin kishi ya motsa masa.


“Duba nan, yanzu miye amfanin waɗannan hotunan? Kina tallar kan ki kamar ba mace ba, miye abun burgewa a sakin jiki wasu mazan na kallo, ke a ɗaukar ki duk wayewa ce ko? Dole ne sai kin sa hotunan ki a instagram ko facebook?”


“Wallahi ni ba da wata manufar na yi ba”


“Nasan ba wata manufar kika yi ba, su yanzu waɗanda suke da wata manufar ai sun ɗauka sun yi yadda suke so da shi. Duk abunda addini yake hana ƙu baku ganewa, duk abunda kika ga musulunci yace a bar shi barin shi yafi alheri amman baku ganewa, dubi wannan abun wani gurin ma ai rabin jikin ki a waje, ba editing kaɗai ba har asiri sai a ɗauki hoton ki ta nan aje a miki”


Yaja tsaki yana mai miƙewa tsaye.


“Kamin na dawo ki tabbatar kin goge duka hotunan ki da suke facebook da Instagram, ban hana ki yin chat ba amman ban yafe ki yi da wani namiji ba da aurena, duk mazan nan nan friends ɗin ki yi unfriend ɗin su, kuma Wallahi kar na sake ganin hoton ki a social network”


“Wallahi ni daga yau ma na daina chat ɗin gaba ɗaya, amman ka yarda da ni dan Allah”


“Idan ban yarda da ke ba, zan zauna ina magana da ke haka? Very soon an gano wanda yayi wannan abun, akwai mai son shiga tsakanin mu ne”


Gabansa ta dawo ta risina ta riƙe ƙafafunsa.


“Na gode Allah ya saka mana”


Ɗagota yayi ya rumgume. Zuciyarsa cike da kishin hotunan can daya kalla, duk da yasan cewar ba haɗi ne amman yana kishin hakan.
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 30*


NOT EDITED ⚠️


Ƴan ƙuɗin da suka mata saura a jakarta, da kuma dubu ashirin ɗin nan Hajiyar gidan ta bata, su ne take ta maneji ta su tana siyen abinci.


A kullum gidan su Mardiya take kwana, wani lokacin har zanenta take ɗaurawa, kamin ta ɗinka kala biyar a cikin kuɗin. Tayi ta zuba ido tana jiran kuɗin Anty Amarya har ta gaji, tun tana sa ran zata ta kira wayar har ta gaji da jiran ta fara tunanin wata mafitar.
Da ta fito daga gida kai tsaye ta nufi gidansu Hajiya Saratu, har ta isa zuciyarta na nuna mata illar abunda zata yi, ko ba komai zai nisanta ta da Ubangijinta, sannan duk wanda yasan abunda ta aikata mutuncinta zai zube a idonsa, ashe Allah zai jarrabeta da wani matsi har kuma ta nemi tsaɓa masa, idan har ta yi haka bata kasance cikin nagartaccin bayi ba.


Juyar da fuskarta tayi gefen ti-ti tana kallon motocin dake kai da kawo, hawaye na silalawo daga idonta, wani bangare na zuciyar yana ƙoƙarin rinjayarta akan idan har ba ita ba, bata da wata mafita, babu kuma wanda zai taimake ta sai ita. Haka ko wane bawa zuciyarsa take nasalta masa alheri da sheri duk ɓangaren daya rinjaye ka shi zaka aikata.
Hannu ta kai ta share hawayenta, tana mai jin ƙyamar abun a ranta, yanzu idan taje garin aikata ta mutu fa? Me zata cewa Allah? Haƙiƙa an jarrabi wasu gabaninta da suka yi haƙuri kuma sai Allah yayi musu mafita, kuma bayan ita za a jarrabi wasu a bayanta, haka Ubangiji yake jarraba bayinsa dan ya auna imaninsu da kuma yarda da ƙaddara.


“Haƙiƙa za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawayar dukiyoyi da rayuka, da ƴaƴan itatuwa , ka yi albishir ga masu haƙuri (Wajen jure waɗannan jarabce-jarabcen) Waɗanda idan masifa ta same su sai su ce INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN ma'ana :- mu ga Allah muka fito kuma a gare shi za a maiyardar mu. Wanɗannan gafara da kyakkayawan yabo daga Ubangijinsu sun tabbata gare su, da rahama kuma waɗannan sune shiryayyu.” (Baƙara: 155-157)


Tuna waɗannan ayoyin ya ankarar da ita abubuwan data manta, ji tayi kamar an tsikareta, gashin jikinta ya tashi, a nan ta soma tambayar kanta, dan me zata yarda zuciyarta ta rinjayeta ta tsaɓi Ubangijinta? Ta fita daga waɗancan bayin da Allah ke yabo? Ashe Ubangijinta be mata dukan gata ba? Ashe daman Imaninta ƙanƙane ne?


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Ta furta a fili, har sai da mai Napep ɗin ya kalleta.


“Hajiya lafiya dai?”


“Lafiya ƙalau dan Allah juya da ni ka kai ni babbar Asibiti”


“To amman fa wasu kuɗin zaki sake biya”


“Na ji mu tafi”


“Tau Hajiya lafiya kike kuka?”


Sai a lokacin ta tuna da hawayen dake fuskarta, sa sauri ta share hawayen ba tare data ce masa komai ba har suka isa asibitin, sannan ta fita ta ciro kuɗinsa ta ba shi.
Ko da ta shiga cikin ɗakin Asim na zaune, kamsa ya kumbura sosai har idonsa ɗaya ya liƙe, hankalinta ya tashi dan yanzu wannan kumburin ya fi na jiya.
Kusa da shi ta zauna zuciyarta cike da tausayinsa, har idaniyarta na ƙoƙarin zubar masa da ƙwalla.


“Asim kaga har yanzu Anty bata kira ba, kuma bata aiko ba, ni kuma bana da wata mafitar, ga kuɗi da ake bina ma ban san yadda zan yi ba, wannan kumburin naka yana tsorata ni”


Ya matse ƙallah data cika masa ido.


“Namra ko gida za mu koma ne?”


“Idan mun koma za su ce mun kwaso ciwo mun dawo”


“Likita yace idan ba allura nan aka min ba yana da wahala naji sauƙi da wuri”


Hannayenta tasa ta rumgume shi tana kuka. Shi kuma a take yaji sha'awarta ta saukar masa, ya kai hannu yana ɗan shafa ta. Data anƙaro da abunda yake nufi da ita sai tayi saurin ɗagowa daga jikinsa.


“Ina Mama?”


“Tana waje”


Ya sake miƙa hannu yana shafa fuskarta, yana ƙoƙarin ɗaga hijabinta ya zura ɗayan hannunsa ciki.


“Asim asibiti muke fa, kuma dubi halin da kake ciki”


Yawun bakinsa ya haɗe, ba tare daya daina abunda yake mata ba. Ana taɓa ƙofar ɗakin tayi saurin tashi tsaye, shi kuma ya bita da kallo idonsa har sun fara canja kala.


“Mama ina wuni?”


“Lafiya ƙalau ya rana?”


“Alhamdulillah”


Ta ɗan kalleshi cike da kunya, dan gani take kamar Mama ta lura da abunda suke.


“Bari naje gurin Hajara”


Bata jira abunda zai ce ba ta fice. Sai Mama ta zauna a kujerar dake kusa da Asim tana faɗin


“Lamarin nan naka fa ƙaruwa kawai yake yi”


“Tau Mama nayi maganar kuɗin adashen nan kin kawo wasu hujjoji na daban, ko mutuwa na yi ai ke kika rasa ni tun da su ƴar su wani zata aura”


“Shawara da nake kenan a zuciyana, zan je nayi mata bayani sai na karɓo kuɗin daman dubu ɗari uku ne, idan Allah yasa ka samu sauƙi sai a shiga wani kuma”


“Haka yafi, tun da kin ga har yanzu basu saje kira ba ma balle su aiko. Yaushe zaki je?”


“Gobe nake son naje, nima kuɗin da suke hannun na duk sun tafi gurin siyen abinci, ga tufafin nan ƙala ɗaya kullum ƙara naje ya ɗauko wasu tun da waɗanda muka zo da su sun ƙone, da Hajara zan koma in yaso sai na dawo ni kaɗai, daman Haruna ya matsa da maganar yaushe zata dawo”


“Ni Wallahi inda da hali ma da kin tafi yanzu, sai ki dawo gobe da wuri, dan ni kaɗai na san halin da nake ciki, kuma kin ga yanzu aka yi ƙarfe ɗaya, nasan zuwa yamma kin isa”


Ta ɗan yi shiru tana nazari.


“Rana be yi ba?”


“Be yi ba Wallahi, tun da kin ga ma Namra ta zo sai ta zauna nan har ki dawo”


“Tau bari na gani, ai duk na natse ma da wannan kumburin na ka”


Ta tashi ta fita cikin yanayin damuwa. Wayar Asim dake hannun Hajara Namra ta karɓa, ta saka number Babban Yayansu ɗan Hajiya Barau, sai ta matsa can nesa da Hajara ta kira shi.




KALSOOM POV.


Ba itace da girkin ba, amman sanin halin Rashida yasa bata tsaya jiranta ba ta shiga kitchen ta ɗora musu breakfast, daman wani lokacin ita take shirya musu tun da Rashida aiki take zuwa.


Sai da ta shirya komai, na karyawa sannan ta ɗauko kulolin su ta zuba musu abincin su, sannan ta kira su ɗaya bayan ɗaya ta miƙa musu kulolin.


“Ku je gurin mota zan tashi Daddyn ku yanzu”


Ta nufi ɗakinsa, tana buɗe maɓallan rigar bachin ta. A tsakiyar gado yake kwance yana lulluɓe irin yana jin tsayi ɗin nan.
Air conditioner ta fara kashewa sannan ta nufi window ta buɗe su duka ta ɗage labulayen sannan ta nufo inda yake kwance ta yaye bedsheet ɗin tana taɓa masa kunne.


“Likita tashi safiya yayi fa”


Hannu ya kai ya janyo ta saman gadon ya rumgume ta


“Ban gaji da bachi ba”


“Yara suna gurin mota suna jiran ka”


“Ya salam”


Ya ƙara rumgume ta tsamtsam ƙirjinsa, kamar ba zai tashi ba, sai faman lumshe ido yake alamar bachi na masa daɗi.


“Doc. Doc. Doc”


Shiru be motsa bama balle ya amsa ta, hannu ta kai ta murɗa masa kunne, har sai da tayi ƙara ya kama hannunta ya ciza sannan ya tashi, yana jan kitson ta.


“I hate dis Morning”


“Really”


Ta tsire baki tana koyonsa.


“I hate dis Morning”


Ya zare ido, lokacin da idonsa suka kai kan ƙirjinta.


“Wow”


Ya kai hannu zai taɓa ta, ta fisgi kanta cikin zafin nama, ta sauka saman gado ta fice daga ɗakin tana masa dariya.
Tashi yayi ya shiga bathroom ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya kai yaran makaranta. Ko da ya dawo babu kowa falo, sai kawai ya nufi ɗakin Rashida dan yaga motarta waje alamar yau bata fita da wuri ba kenan.


Tana ganin ya shigo ta juya kwancinta ta bashi baya. Hakan be da me shi sai ma dariya da yayi ya ƙarasa kusa da ita ya juyo da ita, hawayen daya gani a idonta ya tashi hankalinsa.


“Lafiya Pyar?”


“Bana jindaɗi ne”


“Me ke damun ki”


“Nima ban sani ba”


“Amman miyasa baki faɗa min ba?”


“Taya zan faɗa maka bayan ta shiga haƙƙina taje ta tashe ka, kuma ta san yau ba girkin ta bane”


“Ta riga ta saba ne, saboda kina fita sa sassafe ba tare da kin damu da tashi na ba, balle haɗa mana abun karyawa”


“Ni gaskiya ta daina shiga min haƙƙi bana so”


“Shikenan zan mata magana, amman yanzu faɗa min me kike ji yana damun ki”


“Fever, sneeze, headache and nauseous”


“Zan diɓi jininki da fitsari idan zan fita, yanzu tashi mu karya sai ki sha magana”


Ta ƙara manne masa a jiki.


“A'a ni bana so cin komai”


“Tea fa?”


“Sai dai idan kai zaka haɗa min da kan ka”


“Yes ni zan haɗa miki ai”


Ya faɗa yana murmushi, sannan ya tashi ya fice. Ajiyar zuciya Rashida ta sauke, ranta yana mata ba daɗi, idan har zarginta ya tabbata gasjiyar tana da ciki, tana cikin matsala dan bata iya tantance na waye ne,


‘Taya wani zai gane idan ba ni ma faɗa ba?’


Tambayar da tazo mata kenan a zuciyarta, sai kawai ta tashi ta shiga banɗaki.


Hilal sai da ya shiga ɗakinsa ya ɗauko maganinka sannan ya nufo ɗakin Kalsoom, a lokacin tana zaune gaban madubi tana shiryawa dan fitowarta daga wanka kenan.
Daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta yace


“Wifey Yau madam babu lafiya, ba zata fito ba tea kawai zata sha, ni ma kuma bana jin cin komai”


Kai ta ɗaga masa tayi murmushin da be kai zuci ba. Har ya wuce, sai kuma ya dawo ya tsaya bakin ƙofar ya miƙa mata hannu.


“Taso na haɗa miki breakfast”


Ba musu ta taso ta miƙa masa hannun ba dan ranta na mata daɗi ba. A kujerar data saba zama ya zaunar da ita, ya ɗauki kofi biyu ya haɗa tea, ya aje mata ɗaya gabanta ya zuba mata ƙwai da sauran abubuwan da suke gurin, sannan yaƴi mata kiss ya ɗauki tea ɗin ya nufi ɗakin Rashida.


Da kallo ta bishi, zuciyarta na sosuwa da lamarinsa, tabbas yana son matarsa fiye da yadda yake son kansa, yanzu ya kasa karyawa saboda bata da lafiya, ta lura da yadda yanayinsa ya canja a take, taya zata shiga rayuwar irin waɗannan ma'auratan sannan tace zata samu farinciki?
Hannu ta kai ta shafa cikinta, hawaye masu zafi suka silalo daga idonta.


Sai da ya bata tea ɗin tasha sannan ya bata magani, sai ya sake fita yaje ya ɗauko wasu robobi guda biyu ya miƙa mata babbar.


“Kiyi fitsari a wannan”


Hannunsa sanye da safa, ya ɗibi jininta ya zuba a ƙaramin robar sannan ya manna mata kaɗa ya lunda mata, ya kwance robar daya ɗaure mata hannun da shi, kwashe kayan yayi ya fice. Bayan kamar thirty minutes ya dawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login