Showing 150001 words to 153000 words out of 281103 words

Chapter 51 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61249

saba, ya maida hankali akn aikinsa sosai dan aiki ne mai muhimmanci.

Yau kam be kira Ummi da safe ba har sai da ya shiga office, yana shirin kiranta sai gata ta kira shi. Da sauri ya ɗauka Cikin jindaɗin kiran na mahaifiyarsa


“Ummi na ta kai na good morning”


“How are you?”


“Im fine i miss you, na ga nawa satin nan ya zo na zo gida na ganki”


“Nima ai ina son ka zo akwai maganar da zamu yi da kai”


“Wace magana ce?”


“Idan ka zo zaka ji, akwai kayan da nayi oda daga paris za su iso Lagos jibi, zan tura maka address ɗin sai ka aika a karɓo min”


“Yes Ma'am”


Dariya tayi ta kashe wayar shima ya sauke yana murmushi cike da ƙaunar mahaifiyarsa.


Ɗayan ɓangaren kuma yana jin rashin daɗin maganar da tayi ma mai martaba na cewar yace a nema masa mata, sai dai babu yadda ya iya tun da shi kansa ya san yana buƙatar auren a yanzu, idan be yi ba a yanzu sai yaushe, lokaci tafiya yake baya jiran kowa, kuma shi har yanzu be da wacce zai iya fitarwa a matsayin matar aurensa.
Sai dai shi kuma ya sha alwashin aurar da duka ƙanensa dan ba zai yarda Ummi ta riƙa matsa masa ba bayan ga ƙanensa mata nan duk sun isa aure.




*Ummi*
Tana gama waya da shi, sai ga Amira ta shigo da sallama cikin ladabi, already ta gaishe da Ummi da safe so bata buƙatar repetitive, sai kawai tace


“Ummi me za a girka na rana?”


“Ayi mana mana miyar kuɓewa sai Shukura tayi tuwon semo”


“Tau”


Ta miƙe tsaye ta fice cikin tsantsar ladabin nan. Bata kira Shukura ba da kanta tayi tuwon semo miyar kuɓuwa sannan kuma tayi miyar agusi dan kawai ta burge su. Ko da azahar tayi har ta gama komai ta jera a dinning sannan ta shiga tayi wanka.
A lokacin ne su Amal suka dawo makaranta tare da Haleema, daman yau Meesha bata je ba, dan su da lacca. Fauza ce kawai ta tafi sai Haleema.


A ɗaki suka samu Ummi da Meesha suna duba wasu atamfofi da aka turo ta whatsapp. Jikin Ummi Amal ta faɗa tana zuba shagwaɓa wai ita ala dole ga auta.


“Ummi yunwa”


“Ai ga abinci can ana gama”


“Me aka girka”


Haleema ta tambaya tana zaunawa kusa da Meesha.


“Tuwon semu miyar kuɓewa”


“Ɓi bana so, sai dai ki girka min makaroni”


“Kai Amal kin cika son rigima wallahi, miyar tayi daɗi fa”


“Wa yayi? Wannan Amira ko”


“Eh miya har kala biyu tayi”


.“Ni bana so bata iya komai ba sai ƙazanta”


Haleema ta buge mata baki


“Data saba girkawa kina ci fa? Wai Amal miyasa baki da kunya, ke uban kowa kin raina, Amirar nan aiki da take ko da muke cikin gida albarka, tana ƙoƙari sosai wallahi”


“Ta riga ta saba wahalar ne tun gidansu, maybe talakawa ne”


Cewar Meesha, tana taba eyebrows.


“Ba wani sabo wallahi kawai dai tana da mutunci ne, kuma gani nake kamar Big bros take so, dama an haɗa su wlh dan zata kula da shi”


Meesha ta tofarda yawu


“Tuuu Allah kiyaye big Bros da wannan yarinyar amman wallahi Haleema baki da hankali zuwa makaranta be amfane ki ba, daga ganin yarinya an taimaka mata ki ce wai ta auri yayanki, ke anya kina son yaya kuwa? Ke nifa ban ma yarda da yarinyar nan ba, tsantsan ɗinta yayi ta cika shige mana jiki, waya sani ko cutar mu ta zo tayi”


Amal ta haye saman gadon Ummi tana hararar Haleema.


“Sai na gayawa Dude, mu mana son ta”


Ummi ta kama kunne Amal.


“Bana raba ki da yi ma manya rashin kunya ba?”


“Ooo Ummi it hurt”


Ta riƙe kunne, tana son kuka. Haleema yaja wani dogon tsaki


“Ke kin wuce shiga halin da ta shiga ne hala? Idan Allah ya tubuta shine mijinta ya zaki yi?”


Ummi ta kalle ta kallo da babu wasa a fuskarta.


“Ke Haleema ki daina wannan maganar, yarinya daga taimako sai kuma neman wuce gurin tana da tarbiya zata bar gaban iyayenta ana neman ta koma bata so sannan ki ce ta auri ɗan'uwanki dan baki da tunani? Kin san iya zaman da ta yi taraiya da su? Wanda yayi maka hallaci ya cancanci hallaci shiyasa take zaune tare da mu, amman nan gaba kan gurin iyayenta zan maida ta, Allah ya bata miji na gari”


“Amman Ummi ta mana hallaci wallahi, kuma idan ba a barta ta auri Yaya kamar ba a mata hallaci ba”


Meesha ta zungureta


“Ai ke sai ki mata hallaci ko? Yayan manya ma Big Bros be so ba sai ita yarinyar data ƴan fashi, ashe za'a iya haɗa kai da ke ayi ma masa wani mugun abu, haka kawai daga ganin yarinya ki ce a haɗa su amman baki da hankali Haleema”


“Ke da kika da shi ai sai ki ara min na saka, ko ita ba mutum bace? Ke idan kina so wani ya zaki ji”


“Ba zan so wanda ya fi ƙarfina ba balle har na damu, ke daga ganin ajin Yaya kin san yafi ƙarfin Amira wallahi, yarinyar data gama bada kanta ga mazan banza sai kuma ta dawo yaya ya aureta, ai abun kunya ma ne wallahi”


Cikin faɗa Meesha ta ƙarasa tana jin kamar ta kama Haleema tayi mata shegen duka. Ita Haleema ji take kamar ta daki yar'uwarta. Har sai da Ummi ta katsa musu tsawa.


“Haleema kar na sake jin irin wannan kalamin a bakin ki, Aisha ke kuma ya isa tun da ba cewa aka yi za a aura masa ita ba, ku Shafa min lafiya dan Allah ku tashi ku bani guri”


Duk miƙewa suka yi suka fita, ban da Amal data laƙe jikin Ummi ita ala dole sai an dafa maya makaroni.


“Ai kema kin iya dafawa, Amal har mota kike tuƙi fa amman ki zo kina min abu kamar jaririya, idan yanzu aka miki aure ai sai zama dan kin girma, ba kece auta ba autana tana nan zuwa”


Ummi ta faɗa da raha a fuskarta. Amal ɗin tasa dariya dan tasan abu ne mai wahala a yanzu.


“Za a ce tsohuwa ta haihu”


Ummi ta tiƙi bayanta tana dariya


“Yes Tsohuwa maman Amal, tashi ki cire uniform”


Tashi ta yi ta fice tana dariya.




*NAMRA POV*


Kamar yadda suka saba yi duk mai ciwo, bayan ta faɗa masu matsalarta sai suka bata gwajin jini da fitsari, suka sa kuma taje ta yanki sabon kati dan duba wacan matsalar nata na robar dake hannunta dan a bayanin da ta yi ma likita ya fahimci ciki ne a jikinta. Sai dai bashi da tabbacin haka tun da ta faɗa masa tana saye da roba, duk da yasan ana samun irin wannan matsalar a wani lokaci.


Awan fitsari kawai ta samu yi, a take, na jini cewa suka yi sai da yamma ta zo ta karɓa, su kuma waɗanda zasu dubata a ɓangaren robar sun tashi aiki.
Tun da karɓo results ɗin ta kasa ta buɗe dan bata son ta ga abinda yake ciki, tasan idan har ciki ne tana cikin matsala dan bata gama warkewar ciwon mahaifarta, kuma ga roba jikinta ace tayi ciki tasan duka ƙarin matsalar ne. Ko da ta koma gurin likitan yana shirin tashi, har ya haɗa kayansa, a tsai-tsaye ya duba takardar tana fuskarsa da mamaki ya ce


“Kina ɗauke da juna biyu”


Ras ras ras gabanta ya faɗi, sai ta faɗi saman kujera tana hawaye. Da sauri likitan ya aje kayan hannunsa.


“Hey wannan ba wata matsala bace ana samun irin haka daman, amman abunda yafi zan rubuta miki hoto sai kije ayi hoto a bincika lafiyar cikin, kuma ki tabbar kin je an cire miki wannan robar”


“Doc mahaifa tana da matsala shiyasa aka samun robar”


“Ba lallai ne har yanzu matsalar ki tana nan ba, shiyasa nake son ki yi hoton”


Ya ɗauki wata takardar yayi rubutu ya miƙa mata.


“Kije ayi miki hoto, zuwa gobe sai ki kawo na duba ki, ko kuma ki dawo wani likitan ya duba ki, ki kwantar da hankalin ki ba wani abu nima mai ɗaki na ta taɓa haka”


Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya face. Sannan ita ta tashi ta fito tana hawaye, maimakon taje gurin hoton sai kawai ta yanke shawarar komawa gida dan ita har yanxu jikinta na bata ba ƙalau take ba, balle bata da kuɗin da zasu isheta hoto tun katin ganin likita na asibitin ma kusan ɗari bakwai ne.


Tun cikin Napep take ta kiran Asim amman ya ƙi ya ɗaga saboda yana gaban Hajiya, wacce ta zame masa kamar uwa a yanzu, yadda yake jinta ko Mama data haife sa baya jinta haka nan.
Hakan yasa ta yanke shawarar tura masa saƙon karta kwana.


Ƙin ɗaga wayar yayi dan akwai yana gaban Hajiya, ita ta jidaɗin hakan da yayi ko ba komai tasan ya girmamata, gashi tun da yazo gidan be taɓa fita da sunan yaje gida gurin matarsa ba.
Sai da ta gama lissafa masa abunda zai siyo mata sannan ta bashi kuɗin tana murmushi ciki ladabi ya karɓa ya tashi ya fice.


Sannan Hajiya tayi murmushi ta maida dubanta ga ƙawarta, Hajiya Ubaida.


“Gaskiya yaron nan yana da ladabi ina kika damo shi?”


“Uhmm tsuntsune daga sama gasasshe Allah ya bani daga gyaran gate”


A nan ta kwashe labarin komai ta bawa Aminiyarta yadda suka haɗu da sharaɗin data gundaya masa da kuma zaman gidan da yake, da kuma ƙudirinta a kansa.
Hannu Hajiya Ubaida ta bata suka taɓa


“Shegiya Sadiya duk abunda kika sawa gaba sai kin ga bayansa, hala yarinyar mai kyau ce?”


“Tana da kyau wallahi ta haɗu ba ƙarya, sannan kin ga na samu dama biyu, daman Alhaji Usaini ya dame ni na samo masa sabin shiga, wai duk wanda nake kai masa basa da ladabi kuma an taɓa amfani da su, kwana biyu sai su fara masa tsageranci”


“Ai kin san manyan mutanen nan sun fi son tsaida mutum ɗaya, wanda zasu riƙa amfani da shi kullum”


“Eh shi ma haka yace, wai idan yana bin irin guys ɗin nan za'a iya gane shi, yafi son tsaida mutum ɗaya, kuma kin ga irin wannan zai fi jindaɗinsa dan ga alama zai yi ladabi, sannan garin su ɗaya, idan ta kama ya koma can ma, ni sai ya barmin matar a nan, dan ba zan taɓa nuna masa ina don matarsa ba, shi wata rana zan iya buƙatarsa”


Hajiya Ubaida ta ƙalƙyale da dariya.


“Ke Allah dai ya yafe mana, ya shirya mu”


“Amin kedai ai ina son tuba amman sai nan gaba, dan bana son Zeenat ta san halin da nake ciki”


“Gaskiya kam, ai ƙara ai daina da wuri kar azo aji kunya”


Hajiya Sadiya tayi fuskar tausayi kamar mai tsoron Allah da gaske, tana kallon Hajiya Ubaida wacce sana'arsu ta zama ɗaya.




*ASIM*


Be wuce kasuwar ba, sai da ya bi ta gida dan jin abinda Namra zata faɗa masa, badan saƙonta da yaga ni babu ma abunda zai sashi bi ta gidan. Kamar baƙin haɗari haka ya doshi gidan bakinsa ƙumshe da maganganu kala-kala, dan gani yake a yanzu shi ma ya kai matsayin da zai iya faɗawa magana son ransa, balle Namra da yake gani kamar banza.


A ɗaki ya tararar da ita kwance sai hawaye take. Daker ta ɗago ta kalleshi, duk da tana cikin yanayin damuwa hakan be hanata, kallon irin shigar dake jikinsa ba. Takalmin dake ƙafarsa kaɗai zasu iya kaiwa dubu 10+ balle wando da T-shirt.
Be ji zai iya zama a ɗakinba, sai kawai ya tsaya jikin ƙofa yana mata wani kallo, azuciyaraa yake hantararta ganin yadda ta ƙara lalacewa.


“Ya aka kika samu ciki?”


Wani kallo tayi masa zafin furucinsa yana zuciyarta.


“Kamar ya? Ina da wani mijin ne bayan kai”


“Ni ya za'ayi na sani, yanzu ai ba a shedun mutum”


“Shigowarka Asim irin wannan furucin zaka min? Tun da kasa ƙafa ka bar gidan nan babu ruwanka da ni kamar ba matar ka”


“Ya kike so nayi Namra aikin zan bari na zo na tisaki gaba nayi ta kallo ko me? Yanzu ma a hanya nake saƙon da kika min ne yasa na biyo”


Kawarda kai tayi ta haɗe hawayen da take da tabbacin idan har suka fara zubar mata bata san lokacin tsayawarsu ba.


“Daga Asibiti na ke likita ya ce ina da ciki, kuma akwai roba a jikina”


“To ya aka yi haka?”


“Nima ban sani ba, amman yace min daman akan samu hakan wani lokaci, yace naje nayi hoto aga lafiyar cikin, Asim ina tsoron ko mahaifata bata gama warkewa ba”


“To a zubar da cikin mana”


Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa.


“A zubar fa kasa kasan abunda kake faɗa?”


“Na sani mana, Namra wannan ba lokacin samun yara bane, muna planning na neman kuɗi kuma yara zasu shigo, ki duba irin wahalar da muka sha a baya yanxu kuma hanya ta fara buɗe mana sai kuma haihuwa ta zo, gaskiya ni ban shirya ba”


“Ni kuma na shriya Asim, ni nake da matsalar da nake da a mahaifata kuma im ready to give birth saboda nima haihuwata aka yi, Allah ba xai bani kyauta na jefar ba”


Cikin wata murya tayi furucin muryar da bata san tana da ita ba sai a yau. Shi kuma ya gyara tsayusarsa yana mamakin ta


“Wallahi Namra sai yanxu na gane lallai ke ba masoyiyata bace. Kin manta lokacin da nake cewa kije ki cire robar nan amman ki ƙi, ko wannan zubar da ciki da kika sha ban san lokacin da kika sha ba, wata ƙila kin yi zubar da cikin ne shiyasa har mahaifarki ta samu matsala, sai yanxu da kika ga zan yi kuɗi ko shine zaki nuna min baƙin hali ki ɓullo min ta haihuwa, to ni ban shirya haihuwa yanzu ba dan haka dole a zubar da cikin nan”


“Wallahi tallahi ba zan zubar da wannan cikin ba, ko da kuwa wannan cikin yana nufi ya rayu, ni na mutu”


“Haka kika ce?”


“Haka na ce kuma haka xaka gani”


“To sai dai ki zaɓa ko ni ko cikin nan...!”


Wani kallo tayi masa na ƙara tantance zancen daya fito daga bakinsa. Shi kuma sai ya ɗaga mata kai dan ya tabbatar mata da maganarsa.


“Yes Idan har baki xubar ba sai dai kije can gidan ku ki haife ɗan, ke kan ki ba samun lafiyarki bane ace kin haihu cikin kuɗi kuma a lokacin mahaifarki tana lafiya ƙalau, na baki lokaci ki yi tunani akai”


Juyawa yayi ya fice, zuciyarsa cikr da tabbacin abinda yayi be yi kuskure ba.



*ANTY AMARYA POV*


Sai da dare Abbah da Hajiya Barau da Anty suka samo ganin lefen da ka kawo, Abbah ya yaba sosai, Hajiya Barau ma ta yaba amman yabon baka yabon daya zame mata cilas dan sam bata jidaɗin ganin yadda aka zubawa ƴaƴan Anty wannan uban lefen ba. Hindatu kala 54 Maryam kuma 79 cikin su kuma babu shege balle ɗan iska.


“Allah yasa alheri ya nuna mana lokacin, amman na ɗauka Namra zata xo tarbon lefen nan”


Anty Amarya taji babu daɗi, sai dai bata nuna ba, sai kawai ta ce.


“Ta so tazo mijin nr ya hana ta yace wai ta bari dai nan gaba sai su zo tare”


“Allah ya taimaka, lefe yayi mashallah”


Haka ta taso ta fito daga falon da ƙahon baƙinciki daya tsaya mata a zuciya. Part ɗinta ta shigo tana shiga ta shige ɗakinta ta zauna, babu abunda take tunanu sai duniyar da Abbah xai kashe masu gurin auren, kamar ita ba a ma ƴaƴanta.


Ummi ce ta shigo ƴar gurin Hajiya Barau mai sunan mahaifiyarta hakan yasa take kiranta da Ummi.
Duk cikin ƴaƴanta mata ita kaɗaice tazo tarbon lefen. Kusa da mahaifiyarta ta xauna tana kallon yanayinta kallonta Hajiya Barau tayi


“Kin gani ke kina son kashe na ki aure su kuma suna yi, idan so kike ki dawo gida mu zauna sai ki dawo”


“Haba Hajiya wallahi ni na gaji da irin wannan rayuwar da yake nuna min, kwata kwata bana gabansa, baya da aiki sai neman mata, tun abu na ɓoye har magana ta fara fita, ko fita nayi sai ya kawo wata a gida”


“Ina ruwanki da neman matansa? Ai kedai yana baki ci da sha ko yana baki na kashewa ina ruwan ki da lamarin, yanzu neman maza ma ake balle mata, abun ai yyi ne wanda be yi ba to bashi da kuɗin yin ne, ko ni ya nema kya ce ki kashe auren ki ki dawo gida balle kuma wata can daban”


Miƙewa tayi tsaye cikin ɓacin rai ta fice, dan tasan duk yadda take son mahaifiyarta ta fahimci matsalarta ba fahimta zata yi ba.
Ƙwafa Hajiya Barau tayi taja wayarta tana soma labartawa abokin gulmarta rashin zuwan Namra tarbar lefen ƙannenta.


Duk hirar da suke be nuna mata jindaɗin hakan ko rashin jindaɗin saboda yana gaban Yasmin ne, yawancin maganar bata wuce uhn a'a ato, Har suka gama wayar.


Ƙaton cikin Yasmin ya kalla yana murmushi.


“Allah yasa karki haifa minɓɗa mai kahuwa”


Ta tsuke baki


“Mai hali dai baya fasa halinsa, ni wallahi haushi kake bani sosai”


“Daman duk kina da ciki ai baki ƙaunata kamar na kashe miki wani”


Ya faɗa yana jawo wayarsa da tayi ringing, number abokinsa Tahir ya gani.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”


Shine abunda ya furta bayan ƴan daƙiƙu da karɓa wayar.


“Okay gani nan zuwa”


Ya tashi tsaye da sauri, har Yasmin ta kalleshi


“Lafiya?”


“Wai Najeeb yayi hatsari, nan cikin gari”


“Subhanallahi, ina fatar be ji ciwo ba”


“Ban sani ba, sai naje tukunan”


Da sauri ya ɗauke Adnan da ke saman jikinsa ya ɗauki wayoyinsa ya zuba aljihu tare da keys ya fice hankali tashe.


*HILAL POV*


Lallaɓata yayi har sai da tayi shiru sannan yaja ta zuwa saman gadonsa ya zaunar da ita ya kama hannayenta ya riƙa.


“Na yarda ba ki aikata ba shikenan?”


“Har zuciyarka ka yarda da ni?”


“Na yarda da ke?”


“Zaka daina fushi da ni?”


“Zan daina”


“Zaka dawo da su Ezzah”


“Idan Hajiya ta yarda”


Haka yake ta amsa mata kamar tambayar babba da yaro, sai ya hau saman gadon yaja ta ƙirjinsa ya rumgume.


“I Love You”


Ƙamkamshi tayi


“I love you too”


Sun daɗe a haka kamin ya sake ta ya shiga yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sai ta ɗauko masa abinci. Ba dan yana so ba ya zauna yayi ƴan lomomi kaɗan ya tashi ya nufi gidan Hajiyarsa.


Da shigarsa Ezzah da Ulfah da sauran yaran gidan suka rugo da gudu suka tarbeshi. Ulfah ce kawai ta tambayi Kalsoom Ezzah kan ko a jikinta. Bayan ya gama ganinsu ya miƙa musu chocolates ɗin ya shigo da shi sannan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login