Showing 267001 words to 270000 words out of 281103 words
Chapter 90 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
da turen abinci Meesha kuma ɗauke da drinks.
“Ummi tace ki ci abinci Mai Martaba ya aiko kiranku tare zaku je”
“Ba da ita zamu yi walima ba?”
Meesha ta tambaya
“Haka Ummi tace wai ko basa nan za ayi walima”
Tashi suka yi suka bata guri yadda zata samu ta ci abinci. Amman har suka dawo yadda suka bar abincin haka suka tararda shi, Meesha ta lallaɓata akan ta daure ta ci abinci amman ta ƙi ita yanzu ba abinci ne a gabanta ba.
Sai da aka fita da ita aka sakata cikin mota sannan Ummi ta dawo ɗakin ta sake wani shirin ta fito tana kiran Hajiya Sadiya da wata ƴar'uwarta guda ɗaya wacce zasu je tare. Amman sai Hajiya Sadiya ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba zata je ba, aka yi aka yi tace ba zata je, har sauran ƴan'uwanta suka ce a canja aje da wata mata sai kawai Ummi ta kashe ƙafafunta da cewar ai ƙara ita dai tun da Asim ya taɓa mata aiki kuma har tasan da sakin Namra. Ba su ba har Namra sai da tayi mamakin jin kalamin Ummi, domin Asim be taɓa faɗa mata cewar yayi aikin a gurin Hajiya Sadiya ba, sai a lokacin ta tuna da ya taɓa faɗa mata uwar ɗakinsa ai macece. A nan kowa ya saka baki akan ƙara ita taje ɗin saboda tasan shi, sai ta sake nuna ƙin son zuwa ɗin a nan wasu kecewa ko dai tasan da wani abu ne idan ba haka be mai xai haka taje bada shedan akan matar ɗanta tun da Abdool zama ɗa yake a gareta.
“Bama fa lallai Asim ɗin yaje ba saboda Mai Martaba ne ya kira ni yace na zo da ita da kuma wasu ƴan'uwana ba lalle bane ya zama Asim ɗin yana nan, wata ƙila ma wani zancen ne zai yi daban”
Cewar Ummi tana ƙoƙarin kawar da Hajiya Sadiya tunani, sai dai hakan be hana ƴan uwanta tursasa taje ɗin ba. Babu yadda ta iya a dole ta shiga motar aka je da ita, uta kanta ba dan tana gudun abunda zaije ya dawo ba da babu abunda xai hana ta faɗi gaskiya game da Asim.
Suna isa cikin gida sai Ummi tasa direban yayi parking a ɓangaren Mai Martaba dan bata buƙartar shiga cikin gida, daman ita tama manta when last ta ganta a gidan, ba kasafai taje zuwa ba sai idan za ayi wani babban abu. Direban na fakawa ta kira Mai Martaba ta sanar masa data iso, sai yace ta shigo tun da gidan ba baƙonta ba ne.
Suna gaba ita da Namra su Hajiya Sadiya da Hajiya Mairo da Anty Farida suna biye, gaban Hajiya Sadiya kamar ya faɗo ƙasa saboda fargaba da tsoron abunda zata tarar. Wani Babban falo ne na Mai Martaba wanda ba kasafai yake shiga da mutane ciki ba, a cike suka tararda falon da mutanen amintatun Mai Martaba sai kuma Abbah da Anty Amarya dake zaune a kujera ɗaya, yayinda Abdool yake zaune a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba, sai kuma Asim da ke zaune ƙasa shi da Lamido, sai kuma ƴan'uwan Asim.da ke gefe ɗaya zauna, wato yayar mahaifiyarsa da kuma ƴan uwan ubansa su huɗu.
Mai Martaba kuma yana zaune a wata ƙasaitacciyar kujera Mai Kyau da Haske irin da manyan sarakuna. Namra na haɗa ido ta Anty Amarya sai ta fara hawaye, Anty kuma ta sakar mata murmushi kamar ba komai.
Ummi ta zauna a kujera zaman mutun uku sannan Hajiya Mairo da Anty Farida suka zauna a saman kujerar Hajiya Sadiya kuma ta zauna ɗayar kujerar ta noce kai ƙasa, Namra kuma ta zauna ƙasa.
Asim na ganinta gabanshi ya faɗi, ya rasa yadda akayi ta haɗu da Ummi duk da bsan wacece Ummi sai dai yasan bata rasa nasaba da Namra saboda yaga tare suka shigo, zance ɗaya zuciyarsa ke nanata masa, wata ƙila Namra ce ta faɗi inda take akaje aka ɗaukota, sai kuma wata tambayar ta sake faɗo masa a rai ya akayi Namra ta san yayi mata aiki?
Waziri ne ya miƙe tsaye yana yima kowa sallama sannan ya kalli Mai Martaba ya sake kallon mutane ya ce.
“Muna saba data tara mu a wannan guri saboda jayayyar aure ne, ɗan wannan masarauta wato Yarima Abdool ya auro wata yarinya daga sokoto, kamar yadda kowa ya sani wannan yarinya bazawara ce, kuma sai da ta shekara ɗaya a gudansu har da wata uku sannan aka ɗaura mata aure da Yarima, bayan an taho da ita a nan Katsina sai Tsohon mijinta ya taso da zancen cewar shi be saki Matarsa ba, kuma har yana iƙirarin akwai ɗa ɗaya a tsakaninsu, a bisa wannan ne Mai Martaba ya tara mu saboda aji bakin kowa”
Waziri ya koma ya zauna, sai Mai Martaba ya kalli Asim ya ce.
“Ko zaka iya faɗa min dalilinka na cewar kai baka saki matarka ba?”
Asim babu kunya babu tsoron Allah ya soma magana ko tsoro baya ji.
“Allah ya taimakeka ni ban saki matata ba, idan har na sake ta dole ne na mata takardar sakinta, kuma babu yadda za'ayi na saketa bayan tana ɗauke da cikina kuma ni mai tsananin son haihuwa ne, ni dai nasan rigima ta shiga tsakani da ita har na dake ta kuma na ta gudu amman ni ban sake ta”
Malamin faɗa ya ɗaga hannu. Sai Mar Martaba ya bashi izinin magana, daga inda yaƙe zaune ya aikawa da Asim da tambaya.
“Yaro karka ruɗi kanka kar kuma kayi wasa da hankalinka, idan har ta gudu miyasa baka bita ba har tsowon wannan lokacin ka ƙyaleta”
“Saboda na san iyayenta basa so na ko naje masan ba zasu bani ita ba”
Kowa sai ya girgiza kai. Malamin ya kalli Namra ya ce.
“Allah shi taimakeki ɗaga baki ki yi magana”
Namra ta ɗago hawaye na bin idonta.
“Idan har yasan ina ɗauke da cikinsa miyasa be bini ba har aka shekara be binciki inda ɗansa yake ba? Taya zan haihu ba a neme shi ba bayan kuma cikinsa ne? Tabbas Asim ya sake ni sanadiyar cikin da naƙe ɗauke da shi saboda yace na zubar na ƙi sai ya sake ni yana faɗa min shi be tashi haihuwa yanzu ba, a sanadin hakan na bar garin Katsina na koma kaduna da zama duk da yake bana da kowa a can, amman sai Allah ya haɗa ni da mutanen ƙwarai wato iyayen Lamido agidan cikina ya ɓari, kuma Lamido gashi nan zaune zai iya bada sheda”
Lamido yayi shiru har sai da idon kowa ya dawo kansa.
“Gaskiya ne wannan, a gidanmu cikinta ya zube, kuma mahaifiyarta ita ce tayi mata komai, na rantse da Allah cikin Namra ya ɓare a gidan mu, na fi tsoron Allah da kowa”
Namra ta lumshe ido tana jin wani rin sanyi a ranta. Ummi ta ce.
“Mai Martaba wannan ƙanwata ce Hajiya Sadiya kuma ka santa, itace wacce wannan yaron yayi aiki a gurinta kuma ita ma tace tasam lokacin da ya saki Namra”
Hajiya Sadiya ta kar da ido tana kallon Asim shi ma yana kallonta kallo-kallo akuya kallon kura.
“Tabbas ya sake ta saboda ya faɗa min a lokacin, har ma na nemi ya dawo da ita amman yaƙi”
“Ke macuciya karki soma samin bakinki a nan, Mai Martaba wacan Matar da ka gani ba musulmar ƙwarai bace, a cikin ƙungiyar asiri take kuma tace Maida Namra ne sabosa tana son ta bada jininta”
Subhanallah kowa ke ta faɗi ana masa kallon marar hankali. Ita kuma ta soma haukace masa.
“Saboda na faɗi gaskiya sheri zaka min? Amman Asim baka da mutunci duk hallacin da na maka?”
“Hallacin me kika min? Kika haɗani da ƴan luwani ko kuma jinin mahaifiyarta da kika shanye, Mai Martaba wannan matar da ka gani itace ta bani apple tace na bawa Namra sai gashi mahaifiyata ta ci ta mutu, kuma ta sake bani wani ni kuma na bawa ƴarta Nabila ta mutu, kuma Wallahi ba ƙarya na ke mata ba, sanadin hakan ta rasa lafiyar jikinta, kuma tiyatar da aka mata saboda maɗigon da take aikatawa ne tana shan Sperm sai ya zame mata kamar ƙanƙara sai da aka mata aiki aka cire shi, wallahi ƴar ƙungiyar Asirice duk ta cinye ƴaƴanta, dan haka ni ban yarda da ita ba”
Mai Martaba ya ɗaga masa hannu.
“Ba shi ya tara mu a nan ba, ko minene acan yake tsakaninku”
Kowa a falon ya cika da mamaki, wasu na masa kallon marar hankali, Hajiya Sadiya kam kuka kawai take tana cewa sai ta yi ƙararsa, Ummi da Mairo kuma mamaki suke, saboda akwai ƙamshin gaskiya a maganarsa. Wata muguwar harara Abdool yake watsawa Asim kamar ya tashi ya shaƙe shi.
Malamin faɗa ya gyara zama yana kallon Asim ya ce.
“Kasan idan aka samu irin wannan matsalar ana zartarda hukumcin rantsuwa ne, saboda haka zaka rantse da alƙur'ane akan kai baka saki matarka ba, saboda kai ne kake jayayya”
Ba shiri Asim ya saki baki yana kallon Malamin.
[8/3, 9:06 PM] Khadeeja Candy♥: *95*
Kallon Malamin yake kamar wanda be fahincin abunda yake faɗa ba, taya zai rantse bayan yasan rantsuwa zata iya kama shi, musamman idan da ƙur'ane ne dama ace ba da alƙur'ane ba da zai iya rantsewa da wallahi ko billahilazin saboda yana tunanin kamar su ba zasu ci shi ba.
“Ni ba zan rantse ba sai dai Namra ta rantse...”
Duk kallonsa suka yi suna mamakin kalaminsa, Abdool ya katsa masa tsawa cikin wani irin zafin rai.
“Karka rainawa mutane hankali a nan gurin, Mai Martaba zai ce ka yi abu kace sai dai wani yayi, wani irin mahaukacin mutun ne kai, idan har kana da gaskiya miya hana ka rantse, idan baka rantse a nan ba zaka rantse a kotu saboda hukuncin da aka maka a nan shi za a maka a can”
Waziri ya ɗaga masa hannu.
“Allah ya huku zuciyarka Yarima Allah ya baka haƙuri”
Ba jikin Asim ba har anta cikinsa rawa take saboda tsawar da Abdool yayi masa ga fuskarsa babu annuri. Sai a yanzu ya gano kuskuren da yayi na saka kansa cikin wannan matsalar, idan har ya ƙaryata kansa yasan dole ayi masa hukunci saboda yayi wasa da hankalin Sarki ne da kuma ɗan sarki har ma da jama'ar faɗa gaba ɗaya, sannan za a tukume shi da laifin tada husuma a gurin walimar babban mutun kamar Abdallah, bayan kuma kuma Namra zata nesance shi har a bada.
Idan kuma ya rantse yasan Allah ba zai barshi ba, sai dai yasan Allah gafurun rahimun ne zai iya yafe masa idan har yayi rantsuwar idan ya koma gida sai ya tuba, shine abunda yake ta saƙawa a zuciyarsa.
“Kai ɗan takalawa, buɗe ka yi magana ko kuma faɗa ta hukunta ka yanzu”
Cewar ɗaya daga cikin manyan faɗar a tsawace yana kallon Asim.
“Ni ba zan rantse ba, sai dai ita ta rantse saboda ita tayi jayayyar cewa na sake ta, bayan kuma ban sake ba, har taje ta yi wani aure, ni dai a iya yadda nake jin labarin faɗar nan ance min Mai Martaba mutun me mai adalci da kamanta gaskiya, shiyasa nayi iƙirarin gaskiyata saboda nasan za a ƙwatar min haƙƙina, da ace wani sarkin nin tsaɓanin wannan babu abunda zai ya fito nayi wannan maganar sai dai na barta da Allah”
Ya faɗa yana ƙoƙarin kwashe ƙafafun Mai Martaba, saboda yasa Namra ta rantse ba shi ba. Abdool ya buɗe baki yayi magana Mai martaba ya ɗaga masa hannu.
“Wannan maganar ta tsaya a haka, idan har muka cilasta wannan yaron yin abunda be tashi ba to mun shiga haƙƙinsa, dan wannan faɗa mai adalci zata bashi damar shigar da ƙara kotu domin tantance wanda yake da gaskiya tsakaninsu”
Abbah ya ɗaga hannu, sai waziri ya ce
“An baka dama farin mahaifi uba ga Gimbiya Namra”
Abbah ya kalli Namra dake kusa da Ummi zaune ya ce.
“Mamana tashi ki yi alwala ki rantse”
Babu wanda be yi mamaki furucin Abbah ga Namra ba, sai dai hakan ya karantar da kowa cewar gaskiya ce Abbah yake son ya buɗe. Namra kamar daman jiran Umarni kawai take sai ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita duk da bata san hanyar da zata sadata da banɗaki ba ko kuma wani gurin makamancin wannan. Hanyar da Ummi ta biyo da ita ta bi tana tafiya har ta fito part ɗin ba, sai barorin dake tsaye habarar gidan suna shanya tufafi suka rugo da gudu suka zube ƙasanta suna kwasar gaisuwa.
“Allah ya taimaki gimbiya ko da wani abun da kike buƙata ne”
Ɗaya ɗaga cikinsu ta faɗa.
“Banɗaki za a kai ni alwala zanyi”
Ta faɗa tana share hawayen da bata san sun zubo mata ba sai a wannan lokacin.
“Yana ta nan Gimbiya”
Sai suka shiga baga tana biye har suka shiga part Hajiya Shafa, a nan wasu Barorin ne suka zube suna ɗubar gaisuwa, Namra zata buɗe baki ta yi magana sai wata daga cikin barorin ta rigata.
“Allah ya taimaki Gimbiya Farida, Gimbiya Namra zata shiga banɗaki ne”
Gimbiya Farida ta miƙe tana aje wayar dake hannunta ta riƙa Namra.
“Muje ta nan”
Tare suka shiga wani ƙaton ɗaki Mai cike da kayan more rayuwa sannan ta kaita bakin ƙofar Bathroom ɗin ta buɗe mata.
“Bilmillah Amaryar mu”
Ta faɗa fuskarta da murmushi Namra tayi bismillah ta shiga, sai da ta fara tsarki sannan ta yi alwala ta fito, a bakin gadon ta samu Farida zaune tana kallon ƙofar ɗakin kamar mai nazari.
Zuwa tayi ta riƙa Namra suka fita tare, ita ta rakata har part ɗin Mai Martaba sannan ta juya ta koma, sai waiwayen Namra take.
Hasbunallahu wani'imal wakil Namra ta karanta sannan ta saka ƙafarta ta shiga falon.
Duk kallon sai ya koma kanta, ita kuma dubanta yana gurin Malamin faɗa dakw riƙe da ƙur'anen fuskarsa da ruwa da alama shi ma alwalar yayi, ƙarasawa tayi ta karɓi alƙur'ane ta riƙe tana kallon Asim ido cikin ido, kamin ta kawarda fuskarta ta kalli Malamin dake karanto mata yadda zata faɗa. Ƙur'ane ta ɗaga sama ta soma ƙaranto rantsuwar kamar yadda Malamin ya faɗa mata, sai da ta rantse sau uku sannan ana ƙarshen tace.
“Ya Allah ka nuna mai gaskiya tsakanin ni da shi”
“Allahu akbar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Shine abunda kowa ya faɗa yana girgiza kai, Asim kan idonsa tsaya dake laƙe suka ƙara fitowa gumi ya soma keto masa ta ko ina.
“Amman Namra baki tsoron Allah da gaske baki so? Yanzu sai da kika rantse? Ni ban sake ki Amman tun da kika rantse amana zata kama ki”
Abunda Asim ya faɗa kenan muryarsa na rawa kamar wanda ya ruɗe. Sai Yayan Mahaifinsa ya soma masa faɗa tana Allah wadan da halinsa. Sai kawai ya soma rantse-rantse.
“Wallahi Baba ban sake ta, idan kuma har na sake ta kada Allah ya tayar da ni a nan gurin lafiya”
Kowa sai mamaki ya kamshi tsakanin ita da shi waye mai gaskiya, ita tayi rantsuwa da Alƙur'ane akan hakan shine gaskiyarta, shi kuma yace idan ƙaryar yake kada Allah ya tayarda shi lafiya, sai dai kowa yasan dole akwai wani abu ya faru da ɗayansu wanda baya kan gaskiya.
Tun da Namra ta soma rantsuwar Abdool ya rumtse idonsa yana saurarenta muryarta, zuciyarsa kuma cike da tsanar Asim. Maganar da Malam ya fara ne yasa shi buɗe ido.
“Tun da har Namra ta rantse akan ka saketa, ya tabbata aurenta da Yarima Abdallah yana nan, idan kuma har akan ƙarya ta rantse to Allah zai nuna mata isha dan Allah ba abun wasa ba ne, daman ana samun irin wannan matsalar idan har miji yayi jayayyar shi akan sashi rantsuwa ne, idan kuma mata tayi musun haka akan sata ra rantse ne, duk wanda yake akan gaskiya Allah ya sani kuma zai masa hukunci. Saboda haka akwai aure tsakanin Yarima Abdallah da kuma Gimbiya Namra, idan kuma har yana da ja akan hakan zai iya zuwa kotu saboda tabbatar da gaskiyarsa”
Allahu akbar suka faɗa. Asim kuma ya girgiza kai yana kallon Namra hawaye na bin idonsa ya ce.
“Da gaske ba zaki dawo gareni ba kenan! Ko da ke kika rantse, shikenan na rasa ki har a bada”
Cikin wani irin zafi rai Abdallah ya miƙe tsaye sai Mai Martaba ya ɗaga masa hannu alamar kar yace komai ko ya aiwatar da wani abu.
Mai Martaba yayi gyaran murya yana kallon Asim.
“Yaron ka gamsu da wannan hukuncin da akan yanke?”
Ya gyaɗa kai hawaye na masa zuba.
“Na gamsu ranka ya daɗe, tabbas na yi kuskure”
Ya maida dubansa gurin Namra da itama hawayen ta ke.
“Ina son ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah, zubar da cikin nan kika yi ko kuma ɓarewa yayi?”
“Babu dalilin da zai sa na zubar da ciki Asim, da ace zan zubar da na yarda na zaɓi zama da kai na zubar da cikin kamar yadda ka buƙata, cikin ya zube ne ta dalilin matsalar da nake da ita a mahaifata na rashin tsayawar ciki”
Murmushi yayi tana tuna lokacin da ya cilasta mata zaɓen cikin ko kuma aurenta, lokacin da yake iƙirarin be shirya haihuwa ba, yanzu kuma yana kan nema Allah be bashi ba, a tunaninsa idan har Namra ta rantse to za'ace ta koma ɗakinta ne, yana tunanin kamar yayi mata wayo yadda rantsuwar ba zata kama shi ba.
“Na gode Mai Martaba da ka saurareni Allah ƙara maka lafiya”
Ya faɗa kamar ba shi ba, gaba ɗaya jikinsa yayi la'asar ya saduda da lamarin dan yasan ya rasa Namra har a bada, bayan kuma yanzu ne yake jin mashin son ta na sukar zuciyarsa, yasan nan Mai Martaba yayi masa da sauƙi ne idan aka je kotu shi za a saka ya rantse, duk da yasan Abdool ba zai ƙyale shi ba.
“Baba ku tashi muje”
Ya faɗa yana fashewa da kuka. Sai duk suka miƙe tsaye jikinsu na rawa suka yi ma Mai Martaba sallama suka bi bayan Asim da ya rigasu fara tafiya. Kamar jira ake ya kai bakin ƙofar fita falon sai gashi yayi waɓi mugun faɗuwa kamar wanda aka kwashewa ƙafafu, Subhannallahi ƴan uwansa suka riƙa faɗa suka ƙarasa da sauri suka mashi suka tayar tsaye, amman sai ya kasa tsaye ƙafafunsa suka murɗe kamar an shanyesu, a nan kowa ya ƙara girmama Allah a take ishara ta bayyana iƙirarin da yayi na cewar idan ƙarya yake kada Allah ya fitar da shi