Showing 114001 words to 117000 words out of 281103 words

Chapter 39 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61233

a mafi yawan lokaci wanenen zata ɗauka jinin haila da na rashin lafiya? Domin ita mai jinin rashin lafiya hukunce mai tsarki na gareta, kuma irin wannan hukumci shine a gurin mace mai jinin planning irin wanda yake zuba idan anyi planning dan ya zama kamar jinin rashin lafiya.


*Hali na farko* Ta zanto tana da masaniyar kwanakin hailarta, kamin jinin rashin lafiya ya same ta. Misali idan tana jinin haila a kwana biyar ko takwas a farkon wata ko tsakiyarsa, watau tasan kwanakin hailarta da lokacinta. To ita wannan zata zauna gwargwadon kwanakin hailarta ta bar sallah da azumi ta bawa kanta hukunci mai haila. Idan kwanakin sun wuce sai haila sun wuce, sai tayi wanka tayi sallah ta ɗauki jinin da ya cigaba da zubar mata da zuba a matsayin jinin rashin lafiya. Dalili shine faɗin Annabi S. A. W, ga Ummu Habiba : ki zauna gwargwadon kwanakin da hailarki take tsare ki, sannan ki yi wanka ki yi sallah. Muslim ya ruwaito shi. Da kuma faɗarsa Annabi ga Fatima Bintu Abi Hubaish: Wannan jinin jijiya ne, ba haila ba ne. Idan hailarki ta zo sai ki. Bar sallah. Bukhari da Muslim suka ruwaito shi.


Idan iyakar kwanakin hailarta ya zo kamar yadda bayani ya gabata, to wajibi ne a gareta tayi wanka. Kuma wanke gabanta domin ta gusar da abinda yake zuba yayinda ta zo yin kowace salla. Kuma tayi ƙunzugu da auduga (pad) ko abu mai kama da ita wanda zai hana kwararar jinin, sannan tayi alwala daga lokacin kowace salla saboda faɗin Annabi : Ta bar salla a cikin kwanakin hailarta, sannan ta yi wanka kuma ta yi alwala ga kowace salla. Abu Dawud da Ibn Maja da tirmizi ne suka ruwaito shi.




Hakan yasa Kalsoom ta cigaba da salla da duk sauran ibadarta, sai dai har gobe halinta be canja ba a kan Hilal idan yana cikin gidan ji take babu wanda tsana a duniya sai shi. Yara kuma abu kaɗan ta dake su, tun yana haƙuri har abun ya fara isarsa dan yanzu shi da ita basa shan inuwa ɗaya, akan yaransa.
Gashi Ezzah kullum uwarta ƙara hure mata kunne take tana koya abubuwan da take ganin kamar abun ƙwarai ne, bayan ita bata san tana lalata tarbiyar ƴarta bane kawai.
Duk ranar da ba makaranta zai kwashi yaransa ya kai su gidan Hajiyarsa. Hajiya ta lura da yanayin ɗanta damuwa ta bayyana a fuskarsa ga ramar dake jikinsa, yadda ma yake yawan kawo yaran akai-akai ta san ba lau ba.


“Wai likita akwai abunda yake damun ka ne?”


Ajiyar zuciya ya sauke, yana aje plate ɗin abincin da ke hannunsa.


“Wallahi Hajiya ni ban san matsalar, daga ina take ba ma, Kalsoom ce yanzu kwata-kwata na rasa ma gane kanta, indai ina gida bana da kwanciyar hankali, sai kuka zara riƙa min tana masifa”


“Me ya haɗa ku?”


“Ba abunda na haɗa mu haka kawai zata riƙa min masifa sai kuka, kin san cikinta ya ɓace”




“Ya ɓace kamar ya?”


“Jini kawai ta ga yana mata zuba, sai aka yi hoto aka ga babu cikin kwata-kwata a cikin ta, amman jinin har yau be tsaya mata ba, yau kusan wata huɗu kenan”


“Subhanallahi, me ya same ta haka ne?”


“Wallahi nima van sani ba? Na rasa gane kanta”


“Abun kamar lamarin iska shi kesa ciki ya ɓata, ko kuma sihiri”


“Sai maganar saki ta ke min, ita dai na rabu da ita na ta huta”


“Kasan me? Ka samu ƙwarya mai tsarki da za'afaran, sai a ruɓuta suratul Yasin da surar wa'ƙia da fatiha da ƙulhuwallahu ahad da ƙula'uzai da Ayatul kursiyu da kuma amanar rasulu har zuwa ƙarshe da suratul baƙara da ayar : ƙul-a-Allahu azine lakum am alallahi taftarun (10:59) to idan an rubuta sai a karya kummallo da shi idan ta sha sai ta samu dabino ajwah sai kayi mata tawada nan da Al-zaitul muraƙƙa sai ta cinye sauran kuma rubutun kuma ta shafe jikinta, da iKon Allah indai sihiri ne ko aljanu ko wane iri ne zai rabu da ita”


“Amman Hajiya irin wannan ai sai dai kisa waki ya rubuta mata a nan sai na kai mata ta sha”


“To zan nemi wanda zai rubuta mata inshallah, amman wannan ko Rashida ai zata iya ƙulle-ƙulle ganin ta ɓata zamanku”


Yayi ƴar dariya.


“Sai dai ko iska ne, amman ai Rashida bata da irin wannan halin”


“Hmmm Hilal ba a shedun mace, yanzu kasa ran tayi maka wannan abun?”


Yayi shiru yana nazarin maganar Hajiya.








[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: »»4»»»»»»8»»»»»»»»»




ABDOOL POV.


Ɓacin rai ne shimfiɗe a fuskarsa, idanunsa sun rine zuciyarsa har wani tafarfasa take saboda faɗan d Mai Martaba yake masa.
Har Mai Martaba yayi ya gama Abdool be ce uffan ba, dan yasan akan gaskiya yake faɗansa, kamar yadda Ummi take masa a kullum.


“Ƙanen ka Babana ƙanenka ace yayi aure har ya haihu kai ba kayi ba, kullum girma ƙara tunkararka yake amman baka ganewa, shekarun tafiya suke Babana yanzu da ace kana da mata da wannan abun zai faru da kai? Sai dai ka zauna a gida ta girka maka, ko mutuwa kayi ba mu da abunda zamu kalla mu tuna da kai sai hoton ka, ai ko mutuwa kayi ka bar mai maka addu'ah ka more, rashin auren nan naka yana damuna Babana, kuma kullum faɗa ake maka amman kamar ba'ayi”


Till now be ɗaga ido ya kalli Mai Martaba balle ta ce wani abu, shi kansa yana da buƙatar auren, sai dai matsalar bayan Namra be ga mace da ta kwanta masa ba, sannan be son ya auri mace da baya so gudun karya tauye mata wasu haƙoƙa nata, dan wanda yake so baya jin zata samu enough time nasa balle wacce baya so.


Hullar uniform ɗin dake jikinsa kawai yake taɓi yana sauke ajiyar zuciya.




“Ba na son cilasta maka auten wacce baka so, shiyasa nake ta ɗaga maka ƙafa ina baka lokaci, amman ka ƙi ka gane”


“Mai Martaba ka gafarce ni, ina nan ina ta addu'ah Allah ya bani matar da nake so”


“Allah ya baka, amman karka zarge ni da abuɓda zan maka nan gaba”


Har ya miƙe tsaye be kalli Mai Martaba ba, dan baya son Mai Martaba ya ga ɓacin ransa.

“Zan tafi, Allah ya ƙara maka lafiya”


“Yau ba za'ayi min fira ba kenan ko? Tun da nayi maka faɗa?”


Ya ɗan murmusa


“Ba haka bane, kana yawan faɗa min na kula da kai na, kuma yamma tayi i want to spend time with Ummi, dan gobe zan koma”


“Ai daman na san ita take ƙara goya maka baya kana fatali da maganar auren nan”


“Ba dan wani abu ba da sai na ce tama fika damuwa da lamarin auren nan”


“Kuma ba kayi komai a kai ba?”


“Zan yi inshallah, a ƙara min lokaci”


“Allah ya kiyaye hanya”


Ya ɗan risina kamar yadda yake masa.


“Na gode Mai Martaba”


Sannan ya juya ya nufi ƙofar fita, a bakin ƙofar ya tsaya ya saka Army shoes ɗinsa dake gurin sannan ya shiga cikin gidan sashen matan sarkin yayi musu sallama ya fito.


Kuɗin dake aljihunsa ya ciro ya miƙawa mutanen dake zageye da motarsa, sannan ya shiga motarsa boys ɗinsa suka shiga wata motar already wasu na cikin motar sake gaba sai kawai suka kama hanyar gida.


Sai da ya fara shiga part ɗinsa yayi wanka ya canja tufafi sannan ya nufo part ɗin Ummi.
Sisters ɗinsa ya samu falon tare da friends ɗin su, cikin murna suka tarbesa, sai ya gaisa da Friends ɗin su sannan ya nufi ɗakin Ummi.


Zaune ya tararda ita ƙasan carpet hannunta riƙe da qur'ane tana karatu. Kusa da ita ya zauna yana sauraren ƙira'ar nata har sai da ta kai ƙarshen suratul Maryam sannan tayi addu'ah ta shafa, ta aje qur'ane a gefe ta cire gilashin idonta ta kalli ɗanta tana murmushi.


“Soja wuta soja”


Yayi dariya yana shafa dogon hancinsa.


“Uwar soja ma soja ce”


“So ya hanya?”


“Alhamdulillah”


“Ka ci abinci”


“Eh na ci tare da Mai martaba”


“Can ka fara biyawa kenan?”


“Eh kuma na sha faɗa akan mganar aure, Mai Martaba be gajiya”


Ummi tayi murmushi irun nasu na manya tana kallon ɗan nata cike da so da ƙauna.


“Kai ma ai baka gajiya da faɗan shiyasa kaƙi kayi auren ka huta, amman Abdool bana son kana cin abincin mutanen”


“Ummi ki daina zargin komai, yanzu ba kamar da bane, suna sona sosai”


“Ba lallai bane ka iya gane haka, ai maƙiyin ɓoye baya taɓa nuna maka baya son ka, kuma dik wanda ya ƙi ni to kai ma zai iya ƙin ka you have to be very careful”


“Na kan yi bismillah idan zan ci, kin san ko minene idan ka yi bismillah ba zai taɓa samun ka ba, kuma ina addu'o'i sosai musamman da safe, kuma kin san irin addu'o'in da nake musamman laƙada ja'akum wace idan aka karanta mutum ma ba zai mutu ranar ba, saboda tsananin tsarinta, idan har zaka mutu a ranar yo Allah ba zai baka ikon karantawa ba, ga a'uzu bikkalimattillahi”


“Hakan yana da kyau, nayi tunanin ko baka samun time ɗin addu'ah ne saboda aikin ka”


“Komai nauyin aikin na na kanyi sai dai ba dika ba, amman dai bana tashi ba tare da nayi addu'o'in tsari ba”


“Allah ya ƙara tsare ka”


“Amin ya rabb”


“Ina labarin yarinyar nan an sallame ta?”


“Ni na hana su sallame ta da tuni sun sallame dan taji sauƙi sosai”


“Ni abunda na ga yafi karka bar yarinyar nan ta koma cikin ƙazamar rayuwa, ya kamata kayi wani abu a a kai”


“I try my best naga ta koma gidan su amman ta ƙi, ta tsaya kai da fata ita ba zata koma gida ba, wai ji take kamar idan ta koma mutuwa za ta yi, ni kuma ban san abunda zan mata ba”


“Why not ta zauna da mu kamin hankalinta ya kwanta sai mu mai da gida gurin iyayenta”


“Kawai yarinyar bata kwanta min bane, ta taɓa zubar da ciki, kuma kin ga ta zauna da mutane ƴan iska kala kala, kar tazo ta ɓata mata tarbiyar Sisters na”


“Ba zata ɓata ba, sai dai su su gyara mata tarbiyanta, she deserved everything Abdool dik wanda ya sadaukar da ransa dan kana ya rayu ya cancanci komai a gare ka, a yanzu bata da gurin zuwa kuma idan har muka bar ta ta koma cikin wacan rayuwar kamar ba mu mata adalci ba, :sannan ka bincika an tabbatar maka da gaske guduwa tayi daga gidansu, ai ya kamata ace kayi wani abu akai na ganin kaima ka maida mata farinciki a zuciyarta ”


“Amman Ummi har yanzu babu tabbacin abunda yasa ta gudu”


“Ai kasan ita da iyayenta ba zasu fito su faɗawa duniya dalilinta na guduwa ba, ya zaka ji idan aka ce ɗaya daga cikin ƙannen ka ne? Put yourself in my shoes zaka ji irin abunda ko wane uba ko uwa take ji”


Ya sosa kansa yana miƙewa tsaye.


“I will think about it, lemme go and pray”


Daga haka yasa kai ya fice ɗakin.






RASHIDA POV.


Kusan kullum sai ta yi waya da malamin nan ko kuma nace boka, amman labari ɗaya yake bata, cewar Hilal da Rashida basa zaman lafiya, kuma har gobe jini na nan yana mata zuba.
Sai da ita bata da tabbacin hakan tun da bata ji wani motsi daga garesu ba, dan har yanzu bata ji ya saki Kalsoom ba, kuma Ezza tana yawan faɗa mata ita bata ganin suna faɗa har sai idan ta dake ta sannan Daddy ta yayi faɗa.
Izzah bata da labarin komai da yake faruwa tun da Hilal baya faɗa da Kalsoom a gaba idonta, ko lokacin da Rashida take gidan idan zai yi mata faɗa ba yayi a gaban idon yaransa gudun abunda zai je ya dawo. Balle kuma.Kalsoom da baya biye mata dan ta fahimci bata cikin hankalin kanta duba da yadda abubuwan da take masa a.yanzu abunda be tsammaci zata masa ba, kuma baya tunanin kishi ne da sai dai ta nuna jindaɗinta akan barin gidan da Rashida tayi ta ƙara mallakarsa, sannan Hajiyarsa tana yawan tunasarda shi akan ya kawar da idonsa gareta, duk wani abun da zata yi ya riƙa sa mata ido.


Tana yawaita bibiyar shafinsa na facebook da instagram da whatsapp, wai ko zata gano idan hankalinsa ya karta kanta amman sai ta ga tsaɓanin hakan, dan har text take masa amman baya mai da mata amsa daga ƙarshe ma sai ya saka ta a blacklist.
Yau kam ta kuɗiri aniyar tura Asmee dan ta binciko mata irin zaman da suke, tun da ta san Kalsoom ta yarda da Asmee kuma zata iya bugun cikinta dan ta ji labarinta, idan ma suna zaman lafiya ko a yanayin fuskarta zata iya karantar hakan.


A gogon ɗakinta ta kalla taga 10:36Pm, ba laifi dare ya ɗan fara sai dai hakan be hana ta janyo wayarta ta kira line Asmee ba.


“Ƴar gari... Yanzu ko na ke maganar ki da Oga”


“Uhmm gulmata kuka yi kenan?”


“A'a Wallahi kawai yana yabon halin ki ne, wai duk yadda kike da haƙuri ace Hilal ya sake”


“Ke dai bari, ai sherin kishiya sai Allah, ni so ma nake kije gobe ki bincika min gidan nan, ya zamantakewar su yake”


“Zan ko miki haka, nima Wallahi ina son zuwa dan naga idon munafukar”


“Da Sassfe zaki je dan Allah lokacin da Hilal.yake gida”


“Karki samu matsala Asmee ce fa ƙawarki”


“Na gode ki gaishe da ogan na ki”


“Zai ji mu kwana lafiya”


Rashida ta kashe wayar tana kallon ƙanwarta Safiya dake tsaye jikin ƙofa riƙe da littafi.


“Shigo mana kika tsaya bakin ƙofa kina kallona”


Ta shigo tana ɗan murmushi


“Wallahi Anty ni jikina duk a mace yake”


“Saboda me mutuwa aka yi?”


“A'a, kin san mun fara zuwa asibiti yanzu...”


Ta ɗan yi shiru tana tunanin ƙarasa zancen, dan tana jin nauyin karya alƙawarin data ɗauka a asibiti na cewar ba zata faɗawa kowa wanda ta gani ba, idan ta shiga sashen masu hiv da sarin tb.


“To shine nake neman addu'ah, idan mun gama zamu fara exam”


“To Allah ya taimaka ya bada sa'ah, nima ina son ki min addu'ah Allah ya maido da hankalin mijina gare ni”


“Adda Rashida kenan, kina damuwa da abunda be kamata ki damu da shi ba, mijin daya juya miki baya meye na addu'a ya dawo gareki, bayan ya ci zalinki?”


“Ba a cikin, hayyacinsa yayi min ba, kin fi kowa sanin yadda Hilal yake so na, kawai sherin Kalsoom ne magani tayi masa, yanzu haka ma su Ezza basa jindaɗin zama da ita, so take ta kore kowa ta mallaki gidan”


“Kada Allah ya bata sa'ah, kuma wallahi indai mugun nufinta kenan sai ta ga abinta, ai karka bi mutum da sheri ka bar shi ya bika da sherin abun zai koma kansa”


“Ba zan bata damar haka ba, Safiya bata isa ta shiga gidan dana shekara ina ginawa ba a rana ɗaya ta rusa min kuma ta kore min ƴaƴa ta mallake min miji sannan na bar ta”


“Ki ƙyale ta ki bar ta da Allah, idan ma wani asirin ne tayi miki Wallahi zai karye zata dawo nadama lokacin da bata da amfani”


»“Haka ne Allah ya shige mana gaba”


“Amin dan Allah ki ma daina sa ran ki a damuwa”


“Ina nan ina addu'ah komai zai dai-daita inshallah”


“Allah yasa, sai da safe”


Safiya ta miƙe tsaye ta fice zuciyarta cike da tausayin ƴar'uwarta. Rashida kuma ta sauke ajiyar zuciya tana busar da iskar bakinta. Lallai tana ji a zuciyarta, ba a banza Hilal ya barta ba, dan tasan yadda mijinta yake son ta dan kawai ya gano tana tare da wani be isa yasa ya sake ta ba, tasan da ada ne da komai tayi ba zai rabu da ita ba.
Sai dai abunda har yau bata sani ba shine, daga lokacin da mijinki ya gano kina mu'amala da wasu a waje tun kin fita daga ransa kenan indai ya san kansa, kuma komai irin son da yake mki ba zai sake ganin darajar ki ba.




NAMRA POV.


Yau ta farka da baƙinciki da kuma tunanin mafita dan samawa kanfa ƴanci.
I zuwa yanzu ita kaɗai tasan abunda take ji a zuciyarta, idan ta soma tunani har numfashinta yake yin sama, tsabar baƙinciki da damuwa.


Dole ne taje a cire mata robar nan, dan ba zata iya da rikitarwar da jinin yake nata ba, kuma ga matsalar Asim da yanzu babu ruwansa da matsalarsa haka zai yi forcing ɗinta ya yi yadda yake so da ita.
Irin yadda yake mata Allah ya isa akan rashin cire robar da bata yi abun har mamaki yake bata, kamar ba mijinta ba, ko kuma wanda be san addini ba, abu kaɗan zai mata Allah ya isa, ga yawan kusheta da yake, shi dai kullum ya fi son ya ganta a cikin damuwa da baƙinciki.


Ba laifi yanzu dan ya ɗan fara fita, har ya koma aikinsa na ƙira da suke da Ƙanen Babansa, sai dai naira ba zai cire ya bata ba, da sunan ta siye abinci balle cefane, babu ruwanshi da matsalarta, sai dai ita tayi cefane kuma haka zai zo ya zauna ya ci dan bashi da kunya. Ita kuma har yanzu bata yi ƙarfin halin da zata iya hana shi abincinta ba.


“Idan na yi kuɗi, zan auro mace mai kyau mai tarbiya”


Sune kalamansa a kullum kuma sune kalaman da suka fi ƙona zuciyar Namra, a yanzu ne take ƙara tabbatar da son Asim be gama fita zuciyarta gaba ɗaya ba.
Ta maida hankalinta sosai gurin siye da siyarwa, na kayan aiki abinci like magi manja da sauran kayan miya, ba laifi ana siye sosai dan a unguwar ita kaɗai ce take wannan sana'ar hakan yasa ta sabo da mutane har ta buɗe islamiya tana ɗan karantar da su abubuwa game da addini da kuma ƙur'ane.








manage it please.....
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: ~4»»»»9»»»»»~


AMIRA POV.


Ta fara sabawa da Abdool cikin ƴan kwanaki ƙalilan ya shiga ranta, har matsuwa take ya zo ya ganta, dan kullum sai ya zo da safe ya duba ta, da rana ma ya kan zo idan baya da aiki, haka ma da dare sai yayi mata sallama sannan ya wuce gida.


Ta karanci abubuwa da yawa a rayuwar Abdool tun daga yanayinsa na rashin son magana da kuma shisshigi, ba kasafai yake dariya ba, ko murmushi sai idan ta kama ne yake yi.
Sai dai hakan be hana annurin fuskarsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login