Showing 111001 words to 114000 words out of 281103 words
Chapter 38 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
ko? Ina miki magana kina min gunguni”
Ɗan wannan abun da Kalsoom tace mata sai kawai ta ɓare baki ta fara kuka tana, ta tashi da gudu ta bar falon.
A harabar gidan ta je ta zauna tana kuka kamar wacce aka cirewa rai.
Haka ta zauna a gurin har mahaifinta ya dawo ta sanar da shi dukan da Kalsoom ta yi mata. Sam be jidaɗi ba dan babu abunda ya tsana kamar duka, komai zai iya ɗauka amman ban da a dakar masa yara, dan shi be sa musu hannu ba ba zai yarda wata ta sa musu ba, Rashida ma data haifesu baya bari ta dakesu.
“Ba ki mata komai ba zata dake ki? Kalsoom ba zata dake ki haka kawai ba”
“Wallahi ban mata komai ba, kawai tace na share falon nace ta bari na gama homework shine kawai ta mare ni”
“To ya isa yi haƙuri zan mata magana”
“Daddy yaushe Ammyn zata dawo?”
“Ba zata dawo ba”
“Miyasa?”
“Tace ta zaɓi haka”
Ya riƙa hannunta suka shiga ciki. Suna shiga falon ta fisge hannunta ta nufi ɗakinsu da gudu.
Kallo ɗaya Kalsoom tayi mata ta ɗauke ido tana masa sannu da zuwa.
“Yauwa me Ezzah tayi miki kika mareta”
Ya faɗa yana mai zama a kusa da ita.
“Mari? Ita tace maka na mareta haka tace maka?”
“Baki mare ta ba?”
“Haba Doc mi zai sa na ɗaga hannu na mareta sai kace wari na? Ni dai nasan na zungureta”
“Amman Kalsoom be kamata ace kin dake ta ba, Ezzah yarinya ce dik abunda take yi ƙurciyace, sannan rashin mahaifiyarta yana damunta dole sai kin yi haƙuri da ita, bata da uwa a yanzu sai ke”
“Amman idan ta ɗauke ni uwa mi zaisa ta min rashin kunya? Did i treated her badly ne? Miye bana mata tun mahaifiyarta na nan, sai yanzu dan daga bata nan zata fara min rashin kunya? I'm tired Hilal I'm tired ba rainon ƴaƴanka na zo yi ba, nima aure na zo, idan rainon ƴaƴanka kake so ayi maka kaje ka nemo mai raino, amman ni ba zan iya, ba kuma zan yi ba, ko da zai zamo silar mutuwar aurena ne!”
Kallonta kawai yake irin yadda take zuba masa ruwan masifa har hantanta tashi suke, gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda abunda be kai ya kawo ba.
But all what he thought tana cikin damuwar zubewar cikinta ne, he feel her pain, hakan yasa ya ɗaga mata ƙafa be biye mata ba, sai kaiwai ya tashi ya barta falon.
Fashewa ta yi da kuka ta cire ɗankwalinta ta jefar tana kuka.
“What is wrong with me? Miye same ni? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta tashi da gudu ta shige ɗakinta tana cigaba da kuka, zuciyarta cike da tsanar Hilal bayan be mata komai ba.
NAMRA POV.
Asim be yarda ta dawo ba, har sai da ya ganta asibitin, aiko ya dinga murna kamar ya ɗauke ta ya haɗiye, Mama ba laifi ta tarbe ta far'ah tana na'am-na'am kamar ba ita ba.
Namra ta jidaɗin haka, sai taga kamar saboda tayi fushi ne Asim ya tsorata yayi canja, duk sai ta ji farinciki ya baibayeta ance so hana ganin laifi, ita dai har gobe zuciyarta na son Asim, duk da da shakkun da take da shi akansa, dan ta ƙudiri aniyar naira biyar nata ba zai sake shiga hannun Asim ba, tun har ta gano nufinsa.
Ya samu sauƙi sosai, dan har likitoci suna maganar sallamarsa ganin yanzu yana taka ƙafar sai dai yayi ɗingishi, Mama ta fi kowa jindaɗin samun sauƙin nasa saboda ta matsu ta koma gida zaman asibitin dik ya isheta.
Ranar da Namra ta kwana biyu da dawo taja ƴar fulani suka je kasuwa ta siye wasu abubuwan na kitchen da na ɗaki, da kuma tufafi da hijabi, da ta dawo da yamma ne ta share ɗakin ta wanke ta zuba center carpet ɗin data siyo da taimakon yarinyar ta kira yayanta namiji ya laƙa mata labulaye sannan ta shiga da katifa, da sauran tarkace. Ta haɗa BQ ɗin ba laifi kasancewar ɗakun biyu ne sai ta mai da ɗayan kamar kitchen ɗinta, ta saka abubuwan zuba ruwa da sauran kayan aikinta ciki.
AMIRA POV.
Washe gari Ummi ta dawo ta ga Amira dan tasha alwashi ba zata bar Abuja ba sai ta yi ma Amira godiyar abunda tayi ma ɗanta.
Amira ta jidaɗin haka, ta san ko ba komai ta samu shiga zuciyar Ummi ganin yadda take tausayinta, har da zubar mata da ƙwalla, gashi jikinta ya nuna ita ɗin wata ce, tun daga kan tufafinta zuwa yadda naman jikinta ya kwanta.
Amira ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye take tana son shige mata jiki.
“Na ji daɗi da kika zo, na ji kamar a'ce ke mahaifiyata ce”
“Ni mahaifiyarki ce mana miyasa kike magana haka, Allah ya baki lafiya”
“Amin na gode”
Ta faɗa tana kife saman gado asibitin. Abdool na tsaye hannayensa a aljihu yana kallonsu, shi dik ya gundira Ummi ta bar ɗakin, coz he don't trust Amira, kuma hankalinsa be kwanta da ita ba for no reason.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»7»»»»»»»»»»»»»»»
“Wai Daddy yace kin ce ba zaki dawo ba”
“Yaushe yace miki haka?”
“Jiya da ina tambayarsa yaushe zaki dawo, wai yace ke kika ce ba zaki dawo ba”
“Baya son ya faɗa miki ne, saboda yanzu baya so na Kalsoom yake so, idan har kina son na dawo dole ne ki riƙa yin abunda na faɗa miki, idan kina irin haka shine sai za ya tausaya muku yace na dawo”
“Amman ita bata jin daɗin abunda nake mata”
“Ke kina jindaɗin data koreni?”
Ta girgiza kai alamar a'a.
“Idan baki yin abubuwan da nake faɗa miki ke ma wata rana sai tasa Daddy ki ya kore ki, sai ta mallake gidan daga ita sai nata ƴaƴan”
Ezzah ta.yi shiru tana tunani sai kallon ƴan makarantar su take masu kai wa da dawowa.
“Ezzah dik duniyar nan baki da kowa kamar ni, duk wacce zata so ki abaya na take, kuma ƙarya Kalsoom take tace tana son ku, tana nuna muku haka ne dan ta mallaki Daddy, yanzu kina jindaɗi zama da ita? Bata dukan ki? Lokacin da ina nan Daddy ki yana miki faɗa?”
Duk ta girgiza kai.
“Dole ne kiyi mata abunda na saki dan na samu na koma gurin Daddy ku, na yi muku alƙawari ddana koma kullum gida zan riƙa zama ba zan sake fita aiki ba”
“Da gaske?”
“Wallahi, dan haka ki cigaba da abunda kike, har abunda ban saki ba ma ki aikata indai kinsa wanda zai hassalata ne”
“Zan riƙa yi”
“I Love you”
“I Love you too”
Rashida ta rumgume ta kamar da gayya. Sannan ta ciro chocolates da Sweet Candy dake jakarta ta miƙa mata, ta kuma bata ɗari biyu na kashewa sannan ta tashi ta fita.
Daga nan Asibiti ta nufa. Yau ce rana ta farƙo da zata fara bin shawarar likita wajen ɗora kanta akan magani, dan samun tsawaita rayuwarta kamar yadda likita ya faɗa mata.
NAMRA POV.
Two months later....
A zuwa yanzu babu wata matsala da take fuskanta a gurin Asim, tun bayan da aka sallamo daga asibiti, jiki sai ƙara sauƙi yake yana mirmirjewa kamar ba shi ba.
Duk wani mugun ƙudiri dake cikin ransa, ya danne ya barwa zuciyarsa, dan yasan babu yadda zai yi da Namra a yanzu sai kallo, idan yace zai rabu da ita matsala ne a gare shi tun da baya sgi kuɗin auren wata, shi dai yanzu ba shi da wani buri sai na yayi kuɗi.
Irin yadda yake nanata maganar har tsoro abun yake ba Namra, ahi dai yayi kuɗi dai yayi kuɗi. Haka Namra zata zauna tana masa nasiha akan duniya da abunda ya ke cikinta, amman sai dai ya kalleta kawai ya nuna mata wa'azin ya ratsashi bayan a ƙasan zuciyarsa kuma mamakinta yake, wai ita zata zaunar da shi ta nuna masa illar kuɗi, bayan ga ubanta can ya tara su ita kuma da su take tinƙaho.
Sam baya ganin wahalar da take da shi, bata saba wanki ba ko a gidansu amman haka zata zauna ta wanke nata tufafin ta wanke nasa, ta kai masa ruwanka, amman kullum sai ta matsa masa yake wanke dan ganin yake kamar tana takurasa, Allah ya zuba masa ƙuiyar motsa jikinsa indai a bangaren aiki ne.
Maganganun da Namra take masa akan rayuwa da neman kuɗi da yake magana a ko yaushe sai ya ƙara riƙe ta a zuciyarsa, wai bata son sa da alheri ta fi son yayi dauwama cikin baƙin ciki da damuwa tun da ita tana da mafita.
Ga matsalar da ci masa tuwo a ƙwarya a yanzu, wacce yake ganin kamar da ganganci ne tayi masa haka dan bata son haihuwa da shi. Ita kanta tana nadamar sanar da shi da tayi robar da aka saka mata, sai dai babu yadda zatayi dole ce tasa ta faɗa masa, tun kullum sai ya tunkareta kuma jinin har yau be tsaya mata ba, daman wani lokacin haka robar yake yi mutane dan ta ji maƙonta suna firar lokacin data shiga gidan su ƴar fulani.
Ta aika tambayarta ga wani malami ya amsa mata da cewar duk jinin daya zube bana haila bane ya zama kamar jinin rashin lafiya ne dan haka ba zatayi fashin sallah ba balle azumi.
Hakan yasa robar ma sai ta fita ranta dan ita bata son abunda zai riƙa rikitar mata da addini, hakan yasa ta yanke shawawar zuwa a cire mata robar in ya so sai tasha ƴaƴan zurma, dan maƙociyarta nan ta faɗa mata indai har ta sha ƴaƴan zurma ɗaya yana matsayin shekara ɗaya ne idan kuma tasha biyu kuma yana matsayin shekara biyu ne.
Sai dai ba kowa yake yi ma aiki ba, amman ta ga wani a whatsapp wanda Khadeeja Candy take tallah shi kam idan an sha tabbas zai maka aiki, matsalar kawai ita ba a garin take ba, kuma tana buƙatar ta bincike dan ta jin yadda abun an ce mata texted and trusted ne. Ga Kuma Asim ya dame ta da maganar kullum, dan shi gani yake kamar da biyu tayi haka.
Yau wake ta dafa da shinka (rice and beans) ta saka mai da taji, daman yana cikin favorite na ta, amman Asim duk lokacin data dafa sai ya riƙa ƙin ci yana ganin kamar tana haka ne dan karta kashi kuɗi da yawa tayi musu abinci mai kyau.
Shi yanzu har ya matso jikinsa ya koma.yadda yake ya fara fita neman kuɗi, dan ya ayyana a ransa kuɗinta zai ranta ya fara sana'ar, har hango kansa yake ya zama wani Alhaji.
Kullum firar da ita kenan, yau bayan ya gama complaint ɗin baya son wake, ya ɗasa mata firar idan yayi kuɗi, ba aza a ƙara cin wake a gidansa ba.
Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda idom Asim ya bude haka.
“Asim kenan. Idan ma zaka yi roƙon baka cewa Allah ya baka halalinka, kawai dai kai kayi kuɗi”
“Wallahi sai na yi kuɗi Namra, Wallahi Wallahi sai nayi kuɗi, kawai naji sauƙi ne”
»“Ban ce ba zaka yi kuɗi ba, Amman yana da kyau ka riƙa cewa Inshallah kuma ka riƙa roƙon halak, saboda gudun sherin zuciya, idan Allah ya rubuta zaka yi kuɗi zaka yi ko da kuwa kama kwance gida ne sai sun tararda kai, saboda an riga an rubuta zaka yi kuɗin sai dai idan kayi gajin haƙuri zaka iya samun ta hanyar da be kamata ba”
“Namra kina bani mamaki, ke yanzu da ba dan kuɗi ba iyayen ki ai ba zasu wulaƙanta ni ba”
“Wulaƙanci kamar ya?”
“Wulaƙanci ne mana, saboda an mai dani talaka wanda ba shi da amfani shiyasa aka saka miki wannan robar ba tare da sanina ba”
“Ba haka bane, kawai matsala ce ta taso kuma likitan yace dole ne nayi planning”
“To Allah ya kyauta, amman ko ma minene ai nafi kowa kusanci da ke, taya za'ayi ki yi min haka”
“Asim matsala ce fa kai yanzu kana son na samu ciki ya zo ya zube ko kuma nayi ta wahala?”
“Hmm kina dai ganin kamar ba zan iya hidama dake ba ke da abunda zaki haifa shiyasa kuka ɗauki wannan matakin”
Ta aje kofin ruwan dake hannunta
“Ba zan ɗauki halin nan naka ba Asim, babu yadda zaka riƙa cin zarafina dana iyayena, kullum mune marar mutumci a idonka, duk abunda muka maka baka gani, na sadaukar da yawa Asim, har inda be kamata na sadaukar ba na sadaukar amman baka gani”
Kamar mai jira sai kawai yayi cikinta da masifa.
“Me kika min ke da iyayenki? Me kika sadaukar min? Ran ki? Ko lafiyarki? Kullum da kin tadhi magana kin sadaukar kin sadaukar tun da na aure ki me na ƙara shi in ɓa tsiya ba? Ɗan abunda na tara dik ya ƙara na zo na kwanta a asibiti jiyan babu wani ɗan'uwanki da ya ɗauki wani abu ya ba ni, an so na mutu ban mutu ba shine yanzu zaki fara buɗe min wani babin na rayuwa, kina da kuɗi a jikin ki amman saboda baƙin ciki ba zaki fitar aci ba sai dai a mutu? To Wallahi Asim ikon Allah ne, duk wani mai son ganin bayana sai dai ni naga bayansa”
“Magana kake irin wannan zancen kamar mai magana da maƙiyansa, maitarka ta kasa ɓoyuwa har sai ta fito fili? Kuɗina sana'ah zan yi da abu na, dan ba zan zauna kullum ni ce biyar dangi a bani ba, kuma Allah be ɗora min alhakin ciyar da kai ba, ni aka ce ka ciyar ka tufatar, yanzu ka fito a siffar ka sak Asim daman dan dukiyar gidan mu ka aure ni ko, amman sai ka nuna mik baka son komai sai ni, ashe zagon ƙasa kake min ka ɗauki halin samarin zamani ka ɗorawa kan ka, masu auren jari...”
Wani irin mahaukacin mari ya kifa mata ya rufe ta da duka kamar ma dukan namiji.
Shuri yake aika mata ta ko'ina tana cigaba da dukan jikinta kamar ƴarsa.
Dukanta yayi sai da yaji ya daki iya kalaman data faɗa masa sannan ya sassauta mata ya miƙe tsaye yana ɗingishi.
“Kuma Wallahi kije aci miki wannan robar ko kuma wallahi na lahira ya fiki jindaɗi”
A fusace ya juya ya bar ɗakin. Kuka tayi har ta gode Allah sannan ta tashi zaune tana cigaba da hawaye.
Sai ynz take tabbatar da tayi kuskuren aure, ta auri mutumen da be san darajarta ba, mutumen da be san kowa ba sai kansa. Daman haka halin Asim yake abu kaɗan sai duka.
Ta share hawayenta dan itama kanta tasan ba kuka bane abunda take buƙata, sam Asim be cancanci hawayenta ba, a yanxu ta san wa take aure dole ne kuma ta shirya zama da shi. Bata da buƙatar kokawa kowa damuwarta ita ya kamata ta gyara zaman aurenta da kanta.
Ta tatsu iya tatsuwa dan haka yanzu ba zata sake bari guminta ya zuba akan Asim ba.
ASIM POV.
Ta ƙarfen dake hannunsa yana dafawa ya fito gate, sai huci yake kamar wani zaki.
Yau ji yake kamar ace ya rumtse ya bude ya gansa yayi kuɗi, ta yadda zai jidaɗin rayuwarsa. Sai yanzu yake nadamar karatunsa daya bari daman can yayi tunanin ko zai samu wani abun a gurin iyayen Namra shiyasa ya baro garin su da ita ta yadda nan zai ta cin karensa ba babbaka sai yayi ta aikata tana samu matsa kuɗi, amman yanzu ya fahimci itama maƙetaciya ce kuma bata sonsa da alheri.
Gashi yanzu ko sana'ah zai yi yasan ba zai samu kuɗi a tashi ɗaya ba, amman idan yana da karatunsa zai iya samun babban aiki.
“Mtssssss aiko karatun na yi ba aiki zan samu ba tun da nigeriyar sai da gata, su kuma waɗannan iyayen nata matsiyata ne ba aiki za su samomin ba, aiko wallahi duk wahalar da zan sha tare da ƴar su zan shata, sai na yi kuɗi tana ganin zata huta kawai na aikata gidan su.
Har ni za'ayi ma mugunta, ai ko sai na yi muku baƙin ciki dan haihuwa yanzu za a fara”
Ya ƙarasa maganar yana kallon Mardiya data doso gurin tana takawa a hankali. Tun daga kan ƙafafunta yake kallonta har zuwa fuskarta.
Shi dai kam yana son farar mace ko ba komai farar mace ko kallonta kawai kayi zata burgeka kuma zakaji kana son ta.
Tsaɓanin Namra da take black beauty, wace yake ganim a yanzu she's not his type, sai dai duk da haka ya ƙudiri aniyar sai ya kai ga jikin cos he need someone near him.
Ba zai je ya kashe kanshi da desires ba, weather blood ɗin ya tsaya mata ko be tsaya ba babu ruwansa yau zai yi yadda yake so da ita.
“Ina wuni”
Mardiya ta gaisheshi cikin ƙirsa da kisinsina. Shi kuma ya amsa mata a far'ah har kunne.
“Lafiya ƙalau Mardiya ya gida”
“Lafiya ƙalau ya jikin na ka?”
“Alhamdulillah”
“Allah ƙara sauƙi”
“Amin na gode”
Da kallo ya bita har ta ɓace masa da gani sannan ya dawo hanyyacin yana yaba kyauwon surarta a zuciyarsa.
KALSOOM POV.
Ita kanta yanzu ta rasa gane kanta balle Hilal da yanzu ya saka mata ido, dan duk ta barkace masa abu kaɗan masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.
Da gangan zata ƙi masa girki ko kuma tasa shi gaba tayi masa kuka, bayan be mata komai ba. Tun daga lokacin ya fahimcin akwai abunda yake cikin matarsa, daman can sha'anin ɓacewar cikin nan nata ya bashi mamaki, ga kuma jinin daya ƙi tsaya mata wajen wata huɗu kenan, babu irin maganin da be bata ba amman abun be tsaya ba, tun yana ganin abun kamar wasa har ya fara tsorota da lamarin.
Ita kanta tasan yanzu wannan jinin ya wuce haila ko zubar ciki ya zama na rashin lafiya, kuma ta san hukunci mai jinin rashin lafiya.
Shi kuma jinin rashin lafiya, jini ne da yake zuba ba a lokacin al'ada ba, daga wata jijiya da ake kira da azil. Al'amarin wanda take wannan jinin yana da rikitarwa, saboda kama da jinin haila yake. Idan mace ta zanto jini yana zuba daga gareta jo yaushe, ko kuma