Showing 243001 words to 246000 words out of 281103 words

Chapter 82 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61299

ɓata min rai ba, na tsani yarinyar nan na tsane ta, idan ma kana son ta ni ina ruwana karka sake kawo ni gurin, idan ma zaka so ka kaje can ka so ta ni karka sake sako ni a matsalar ku”


Shiru yayi yana saurarenta har ta yi masa faɗan ta gama sannan ya tashi motar yana murmushi ya suka nufi hanyar gida. Sarai kalamata suka wanke masa zuciya ɗan ya fahimci inda ta dosa. Yana yin fakin ya buɗe motar ta fita a hasale ta shiga cikin gida.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Abbah suka yi magana sannan ya faka motarsa ya fita ya shiga part ɗinsa.


Yayi awa ɗaya a part ɗin Abbah sannan ya fito tare da Abbah ya shiga motarsa ya kama hanya.




KALSOOM POV.


FIVE MONTHS LATER...
Daga ita har su Izza basa da wata matsala a yanzu, tana zaune da yaran lafiya ƙalau ga Hajiya sai nuna musu kulawa take. duk wani rashin kunya na Izza ta watsar, ulfah kan ba a magana daman tun da warke daga jinyar ruwana zafi sai ta ƙara ladabi, dan sosai yanzu suka gane muhimmanci Kalsoom, gashi lokaci-zuwa lokaci takan kira musu mahaifiyarsu su gaisa, ranar weekend kuma Hilal ya kaisu gidan Hajiya. Idan zai dawo Hajiya ta bashi rubutu ya kawo mata na neman ta sauka lafiya. Babu yadda Teema ba tayi ba akan ta dawo gidan amman Hilal da Hajiya suka ƙi, su Izzah kan ko zancenta basa so.


***
Bayan ta ƙare waya da Salma ne ta kalli Hilal dake kwance gefenta yana wasa da wayarsa tace.


“Salma na gaishe ka”


“Ina amsawa, bari naje na ɗauko su izza scul”


Ya faɗa yana unƙurin tashi, kai kawai ta ɗaga masa dan maganar ma wahala take mata ko wayar da take da Salma na ƙarfin hali ne, tun jiya take jin abu amman ta kasa faɗa, duk da ta kan ji irin haka lokaci lokaci amman wannan ya tsananta mata da yawa. Aiko kamar karya tashi daga gurim ta soma jin ana tsikararta, har zaman ya gagareta sai da ta kwanta.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Shi take ta maimaitawa tana rumtse rumtsen ido. waƴarta na kusa da ita amman ta kasa miƙa hannu ta ɗauka, wani irin juyi take jin duniya na mata, tun tana faɗar Innalillahi a hankali har ta fara yi da ƙarfi tana ta rumtsar ido da buɗewa kamar wacce ta ci bashi. Ko da Hilal ya ɗauko su Ulfah daga makaranta Kalsoom ta jigata, jini har ya fara mata zuba, daman tun safe ya kula da yadda cikin yayi mata ƙasa sosai. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauko kayan karɓar haihuwa ya dawo ɗakinta ya shiga ya rufe ƙofar ya shiga bata taimako, because ya san it too late yace zai ɗauke ta suke asibiti a yanzu bayan ga har kan yaro ya fara fitowa😷






ASIM POV.


Tun bayan rasuwar Mama ya daina ganin kam kowa da gashi, gani yake tun da yayi losing mahaifiyarsa a yanzu baya gudun komai, haka zai shigo cikin sokoto ya kwana gurin ogansa, ba zai leƙa ƙanensa ba sai zai tafi sannan ya basu kuɗi mai yawa, babban gida ya siya musu, dan yana ganin kamar su ne family da suka rage masa yanzu. Sai duk lokacin da ya shiga sokoto sai ya binka labarin Namra ace masa tana nan lafiya, har wani ya ɗauka mai aikin bincika masa labarinta, dan a tunaninsa tana nan ɗauke da cikinsa, burinsa kawai ta haifa masa ɗan ko ya ya ɗauke ta dan kawai ya ɗasa mata baƙin ciki. Sati ɗaya da rasuwar Mama aka saka ranar aurensa da Mardiya, yadda yake kashe mata kuɗi sai ka rantse da Allah shi ne yake buga kuɗi, dan yana samun kuɗi sosai a yanzu manyan mutane yake tare da su. Ya faɗa musu baya buƙatar komai dan tun kamin a kai lefe ya saka komai a gidan da zata zauna, kama daga kayan kitchen har zuwa na kwalliya da sutura kai kace ma be mata lefen gaba ɗaya ba sai taje can, har kayan abinci babu abunda be zuba ba, freezer goma ya saka a gidan jo wace cike take da kayan daɗi.
Ranar talata aka fara event an zubar da naira a kamu sosai kasancewar Asim ya bawa kawaye amarya kuɗi sosai, gashi shi ma yaje shi da abokaninsa dan yanzu yayi sabin abokai yayan manya sai kuma masu irin aikinsa, duk wani gaye mai kuɗi da kasani a cikin garin katsina mai ji da kansa sai Asim yayi abota da shi, dan gani yake sune sa'o'insa.

Friday aka yi walima, a instagram Namra take ganin bikin kamun su, tayi mamakin da ya auri Mardiya dan bata manta lokacin da yake yawan maimaita mata cewar shi sai ƴar da ubanta ya fi nata kuɗi zai aure, wata ƙila farin jikinta ne ya jashi hankalinsa ko kuma bayan ya aureta zai ƙara wata.


Tun ranar da aka gyara ɗakin aka saka komai Asim yake kwana a gidan. Wasu abokansa da suka zo daga sokoto da Abuja sai ya kama musu hotel wasu kuma ya sauke su a ɗayan gidansa dake GRA, shi kuma ya koma Light up road inda gidan amaryarsa yake dan kwana. Light up unguwace ta masu kuɗi ko wanne gida ka gani sai ya burge ka, amman duk da haka a layin da Asim yake gidansa ya fi ko wanne gida kyau da tsari, kana ganinsa kasan ba ƙananan kuɗi aka kashe ba gurin gina shi.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare ya shigo gidan, cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yana jinsa a wani matsayi na daban kwatankwacin matsayin da ya riƙa jin kamsa a lokacin da zai auri Namra, freezer da ke kitchen ya nufa ya buɗe ya ɗauko power horse ya fito falo yana sha. Kansa ya ɗaga sama yana kallon pop zuwa labulayen da aka saka falon, hantin kawai idan ka kalla sai ya burge ka, balle kuma kujera da plasma da flowers, daga kujera har center carpet da labulayen da da fantin ɗakin milk and red ne, dinning area kuma aka ƙawata gurin da red color. Relaxing yayi sama cushion yana furta sunan Namra, a zuciyarsa, haka kawai ta faɗo masa a rai, duk wacan dukiyar da aka narka masa a wacan gidan da Namra ta kama musu haya ubanta ne ya narka masa ita yayinda wannan kuma shi ne ya narka ma Mardiya. Haƙiƙa Namra ta yi masa hallacin da ba duk mace ce take yi ma namiji irin wannan hallacin ba.


“Dole wata rana zaki dawo gare ni Namra, dole idan kika haifa min ɗa ki dawo kina so na idan na karɓe abu na, zaki dawo ki ga yadda Asim yake amsa sunansa a cikin garin Katsina, daga lokacin zan nunawa Ubanki iko na da kuma karfin kuɗi na”


Ya furta yana jefar da kwankwanin power horse ɗin sannan ya ciro wayarsa daga aljihu ya nemo number Sufiyan ya aika masa kira, be damu da ganin dare yayi ba ganin yake tun da yana biyansa kuɗi dole ne ko a wane lokaci ya yi masa abunda yake so.


“Hello oga Allah yasa lafiya ka kira ni a wannan lokacin”


Ya faɗa cikin muryar bachi.


“Lafiya ƙalau, kana da labarin Namra? ”


“Akwai labari oga amman da ka hakƙura har da safe”


“Ba zan haƙura ba, faɗa min kawai”


“Oga wannan monday da ta wuce ta fara zuwa makaranta, na bita har makarantar na ganta Mahaifinta ya ɗaukar mata sabon direba, amman oga sam babu alamun ciki a tare da ita, dole ne idan har akwai cikin da zai tsawon wannan watannin ya nuna ko da kaɗan nan, sam ban ga alamun tana da ciki ba, kuma kaga da tana da ciki da ba zata koma karanta ba yanzu”


“Ka tabbata?”


“Na tabbata oga”


Ya katse kiran yana lasa lips ɗinsa.


“Idan ko har kika yi kuskuren zubar da cikin nan sai kin yi nadama Namra, ke da ubanki sai na kaskantaku”


Yayi ƙwafa tare da busar da iskar bakinsa. Ɗan kishingiɗawa yayi kaɗan sai bachi yayi gaba da shi daman a kwai gajiya sosai a tare da shi. Be yi bachin awa biyu ba ya soma jin hancins ana mugun yaji numfashinsa na sama-sama sai sarƙewa yake, ba shiri ya farka a firgice sai hayaki ya turniƙe masa ido, duhu ya soma gani sai tari yake kamin ya waiga ɗayan gefensa ya hango bedrooms ɗin suna ci da wuta. Wani irin tsalle ya daka ya sai gashi gaban ƙofar falo yana ƙoƙarin ɓanɓanreta amman ina hayaƙi da tsage ƙofar. Mai gadinsa ne ya farko yaga halin da ake ciki ya fita neman jama'a abunka da unguwar masu kuɗi sai kowa yayi maaa banza sai gaba ɗaya mutane suka fiffito, daker aka samu aka ɓalle ƙofar falon, suka fito da Asim, domin hayaƙi ya turniƙe shi tuni ya faɗi a gurin yana haƙi.


Kan kace kwabo sai ga ƴan fire service mota kusan uku aka shiga kashe wutar, amman kamar ana ƙarawa, haka wutar ta riƙa ci har asuba, bata mutu ba sai da ta ƙone komai na gidan.




Ta ɓangaren Mardiya ma ƴan kashe wutar gobara ne suke ta kai da koma amman wutar da ƙi mutuwa, babu abunda yaba jama'ah tsoro kamar yadda wutar take ta sama kamar abar da ake sawa fetur, ba ɗakinsu wutar da tashi ba, amman bata rage komai da yake ɗakinsu Mardiya ba, har da kayan baƙi ƴan zuwa biki sai da wutar da cinye, sannan ka bi sauran ɗakunan gidan duk ta cinye.


Mardiya na maƙota aka faɗa mata, daman tun da aka fara bikin maƙota take kwana ita da ƙawayenta, ko da ta zo wutar ta ci har ta cinye babu abunda ya rage a cikin gidan, a take ta saka kuka ganin komai ya ƙone babu abunda take ji kamar kayan mutane da suka ƙone, babu daɗi ace kaje biki wani abu ya faru. Bata ƙara firgicewa ba har sai da wani abokin Asim ya zoɓya labarta mata halin da suke cikin ma ƙonewar da wacan gidan yayi wanda za a kaita.


Hannu ta ɗora saman kai ta fashe da kuka tana kiran ta shiga uku.




“Allah yasa ba wutar da nake mafarki bace take bi na ba, na shiga na lalace”


Kuka ta riƙa yi kamar mahaukaci sai da ka riƙeta ana bata haƙuri.








RASHIDA POV.


Bayan ta gama sallah azahar ta tashi tayi nafila sannan ta ɗauki carbi tana lazimi, haka take kullum cikin ibada take fatanta kawai Allah ya yafe mata kamar yadda mijinta da Kalsoom suka yafe mata, a iya yanzu ta yarda da ƙaddarar da Allah ya aiko mata kuma ta aminta babu mai iya yaye mata ita sai Allah, tabbas tasan Allah yana son ta tun da har ya ganar da ita tun gabanin ya karɓi rayuwarta.


Ta miƙa lamurranta ga Allah, kwata-kwata ta cire rayuwar daga yin aure dan tasan ba zata samu mijin da zai aureta ba, da ma kuma ta samu bata tunanin zata iya zama aure da namijin wanin Hilal. Daman ta daɗe da aje aikinta, duk wani abunda da take da buƙata Mahaifinta yana yi ma, abokanta kuma suna kawo mata ziyara a gidan, waɗanda suka wayanci miye hiv wasu kuma tuni sun ƙaurace mata gudun kar suma su ɗauka.


Ta ɗauki darasi a rayuwarta sosai, tun daga cin amanar aure da tayi, da kuma neman taimakon wanin Allah wato bokaye da ƴan duba, a iya kallon rayuwar Kalsoom da tayi ta fahimci darasin da yake tattare da itazm, tabbas wanda duk ya miƙa lamurransa ga Allah, lallai Allah yayi alƙawarin jiɓantar al'amarinsa, babu irin shige-shige da bata yi ba wajen ganin da raba Kalsoom da Hilal ko ta raba ta da lafiyarta amman addu'o'in da take suka mata kariya da katangar tsari daga duk wani sherinta. Hakan yasa itama ta tattara lamurranta ta miƙa wajen Ubangiji, ta samu natsuwa da kwanciyar hankali sosai, duk da tasan ciwon dake jikinta ba zai taɓa rabuwa da ita ba, amman tana Allah ya sanyaya mata zuciyarta har ta samu ƙarfin halin sakewa tana fita cikin mutane.


Bayan ta gama istigifari ta ɗauke carpet ɗin ta naɗe ta maida mazauninta, sannan ta nufi kitchen dan ɗora abunda zata ci. Vegetables soup ta girka da white rice daman likita yana yawan faɗa mata ta riƙa cin su. Falo ta fito ta zauna tana cin abincinta hankali kwance tana kallon tv, wayarta ce ta yi ringing sai ta miƙe tsaye ta ɗauko, murmushi ta yi ganin number Hilal a zatonsa zai sadata da su Ulfah su gaisa ne sai kawai ya miƙawa Izzah ta yi masa albishir ɗin Anty su ta haihu.


“Mashallah me aka samu?”


“An samu Baby boy, Momi Mai kyau sosai”


Wannan karon Ulfah ce take magana.


“Allah ya raya ashe kun samu ƙane ko? Ina dady ku?”


“Yana can gurin Anty be san mun kira ba, Momi Boy ɗin kato ne sosai kuma fari”


Ezzah ta faɗa with so much joy and excitement. Idon Rashida ya cika da ƙwalla dan har gobe har jibi tana son mijinta sai dai tasan yayi mata nisa.


“Zan zo gobe na ga Baby kun ji”


“Toh Momi”


Suka kashe wayar, ita kuma ta share hawayen idonta tana tuna lokacin da ta haifi Rafiq yadda Hilal ya dinga ɗauki kamar zai haɗeta ita da yaron.


‘Allah sarki duniya’


Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuma sai ta amsa salamar da Alhaji Bashir yake yayinda yake turo ƙofar falon ya shigo.
[7/21, 10:29 AM] Khadeeja Candy♥: *86*


“Miya kawo ka gidana?”


Murmushi yayi ya zauna saman kujera yana kallonta fuskarsa da annuri.


“Haba Hajiya ai ko baki san inda na fito ba kya saurara min ko?”


“Na fi ƙaunar ganin baƙin maciji da kai, bana son abunda zai sake kusantar da ni a gareka Alhaji bashir dan Allah dan Annabi ka tashi ka fitar min daga gida”


“Ban zo gidanki da wata manufa ba Rashida sai ta alheri”


“Babu alheri a tare da kai, dan Allah ka tashi ka bar min gidana”


“Miyasa kike alaƙanta rayuwar da kika shiga da laifina? Bayan kuma idan baki amince ba ba zan iya miki da ƙarfi ba?”


“Nasan nayi kuskure ai a lokacin shiyasa yanzu na tuba na koma gurin Ubangijina, kuma Alhamdulillah rayuwata da dai-daita”


“Nama ai tuban na yi shiyasa nake son dai-daita rayuwa da taki, har ga Allah Rashida ina son ki ba wai so na zina kawai ba, so na haƙiƙa kawai saboda babu yadda zan yi ne, ni da ke kukan mu munyi kuskuren faɗawa a halaka, ke saboda baki da lokacin da zaki tsaya ki bawa mijinki kulawa shi ma kuma ya baki, ni kuma na kasa ƙara aure duk da ina ganin sha'awar wasu matan saboda sherin da matata ta yi min, yanzu kuma Alhamdullillah na gane kuskurena kuma am ready to marry you idan kin aminta, saboda kin rufa min asiri a lokacin da ya kamata ki tona min, kin rufe bakin ki kin haƙura kin bar ni akan aikina, bayan kuma kina da damar da zaki tona min asiri, ki faɗawa duniya abunda muka aikata”


“Ban shirya aure yanzu ba Alhaji Bashir idan ma shi ya kawo ka ka tashi ka bar min gidana”


“Kin fi son ki yi ta zama a haka? Indai akan Asmee ne karki damu bata isa ta hanani ƙara aure ba yanzu”


“Baka tsoron ace ka auri mai cutar ƙanjamau?”


“Daga lokacin da kace zaka damu da matsalar mutane zaka saka kan ka ne kawai cikin matsala, ni da ke da Asmee duka muna ɗauke da abu ɗaya, miye amfanin ke na ƙyale ki akan gudun abunda duniya zata ce min? Zan yi ritaya gudun kyamar da za a nuna min gurin aiki, amman karki manta ina da hannu jari kuma ina da kasuwancin da zai iya riƙe jikokina ma ba ƴayana da matana kawai ba, ki yi tunani Rashida karki yaudari kanki akan abunda zuciyarki take muradi”


Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya fice. Da kallo ta bishi tana sauke ajiyar zuciya, sam bata shirya irin wannan rayuwar ba, aure yanzu? Ita da yanzun tana jin ta samu sukuni a rayuwarta, taya zata yi aure ta sake jefa rayuwarta cikin wani halin kuma? Ita kan bata shirya kishi da Asmee ba.


KALSOOM POV.


Hilal kamar ya haɗe yaron dan murna, duk wanda ya ga Baby boy ɗin sai yayi mamaki ace da kanta ta haihu musamman da suka ji gida ta haihu, wasu daga cikin abokansa suka riƙa zolayarta wai ai matar doc ce dole ya karɓi haihuwarta. Hajiya ta nuna farincikinta sosai duk bayan kwana biyu sai ta zo gidan duba jikanta, Salman kam kullum tana biye da hanya, sai da aka kwana uku sannan Rashida ta zo ganin Baby shi ma kuma da dare, ta yi siyayya mai yawa ta kawo, sai dai bata yarda ta karɓi yaron ba duk da Kalsoom ta yi kawaicin miƙa mata shi, bata yi minti ashirin a gidan ba ta fito su Ulfah suka rakota har bakin mota ta basu kuɗi da chocolate.


Ranar suna Baby ya ci sunan mahaifin Hilal wato Abubakar aka yi masa laƙani da Rafiq. Fuskarsa sak ta Hilal yaro ya sha stickers har ya gaji, an raba abubuwa da yawa ranar sunan, da yamma aka yi walima ta gani ta faɗa, kuloli da manyan kofuna da agogo sai har ma da handbags masu kyau, wasu kuma su samu shoes.


An kashe kuɗi da yawa gurin walimar nan kai kace ma yanzu ne Hilal yake samun haihuwar fari, yadda ya zuba mata kayan barka ma a abun kallo ne, ga kuma waɗanda ta samu daga ɗai-ɗaikun mutane ƴan uwa da kuma abokan arxiki.


ABDOOL POV.


Tafiya yake shaddar dake jikinsa tana amsa amo saboda maiƙon da ke jikin shaddar da kuma sabuntakarta.


Ko da ya shigo part ɗin Ummi yana waya da Mai Martaba dake faɗa masa yana nemansa, a falon ya zauna sai da suka gama tattaunawa sannan ya kalli Ummi da ke cikin shirin ta na fita ya ce


“Ummi fita zaki yi?”


“Eh Asibiti zan je na duba Hajiya Sadiya kasan ciwon nata ya zama abunda ya zama, kuma kaima ya kamata ace ka duba ta, tuɓ da ta kwanta asibitin nan baka taɓa zuwa duba ta ko sau ɗaya, wai anya ma ka mata gaisuwar yarinyar ta da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login