Showing 21001 words to 24000 words out of 281103 words
Chapter 8 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
dan yanzu Hajiya Raliya ta kira ni wai tana son ta zo Mamanki ta hanata, kuma ƙara mu koma gida kar a fara mana taro, tun da babu wanda yaji abunda ya faru sai ƴan gida”
Namra ta lumshe ido ta jin wani abu daya tsaya mata a zuciya.
Amira ce taje ta biya komai da komai sannan ta zo ta riƙa Namra suka fita tare.
HILAL POV.
A gajiye ya fito asibitin, daker yake driving saboda gajiya, dan wuni yayi yana aiki, har jin yake kamar fever na son rufe shi.
Yau kan baya iya bin gosulon nan na government house, saboda taron da ake.
Sai kawai ya hanka ta cikin estate dan samawa kansa sauƙi sai dai tafiyar zata masa nisa sosai tun da ya biyo doguwar hanya.
“Subhanallah”
Ya faɗa lokacin da idanuwansa sukayi arba da wata kyakkyawar fuska, dake takowa izuwa hanyar daya fito. Sai ya rage gudun da yake, ya mai cigaba da kallonta.
Tana da kyau sosai mai jan hakali da saka natsuwar zuci, sai dai fuskarta kawai yake iya gani, domin jikinta rufe yake da ƙaton hijabi. Hakan kuma ba ƙaramin burgeshi yayi ba, ganinta cikin kamala ga tafiyarta a natse.
Kamin ta ƙaraso kusa da shi ya faka gefen ti-ti yana ƙare mata kallo.
Tana da tsayi da dogon hanci ga idonta dara-dara, farin fuskarta fes, sai dai a iya yadda ya fahimta kamar bata da jiki sosai.
Dai-dai lokacin data kawo kusa da shi sai ya sauke gilashin motarsa yana miƙa mata sallama.
“Assalamu alaikum Malama”
“Wa'alaikassalam”
Ta amsa mishi da zazzaƙar muryarta sai dai hakan be sa ta tsaya ba, sai ta cigaba da tafiyarta kamar ba ita ta amsa masa sallamar ba.
Da sauri Doctor Hilal ya buɗe motar ya fito ya biyo ta da ƙafa.
“Dan Allah ɗan tsaya na tambaye ki wani abu”
Allah daya haɗa ta dashi yasa ta tsaya, da badan haka ba babu abunda ze sa ta tsaya dan iya yanzu ta sallama a lamarin maza.
“Dan Allah ke matar aure ce?”
“A'a”
“Dan Allah ya sunan ki, kuma ina ne gidan ku?”
Sai a lokacin ta kalleshi, wani faɗuwa gabanta yayi lokacin da idonta suka sauka cikin nasa, kyausa yayi mata kwargiji, wanda yasa tayi saurin sauke idonta ƙasa, tana sauraren bugun zuciyarta.
“Miyasa ka tambaya?”
“I ask you first”
Ba amfanin yin ƙarya, dole ta faɗa masa gaskiya.
“Sunana Ummul-Kalsoom amman ana kira da Kalsoom, gidan mu yana ta nan gaba number 5 gidan Alhaji Faruk Kafinta”
“Toh na gode”
Bata sake ce masa komai ba, ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya bita da kallo har sai da yaga inda ta shiga, sannan ya shiga motar yana murmushi, a take ya ji duk gajiyar da take tare dashi ta wartsake, cikin farinciki da annashuwa ya kunna motar ya hau ti-ti.
__________________________
What do you expect next?
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa11.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
NOT EDITED ⚠️
*PAGE - 11*
NAMRA POV.
Keke Napep Amira ta tare musu ta faɗa masa inda ze kai su, sannan suka shiga.
Be sauke su ko'ina ba sai Ƙofar gidan, Amira ta biya shi sannan ta riƙa hannu Namra suka shiga cikin gidan.
Kamar mai nauyin ƙafa haka Namra take tafiya tana hawaye, gaban na bugawa da ƙarfi. Da wane ido zata kalli Anty Amarya? Idan Abbah ya kalleta me zata ce masa.
Mama Zainab ce gaba da sallama sannan Namra, sai Amira ta biyo baya. Hajiya Raliya ta amsa musu sallamar, Anty Amarya kam yi tayi kamar ma bata gansu ba, ta tashi tayi ta nufi kitchin.
Saman Kujera Amira ta zaunar da Namra, sai ta zauna kusa da ita tana amsa ya jikin da Hajiya Raliya take mata.
“Da sauki har an sallamota”
“Wallahi babu yadda ba mu yi ba ni da Aisha da Hindu muje ganin ki amman Larai ta hana, sai gashi Abbanki ya zo shi yace kar wanda ya fita da sunan ganin ki a gidan nan, toh kar ma ya kuskura ya dawo”
Fashewa ta yi da kuka, ta kwantar da kanta jikin Amira dake hawaye.
Shigowar Hajiya Barau ne yasa ta noke kanta, Amira da Mama Zainab suka amsa mata. Idonta kar kan Namra sai kallon jikinta take.
“Namra kin dawo? Wallahi Alhaji ne ya hana mu zuwa ganin ki, ya jikin?”
“Alhamdulillahi”
Mama Zainab ta amsa. Zaunawa tayi kusa da Amira.
“Ince dai babu abunda ya same ki ko?”
“A'a ba komai likita ya bincika yace babu abunda yake damunta”
Cewar Amira
“To Alhamdulillahi, Allah ya tsare gaba”
Sai ta tashi sun-sun-sun ta fice. Hajiya Raliya ta kalli Namra cikin damuwa ta ce
“Haba Namra haka kike so maƙiya su yi ta miki dariya? Ansa ranar aurenki kije ki gana da wani? Haka aka kawo mana ke shame-shame mazan unguwar nan zagaye da ke, shi haka shine daɗi?”
Amira ya share hawayenta
“Dan Allah ku daina wannan maganar, zaku ɗaga mata hankali ne kawai, ita kan ta ba'a son ran ta hakan ya faru ba, kusan babu yadda Namra zata kai kanta ga halaka ko kuma inda ta san mutuncin ta ze zube”
Namra kan kuka kawai take, tana jin wani irin ƙololon baƙin ciki ya riƙe mata zuciya. Kamar daga sama sai ga Abbah ya shigo falon fuska babu annuri.
A take cikin Namra ya ɗauki ƙugi, ko Amira sai da ta razana da yanayinsa, yana katsawa Namra tsawa jikinta ya hau rawa.
“Khadija ki tashi ki koma can gurin saurayin na ki bana son ganin ki a cikin gidan nan!”
Cikin baƙar zuciya Anty Amarya ta fito daga kitchen ta nufo inda Abbah yake tsaye tana faɗin
“Babu inda Namra zata je, ko kisan kai ta aikata idan ta shigo nan gidan ta samu mafaka, dan gidan ubanta ne ciki da waje, komai Namra ta aikata sai ance ƴar Alhaji Usaman ce ko da bata duniya, duk inda aka ga sunan Namra sai anga naka kuma dole ace ƴar ka ce”
Abbah ya nuna Anty Amarya
“Ai daman ke kike goya mata baya take duk abunda take”
Anty Amarya ta nuna kanta tana hawaye.
“Ƙwarai, nina goya mata baya nace ta fita cikin dare taje taga Asim, kuma idan taje ta faɗi ta suma jama'a su ɗauko ta su kawo maka cikin gida ni nace....”
Mama Zainab ta rufe mata baki, tana ba Abbah haƙuri. Da ƙarfi Anty Amarya ta buge mata hannu ta matsa tana faɗin
“Ki ban ni ina faɗi ciwon bakin na, wannan ƙurjin ya daɗe yana min ƙaiƙayi a cikin rai, duk abunda Namra ta aikata gare ni yake dawowa, ni nake tura ta, faɗa min wace uwa ce zata so abunda ya faru da Namra ya faru da ƴarta, amman ni yake ɗorawa laifi”
Shiru Abbah yayi yana kallon Anty Amarya data cika falon da ruwan bala'i tana zazzaga masa rashin mutuncin har yata gama be sake cewa uffan ba.
Hajiya Raliya ce keta bashi haƙuri tana cewa kar ya tanka mata, shi ma daman be da niyar sake ce mata komai, dan yasan Anty Amarya bata iya faɗa ba, idan ta birkice masa babu mai iya tare ta sai Allah, haka take wani lokacin kamar mai aljannu, shiyasa Hajiya Barau ta sallama ma lamarinta.
Tsaye Anty Amarya ta yi masa ƙyam, tana jira ya ce mata kulle ta ce masa chas, dan idonta yanzu a murje yake, zuciyarta kuma ta kawo. Abbah be yarda ya sake ce mata ƙomai ba, ya juya ya fice.
Sannan Anty Amarya ta kalli Amira a tsawace tace
»“Ke Amira tashi ki je gida”
Da sauri Amira ta ɗauki jakarta ta rayata, ko sai ajima bata ce ba, ta fice jikinta na rawa.
Tasss! Tasss!! Tasss!!! Anty Amarya ta sauke ma Namra mari har sau uku, sannan ta nuna mata ƙofar ɗakinta
“Tashi ki wuce ɗakin ki, kin samu farinciki kin jidaɗi”
Zubewa Namra ta yi ƙasa daga kan kujera tana kuka, ta riƙe ƙafafun Anty Amarya.
Riƙo fuskar Namra Anty Amarya ta yi ta sake sakar mata wani marin sannan ta tureta ta fisge ƙafarta, ta wuce ɗakinta cike da ɓacin rai.
Daga Hajiya Raliya har Mama Zainab tsaye suka yi basu yi unƙurin yin wani abu ba, dan sunsan halin ƴar'uwarsu kan akwai haƙuri amman idan ta hasala bata da daɗi.
Sai daNamra tayi kukanta mai isarta sannan ta tashi ta nufi ɗakinta. Saman gadonta ta faɗa ta sake fashewa da sabon kuka.
Har La'asar bata fito daga ɗakin ba, kuma babu wanda ya shiga inda take inba Aisha ba, itama tun da ta fita tayi shirin islamiya babu wanda ya leƙo ɗakin.
Tasan dole ne Maryam tayi fushi da ita, dan Maryam tafi kowa ɗaukar zafi idan wani abu ya faru. Sai da dare Aisha ta shigo ta aje mata abinci ta fita.
UZAIR POV.
Yana tasowa daga gurin aiki kai tsaye ya wuce guesthouse ɗin Jafar, daman tun yana gurin aikin suka sha masa kai da kira, wai duk sun hallara shi kawai suke jira.
Yana shiga ruwa kawai ya sha Najeeb ya tambaye shi.
“Ya Labarin yarinyar?”
“Wai asibiti ta kwana, Kishiyar mamarta take faɗa min ɗazu da safe, sai na nuna mata kamar ban ji ba”
“Amman kaje ka ganta?”
Jafar ya tambaya. Sai ya girgiza masa kai
“A'a na dai je gurin Hajiyata na faɗa mata maganar janye auren tace zata je ta faɗawa Abbah”
Najeeb yace
“Amman ai da kaje ka ganta Uzair sai ka nuna kasan abunda ya faru, anyway muje ciki malamin yana ciki tun ɗazu ya iso”
Uzair yayi sauri haɗiye ruwan bakinsa.
“What? Na ɗauka zuwa zamu yi gurin shi”
“No Ba zamu iya shiga dajin nan ba, sai na aika direba ya ɗauko shi, kasan su kuɗi kawai suke so da sun ga ƙuɗi komai zasu iya”
Cewar Najeeb. Tahir ya aje wayar dake hannunsa saman tebur ya miƙe tsaye.
“Muje ayi abunda za'ayi akwai inda nake son naje”
Sai duk suka ɗugunzuma suka nufi wani ƙaramin falo, da ba kasafai suke zama cikin shi ba.
Dattijo ne sanye da babbar rigarsa, kansa ya sha uban rawani, haƙorasan duk goro, ga wani ƙaton faifai dake gabansa, mai cike da jar ƙasa. Idan ka kalleshi sai kayi masa ɗaukar mutumin kirki, a fuskarsa ba zakayi zaton zai iya aikata wani mugun abu ba.
Duk guri suka samu suka zauna, bayan sun gaisa, Jafar ya kora masa da bayani
“Am daman na faɗa maka tun ɗazu, abokin mu ne yake ciki wata ƴar matsala, wata ƴar'uwarsa ce take ƙoƙarin masa zagon ƙasa, saboda ta kamashi yana aikata luwaɗi, shine take son tona masa asiri, babu yadda be lallaɓata ba amman ta ƙi yanzu haka so take ta rabashi da matarsa, da kowa nasa”
Lokacin da Jafar ya kai aya sai ya zumguri kafaɗar Uzair alamar yayi magana, sai shi kuma ya ɗora.
“Yanzu haka ta ɓata min suna a cikin familyn mu kuma yanzu haka tana nan akan bakanta na cewar ta faɗawa duniya da ƙwaƙwarar hujjah”
Malamin yayi murmushi yana gyara zamansa.
“Yanzu me kake son ayi mana, shin kana son a kulle mata baki ne ko kuma ayi mata kurciya ta bar garin gaba ɗaya?”
Kallo-kallo suka riƙayi, kowa na tunanin abun cewa, can sai Najeeb yace
“A ɗaure mata bakin kawai ta yadda komai ta gani ba zata iya faɗa ba”
“Ko kuma ayi mata kuciya ta bar garin gaba ɗaya”
Cewar Jafar. Uzair ya girgiza kai
“Idan muka mata haka ba muyi mata adalci ba, why not dai ayi mata na rufar bakin”
Najeeb yaja tsaki
“Ita ba naka sunan ta ɓata ba? Idan aka mata kuciyar ta bar gari kana tunanin wani zai zargeka ne? Sai dai ace ai halinta ne, kuma wannan shine kawai mafita”
Uzair yayi shiru yana nazari. Sai Malamin yace
“Minene sunan ta? Sai mu duba muga irin aiki daya dace ayi mata, dan aikin da ke yima wani bashi ke ma wani ba”
“Sunanta Khadija, amman Namra ake kiranta”
A take Malamin ya gyara ƙasar ya shiga bincike, yana wasu tsiface-tsiface.
Ya ɗauki tsawon lokaci yana bincike amman be gano komai ba, can ya ɗago kai ya kallesu yana jinjina kai yace
“Lallai wannan aikin ze ci ƙuɗi da yawa, kuma magana ta gaskiya wannan yarinya akwai tsari tare da ita na musamman, ba lallai bane ko wane irin aiki ya kamata sai dace”
Duk sun cika da mamaki, bama kamar Tahir daya kasa haƙura har sai da ya tambaya
“Saboda me?”
“Ban san dalili ba amman lallai akwai tsari mai ƙarfi a tare da ita, kasan ni bana aiki da munafurci kuma idan har abu baya yi zan fito fili na faɗa maka gaskiya”
Uzair ya sauke ajiyar zuciya
“Yanzu ba wata mafita kenan?”
Lailaya ƙasar yayi
“Bari mu bincika mu gani”
Sai ya koma bincike yana watsa wani farin miski a jikin ƙasar.
Zuwa can ya ɗago ya kalli Uzair yace
“Ta ƙi bayyana a binciken mu, sai dai an samu mafita, za a iya samun sa'arta ne kawai da asuba ko kuma lokacin da take haila”
Lokacin asuba lokacin ne mala'ikun da suke tsare bawa idan yayi addu'ar bachi suke tashi, Idan be yi saurin tashi yayi sallah ba, a lokacin har sheɗan yake samun sa'arsa ya saka masa kasala, da ƙuiyar yin sallah har sai rana ta fito.
Lokacin Haila kuma lokaci ne da ba ko wace mace ba ce take tsare yin addu'ah a wannaɓ lokacin ba, saboda ganin tana al'ada, bayan kuma duk kan addu'o'i an yarda mai haila ta karanta sallah ce kawai aka ɗauke mata, da ɗaukar cikakken ƙur'ane, da kuma ɗawafi.
Dan haka yan'uwa mu kiyaye addu'ah a wannan lokacin, kuma mu kiyaye Sallah asuba a cikin lokaci, tana da muhimmanci sosai.
Najeeb yace
“Amman kana ganin idan har anyi aikin zai ci kuwa?”
“Zai ci dan wannan aikin ba za a yi shi ace ba a ga nasara ba, sai dai ya zamo wanda ake son ya sama ɗin be same shi ba”
“Kamar ya?”
Tahir ya tambaya da sauri.
“Zamu yanka baƙin bunsuru guda biyu, da rago, sai a samo mana tunfafiya da kurciya da su zamuyi aikin, sai a rubutu wasu abubuwan da jinin bunsurun a watsa a riga ko zane da zata ɗaura sai a bata ta saka, inda har ba wanda ya bata ɗin nan bane yayi kuskure toh lallai babu tantama aikin zai kamata, amman fa a lokacin da take Haila ko kuma kamin sallah asuba”
Jafar ya riƙe baki
“Babbar magana, dole sai ta wannan hanyar kawai?”
“Ba dole sai ita ba, amman ita ce tafi ko wace sauƙi”
Tahir ya kalli Uzair
“Toh kai kana da mak maka wannan aikin ne?”
“Akwai wata ƙawarta ina jin kamar zata iya, amman what if ba ayi nasara ba?”
Tahir ya dafa shi.
“Ka yarda kawai za'ayi nasara, karka sawa kanka wannan”
Kai ya girgiza
“Ni dai ko na haƙura kawai na ƙyaleta”
Ganin yadda Uzair ya tsorata yasa Malamin shiga kwantar masa da hankalin
“Za'ayi nasara, karka damu, ka haɗani da wadda zata kai mata rigar na san yadda zan tsara mata komai”
Shiru Uzair be ce komai ba, shi dai sai tunani yake. Ganin hakan yasa Najeeb yace da Malamin
“Shikenan a fara aikin kawai, zan turo maka dubu ɗari a account ina tunanin zasu isa? Idan ma da wani abu sai ka kira a waya”
“Zasu isa inshallah, amman za a kawo rigar da taɓa sawa, dan da ita zamuyi aiki, kuma ina son ganin yarinyar”
“Ba matsala zuwa gobe duk yadda muka yi zaka ji ni”
Daga haka suka yi sallama, Najeeb yasa direba ya maida malamin. Sannan suka ya dawo falo suka shiga tattauna maganar.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa12.html
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺
_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*
Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated
NOT EDITED ⚠️
*PAGE - 12*
HILAL POV.
Wanka yayi ya shirya cikin wata gizna, maroon color, sannan ya ɗauki hulla mai kyau ya saka, ya ɗauki agogon hannu ya saka ya feshe jikinshi da turare, sannan ya buɗe wardrobe ya ɗauko sababin kuɗi ya saka a aljihu, sannan ya dawo gaban madubi ya sake kallon kansa, ya tabbatar da kwaliyarsa ta fito, sannan ya ɗauki keys ɗinsa ya saka baƙaƙen takalmi, ya fice.
Ko da ya fito falo, Rashida na gaban dinning tana shirya musu dinner, su Ulfah zagayeta suna nuna mata assignment ɗinsu.
Kusa da ita ya ƙarasa yana leƙon abincin da take zubawa.
“Pyar a zubawa yara nasu nawa sai na dawo mu ci”
“Ina zaka je?”
“Ango zamu je rakawa ba zan daɗe ba”
Juyowa tayi ta kalleshi daga sama har ƙasa, yadda kyau nan nasa ya fito ya bata tsoro. Shi kuma sai yayi kamar be ga kallon da take masa ba sai ya kalli agogon hannunsa.
“Bari naje kar nayi latti, ni kawai suke jira”
Hannu yasa ya rufe idon Ulfah sannan yayi mata kiss a baki, sannan ya nufi ƙofa sai ƙanshi turare yake.
“Allah ya tsare min kai ni dai”
Ta faɗa lokacin da zai fice. Murmushi kawai yayi ya saka kai ya fice.
Motarsa ya shiga yayi horn mai gadi ya buɗe masa, ya hau ti-ti zuciyarsa cike da nishaɗi.
Cikin ƴan mintuna ya isa estate ɗin su Kalsoom. Numbers ɗin gidaje ya riƙa dubawa har ya kai ga number.
Dai-dai gate ɗin ya tsaya yayi horn yayi mai gadin gidan ya leƙo sannan ya buɗe masa, sannan ya shiga harabar gidan yayi parking. Sai ya fito ya nufo mai gadi ya bashi hannu suka gaisa sannan yace
“Dan Allah ko nan ne gidan Alhaji Faruk Kafinta?”
“Eh nan ne”
“Dan Allah mai gidan yana ciki?”
“Eh yana ciki”
“Dan Allah kayi min sallama da shi”
“To wa za'ace masa?”
“Ce masa Doctor Hilal ne”
Da sauri mai gadin ya nufi cikin gidan. Doctor Hilal kuma ya dawo gurin motarsa ya tsaya yana ƙarema gidan kallo.
Hilal ya kusan minti goma tsaye a gurin sannan Abban Kalsoom ya fito, yana ganin Doctor Hilal ya washe baki.
“Maraba da bokan turai, yau likita a gidana na”
Da sauri Hilal ya miƙa masa hannu suka gaisa, har da ɗan risina masa yana murmushi.
“Wai daman nan ne gidan ka?”
“Nan ne kasan abu ga talaka”
Ya faɗa yana dariya, yasan Doctor Hilal sosai dan shine likitan da yake dubashi a duk lokacin daya je asibiti, sai dai Doctor Hilal be