Showing 54001 words to 57000 words out of 281103 words
Chapter 19 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
sannan ta shigo ɗakin da suka kwana da Mardiya ta tasheta.
Tashi tayi zaune tana murtsikar ido.
“Ina kwana har kin tashi?”
“Ba dole na tashi ba, har na haɗa muku abun karyawa,dan Allah shiga ki wanke bakin ki ki karya, idan kin san gidan wat dillaliya ki kai ni ko kuma ki kira min ita ta zo ta siye gadona”
Mardiya ta daki ƙirji
“Gadon ki kuma? Haba Namra karki siyar da gadon ki mana”
“Idan ban siyar da shi ba, kai na kike son na siyar ? Ko sata zan yi? Ba ki ga hali da mijina yake ciki ba”
“Amman ba ku da ƴan'uwan ne da za su iya taimaka muku?”
“Ƴan'uwana sun juya min baya, shi kuma ƴan'uwansa ba wani hali ne dasu sosai ba, nasan ko da za a samu ba zai wuce ayi karo karo ba, kuma kin ji abunda likita yace kar ya wuce kwana biyu ba'ayi masa aikin ba”
Sosai Mardiya ta ɓata rai tana nuna mata rashin jindaɗinta akan siyar da Gadon da Namra zata yi.
“Gaskiya ni ban jidaɗin haka ba”
“Ba komai Allah zai bani wani, tashi ki shirya ai kin san wata mai siye ko?”
“Eh akwai wata a nan unguwar mai siye sosai”
“Dan Allah ki min magana da ita yanzu kar rana yayi, kuma ina son kije ki kai musu abincin su”
“To bari na tashi”
Ƙoƙarin tashi take tana wani kare-karen zane, kar sarƙar dake jikinta ta faɗo. Ita kam Namra bata ma kula ba sai ta tashi ta bar mata ɗakin.
A haɓar zanenta ta ƙulle sarƙar sannan ta shiga banɗakin, ta wanke fuskarta, koda ta fito har Namra ta kawo mata taliya a plate da ruwan sanyi ta aje mata.
Haka ta riƙa aika abincin kamar wata tsohuwar mayunwaciya, nan da nan ta ƙare ada plate ɗin, ta sha ruwa sannan ta fito falon tana faɗin
“Bari naje na kira miki ita”
“Toh dan Allah ki yi sauri”
Namra ta faɗa tana shan tea ɗin dake hannunta, idonta duk sun wani zurun-zurun kamar ita ce marar lafiyar.
Mardiya bata ɗauki dogon lokaci ba ta dawo tare da matar, sai da suka gaisada Namra sannan Namra ta ta shiga da ita cikin ɗakin ta nuna mata gadon. Tana ganinsa tasan sabo ne, amman duk da haka sai da ta gama duba ko ins nasa sannan ta kalli Namra tace
“To nawa aka masa kuɗi?”
“Babu wanda ya taya, ki siya kawai”
“Toh ai ba siyen ba, kin san irin wannan manyan kayan ba ko wace mai keya ke siyen su ba, sai su daɗe baka sai da ba amman ke nawa kika ga zaki iya sai da su?”
“Ni dai miliyan ɗaya har da wani abu Abbah ya siya min su, ke kuma sai ki kwatanta”
“Kai kai aiko an daki hancinsa, dan wannan kayan yanzu wasu ma sun daina yayinsu, ai sun faɗi sosai. Sabin ma ba zasu wuce ɗari bakwai ba”
“Tau ki bayar da haka ɗin”
Tayi ma Namra wani kallo tana taunar goron dake bakinta.
“Ni ko ai ba zan ci riba ba, magana ta gaskiya zamu yi, dan ni bana son nakkasa mutum, ƙara ayi ciniki babu cuta babu cutarwa, indai zaki iya bari ɗari, shima dai ƙoƙartawa zan yi dan ba duk dillaliya ke zuba kuɗi da yawa ta siye kayan data san ko ta sai da ko karta sai da ba”
“Haba baiwar Allah, Wallahi lalura ce tasa zai sai da abu na, ba kiga sabo ba ne”
“Na gani amman ai kin san duk abunda aka riga aka fitar indai kuɗi kake so sai ka faɗi, amman yanzu zan yi miki magana ɗaya idan yayi miki na siye ɗari uku da ashiri”
Kallon gadon Namra tayi ta sake kallonsa ta kalleshi sannan ta kalli Matar tace
“Kawo kuɗin”
“Amman fa sai naga mai gidan ki, dan wani lokacin ana siyen kaya sai kuma miji ya zo yace shi ba za'a siyar da kayan matarsa ba”
“Mijina ba shi da lafiya kuɗin magani nake nema shiyasa zan siyar da wannan gadon, yanzu haka yana asibiti aiki za a masa”
“Allah sarki, Allah ya sauwaƙe, amman duk da haka zan zo da ɗana sai yayi mana takarda guda biyu saboda gudun matsala”
“Ba matsala, kuɗin fa?”
“Kuɗi gaskiya sai zuwa gobe na kawo miki sai na ɗauki gadon, dan yanzu ƙuɗin da suke hannuna ba su wuce ɗari biyu ba”
“Bani haka gobe sai ki kawo min sauran ki ɗauki gadon”
“To ba matsala amman sai kin biyo ni gida na baki ga ban ƴan gidan mu saboda shedu”
Sai da Namra ta bawa Mardiya abincin da za a kai ma Mama sannan ta saka hijabinta ta kulle gidan suka fita tare.
Gida matar suka shiga, ta ƙirgo kuɗin gaban mutanen da suke gidan ta bawa Namra bayan ta faɗa musu yadda suka yi, da Namra tun a gida. Sannan tasa ɗanta ya ɗauko takarda yayi shedu guda biyu ya bata ɗaya ya bawa Namra ɗaya.
Tare da Mardiya Namra ta fito gidan, suka tare napep ta kai su Asibiti. Mardiya ce ta wuce kai musu abincin Namra ta nufi gurin biyan kuɗin magani. Dubu ɗari da talati ta biya na aikin, sannan ta biya na magani suka zo suka ɗibi jininsa suka auna sannan suka tura ta lab gurin siyen jini, tayi sa'ah an samu irin wanda ake so, gora uku ta siyo sannan ta dawo ta kawo musu.
Cikin dubu ɗari biyu, kuɗin daya rage be wuce dubu bakwai da ƴan canji ba. A kasale ta shiga ɗakin da yake, sai ta tararda shi cike ƴan'uwan Asim na Sokoto da Bakori sun zo dubiya.
Cikin far'ah da ƙarfin hali ta gaisa da su, sannan tayi ma Mama ina kwana. Sai kusan azahar wasu suka koma aka bar mutum biyu su wai ba yau zasu ba.
Ganin azahar tayi yasa Namra ta ba Mardiya makulli taje ta girka mata abincin rana, ita kuma ta dawo kusa da Asim ta zauna, ta zuba masa ido kamar ba gobe. Daker ya ɗaga ido ya kalleta ya sake rufewa ji yake kamar ba duniya yake ba.
Ita kuma wani irin tausayinsa take ji take ciwon kamar a jikinta yake.
Uku dai-dai nurses suka shigo suka fita da shi zuwa ɗakin da za'ayi masa aikin.
ABDOOL POV.
Hannu ya kai ya kunna air conditioner dake ɗakin sannan, ya rage tufafin jikinsa, ya buɗe freezer ya ɗauko power horse ya sha.
Sai ya dawo saman sofa ya zauna, yana kallon window. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ya miƙa gurin windowdake garden yana sauraren birds singing.
Yana jindaɗin saurarensu sosai da sosai, hakan yasa lokuta da dama idan ba shi da wani aikin ya kan tare a garden dan kawai sauraren sautin na su.
Hannayensa ya zuba a aljihu ya tashi yana wani irin taku na sarauta da ƙasaita ya nufi window, Peacock ɗin dake ƙarƙashin apple tree yana sha'aninsa ya tsurawa ido. Kamar wanda ya tuno wani abu sai kawai yayi wani ƙayataccen murmushi ya wanda ya sanya dimples ɗinsa fitowa, lumshe ido yayi yana shafa fuskarsa.
“Because of her, half the time I don't even know that I'm smiling, she insult me but i still need to see, who's she?”
Abund ya furta kenan a fili sai kuma ya bawa kansa amsa.
“The Unique one”
Murmushi yayi mai sauti, ya rumgume hannayensa yana ƙara saita tunaninsa.
Taya akayi ya zure haka? Mema ya kai shi kula wata har yayi ƙoƙarin mata magana, shi da bay da lokacin wasu mata. Hannu yasa a aljihun wandonsa na Army, ya ɗauko wayarsa ya kira wata number, bugu ɗaya ya ɗauka.
“Ali ya ake ciki?”
“Naje har gurin shugaban masu Napep ɗin na bincika, sai aka kawo min mutumen yace shi be santa ba kuma a bakin babbar asibitin funtua ya sauke ta, wai yana ganin jinya take”
“So what's the solution?”
“Sir want i think is better mu shiga cikin asibitin mu bincika”
“No”
Ya girgiza kai alamar shawarar bata masa ba, ya ɗan ɗauki dogon lokaci, be ce masa komai ba, ba dan kuma baya da abun cewar ba, sai dan isa da izza.
“Ka cire kuɗin da zai isa, a shirya takeaway da five thousand sai muje mu raba ma Patients ko Allah zai sa mu samu ganinta”
“Okay but Sir Akwai meeting da zaka je gobe Abuja, kuma the next day akwai meeting ɗin Mr President ya shirya za ku yi akan matsalar tsaron nan na Maiduguri da Zamfara”
Lumshe ido yayi ya buɗe.
“I know that, nasan end of this month ina da free days, a cikin wannan rana ku zamu je, sai ka saka mana date”
“Alright Sir zan duba the most expensive free day na ka”
“Good of you”
Sai kawai ya kashe wayar, ya mayar aljihu. Da ƙarfi aka banko ƙofar ɗakinsa, sai kawai yayi murmushi.
“Hey Dude”
Wanda ya kira da sunan ta fito daga cikin labule tana dariya, yarinya matashi wanda ba zata wuce fourteen to sixteen years.
“Yarima Ummi na kiran ka”
Ta faɗa tana taɓa hannayenta. Hannayen nata ya riƙa yana murmushi.
“Dude Yarima has finally found his princess”
Ta zaro ido
“Wow, when? How? Who?”
“At funtua i don't know who's she”
“Is she really cute?”
Wa wara manyan idanuwansa.
“Yeah she's so pretty, she had that diamond eyes, her lips is so cute, i like her face, she's tall, she wearing Hijab and she's black, Dude you know how i love black girls huh?”
“Yes Dude so how are we going to meet her?”
“I don't know, she slap me Dude”
Ya wani ɓata fuska kamar ƙaramin yaro. Itama ta ɓata fuska kamar tayi kuka.
“So heart touching”
“Don't worry i will slap her heart when i have a chance, but i still feel her soft fingers on my cheek”
“ I will be the first one to tell Ummi”
Ta faɗa tana dariya. Sai yayi saurin rufe mata baki
“No Dude wannan sirrin mu ne, no one will ever know”
“Yes I won't tell”
Ta faɗa tana ɗaga hannu sama alamar tayi alƙawari.
“So tell me why Ummi take son gani na?”
“She want you to go and meet Cute Eysha, daughter of Hajiya Saratu”
“What? Please tell her I'm sick”
Har ta buɗe baki sai kuma ta rufe ta saki hannunsa ta fita. Batayi minti biyar da fitar ba yaji alamun shigowar Ummi.
Da sauri ya haye saman gado yaja bedsheet ya lulluɓe ya makore kamar da gaske ba shida lafiya.
“Ai dole ka riƙa ciwo, kullum baka da hutu kai ne agogo sarkin aiki, idan an maka maganar aure kamar ance ka faɗi ka mutu, duk yaran garin nan kace basu maka ba, ko so kake ni da Mai martana mu mutu ba muga auren ka ba?”
Ɗan ɗagowa yayi kaɗan yana pretending like he's really sick.
“Ummi yanzu kuma miye nawa? ”
“Ƴar wajen Hajiya Saratu nace kaje ka gani, tace min jiya ta dawo daga Kaduna”
“Ummi ko na yi aure babu wanda zata zauna da ni, saboda ina da lalura ta rashin lafiya yanzu haka Dr Alex ya ɗora ni akan magani”
Ya faɗa yana ƙoƙarin mayarda ƙaryarsa ta zama gaskiya. Ita kuma sai ta amsa da ƙarfi.
“What?”
Sai kuma ta kalli ƙanwarsa.
“Afrah go and watch your favorite channel”
Sai da suka yi ido biyu da yayan nata sannan ta fice.
ANTY AMARYA POV.
Ji take bata kyautawa Namra ba, idan har bata mata ba babu wanda zai mata sai Allah, soyayya irin ta ƴa da uwa ta hana Anty Amarya ƙyale Namra har sai da tasa Maryam ta tura mata dubu ɗari da Hansi.
A gajiye Maryam ta shigo falon ta zauna kusa da Anty Amarya tana miƙa mata atm ɗin ta.
“Kai yau nasha wahala Wallahi, sai kusan 4 muka tashi lacca, naje back kuma na tararda layi”
“Kin tura mata?”
“Eh but her phone is still switch off ”
“Maybe ta siyar ita ma”
“Kai why not su dawo nan garin? Zama acan zai mata wuya”
“Leave here ita ta so ai, sai taje tayi abunda take ganin yafi mata”
“Amman Anty Namra zata sha wahala tun da tana gudun zuciyar mutane”
Ajiyar zuciya Anty Amarya ta sauke, tana wani nazarin na daban.
_________________________________________
Five words for this chapter... 😻
Waiting for your comments... 😘
Best regards to you all... 💖
CANDY🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*
Website
www.khadeejacandy.com.ng
This page is for Birthday Girl Salwees. Happy Birthday Dear 💖
*PAGE - 26*
NOT EDITED ⚠️
Hankalin Namra be kwanta ba har sai da aka fito da shi daga ɗakin da aka masa aikin.
Sai suka dawo da shi, ɗakin da yake, anyi aiki cikin nasara da taimakon Allah.
Sai da yamma Mama ta je gidan Namra ita da Hajara dan yin wanka ta kuma ɗan huta, Mardiya Namra ta bawa keys ɗin gidan dan ta taba musu abinci kuma ta taya su zama. Ita kuma ta kwana da Asim a asibitin.
Babu irin inda Mama bata shiga ba a gidan, sai baya kyau gidan take da girmansa. Mardiyace ta faɗa mata Namra ta siyar da gadon har an bata wani abu daga ciki.
Babu irin tsinuwar da Mama bata yi ma iyayen Namra ba, a zatonta sune suka turo mata da kuɗin aiki dana magani, a nan ne Mardiya ta ƙara fayyace mata matar data taimaka ta kawo Asim asibiti ba yar'uwarsu bace, nan ma Mama ta cika da mamaki, dan a zatonta ita yar'uwarsu.
“Kai tirr da wasu mutune Wallahi, wato su babu ruwansu da lamarin mijinta tun da ba ita bace ko? Hmmm ni ban taɓa ganin iyaye irin nata ba, daman ba son auren su ke”
Taja wani godon tsaki sannan ta fito daga ɗakin, ta shiga kitchen ta fito ta shiga ɗayan ɗakin. Mardiya dai na biye da ita har ta gama duba gidan. Shikafa da miya Mardiya ta dafa tare da Hajara.
Washe gari ma wani abincin Mardiya ta sake dafa musu, bayan sun ci ta zuba wanda zasu tafi dashi a asibiti, sannan suka wanka suna cikin shiri Dillaliyar ta zo Mardiya tace mata bata nan, sannan ta rufe gidan suka nufi asibitin.
Namra suka tarar zaune a kujerar dake ɗakin tana bawa Asim tea. Ba laifi alamun sauƙi ya bayyana a yanayinsa, wanda a ada ma idan ya ɗaga ido sai yayi saurin rufewa yanzu kuma gashi har yana shan tea.
Farinciki gurin Mama ba'a magana, sai ta zauna saman gadon kusa da shi, tana murmushi
“Mashallah Ibrahim, Allah ya ƙara maka lafiya”
Ɗan murmushi yayi kaɗan irin yana jin zafin ciwon nan yana ƙarfin hali. Mama ta kalli Namra
“Yaushe ya farka?”
“Tun da asuba, har likita ya duba shi ya bada wata takardar ta gani yace allura ce za a masa guda bakwai, kullum ɗaya saboda jinin daya bugu a kansa”
“Allah yasa dai babu tsada”
“ Pharmacy asibiti sun ce duk ɗaya, dubu tara ne, ga kuma maganin da suka rubuta shima sai yaci dubu biyar”
Mama ta rafka uban tagumi.
“Tau ai fa kaji matsalar babbar asibiti, yanzu ina za a samu wannan kuɗin kuma? O Allah”
Namra ta saci kallon Mardiya da idonta ke kansu, tace
“Mardiya kuje waje ke da Hajara”
Tashi tayi ta fice ita da Hajarar. Sannan Namra ta kalli Mama tace
“Akwai kuɗin da zan siya da su, amman da abinci naso mu siya dan abincin mu ya ƙare”
Kai Mama ta girgiza
“Wai Namra iyayenki haka zasu zura miki ido, babu wani taimako? Naga dai suna da shi, amman ko ɗan abincin nan ai sa taimaka muku da shi, amman ace kayi ta sai de sai de anya haka yayi?”
Wani kallo Namra tayi mata.
“Iyayena sun yi iya ƙoƙarinsu duk kan abuɓda zasu min a yanzu kyautatawa ce, amman ba dole ba, balle kuma mijina ”
“Haka ne, daman can ai ba son auren su suke ba, sun fi son ku yi ta wahala kamar ba ƴarsu ba”
“Mama ya kamata ki kina tauna magana kamin furta ta, iyayena, iyayena kuma sun min komai tun da har suka bar ni na auri Asim”
“Amman idan ga mutunci ai da ke da shi kun zama ɗaya, ki duba kiga ko dubiya har yanzu babu wanda ya sake leƙowa daga danginku, Kuma wallahi inda wani guri ne dole ne su ɗauki nauyi naganinsa tun da da motar gidan yayi haɗari, amman sun ɗauki ƙiyayyar duniya sun ɗora masa akan auren ki kamar wanda ya kashe musu wani abu”
Zuciyar Namra ta kawo sosai, a take idonta ya cika da ƙwalla.
“Asim yayi haɗari da motar gidan mu saboda an rubuto zai yi haɗarin, wai Mama mi na tare miki ne? Miyasa kike abu kamar wanda bata yarda da ƙaddara ba, miyasa zaki ɗauki laifin haɗarin motar da Asim yayi ki ɗora min?
Kin manta da ni matarsa ce wace mace ce zata so mijinta ya kasance a halin da Asim yake? Duk abunda na masa baki gani ba? Mahaifiyarsa ce ke amman sisi ban tambaye ki na siyer da kayan ɗakina na biya masa kuɗin magani, amman duk wannan be isa a goge laifina ba? Kin kira aure na da ƙaddara kina tunanin hakan yayi min daɗi? Me kike son na masa ne? Rai na kike son na cire na bashi ko kuma ciwon kike son na maida jikina?
Haba Mama ku bar ni na ɗaya mana, da matsalar iyayena zan ji ko da ta mijina, ko kuma wanda kike ƙoƙarin sani, ke uwace wata maganar be kamata tana fitowa daga bakin ki”
Mama ta cika da mamakin jin furucin da Namra tayi mata, wani dogon numfashi taja ta sauke tana taɓe baki.
“Kin goge ladarki Namra, daman kin masa duk abunda kika masa ne dan ki faɗa kin masa, ai kaji tsiyar taraiya da mai arziki, so kike ace ɗana ya cinye miki komai ko? A ƙaƙaba masa, kamar yadda aka masa na satar ki ko? Ni da zuciya ɗaya na bar ɗana ya aure ki ba da wata manufar ba”
Ta ƙarasa maganar da kuka har da hawaye. Uffan Namra bata ƙara cewa ba, sai kawai ta ɗauki jakarta ta fice.
Sai da ta biya gurin da su Mardiya suke ta karɓi keys sai Mardiya ta biyo ta suka yi gida tare. Tun a Napep Namra ta soma yi ma Mardiya faɗa.
“Dan me zaki faɗawa Mama na siyar da gado na ? Ina ruwanki da rayuwata tana mijina? Jaka zaki tallata ni a unguwa? Ko akai na farau? Abunda ya shafi mijina da mahaifiyata nawa ne babu ruwanki a ciki,