Showing 147001 words to 150000 words out of 281103 words
Chapter 50 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
yayi na siyar da gidan nan, idan ya zo sai na riƙa juyawa ina siyen zinari ina sai dawa, ga wannan albashi walh nan da nan za ka ga na yi kuɗi, sai dai kuma ban sani ba ko bata son na haɗa da wani aikin, wata ƙila ma zata iya min kyautar mota fa, ji yadda ta yarda da ni nan take har da ba ni atm ɗinta ta faɗa min password, daman mai haƙuri mawadaci’
Shine abinda yake ta saƙawa a zuciyarsa yana tukin motar da yake hango kansa a matsayin wani ƙaramin alhaji.
*RASHIDA POV*
Ajiyar xuciya ta sauke har da hawayen ƙirƙira dan kawai Teema ta tausaya mata, haƙiƙa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne Teema ta tausaya mata sosai har tana jin kamar tayi mata maganin matsalarta yanzu.
“Ki kwantar da hankalin ki Rashida, zan taimake ki akwai wani malami yana nan ɗan ƙauye sokoto ne, wlh malamin har ƙasa ƙasa ake ɗaukarsa yayi aiki, aikinsa kamar yankan wuƙa yake, a take komai kike so zai miki zan kai ki gurinsa idan kin shirya”
“To ai ni kullum a shirye na ke, ni ko yanzu kika ce muje zamu je wlh”
“A'a ban da yau dan ban shirya ba amman dai gobe ki zo da wuri sai mu tafi”
“To inshallah zan zo”
“Amman aikin ki fa nasan ba hutu kuke samu ba”
“Karki damu da aikina wannan ita ce muhimmiya”
Teema tayi dariyar mugunta. Tashi Rashida tayi, Teema ta raka ta har gurin motar ta ta shiga motar tana ɗagawa Teema Hannu.
Daga gidan Teema ta wuce Asibiti dan karɓar maganinta, a mota ta tsaya ta saka niƙabi da hijab sannan ta fita.
A wani gurin ta tsaya kusa da inda ake ba da maganin, tana kalle kalle mutane, daman haka take duk ta zo wai gudun kar taga wanda ta sani. Duk da wannan shine zuwanta na biyu.
Bayan ta gama dube dubaneta ta shiga ciki ta ga likita, ya ƙara mata shawarwari, sannan ta fito ta nufi gurin karɓar maganin kai tsaye. Security dake gadin ƙofar asibitin ce ta saka ta cire nikaɓ ɗinta dan haka dokar asibitin ta gada, Rashida bata damu ba ta cire niƙab ɗin daman ko wacan zuwan da tayi sai da tasa ta cire shi.
Da fargaba ta kunna kai a gurin tana ɗan kallon mutane ƙasa-ƙasa, gabanta sai faɗuwa yake kamar zai faɗo. Kamar daga sama taji an dafata ana ƙoƙarin juyowa da ita, juyowar da ta yi sai kawai suka yi ido huɗu da Safiya cikin Uniform ɗinta.
Wani irin kallo Safiya take mata kamar wacce ta rude cox she's can't believe Rashida ce ta gani a nan ƴar'uwarta jininta.
Ita kanta Rashida mamakin ganinta take, dan iya saninta wannan ba asibitun su bace, ya aka yi ta zo nan me ya kawo ta.? Yawu Safiya ta haɗe ta wuce da sauri ta fita daga gurin gudun kar wani daga cikin manyan su ya ganta, daman fitowarta kenan daga wani ɗakin ta hango mai kama da Rashida, ashe ba kama bace, ita ɗin ce amman mai zai kawo Rashida HIV/TB unit.? Shine abinda ya tsaya mata a rai.
Miƙewa Rashida tayi cikin dakewar zuciya ta cigaba da tafiya tana son ɓatarwa da Safiya da lissafi, sai dai kuma yanzu bata san liyin da zata bi, tb ko hiv?
*HILAL POV*
Asibitin ya wuni, da rana ma Hajiya ce ta kawo masa abinci. Duk wanda ya zo sai ya tauyasawa Rafiq ganin yadda ya koma musaki sai dalalar da yawu yake. Tuni Hilal ya ɗosa shi akan magani, yasa aka sake masa wasu hotunan dan ganr ainahin matsalarsa.
Ƴan'uwansa da dama sun yi ta xuwa ganin ɗan nasa, ƴan uwan Rashida ma sun zo, sai dai ba sosai ba, Dady Kalsoom ma ya zo shi da Momy, duk da suna jin nauyi ganin kamar ƴarsu ce ta aikata abun.
Sai da yayi ma Rafiq Alurra bachi sannan ya rufe ɗakin. Ya koma office ya cigaba da aikinsa, bayan ya gama, ya sake leƙa ɗakin yaga har yanzu bachi yake. Sai kawai ya nufi gurin motarsa dan yana buƙatar taje gida yayi wanka.
Yana hanyarsa ta tafiya Hajiya ta kira shi wai zata shigo da dare akwai magana mai muhimmanci da take son suyi, shi dai da to kawai amsa mata ba dan ransa yana cikin daɗi ba, ya faka a rabar gidan ya fito jiki ba ƙwari ya shiga ciki.
Tun a falo gabansa ya soma faɗuwa jin sautin kukan Kalsoom, da sauri ya karasa ɗakinta, sai dai kamin ya shiga ya ji ba acan kukan yake fitowa ba, a ɗakin su Ezzah ne. Ƙarasa yayi ɗakin ya tsaya daga jikin ƙofa yana kallonta. Juyowa tayi ta kalleshi da idonta da suka yi ja saboda kuka.
“Haƙiƙa ina son ka Hilal, dukan abunda ya dangance ka ina sonsa ko da kuwa abun nan mai cutar da ni ne, miyasa zuciyarka ta yarda na aikata bayan ban aikata ba? Ka raba ni da ƴaƴanka Hilal bayan yanzu sun zamo jinin jikina, ban aikata abinda kake zargina da shi ba Hilal Wallahi ban aikata ba”
Ya rumgume hannayensa yana mai jingina da jikin ƙofar.
“To waya aikata?”
“Ban sani ba, amman na rantse maka da Allah ban aikata ba, idan har na aikata Allah ya isar masa ya saka masa, kuma ya bayyana gaskiya”
Jikinsa yayi sanyi sosai, yasan ba zata yi ma kanta wannan mugun furucin ba. Kasa cewa kamai yayi sai kawai ya juya ya nufi ɗakinsa. Saman gado ya zauna, ya dafe kansa dake masa wani zafi.
Jin yayi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ɗagowa da zai ya ga hannunta rike da ƙur'ane da dukan alamu rantse masa zata yi. Da sauri ya tashi ya ƙarasa inda take.
“No need Please ki aje ƙur'anen nan Kalsoom”
“Rantse maka zan yi Hilal ko zaka yarda da ni”
“Na yarda da ke aje please”
Bata son musa masa, sai kawai ta aje ƙur'ane saman durowarsa tana kuka. Rumgume ta yayi tsantsan a ƙirjinsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.
*NAMRA POV.*
Tun lokacin da Asim ya bata 500 yace tayi cefane bata dake saka shi a idonta ba, kullum idan ta kira zai ce mata aiki ne ya sashi gaba, yau kusan kwana uku kenan.
Ita kam abun duk yabi ya dame ta, musmman yanzu da take ɗan samun sakewa da shi sai kuma aiki ya ɗauke masa hankali.
Sai dai kwana biyu bata jindaɗin jikinta, yawun bakinta ya kan canja ɗanɗano, ga kasala da take fama da shi, sai yawan amai akai akai, ga ciwon kai.
Sai dai bata kawo ma kanta komai ba, sai hawan jini, duk da bata san alamominsa ba, amman tana jin kamar wannan ba zai rasa nasaba da hawan jinin ba, a iya saninta ta saka roba balle tace ko ciki ne, dan tana jin irin alamomin da ake faɗi na masu ciki. Tun jiya ta ci alwashin zuwa asibiti dan bincika matsalarta gudun kar ciwo yayi mata zurfi a rasa gane kansa, amman Allah be yi ba sai yau. Dan haka da wuri ta shirya ta nemi ƴar fulani data raka ta suje tare, dan bata son xuwa ita kaɗai musamman inda bata saba zuwa ba.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *59*
*RASHIDA POV.*
Ganin Safiya ta fita yasa ta juyo bata tsayawa karɓar maganinba, ta fito gabanta dai faɗuwa yake, saƙe-saƙe take na abinda zata cewa Safiya yau kan ta san kashinta ya bushe, bata da wata mafita sai ta Allah.
Kalle-kalle ta fara lokacin data fito harabar gurin ko zata Safiya amman bata ganta ba, da sauri ta nufi harabar asibitin gurin da tadan tayi parking motarta.
Zagawa tayi ta ɗayan ɓangaren ta buɗe motar sai taga Safiya tsaye tana kallonta, idonta cike da hawaye. Yanzu kan babu kayan ɗazu a jikinta, daman suna saka su ne idan zasu shiga ciki.
Dakewa ta yi tana ƙoƙarin ɓoye tsoro da fargabar dake ranta ta kalli Safiya tana murmushin ƙarfin hali
“Ke baki wuce ba, tun ɗazu nake neman ki fa”
“Ke na zo nema daga asibitin ku nake aka ce kun zo nan ku yi wani aiki”
“Ni...?”
Ta nuna kanta cike da mamakin yadda ƴar'uwarta take ƙoƙarin canja abunda yake a zahiri.
“Amman bayan kin gan ni kin cigaba da tafiya ciki...!”
Ajiyar zuciya Rashida ta sauke a hankali yadda Safiya ba zata ji ba, sannan ta kalleta da fargaba ta ce
“Safiya kar dai kina zargina da wani abu ne? Don't you trust your sister?”
“I trust you but... Me kike nema gare ni?”
“Akwai inda na so ki raka ni, but seems you don't trust me ba sai na je da ke ba”
Bata tsaya jiran abunda Safiya zata sake cewa ba, ta buɗe motar tana mai nuna tsananin ɓacin ranta ita ala dole abunda Safiya ta gani ba shi bane, gaskiya take son canjawa ƙiri-ƙiri.
Da kallo Safiya ta bita har ta tuƙa motarta ya bar harabar asibitin, kallo na mamaki abinda Yayarta take son canjawa, da kuma tunanin abunda ya kawo ta asibiti a hiv unit. Tana ɗa buƙatar bincike dan gano gaskiyar lamarin, dole ne ta bincike ƴar'uwarta, wata ƙila ma tana da masaniya akan Asmee tana da shi.
‘What if ita ma tana da shi fa?’
A zuci tayi furucin tana tafiya, da sauri ta girgiza kai.
“No no A'uzubillahi min shaidanin rajin”
Ƙoƙarin kawar da abin take, dan tana ganin kamar hakan ba zai faru ba, idan kuma har ya faru to sai idan Mijinta ne ya laƙa mata shi, dan bata san yayarta da ɗabi'ar banza ba, sai dai kuma abinda ya tsaya mata a rai tunanin abinda zata faɗi a gida, idan ta faɗi ta tonawa ƴar'uwarta asiri idan kuma ta rufa na su asirin ya tonu.
Tun a cikin mota Rashida ta fara kuka, ganin take kamar asirinta ya tonu, tun da Safiya ta ganta, har kuma ta soma zarginta, idan kuma har ta faɗa a gidan to tasan kowa zai gujeta ne, sunanta zai ɓace haka zai dagula lamarin komawarta gidan Hilal, sannan kowa zai dan dalilin fitar ta gidan, za'asan alaƙar dake tsakaninta da mijin Asmee taren su da Asmee zai lalace, duniya zata san ko wacece ita...!
“Anya zan iya bari wannan abun ya faru? Ya zan yi na hana Safiya faɗa? I can't let her do this, zata saka rayuwata a matsala data tsaka ni a matsala ƙara komai zai faru ya faru”
A fili ta yi furucin, bayan ta faka motarta a harabar gidan, ta ɗan ɗauki lokaci kamin ta buɗe ta fito tana farucin
“Idan Asirina ya tonu ai zaman gidan nan ma sai ya gagare ni, duniya ba zata kawo ƙarshe yanzu ba, i can't let it happen”
Jakarta ta ɗauka ta rufe motar already ta cire hijabin tun a hanya. Sannan ta nufi ciki tana ra saƙe-saƙe a ranta, da tunanin mafita.
Bata bari kowa yaga dawowar ta a gidan ba, saboda bata son a takura da magana ko wani abun na daban, nata ya isheta, har aka yi salla magariba bata leƙa falo ba, sai ana daf da salla i'sha, shima kuma dan taji muryar Safiya ne, sai ta fita ta zauna falo tana ganin kamar idan tana gurin Safiya ba zata iya faɗar komai ba.
Kallonta kawai Safiya take tana saƙe-saƙen faɗar ko a'a, ita kuma taɓa mata kallo ɗaya ta ɗauke kanta tayi kamar bata san da ita ba a zaman falon. Da zaman ya isheta ne yasa ta tashi ta nufi kitchen ta ɗubi abinci ta zo falo ta zauna tana ci ba dan taɓa son cin ba sai dai ta nunawa Safiya kamar babu komai a ranta.
Ita dai Safiya bata ce mata komai ba, bata kuma nuna mata ba sai kallon mbc 2 take, sai dai a ranta ta ƙudiri aniyar sai ta binciki ɗakin Rashida gobe da safe tun da tana rigan kowa fita a gidan saboda aikinta.
Sai da ta gama ci tsab sannan ta tashi ta maida plate ɗin ta sha ruwa, ta wuce ɗakinta, babu komai a zuciyarta sai tashin hankali. Saman gado ta zauna tana mamakin yadda duniyarta ta canja mata lokaci ɗaya, lallai duniya idan ta so ka, kai wawa ne, idan kuma ta ƙi ka, ka shiga uku, kai ne ya kamata ka ƙi ta a lokacin da take so ka, take zaurencen ka, ka so ta a lokacin da take ƙin ka, tana nuna maka kai ba kowa bane, ta haka zaka gama rayuwarka ba tare da ta yaudare ka ba.
Hawaye take, irin hawayen da baƙin cikinsu kan hana kuka fita, makomarta kawai take tunani ta san ko yau ba, wata rana zata samu kanta a irin wannan rayuwar da take gudun shiga, dan tasan asirita ba zai cigaba da rufuwa ba har abada.
“Na yi dama wallahi, duk wannan Alh Bashir ɗin ne yaja min, laifin Asmee ne ita taje ta ɗibo a wani gurin ta saka mana, wallahi duk na shiga matsala ita sai ta shiga, sai na sata a matsala”
Kaɗan-kaɗan take rera kukanta dan bata bukatar kowa ya ji, yau ma ya zame mata kamar ranar da Hilal ya sake ta, har garin Allah ya waye babu abunda take tunanin sai rayuwar da ta yi a baya, yadda take farkawa a gidan, ta wuni da Hilal sahibin ruhinta, yau kuma duka babu wannan, wacan rayuwar ta zamar mata kamar mafarki.
Wani abu taji ya tsaya mata a ƙahon zuciya ya yana numfashinta tafiya dai-dai har tayi salla asuba. Haƙiƙa wanda Halal be wadata shi ba, to Haram ba zai wadatar da shi ba, ko da kuwa ya wadatar da to ya aure shi ne na ɗan wani lokaci ya sake shi, a lokacin ne zai gane illar abinda ya aikata. Zina ya zama ruwan dare yanzu babu matan aure babu budare, an maida abun ado, wasu har gobe suna cin ribar abun saboda Allah yayi musu istijira'i na ɗan wani lokaci, kamin su haɗu da shi, wasu kuma tun a duniya Allah zai bayyana su. Da yawa sun ɗauko ƴaƴan da bana miji ba an kawo ciki gida walau ta gurin bin bokaye ko kuma ta gurin aiki ko abokan banza, shiyasa zaka ga yara suna kashe iyayensu ko kuna musguna musu ko suna wani abu da bae dace ba, wanda abu ne mai wahala ɗan halak ya aikata haka. A social media ma yanzu zina ake macen aure ta kawo wanda ba muharraminta ba gidan mijin ta,, gidanta na sunna, har ta jashi su aikata alfasha. Wasu akan yi musu lamani kaɗan, wasu kuma da yawa, sai dai babban tashin hankali gurin haɗuwa da Ubangijin ka...!
Sai a yanzu ta soma nadamar abunda ta aikata, sai dai nadamar bata yi tasirin yanke kuɗirin dake zuciyarta ba, na komawa gidan Hilal, ta yarda asirinta ya tonu amman a gidan Hilal, ta yarda ta kauce dukan hanyar da zata kauce inda har zata koma a gidan Hilal.
Bayan ta yi wanka ta shirya cikin atamfa pink color ta ɗauki mayafinta ta yafa sannan ta ɗauki handbag ɗinta, bata tsaya karyawa ba ta fice, daman ko ta tsaya ba zata iya cin komai ba. Kai tsaye gidansu Teema ta nufa ita kanta tayi mamakin sammakon data dako mata tun da safe, sai ta shirya ta karya sannan Teema ta faɗawa Iyayenta wai zata raka Rashida gidan Rasuwa, sannan suka fita.
Rashida take driving Teema na nuna mata hanya har suka isa garin ɗan-ƙane, cikin dajin suka kai kutsawa har suka isa gidan mutumen. Wannan kan ba'a kira sa da malam ba sai dai boka, dan babu komai a jikinsa sai walki da fatu, irin arnanan ne na kaduna masara imani waɗanda zasu iya aikata komai ba tare da fargaba ba.
Sun tarar mutane da dama, cikin har da ƴan siyasar da Rashida ta sansu, da kuma wasu matan manya, inda Allah ya taimake ta ta saka niƙab ba kowa ne zai gane ta ba.
Sai da mutane da ke gabasu suka gama shiga, sannan suka shiga a lokacin sun cin ma layi.
Irin kayan tsafe-tsafen da ta gani yasa gabanta faɗuwa, har da wani ƙaton madubi baƙi an masa rubutun larabci da jan jini. Cikin fargaba da tsoro ta zauna gaban bokan tana kallon walkin dake jikinsa.
Zata fara bayani ya ɗaga nata hannu.
“Bana buƙatar ki faɗa min komai, ni zan baki labarin duniyarki, sai dai idan baki son kowa ya ji zamu iya sallamar ƙawarki”
Ta jidaɗin maganarsa dan har ga Allah bata son Teema ta ji sirrinta, dan daga ganin wannan mutumen ba zai ɓoye komai ba.
Ba tare da tace ba, Teema ta tashi ta bar mata ɗakin.
Shi wannan bokan da jini yake duba a maimaikon ƙasa da wasu suke yi da ita, sai da yayi rubuce-rubucensa sannan ya dubeta ya ce
“Auren ki ya mutu, saboda mijin ya gano kina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, kin yi asiri wa kishiryar ki da take gidan mijinki ya faɗawa ɗan ki! Wata ƴar'uwarki na daf da shirya miki wani abu, akwai yiyuwar ki koma gidan mijinki amman idan har kin yarda ki daina salla azahar na tsawon sati ɗaya, tabbas buƙatar zata biya, idan har kika zake jefar abokiyar zaman ki to buƙatar ki zata biya zaki same ta, amman akwai yiyuwar jifar ta dawo kan ki, haƙiƙa baƙin duhu yana bibiyarki, wannan baƙin duhun baƙar rana ce...!”
Da sauri Rashida ta miƙe tsaye tayi baya-baya tana kallonsa tashin hankali ƙarara a fuskarta. Bata iya ce masa komai ba ta fice daga ɗakin kamar wacce ta ruɗe. Tana fitowa hannun Teema kawai ta kama ta jata tana hawaye suka fice daga gurin. Teema na tambayar lafiya amman Rashida bata tsaya faɗa mata komai ba, ta shiga motar tayi mata key ganin hakan yasa Teema ta shiga gidan gaba, kamar za su tashi sama haka Rashida ta riƙa tuƙin motar suna ratsa dajin, har sai da Teema ta riƙa ta tana girgizawa, sannan ta dawo hayyacinta har ta rage gudun ta faka gefen titi tana kuka.
*ABDOOL POV.*
Satinsa biyu a kaduna, kusan kullum sai Amira ta tura masa saƙon barka da safiya da dare ma haka, sai dai har yanzu be taɓa mata reply ba, shi kan ba ma ita ce gabansa ba. Kusan kullum sai yayi waya da Ummi kamar yadda ya