Showing 36001 words to 39000 words out of 281103 words

Chapter 13 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61254

da sukayi maganar da Namra, Asim ya sanar mata a wayar Maryam cewa iyayensa zasu zo ganin Abbah ya saka musu rana. Ita kuma sai ta faɗawa Anty Amarya tayi masa magana, ya saka musu ranar lahadi.
Ranar lahadin na zuwa suka zo, Abbah yayi musu tarba daidai gwargwado, sai dai basu ga annurin fuskarsa ba ko kaɗan.
Dubu Hansi yayi musu sadakinta, yasa musu date 23 ga wata mai biwa wanda zai shigo, su kuma suka tafi akan sai sun yi shawara.


A Ranar Namra kuka tayi kamar zata mutu, sai dai bata yarda ta faɗa ma Anty Amarya ba, balle Maryam, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin ƙawarta Amira.
Sai da dare Asim ya kirata a wayar Maryam, a lokacin tana zaune falo sai ta tashi ta shige ɗakinta, sannan ta amsa wayar.


“Assalamu alaikum”


“Asim ya kake?”


“Lafiya ƙalau Dear, yau dai kin ga kamar mafarki an yanka min sadakin ki”


“Daman inda haƙuri ai komai mai faruwa ne”


“Haka ne Allah ya bani ikon biya”


“Ameen, amman Asim nace kana ganin zaman a can zai yiyu ko dai haya zamu kama”


“Haya kuma? Haba Namra ina naga kuɗin kama haya a yanzu, ni da nake tunanin sadakin ki da lefe kuma?”


“Ni zan biya kuɗin hayar, kuma zan taimaka maka da kuɗin da zaka haɗa lefe, amman Asim bana son kabar karatun ka”


Wani irin ajiyar zuciya ya sauke.


“Amman gaskiya Namra ba zan bari kiyi gaka ba, ni ban aure dan kiyi min haka ba”


“Ban maka hakan dan wani abun ba, sai dan nema maka mutunci da girma”


“Zan yi tunani a kai, amman gaskiya wannan shawarar bata yi ba”


“Kayi tunani Asim, matuƙat Abbah yaga inda zaka aje ni ba zai bari na aure ka ba”


“Allah yayi mana mafita”


“Amin”


Daga haka suka yi sallama. Sai ta tashi ta nufi falo dan mayarwa da Maryam wayarta. A lokacin ne Anty Amarya tace mata


“Namra wai ya maganar karatun ki? Kin san kwanan ki nawa baki je makaranta ba kuwa?”


Tsaye tayi cak kamar hoto tana kallon fuskar Anty Amarya.




A waje Asim yayi waya da Namra, ya daɗe a gurin zaune yana nazari sannan ya tashi ya shiga cikin gida. Aiko Mahaifiyarsa kamar jira take ta hau shi da masifa.


“Ai sai kaje ka samu kuɗin biyan sadakin kuma, dan babu wanda zai taimaka maka da komai, tun da kai kacw kaji ka gani”


Zaunawa yayi saman tabarma cike da damuwa.


“Haba Mama ai maimakon ki ƙarfafan gwuiwa sai kuma ki riƙa min faɗa?”


“Na ƙarfafa maka gwuiwa kaje ka aure wannan yarinyar? Ai ba da ni ba Wallahi, yarinya data gudu ta bi wani saurayi yayi mata abunda zai yi, mijin da zai aureta ma cewa yayi ya fasa sai aka ɗauko aka ƙaƙaba maka, kai kuma da kake sakare kace kaji ka gani, gudun jin kunyar mutane ko? Waya sani ma ko wani abun aka ganta da shi”


“Subhanallahi irin wannan kalaman sam basu kamata ba Mama”


Tsaki tayi ta tashi ta shige ɗakinta, tana cigaba da nanata maganar.
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


I dedicated this chapter to.
Angel
M Mimi
Mum Khady
Sarwee
Khady U Dome
Husaina daughter.
And all members of ZAGON K'ASA FAN'S grp. And KHADEEJA CANDY NOVELS 💖


I changed my phone so if your massage are still pending please PC me now.




NOT EDITED ⚠️




*PAGE - 18*


Kalsoom na fita tare da Salma, Rashida taja tsaki.


“Aifa an auro min iyani, ina ruwana da wata ƙawarki can”


Wayarta ta jawo ta danna ta nemu number Asmee ta danna mata kira.


“Ke ƴar gari ya akayi?”


“Toh gani nan dai, kin san yau ba'a zuwa aiki”


“Haka ne nima ina gida ai. Ina Amaryarki ance jiya an kawo miki amarya?”


“Tana nan yanzu ta fita raƙa ƙawarta”


“Hmm wai kisan yarinyar nan da taurin kai, babu irin zugar da da ban mata ba amman Wallahi ta tsaya kai da fata ita sai ta aure shi”


“Ai dole ta aure shi mana, babu mace da zata ga Hilal bata so shi ba balle har shi da kan sa yace yana son ta, kuma ance fa kwantai tayi babu mijin aure ba dole ta laƙe masa ba”


“Aiko dai ce ni na faɗa miki gurin aikin mu ɗaya da ita Wallahi, ƙanenta duk sun yi aure ita tana nan, Allah ya agaje ki dai kar tace zata fitar dake a gidan”


“Idan kuma bata fitar da ni ba ta karɓe min gida ba, dan naga yana ta wani rawar kai akanta”


“Ke ma ai kin sani duk mace data daɗe bata yi aure ba idan zata shiga a gidan ai sai ta shirya, kuma irin su ne suke ƙwace maza su tiyar da matar gida”


“Shiyasa fa nake tsoron auren nan na zamani”


“To ai laifin ki ne Rashida, shi kenan dan kana aiki sai miji yaje ya ɗauko maka wata banza da hujjar wai baka bashi lokacin ka! Ai wannan zancen banza ne, ni ɓa gani ina aikin ba amman mijina shiru kake ji ko ƙorafi bayayi”


Rashida tayi dariya tana mire baki


“Asmee kenan ke ai mijin ki be isa yace ze ƙara aure ba, wanda ko kallo mata ba yayi. Ke nima fa da nake matar abokinsa, sai da wani ƙwaƙƙwaran dalili yake min magana balle kuma har ya shiga office ɗina”


Asmee tayi dariyar jindaɗi, daman haka take son ji, kuma Rashida ta kan yawaita faɗa mata mijinta babu ruwanshi da mata, kasancewar gurin su ɗaya da Rashida.


“Kema ai idan kin tashi sai ki zo aka kama miki kan shi, wallahi ba dai wata ta gane kan gidan ki ba, dan kin san ba'a shedun Namiji anjima kaɗan zai canja miki, ballantana kin ga wannan Uwar tasa ba son ki take ba”


“Toh yanzu ya zamu yi kin san ai ba nida lokacin zama ma balle na fita”


“Ba ki da matsala da wannan, indai kin yarda kuɗin ki kawai zaki bada, ba sai kinje ba”


“Haka zai yi, amman ta san muna abota dake ?”


“Bata sani ba ai ban taɓa nuna mata ba, ce mata nayi mijinta ne abokin mijina kuma ni maƙociyarki ce, na nuna mata sam bana ma shiri dake”


“Hakan yayi kyau sai kiyi ta bugun cikinta”


Ƙyaƙyalewa Asmee tayi da dariya. Rashida tace


“Kin ga suna min warning wai kuɗina ya ƙare, ki shigo gobe ganin amaryar mu daman gobe monday bana gida”


“Toh Allah ya kai mu, na gode sai anjima”


Tana kashe wayar ta tashi ta nufi kitchen daɓ ɗora girkin rana.


DOC. HILAL POV


Tun da ya fita be dawo ba sai dare, da ledodi ya shigo gidan, sai da ya fara biyawa part ɗin Rashida ya kai mata nata, sannan ya shiga ɗakin Kalsoom. A bakin ƙofa ya tsaya ya ware mata hannyensa yana murmushi.


“Taso ki tarbe ni mana”


“Ka ƙaraso dai kawai tun da ka riga ka shigo”


Ta ƙarasa da murmushi tana mai sauke idonta daga gareshi. Ba dan yaso ba ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, ya aje ledar gefe ya jata jikinsa ya rumgume yana shinshinar ƙamshin turarenta yana wani lumshe ido.


“Wannan ƙamshin na nawa ne?”


Hannunsa ya saka mata a riga, unƙurin tashi tayi sai yayi saurin walƙatowa ya danne ta, a kunne ya raɗa mata.


“Kin fa san daren yau nawa ne, jiya ma dan nasan kin gaji ne shiyasa na ƙyale ki”


Dariya tayi, cikin dabara ta zame jikinta daga nashi ta tashi tana faɗin.


“Bari na haɗa maka ruwan wanka”


Kai kawai ya ɗaga mata ya bi bayanta da kallo a zuciyarsa yana ayyana lalai yau sai ya shiga gonarsa.
Fita tayi daga ɗakinta ta shiga ɗakinsa ta haɗa masa ruwan wanka, sannan ta fito ta dawo ɗakinta ta same shi still yadda ta bar shi.


“Ga ruwan can na haɗa maka”


Kwantawa yayi saman gadon, yana wani nuna jikinsa ya mutu.


“Ni da zaki taimaka min ki ɗauke ni ki kai ni bathroom ɗin kiyi min wanka da na gode Wallahi”


Dariya ta suɓuce mata, sai tayi ƙoƙarin rufe bakinta.


“Na ɗauke ka kuma?”


“Yes wannan ɗan jikin da kike gani ba wani nauyi da ni ba, kina ɗagawa zaki ji nayi sama suuuu”


Kai ta girgiza still tana murmushi.


“Baka tashi wanka ba, bari na ɗauko maka abinci”


“Wait...”


Sai ta tsaya, har ya taso ya ƙaraso kusa da ita ta yadda zasu iya shaƙar numfashin junansu, ya kama hannayenta, yana kallon tsakiyar idonta yace


“Kalsoom I love you with all my heart, ina fatar auren ki ya zame min alheri kuma farinciki”


“Inshallah”


Ta faɗa tana kawar da fuskarta daga kiss ɗin da yake ƙoƙarin aika mata.
Hancinsa ya goga saman nata yana murmushi mai sauti.


“Wannan kunyar ta ki tana burge ni My Queen, shi yake nuna min lallai ke mace ce”


Ya tsunsa yasa cikin nata, sai ta zame jikinta tana dariya.


“Ruwanka yana hucewa”


Cikin sauri ya janyota, ya walƙato da ita cikinsa, ya riƙe ƙugunta kanshi saman wuyanta, ya tura ta.


“Aya muje ki taya ni”


Ƙofar ɗakinta ta riƙe suka riƙa ja-in-ja, shi yana son ta bishi ɗakinshi, ita kuma tana jin kunya, taya zata iya taya shi wanka, daga kawo ta jiya-jiya. Ganin ta kafe masa yasa yace


“Kema kije kiyi wanka yanzu, or else na taya ki idan na fito”


“Nayi wanka fa tun ɗazu”


“Wannan be min ba, a sake wani”


Kai ta ɗaga masa. Sannan ya saketa ya nufi ɗakinsa.
Wanka yayi ya feshe jikinsa da turare ya saka kayan bachi, sannan ya fito falo ya kashe kayan kallo ya nufi ɗakinta.


Zaune ya tararda ita tana cin naman daya shigo da shigo dashi.


“Kai....!”


Ba shiri ta zabura tana masa kallon tsoro. Ya ƙarasa shiga ɗakin.


“Waya ce ki min nama?”


“Ba ni na siyo ma ba?”


“Dana kawo na aje cewa nayi gashi na siyo miki? Aiko dai yau sai kin biya ni”


Dariya tayi ta ƙara ɗaukar wata ciɓyar kazar ta kai baki.


“Anƙi a biya ka ɗin sai kace wani yaro”


Kusa da ita ya zauna ya buɗe mata bakinshi.


“Toh ɗan sammin na ci, amman fa sai kin biya ni gaskiya”


Ledar kazar ta tura masa, sai ya girgiza mata kai


“Na bakin ki zaki ba ni”


Sai tayi saurin haɗewa tana zare ido. Fuskar shanu yayi ya riƙa kunnenta ya murɗa har sai da tayi ƴar ƙara


“Oh ouch that hurt”


“To dan nace ki sammin shine zaki cinye?”


“Ɗauko min abinci ne na ci, ba zan ma ci kazar ba”


Bayan sun gama cin abincin, sukayi shirin kwanciya, sai ya rigata hawa saman gadon ya kwanta yana kallon yadda take ƙoƙarin canja kayan jikinta zuwa na bachi. Ita kuma duk ta tsargu ganin yadda ya sakar mata, tasan jira yake tayi kuskuren saki wani ɓangare na jikinta ta kallah, hakan yasa ta nufi bathroom, sai kawai ta ji an riƙe ta.


“Wallahi ba zaki je bathroom saboda canja kaya ba, ni dodon ki ne hala?”


“To ka sakar min ido kana ta kallo na”


“An kalle ki, ke ya kika yi kika ga ina kallon ki?”


Ta ɓata rai kamar zata masa kuka


“Haba Doc”


“Haba Mrs Doc”


Zata ƙara magana, ya saka mata yatsunsa biyu na dama cikin baki immediately ya soma wasa da halshenta, ɗayan hannunsa kuma a jikinta yana murza fatarta. Ba yadda ta iya daman tasan ƙarshen wasan kenan, a dole ta lumshe ido yana karɓar saƙwannin da yake aika mata.


Da haka yayi nasarar kwantar da ita saman gado, ya ƙarasa cire mata kayan, sai ga komai nata bayyane, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da haɗe yawun, ya shiga aikama mata da saƙwannin cikin salo na musamman. A take jikinta ya mutu sai dai duk abunda yake mata jikinta rawa yake abun ka da wace bata saba ba, daker ta iya buɗe idonta karaf ta sauke su cikin nasa, yadda taga launin idonsa ya riƙiɗe yasa gabanta faɗuwa, gashi kuma ta ganshi a yanayin da take ganin be kamata ta kalle shi a haka ba, sai tayi saurin maida idon nata ta kulle gam.
Hakan ya bashi damar riƙe kanta yana karanto addu'ar da Annabi ya koyar da mu kamin sexual intercourse.


“بِسْمِاللَّهِ، اللَّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْـتَنَا“


Bismillaah. Allaahumma jannibnash-Shaytaana, wa jannibish-Shaytaana maa razaqtanaa”




*** *** ***


Tun da asuba ya tashi ya haɗa ruwan wanka yayi sannan ya tashe ta, duk yadda yaso ya taimaka mata tayi wanka ƙin yarda tayi a dole ya ƙyaleta tayi da kanta sai zolayarta yake, wai jiya duk ta hajiyar da shi.
Ita kam kunyarsa ma take ji, ta gasa kanta sosai gurin wanka saboda yadda ƙasanta yake mata zafi da raɗaɗi, a tare suka yi sallah. Ita kam bata tsaya komai ba suna sallamewa ta hau gado sai bachi.
Bata farka ba sai tara har da tabi, a lokacin Hilal har ya gama haɗa musu breakfast dan yau Rashida da wuri ta fita ko gaisa bata bari suka yi ba, shi ya kai yara makaranta, sannan ya shigo ɗakin ya tashe ta.




NAMRA POV.


Ta daɗe a gurin tsaye tana tunanin abunda zata cewa Anty Amarya, ita kanta tana buƙatar karatun dan tana da yaƙinin zai taimaki rayuwarta, sai dai tana ganin hakan kamar ba me yiyu bane, tun da Asim yana nuna mata alamun baya son ta cigaba da karatun, gashi ma yace ba nan zasu zauna ba.


“Anty naga zan yi aure shiyasa na bar zancen karatu”


Duk kallonta suka yi suna mamakin irin sakarcin da take ƙoƙarin aikatawa.


“Namra kenan, ai karatu baya hana aure kuma aure baya hana karatu, karki yarda ki bar karatun ki”


“Anty yace ba a nan zamu zauna ba, a katsina zamu zauna”


“Katsina kuma?”


Maryam ta amsa, sai ta taso ta dawo kusa da Namta ta zauna.


“Dan Allah, karki yi haka Anty Namra taya zaki bishi zuwa katsina? Kibar karatun ki? Idan shi be san darajar nashi karatun ba ke ya kamata ace kin san naki, yanzu kina son ki zubar da duk shekarun da kikayi ki zubar da su?”


Anty Amarya ta riƙa hannunta.


“Namra karki yi ma kanki zaɓen tumun dare dan Allah, kar kije kiyi abunda zaki yi nadama”


Fashewa tayi da kuka


“Anty idan nace na zan aure shi zai ce naci amanarsa kuma kin ga yanzu har an yanka masa sadaki taya zan ce na fasa? Bayan kuma Abbah ya bani dama, baya da gurin aje ni a nan sai can, ɗan zuwan nan yayi ya samu aiki da zai iya taimakawa kansa da shi”


Anty Amarya ta dafe kanta tana sauke ajiyar zuciya. Zuwa can ta ɗago ta kalli Namra


“Ki masa magana idan ya aminta zan baku gidan da zaku zauna a nan garin, in yaso sai ku cigaba da karatun ku muga abunda Allah ze yi kuma”


Namra ta jidaɗin abunda Anty take ƙoƙarin mata, cikin murna ta share hawayenta tana mata godiya.


“Na gode sosai Anty, zan masa magana anjima inshallah”


“Ba komai Allah ya sanya alheri”


Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakinta. Sai da ta shige sannan Namra ta kalli Maryam tace


“Dan Allah Maryam ina son na nemi taimakon ki”


“Na me?”


“Abu nake son ki ara min dan Allah”


“Minene faɗa min mana, kina abu kamar mai jin kunya na”


Sai da ta sosa gefen wuyanta, cikin jin nauyi da kunya tace


“Kuɗi naƙe son ki ara min, zan yi wani abu ne, kuma kuɗin da yake account ɗina be wuce dubu ɗari takwas ba”


“Kamar nawa kike so?”


“Zan samu 1.5 million?”


“Zaki samu kan, ai kin san budurwar Sadiq ba za'a rasa kuɗi a account ɗin ta ba, kullum Sadiq samin kuɗi yake min Wallahi”


Namra ta harareta


“Dan kuma nace ki ara min kuɗi ai ban ce ki min gori ba, muma na mu lokacin yana zuwa ”


Dariya Maryam tayi ta kai ma Namra dudu a baya.


“Dole nayi miki dariya mana, duk manyan garin nan wasu-wasu ne kawai basu nemi aurenki ba, amman kika ƙi kula kowa ke sai Asim, Allah yasa dai ba auren jari zai yi dake ba”


“Dan Allah ki daina zargin Asim mana haba, ni dai kiyi min transfer kuɗin gobe”


Tashi tayi ta bar mata falon cikin jin zafin furucin Maryam.




*** *** ***


Sai da aka kwana biyu sannan Asim ya samu damar zuwa gurin Namra, duk kuwa da damuwarsa da take da waya, sai yace mata wai neman kuɗi yake.
Guraren takwas da rabi na dare ya shigo gidan, bata ɗauki lokaci ba ta fito cikin hijabi. Sai da suka gaisa sannan ta koro masa da bayanin da gidan da Anty Amarya tace zata basu su zauna.
A maimakon ta ga jindaɗi a fuskarsa sai kawai ta ga ya canja fuska kamar ransa be so ba.


“Har yanzu ƴan gidan ku basu yarda dani ba Namra, har yanzu basa son aure na dake, a tunani zaki iya zama a duk inda zan aje ki, kwata-kwata bana da ra'ayin zama garin nan, a can nake da sana'ah”


“Idan mun zauna a nan zamu iya cigaba da karatun mu, kuma a nan ɗin ma ba zaka rasa sana'ar yi ba”


Miƙewa yayi tsaye irin ya fusata ɗin nan sosai.


“Ba zan zauna a nan ba, Katsina nake son zama, idan kuma baki da ra'ayin aure na kawai ki faɗa min”


Ita miƙewa tayi tsaye tana girgiza masa kai


“Abun be kai ga haka ba Asim, magana ce ta fahimtar juna, bana nufin ƙin aurenka ko kaɗan a cikin rai na”


Takardar dake hannunta ta miƙa masa tare da zinarin da Abbah ya bata ranar da aka musu walima.


“Kaje ka cire wannan kuɗin miliyan biyu ne da dubu ɗari uku, nasan ze isa kayi komai, na mai ƙaramin ƙarfi, ba sai kayi lefe mai yawa ba kala ashirin ma ya isa amman kasa me ɗan tsada dan Allah”


Kawar da kai yayi yaƙi karɓar kuɗin.


“Ni bana buƙatar wannan kuɗin Namra”


“Idan baka amsa ba kana da wata mafitar ne? Wallahi ba zan faɗawa kowa kai na ba ba, dan Allah ka karɓa Asim”


Sai da tayi ta masa magajiya har da kukanta sannan ya karɓa. A fuska yake nuna mata baya son karɓa amman a ransa farinciki ne fess shi da be taɓa mallakar dubu ɗari biyar nasa na kansa ba yau gashi ta miƙa masa million


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login