Showing 48001 words to 51000 words out of 281103 words

Chapter 17 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61252

idan na kawo maka ƙuɗin gobe sai ka bani wayana, mijina ba lafiya kuma bani da kuɗin yanzu, amman nasan gobe Mamana zata zo”


Ba musu ya karɓi wayar, ya miƙawa ɗayan


“Duba mana wannan ba fake ba ce?”


Sai da ya duba gabanta da bayanta, ya ce ta cire mishi password ya duba komai, sannan suka bata maganin.


Tana fitowa cikin pharmacy ɗin, wani ƙaton mutum ya sha gabanta.


“Malama ana magana da ke a can”


Ya nuna mata wata shegiyar Mota mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali. Ɗauke kai tayi kamar bata ji shi ta cigaba da tafiyar tana kallon ti-ti ko zata samu Napep.


Jin tayi ana binta a baya, kuma ba takun mutum ɗaya ba, juyowar da zata yi sai ƙamshin wani daddaɗan turare ya daki hancinta.


Tsayawa tayi cak tana masa kallin jin dalilin binta da yake shi da bodyguards ɗinsa. Shi kuma ya tsaya a gurin yana mata wani kallo mai wuyar fassara.


Mashallah kyakkyawa ajin farko kuma ajin ƙarshen a kyau. Manyan idanuwansa, su suka fi komai kyau a halinta dake fuskarsa, manya ne sosai farin yayi fari, baƙin kuma kamar an shafa masa kwalli, hancinsa ya zauna a tsakiyar fuskarsa kamar anja masa layi, a ƙasan hancin an yanka masa wani hot lip pink color, shape ɗin fuskarsa mai faɗi kamar ƙirginsa. Robe ce a jikinsa mai kyau da ɗaukar hankali.


Ganin be ce mata komai ba, yasa ta juya da nufin cigaba da tafiyarta. Sai kawai yayi kuskuren kai hannunsa ya riƙa hijabinta, da nufin juwo da ita.


Tassssssss. Ta sauke masa lafiyayyen mari a fuska. Da sauri Bodyguards ɗinsa suka zaburo za su kai mata duka, sai yayi saurin ɗaga musu hannu.


“Baka da hankaline da zaka kai hannunka ka taɓa min Hijabi? An faɗa maka kowa wace mace ce ƴar iska? Kasan muhimmancin hijabi da zaka saka wulaƙantacen hannunka ka taɓa min Hijabi? Ni matar aure ce dan haka ka shiga hankalin ka”


Duk balbalin bala'in da take masa, kallonta yake fuskarsa da murmushi, har yanzu sanyin da laushin hannunta yake ji a gefen fuskarsa.


“Nima Mijin aure ne”


Ya faɗa lokacin daya ga tana ƙoƙarin juyawa. Awww Mashallah his voice was soft and sweet, such a nice voice irin ta larabawan nan masu ƙalƙala, wandanda baka gajiya da jin muryar su.


Wani dogon tsaki taja dai-dai lokacin data tsayar da mai Napep ta shiga tayi tafiyarta.
Har cikin ransa yake jin tsakin nata, yana yawo a ƙwaƙwalwarsa kamar wani blood.


“Abdul”


Da sauri wanda ya kira da Abdul ɗin ya matsa kusa dashi yana tsare masa.


“Sir”


“Rubuta Number Mai Napep ɗin can. 771A97K Funtua”


“Yes Sir”


Da sauri ya juya ta nufi gurin da suka yi parking ɗin motocinsu. Shi kam sai da ya daina hango Napep ɗin sannan hankalinsa ya dawo kansa.


‘For the first time in history wata mace ta ɗaga hannu ta mari Abdullah Ahmad Mai-doki’


A zuciyarsa yayi furucin yana mamakin kansa.


“Unique one”


Ya furta a fili. Sannan ya ce su zo da motocin ya shiga suka kama hanya.




Tana isa cikin asibitin ta kai ma likitan maganin yace ta bawa Nurse. Haka suka kwana a kansa ita da Mardiya, ko wanne ya shimfiɗa ɗankwalinsa ya kwanta. Sai dai Mardiya ce kawai tayi bachi Namra kam har safe idonta biyu.
Da safe ita ta bawa Mardiya kuɗi tta siyo abinci a ƙofar asibitin ta karya, ita kam jasa cin komai tayi har likita ya shigo.


Bayan ya gama duba shi ya sake sa masa drip, a cikin drip ɗin yayi masa alluran da aka siyo sannan ya miƙa mata wasu magungunan yace idan ya farka ta bashi.


“Amman likita har yanzu be buɗe ido ba”


“Zai buɗe yana da rai fa, kawai yaji jiki ne, mai yiyu juwa anjima ya buɗe idon, amman inda hali ku kai shi babbar asibitin Katsina dan akwai yiyuwar sai an masa aiki a ƙafarsa, saboda kashinsa na cinya ya shige ciki”


“Innalillahi wa'inna ilaihi”


Ta faɗa tana faɗuwa zaune saman kujerar roba dake gurin.


“Allah ya bashi lafiya”


Wucewa ya yi gurin wasu marar lafiyar ya barta tana aikin kuka. Likitan be yi minti talatin da barin gurin ba, Sai ga Mama ta iso da kukanta. Aiko hankalinta ya tashi sosai da taga yadda fuskar ɗanta ya kumbuɗe kamar an busashi, gaba ɗaya halittarsa ta canja.
Yadda take rusa kuka sai yasa hankalin duk wanda yake gurin ya koma kanta, ƙanwar Asim sai haƙuri take bata tana kuka.


Guraren shaɗaya da rabi Anty Amarya ta iso tare da direban su da Aisha. Namra na ganinta ta fashe ta sabon kuka ta kwantar da kanta jikin Anty Amarya.
Anty Amarya ta danne kukanta, tana lallasar Namra.


“Ki yi haƙuri, Namra ki kwantar da hankalin ki, duk abunda ya kamata ayi masa za'a masa kinji? Idan ma waje ya kamata a fitar da shi za'a fitar, amman ki kwantar da hankalin ki”


Karaf Mama ta tsuma baki, tana mai jin zafin yadda Anty Amarya take lallarsar Namra ita ga ɗanta kwance.


“Ta kwantar da hankali kamar yaya? Ga mijinta kwance ki ce ta kwantar da hankalinta, ta nata ma kike ba ta Ibrahim ba, daman ai nasan ba son ƙwarai kuke masa ba, ni wannan aure bai zo da komai ba sai abun baƙinciki, gashi nan daga shigowarki gidansa ya koma da ƙafa ɗaya”


Da kuka ta ƙarasa maganar. Kallonta kawai Anty Amarya tayi ta ɗauke kai, tana mai jin zafin kalamanta. Bata wani daɗe ba ta tashi ta fito harabar asibitin tare da Namra.


“Allah ya sauwaƙe Namra mu kan za mu koma”


Da sauri Namra ta kalleta


“Yanzu Anty?”


“Eh daman Abbah ki yace min kar na kwana, ƙara mu kama hanya yanzu kin san tafiyar dare bata da kyau, Maryam tace tana gaishe ki”


Nan da nan sai tasa kuka, a zatonta Anty Amarya zata kwana ne. Har suka ƙarasa gurin mota Namra kuka take, daker Anty Amarya ta lallaɓata tayi shiru.


“Anty ba mu da kuɗin biyan Hospital bill, kuma ba ni da ko naira yanzu a hannuna”


Ta faɗa tana ƙara share hawayenta.


“Ai ga mahaifiyarsa can sai ta biya masa”


Anty Amarya ta faɗa tana shirin zama cikin mota. Namra bata ƙara cewa koma, sai idonta dake zubar da ƙwallah.
Sai da Anty Amarya ta rufe motar ta zuƙe gilashin sannan ta ce.


“Zan miki transfer 100k Allah ya bashi lafiya”


“Amin na gode Allah ya kai ku lafiya”


A haka suka yi sallama. Namra ta bi motar tasu da kallo har suka bar asibitin.








____________________________________


Share it please.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa24.html




*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 24*


NOT EDITED ⚠️


Har Anty Amarya ta koma gida tana jin zafin kalaman da Mama ta yi a gabanta. Sai yanzu take jin zafin rashin mayar mata da magana da bata yi ba.


Bayan Sallah Magariba Hajiya Barau ta shigo ɗakin, tana tambayar Anty Amarya ya mai jikin, a lokacin Maryam da Hindatu har Aisha suna ɗaki suna maganar.


“Jiki da sauki sosai, yaji ciwo a ƙafa da hannu, sai gefen fuska”


“Toh Allah ya ƙara sauki ya tsare gaba, mu kam sai an kwana biyu sannan muje mu ganshi”


“Ai ba komai da sauki ma sosai, ƙaddarori ne kawai idan Allah ya kawo”


“Allah ya sauwaƙe ya ɗauke Wahala”


“Ameen”


Ta tashi ta nufi ƙofa tana faɗin


“Maryam ki zo ki karɓo dambu ɗazu Hajiya Hadiza ta aiko min da shi”


Tashi Aisha ta yi, ta bita suka fita tare. Maryam ta yi ƙwafa tana maimaita maganar ɗazu.


“Amman Wallahi matar nan bata da kirki sam, kuma ta ci sa'ah ba da ni aka je Wallahi da sai nayi mata tasss”


“Hmmm kin san wasu ba su iya yarda da ƙaddara ba, idan abu ya same su sai riƙa ganin kamar wani yayi musu ba Allah ba”


Cewar Anty Amarya, tana gyara zamanta. Hindatu tace


“Ni fa gani nake daman can kamar ba son auren take ba, shiyasa ma ya siye gida can su zauna”


Maryam ta ƙara tsire baki


“Ai mune ma ya dace muce haka ba su ba, dan yanzu na san ita za a bari ɗmda wahala, kuma wannan gidan ba siyen shi yayi ba, sai dai idan haya ya kama, idan ma siye yayi Wallahi Anty Namra ce ta bashi kuɗi, dan ta rance 1.5 million gare ni tace kar na faɗa”


Daga Anty Amarya har Hindatu da Aisha data shigo yanzu kallon Maryam suka yi da mamaki.


“Dan Allah da gaske?”


Hindatu ta amsa da ƙarfi. Maryam ta watsa mata harara


“Haka kawai zan ƙirƙiri ƙarya na faɗa, kuma nasan Wallahi shine ya zuga ta yace ta bashi wai kuma fa ta ƙara masa nata masu yawa, idan ba haka ba taya zai yi wannan lefen har ya samu gidan kai ta”


“Ko Motar nan waya sani ko sai dawa zasu yi ta bashi kuɗin, Wallahi Anty Namra bata da wayo sam”


Cewar Aisha tana ɗire wainar gaban Anty Amarya. Gaba ɗaya yanayin Anty Amarya ya canja, sai ta kawar da fuskarta wani gurin tana ƙoƙarin ɓoye damuwarta, babu abunda take tunani sai lamarin Namra.


NAMRA POV.


Asim be farka ba sai washe garin ranar da la'asar, har lokacin Namra bata sa komai a cikinta ba, dan bata jin yunwa ma a tare da ita.
Daker ya buɗe idonsa kumburarrin idonsa sai kuma ya mayar da sauri ya rufe, saboda zafin da yaji suna masa. Hannunsa ɗaya ta kama, idonta cike da ƙwalla.


“Sannu Asim”


Sai ta tashi da sauri taje ta kira likita. Abun ka da Nigeria sai da likitan ya kusan minti ashiri sannan ya iso tare da abun awonsa.
Sama-sama ya duba sa, ya kira sunan sa kusan sau uku, amman be amsa ba, sai motsa ido yake yana jin abunda yake ji.
Likitan ya kalli Namra yace


“Gaskiya bawan Allah nan yana buƙatar kulawar gaggawa, idan hali zan muku transfer zuwa babbar Asibitin Katsina dan ya samu kyakkyawar kulawa indai kuna buƙatar ransa”


A dai-dai lokacin ne Mama ta iso, sai kawai tasa kuka tana faɗin ta bani ta lalace. Nurse ɗin dake tare da Likitan ta katsa mata tsawa


“Haba Inna muna da wasu majiyanta fa, kukan ki zai iya takura musu”


Namra ta share hawayen idonta tana in'inna tace


“Likita a yi mana”


A take ya karɓi file ɗin dake hannun Nurse ɗin ya fiddo wata doguwar takarda, yayi rubuce-rubuce ya miƙa Nurse ɗin yana faɗin.


“Ki basu takardar biyan hospital bill kuma ki faɗa musu inda zasu je su biya”


Daga haka ya wuce, ya bar Nurse ɗin tana duba adadin abunda aka kashe musu, sai ta ware wata takardar ta daban ta rubuta mata kuɗin ta miƙa mata.


“Idan kin wuce pharmacy zaki ga gurin da ake biya, idan kin biya sai ki zo na baki transfer”


Daga haka ta wuce ta bar Namra da Mama tsaye suna hawaye. Zaunawa Mama tayi a kujerar roba da take gurin. Namra kuma ta fito ita da Mardiya tana duba jakarta.
Kwata-kwata kuɗin da yake ciki be wuce ɗari bakwai ba, saboda abincin data siya ma Mama da Mardiya da kuma ƙanwarsa.


“Amman yanzu kina da kuɗin biya kuwa”


Mardiya ta tambaya tana kallon yadda idon Namra ke zubar da ƙwalla.


“Muje ki raka ni na karɓo waya na”


Shine kawai abunda Namra ta faɗa, taja hannun Mardiya suka nufi gate. Napep suka tare suka shiga, ta sauke su dai-dai bakin pharmacy. Namra ta bashi ɗari biyu sannan suka shiga cikin Pharmacy.
Bata sha wahala gurin su gane ta ba, saboda kayan jiya ne a jikinta. Bayan sun gaisa tace


“Ka gane ni?”


“Eh ba kece ta jiya mai waya ba? Ana ta kiran wayar ta tun jiya”


“Dan Allah wayar zaka bani na kira”


“Tau kin zo da kuɗin ko?”


“A'a waya zan kira naji ko an turo”


“Toh sai dai idan nan a zakiyi kiran”


“Eh a nan zan yi”


Sai da suka yi kamar kar su bata sai kuma ɗayan ya ɗauko ya miƙa mata. Number Anty Amarya ta fara kira, daman ta ga missed call nata a calls list. Ringing biyu Anty Amarya ta ɗauka da sallama.


“Anty ina wuni ya hanya?”


“Alhamdulillah ya jikin Asim ɗin?”


“Ba sauƙi Anty yanzu haka likitan ya tura mu
zuwa babbar asibitin Katsina, kuma ba ni kuɗi”


“Allah ya sauwake, nima kuɗin da nace zan aiko miki ban samu ba, daman ina jiran Abbah ku ya bani kuɗin da nake binsa ne sai na aiko miki”


Wani irin abu Namra ta ji ya daki tsakiyar kanta zuwa cikin ƙafafunta. Ta san da gangan Anty Amarya tayi mata haka ba dan bata da kuɗin ba. Da na gode ta amsa mata ta kashe wayar, tana hawaye.


Number Maryam ta lalabo ta danna mata kira, tana yin pincking sai Namra tasa mata kuka.


“Maryam dan Allah taimako nake nema a gareki”


“Taimakon me?”


“Dan Allah kuɗi nake son ki ara min ko nawa ne dan Allah, Wallahi zan biya ki har da waɗancan ma”


“Anty Namra ban taɓa ara miki kuɗi dan ki biyani ba, duk abunda na baki a kyauta nake baki shi, gaskiya yanzu bana da kuɗi hannu na, amman ki tambayi Anty ba za'a rasa ba”


Namra bata ƙara cewa komai ba, sai kawai ta kashe wayar, ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Mardiya duk sai ta tsargu ta duƙa a gurin tana bata haƙuri.


Wata Hajiya dake kusa da ita ta kalle tana tambayar lafiya. Sai masu pharmacy suka mata bayani, cike da tausayawa ta kalli Namra tace


“Tashi Bawai Allah zan biya miki, Allah ya bashi lafiya”


Gyalenta Namra ta riƙa tana mata godiya.


“Allah ya saka miki da Alheri, na gode sosai”


Sai ta kalli Mutumen.


“Dan Allah ina ka san za'a iya siyen wayar nan?”


“Gaskiya sai kasuwar Ƴan wayoyi, dan wannan wayar mai tsada ce can ne kawai zasu iya siyen ta”


Yana faɗar hakan Mardiya ta zaro ido tana ƙara kallon wayar dake hannun Namra. Hajiyar ta kalleta.


“Haba ke kuwa kar ki siyar da wayar ki mana”


“Dole ne na siyar kuɗin asibiti zan biya”


Namra ta faɗa cikin kuka. Tun daga sama har ƙasa Hajiyar ta kalli Namra sannan tace


“Nawa ne kuɗin?”


“Dubu ashirin da shida da ɗari bakwai”


Hajiyar ta kalli yaron pharmacy


“Nawa ne kuɗin ka har nata?”


“Ya kama dubu takwas da ɗari huɗu”


Dubu tara ra ƙirgo ta miƙa masa, bata tsaya karɓar canja ba, ta kalli Namra.


“Muje cikin Mota na muga marar lafiyar”


Da sauri Namra ta fita ita da Mardiya, har suka riga Hajiyar isa gurin motar. Sai da ta buɗe ta shiga sannan ta buɗe musu tace su shigo.
Namra ce a front seat Mardiya a baya. Hajiyar tana yi tana satar kallon Namra. Ita kuma natsuwarta bata tare da ita, tambayar da take mata ma sama-sama take amsa mata.


“A nan garin kuke?”


“A'a Katsina nake zama, shine ma suka mana transfer zuwa can”


“Allah sarki wane unguwa a katsina, nima a katsina nake”


“Nasarawa”


Ta amsa mata dai'-dai lokacin data tayi parking, a harabar asibitin. Sai da taje ta duba Asim tayi ma mahaifiyarsa sannu ta suka je tare da Namra ta biya mata kuɗin Asibiti. Aiko Namra da dingi mata godiya kamar wanda tayi mata kyautar rai.


“Ba komai Wallahi, ai yi ma kai ne. Muje ki kai musu takardar su baki wacan sai muje katsina ɗin, dan nima yanzu can zan wuce”


Komawa suka yi, Namra taje ta kai ma Nurse ɗin takardar ta bata ta transfer ɗin, sannan ta dawo ta kawo ma Hajiyar. Ita ta ciri kuɗi a jakarta ta miƙawa Mardiya tace taje ta siyo masa shorts da ƴar riga a saka masa. Sannan taje ta biya dubu biyu aka basu ambulance, wanda za'a kai Asima ciki.


Mama da Hajaru (ƙanwar Asim) ne suka shiga ambulance ɗin tare da Asim. Namra da Mardiya kuma suka shiga motar Hajiyar, Tun kamin motar ta tashi Mardiya ta karɓi jakar Namra wai ta kawo ta riƙa mata. Ba musu Namra ta miƙa mata daman jakar ta yi mata nauyi.


Yadda take tuƙa motar kamar wata fitacciyar direba, dan da ita da ambulance ɗin ba zaka iya gane wanda yafi gudu ba.
Daf da Magariba suka isa Katsina, kai tsaye Babbar Asibitin suka suka wuce. Emergency Motar ta shiga Hajiyar na binta a baya. Suna shiga aka karɓe shi aka wuce da shi Anas room wato ɗakunan da aka tana na marar lafiya shi kaɗai dan bashi kulawa na musamman. Sai da Hajiyar ta biya dubu goma sha shida na ɗakin sannan aka aje shi, nan take suka soma bashi kulawar gaggawa abunka da babbar asibiti.


Godiya sosai Namra tayi ma mata har ta rasa yadda zata nuna mata jindaɗinta.


“Babu komai Allah ya bashi lafiya, ni yanzu zan wuce gida idan wani abun ya taso ki neme ni a wannan address ɗin”


Hajiyar ta faɗa tana murmushi tare da miƙa mata katin ta. Da hannu biyu Namra ta karɓa, ta raka ta har gurin motar ta, sannan ta dawo.


A Dai-dai lokacin ne likitan ya fito daga ɗakin da Asim yake ya nufo Mama yana magana da ita.


“Za'ayi masa gyara a cinyar ƙafarsa, sai kuje ku biya kuɗin, kuma za a siye masa jiki kamar na gora uku, kuje kuma ku biya kuɗin magani”


Ya ƙarasa faɗar yana miƙawa Mama takardun hannunsa guda uku. Da muguwar damuwa Mama ta karɓi takardar irin bani da madafa ɗin nan. Sai Namra tasa hannu ta karɓa, tana kallon likitan


“Idan ya kai gobe ba komai?”


“Ba matsala, amman dai ku ƙoƙarta kar ya wuce goben”


“Tau mun gode”


Bayan likitan ya wuce Namra ta shiga kwantar ma Mama hankali


“Mama ki shiga ki zauna da shi, ni zan je gida naga ko akwai abunda zan samo”


“Tau”


Ta faɗa da muryar kuka sannan ta shiga ɗaki. Namra ta juya ita da Mardiya suka nufi gida.


Mai Napep na sauke su Mardiya ta miƙawa Namra jakarta, ta nufi gidansu. Cikin kasalar jiki Namra ta buɗe ƙofar gate ɗin ta shiga. Ta daɗe a tsaye jikin ƙofar falon tana kuka, sannan ta buɗe ta shiga.


Wanka ne abunda ta fara yi, ta saka wasu tufafin sannan ta shiga kitchen ta ɗora indomie, a gaggauce ta dafa ta zuba a kula, ta haɗa ma kanta tea kaɗan ta sha, sannan ta dawo ta fito da tabarma da filo da bargo guda biyu, ta aje falo ta ɗauko plates huɗu da spoons da kofuna ta saka a basket, ta aje a falo. Duk abunda take Asim ne a ranta, tunani take inda zata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login